Showing 30001 words to 31306 words out of 31306 words
da bare
ma...domun ko biki ne akeyi kaman a yau aka daura auren Anwar da Shatu....Duk girman
harabar gidannan babu masaka tsinke yayan Hjy Yalwa na kasashe da garuruwa duk sun
hallara .
Don dole Anwar ya taho Bauchi badon yaso ba don damun hjy Yalwa da iyayen nahi da suka
taho....su Sadeeq kam baki yaki rufuwa yau suke ango...Sam Anwar yaki yarda yaje rugar
Surbajo acewan shi shufa batason karnin nono ne ,hakan yasa manyan shakikan Abokan sa
tafiya dan dauko Amarya Shatu ,haka wasu daga cikin dangi ciki har da Mama Rahamatu duk
sun nufi rugar Surbajo dauko amarya ,wasu kuma sun nufi Gidan Anwar na na barikin sojoji
inda xaaa sauke amaryan...
Tun da Su Hameeda suka isa barikin sojojin da shigar su gidan Anwar sukayi arba da Zabeena
dama kam ba shiri ne suke ba ,sosai Hameeda ta tsani Zabeena tun da tana zuwa gidan Hjy
Haula badon kowa ba sai don Anwar da nasu yazo daya ,ita kuma Hameeda yarinyar Hajiya
Rukayya ne ,wato kanwar mahaifin Anwar .
Harara suka hau aika mawa juna kamin su saki buda don suk cikar su kusan su bakwai
yammata ne ,su suka fara isowa barack din ,suna shewa hadi da fadin yau leutanant Anwar
lokaci yayi yau muke ango cewan Hameeda tana kara kama hamci hadi da rangada buda...
Sauran masuka hau shewa maasu budan nayi don sun fahimci Hameeda habaici takeyi .
Sum_sum cike da tukuki Zabeena ta wuce dakin da ta banbake ,niko maman teddy nace zan
gani ko zata fita takoma gidan uban ta yau ,don amarya dai ta zo gidan mijin ta sai ta bata
sararari su gurji amarci ...don na kosa naga yanda zaman tasu zai kaya tsakanin shatu da
Anwar .
Ganin ta shige daki yasa hameeda bin kowani daki tana shiga hadi da fitowa ... Wani
kayataccen daki ta gani da yafi kowanne kyau komai nashi golden da milk har funitures din
bedroom din haka yake...
Don dama ta amshe keys din dakunan a hannun Anwar tun kamin su taho...ganin kayan sa tayi
a dakin ,aiko nan ta kwashe su tass tana sakawa a dakin da yace mata na shatun ne ,Kayan
shatun kuma tana dawo dasu dakin anwar din .
*******
Bangaren Teemah kuwa tunda lbrn Auren Anwar yazo kunnen ta ta kwanta ciwo ,wanda batayi
karfi da jikin ta ba sai da tajiyo yai ne tarewan sa da matar sa ,da kuma jin ashe yar kauyen
bafullatana ya aura ,hakan ya sanyaya zuciyar ta ,tana cewa tabbas yanxu ne xasu fara takun
saka tsakanin ta da wannan gajar bafullatanan ,don ta lashi takobin auren Anwar koda da boka
ne da malam . Tirkashi...!!!
Bangaren kuwa Amarya shatu ,koda su Mama Rahamatu sukaje rugar sam basu hanasu yin
al'adar su ba ,komai nata har kwallaiya ta fulanin su sukayi mata cikin blue din saki ,mai ado da
jan zare ...sun rufa mata mayafin jikin sakin....sosai Shatu tayi kyau na kurewa ,dangi kam su
Mama rahamatu komai za ayi tana tare da Amarya a buka ,har aka kammala komai ,iyaye
sukayi mata nasiha sosaoi. A wannamn lokacin ne zuciyar umman shatun ya karye sai da ta
zubda kwallah sosao sannan tayi mata nasiha ,hadi da amsan lil Zahra da cewa sai ta kwana
biyu a dakin mijin ta zaa'a kawo mata .
Anan ne Shatu ta hau kuka badon komai ba don rabuwa da lil zahra koba komai tasaba da yar
nata sosai...duk da dama va ita take shayar da ita ba.
Umman ne mai kulawa da ita dama .
A hakan ne bakiya da masoya kowa na tafo albarkatun bakin sa ,aka shiga da amarya moto
wanda tun da take a tarihin rayuwar ta bata ta6a shiga ba ,taso tayi kauyanci amma babu bakin
yi don tana cikin damuwa..
A hakq moton su tafara tafiya don barin kauyen....koda akazo wuce rugar su Hardo hawayen ta
ne ya karu don sai da ta hango shi ya zabga tagumi da alama shima dana sani yakeyi...
Tana wannan tunanin ne taji an daki moton su da sanda fadi yake munafukai ina zaku kaimun
mata ku fito mun da shatu na...!!!
Allah da ikon sa a cikin moto cin har na angwayen babu wanda ya tsaya ,kuma abunka ga
wayayyun mutane koda suka fice daga rugar babu wanda yayi mgnan ko tambyar waye
wannan din?.
Itakam Shattu kuka takeyi sosai Hjy rahamatu tana rarrashin ta ,don duk maganan da hardo
yakeyi da fulatancu ta jiyo shi . Cewa yake bazai rabu da shatu ba ko ina taje sai ya biyota...Zai
iya komai akan Matar shi shifa bai saki Shatu ba hushin zuciya ce ta debeshi .....
Nikam nace aikin gama ai ya riga da yagama yanxu kam shatu ta jarumin sojan mu Anwar ne
ko ya kuke ce mosoyan shatu...?
******
Kamin bakwai na dare kowa ya watse yabar gidan Amaryan mu shatu sai Zabeena kadai da ta
kulle dakin ta ba asan ma da ita ciki ba.
Tana zaune tana tunanin abubuwan da zata dauka akan shatum ne tsawon lokaci har 9pm sai
taji motsin shigowar angwaye....
Mikewa tayi tana la6ewa don jin komai na abun da zasuce ,amma sai muryar Anwar taji a
miskilance yana fadin ,tom nagode zaku iya tafiya".
Hhhh kujimun dan rainin hankali ,bamuga amaryar bane kake sa ran tafiyaru ko yaya kai muke
jira ka fito mana da amarya mu ganta ! Cewan Ibrahim wanda sauran nan suka amsa da kwarai
kuwa ciki harda Sadeeq .
To kujira na fito maku da ita ,ni kunga ma tafiyata bedroom dina nayi ,yana fadin haka ya nufi
hanyar da zai sada shi da bedroom din shi kai tsaye...
Lallai wannan dan rainin hankali ne ma ,kazo ka amsa kazan amarcin cewan Sadeeq yana
dariya...banza ya musu yana shigewa ,yyn da Sadeeq din yace gashinan mun ajiye maka a
gaida amarya aji mana da ita sosao plz..dariya duka suka saka kamin su juya suna ficewa daga
falon .
Shikam Anwar Ranshi duk wani irin yakejin zuciyar shi ,yarasa meke damun shi ,a hankali
yafara tunano da sinfurin kalolun azabtarwan da yace zaiyi akan wannan yarinya yana cije
la66an sa hadi da lasansu yana girgixa kai...
Babban rigar sa yafara cirewa na danyar gexna milk kamin ya fara cire wristwatch na hannun
shi a saman mirrow ,mmki ne ya kamashi dago idon sa da yayi kwatsam yaga Shatu a saman
gadon shi an rufe mata fuska da mayafi da kayan ta na fulani...Bude idon shi yakara yana
mutsikasu yana mai fadin No ba itace ba ,kodai tunanin Azaban da zai mata ne yasa shi saboda
kosawa yake ganin hazo hazon ta haka ... Cike da rashin tsoro ya sauke hularsa yana nufar
gadon da cewa indai ko itace aka ajiyemun ita a bed sai naaaaaaaaa....................
Topah dama hausawa na cewa laifin dadi karewa gashi a yanxu labarin take yanxu xamu fara...
Anan na kawo karshen free page na wannan littafi ,idan kin ga wani page na yawo bayan
wannan tom na sata ne kar ki karanta kawai rintse idon ki ki wuce ,kar kuci hakki,babu abu mafi
muni da yakai mutum yaci hakkin da banasa ba...
_*Idan kina bukatar karanta cigaban labarin nan zaki iya mgn ta wannan number
08081202932....ta hanyar turo da kudin ki kaman haka Vip payment 500....Normal payment
200...Special payment 1k ,iya kudin ka iya shagalinkaí ½í²ƒí ½í²ƒ...zaku iya turo da katin MTN ko
kuma ku tura ta wannan account din Farida Hashim Stanbic bank 0028799846....sai ki turo mun
da shaidar biyanki ta wannan number 08081202932....yan niger zaku biya 500f ne kacal katin
airtel zaku na iya tuntu6an wannan number mutanen niger +22797780373*_
_Share and share and share fisabillah_
*Mmn teddyí ¾í·¸*