Showing 33001 words to 34804 words out of 34804 words

Chapter 12 - BAFULLATANAN RUGA BOOK 1 BY Maman Teddy .pdf

19 Oct 2025

820

*A.W.A*

*Kπuπgπiπyπaπ dπaπyπaπ tπaπmπkπaπrπ gπaπ dπuπbπ kπuπnπgπiπyπa mπaπsπuπ
aπkπiπ dπa iπlπiπmi*
```GADON BARCI```






Xaro Ido Waje Tayi tana mai fasa masa irin wani magigicin kara."
Wanda kafin yy yunkurin wani abu tuni ta hau fara kwararo masa amai kaman xata fitar da
yayan hanjin ta,cike da masifa ya dago yana mai shirin balbaleta da bala'in da yasaba,amma
kuma mene da bai gama bude baki ba yaga tayi luuuu ta fado jikin shi.

Cike da fada don bai kawo komai a ranshi ba ya hau cewa"kehhhh tashi mun a jiki ki tafi side
din ki,and then karki kuma kara xuwa inda nake kina jina?.

Ya fadi cike da dan daga murya".

Shirun ta da yaji ne yasa shi dago ta cikin 6acin rai wanda ganin idon ta a lumshe gashi bata ko
fitar da numfashi yasa shi dan girgixata yana mai kirar sunan ta,wanda tun da yake bai taba
kurar sunan ta yakai sau uku ba.

Ganin bata da alaman numfashi ya kuma bama tasan yana yi ba yasa shi saurin daukan wayan
shi ha'di da danna Number n likitan dake duba Anisa.

Nan ba abata lokaci ba doctorn ya dauka.
Ai kafin yace wani Abu tuni Adnan yafara cewa"plz ina bukatan ka yanxu.
Yana fadin haka ya datse wayan yana dan kara kirar sunan ta ha'di da tattabata ko xata mike
don gaba daya ya rasa sanin taimakon da zai mata by this time.

Nan cikin sauri ya nufi wadrop ha'di da fiddo mata da wasu kaya yaxo ya sanya mata,gaba daya
hankli n shi yagama tashi wanda shi kanshi bai san dalilin daga hankalin shi akan
BAFULLATANAN RUGA ba,wanda bai kaunar ta sam. Kuma ayo ko kashe ta yy ya kashe
banxa sai dai inkuma haduwan sa da mahalicci.
Cike da damuwa yake mata komai wanda after 10 munute sai yagi karar door bell.

Ai dajin haka cikin sauri Muhammad Adnan yanufi falon dakin nashi hadi da nufan midle falon
gidan,wanda anan ya hadu da doctorn.

Cikin damuwa yayi saurin nufan doctorn yana cewa ya shigo daga ciki ya duba mai matan na
shi.
Wanda kirar sunan mairo da yy da matan shi ya bai ma doctorn mmki don yasan komai tun
daga Auren Mairo da kuma komai dake tsakanin su da Anisa tunda da farko shi yake du
Anisan.

Da isan su bedroom din nashi yy saurin nufan ta ha'di da dorata jikin shi yana cewa doctor
come and asisst her plz.

Nufo su yy ha'di da fara fito da kayan aikin shi wanda da kai hannun shi xai taba jikin Mairo
yasa Muhammad saurin tare hannun shi yana cewa" yaza ayi ka taba mata jiki,bayan ita ba
maharraman ka ba.kawai inxaka taimaka mata kayi inbaxakayi ba katafi abuka.don baxan yarda
da wannan dabi'a takuba.
Ganin abun na Muhammad da gaske yakeyi baxai taba Mairo ba yasa shi fara bashi baki akan
yy hakuri suma ba ason ransu bane, yaxama masu dole ne hakan da kuma taimakon aluumma.

Da haka dai da kyar Muhammad Adnan ya yarda da magan ganun doctor sannan cike da
kwarewa ya hau fara bata taimakon gaggawa.

Wanda bayan yan mintoci dakuma yan bincike d yy ne ya kalli Muhammad Adnan yana cewa"
komai lfyl Amma inason ganin ka daga waje...

Sai a sannan Muhammad ya sauke wata irin sanyayyan ajiyar zuciya ha'di da shafan fuskan
Mairo wanda sam bai san lokacin da bakin shi ya furta mata sorrrrryyy dear ba.

Kwantar da ita yy akan bed sannan ya nufo falo inda ya tadda doctor a tsaye.

Cike da murmushi doctor ya mika ma Muhammad Adnan hannu bakin shi na ambaton congrat
Captain Adnan matan ka tana dauke da juna biyu na tsawon wata 1 kacal.

Cikin matsanancin farin ciki yayi saurin kara rike hannun doctor yana cewa" are u serious plz
doctor told me d trued.

Cike da tausayin shi likita yace" da gaske nake captain Muhammad wannan shine iya kacin
gskyn don haka plz karinga barin ta tana hutawa da bukatan ka,kadan ja mata baya na wasu
kwanaki saboda samun isashen lfyn babyn naku.

Gadiya yafara sambada ma doctor wanda nan yajuya don bai kuma kara bi ta kan doctor ba ya
nufi side din nashi.

Nufan ta yy yana mai zama gyefen ta yana kwantota jikin shi. Janye yar yaloluwar Rigar jikin ta
yy yana mai shafa cikin nata da yake a shafe da shi.

Surutai ya shiga yi wanda nan ya daga wayan shi ha'di da fara kokarin kirar numbern Ammie
wanda sam ya manta da ba Anisan bace ke dauke da juna biyun shi.da dagawan ta nan ya
hauyi mata albishir da Ammi kwanan nan xaki rike jikanki...

Cike da murna ha'di da farin ciki Ammiy tace Alhmdllh Muhammad yau Anisa ce xata haifo mun
jika kai mashallh.

Ai jin Ammiy ta ambato sunan Anisa yasa shi saurin datse wayan tasa,don sai a lokacin yasan
kalan shirmen da ya tabka.

Shiru yy yana mai tunanin wanda xai mawa wannan kyakykyawan Albishir wanda nan khamis
ya fado masa arai.
Cikin hanxari yafara dirlling Number n shi wanda kira daya biyu ya daga yana mai tsokanan da
yasaba Ango Awajen Anisa Ango mai mata kyawawa yarinya danya kuma da matashiya ango
na wajen Bafullatan Ruga.
Ya akai mutumin kwana biyu ka buya kodai Mairo ce ta hanaka fitowa.
Sai da yagama xubo surutun shi sannan Adnan ya nisa yana murmushi yace" khamis Maryam
tana dauke da juna biyu fah.

Cike da taya aminin nashi murna ya hau hamdalah ha'di da cigaba da masa shakiyan ci wanda
ganin haka yasa Muhammad Adnan kashe wayan yana mai cigaba da shafa ta ha'di da jin wani
iri game da lamarin nata,shiru yy a zuciyan shi yana jin anyah bai yaudari Anisa ba kuwa?.

Suna a tare fiye da shekaru amma wai ace har yy Aure da wata bata sani ba kuma wai har hata
da cikin shi.

Shiru yy tsawon a wanni yana tunanin mafita,amma yakasa samu wanda daga karshe ya nufi
toilet ha'di da doro alwala dayin sallan nafila don nuna gdyn shi ga Allah.

Yana a zaune kan sallaya yaga tafara alaman motsawa wanda ganin haka yasa shi saurin
nufan ta dai² tana tashi daga kwancen ganin shi da tayi yasata saka masa wani wahalallan kuka
tana cewa" don Allah hamma kayi hakuri wlh na tuba.
Ae bata gama rufe baki ba ya kai bakin shi ta hanyar hadewa da nata wanda kusan minti 5 suns
a haka sannan ya saki bakin nata yana dan bubbuga bayan ta ha'di da cemata is okay.

Dagota yy yana mai daga ta cakk yanufi toilet da ita yana cemata yake mata kidan watsa ma
jikin ki ruwan dumi babyn mu ta samu lfy taji dadi itama.

Shiru tayi game laafewa jikin shi don bata fahimtan abun da yake cewa sosai,musamman yanda
takejin jikin ta cikin wani irin kasala.

Haka ya cika baf da ruwan dumi yafara wanketa tsafff wanda sosai take mmkin shi da yake
mata hakan don bai taba ba.

Sai da yagama wanketa ne tsafff sannan shima yafara wanke kanshi wanda ganin haka yasa
tunda Mairo ta rufe ido bata kuma budewa ba sai da taji yana nadeta da towel.

A wannan rana sosai Mairo takeyin mmki yanda yake kula da ita koda kissing din ta xaiyi baya
mata na mugun ta kaman da.

Amma kuma abun da take mmki shine yawan bude mata riga da yakeyi yana kissing din cikin
ta,wanda a ranta take cewa yanzu kuma da wannan abun yadawo mata.

A haka tsawon kwana biyu kenan Muhammad Adnan bai kuma kara saduwa da ita ba.sai dai
kullum suna a manne don san bai son yaji tayi nisa da shi,aikin shi daya yy ta shafa cikin ta
yana surutan da bata fahimta don turanci yakeyi yy ta simbatan shafaffen cikin nata da ko
dagowa baiyi ba.
Bangaren Anisa kuwa kewan mijin nata ne ya isheta gashi kullum tace ya taho yagan ta sai
yace inyasamu free xai xo amma shiru takeji.

Don haka nan ta yanke shawarar ta howa nijeria.

Wanda da isan ta gidan ta na garin kaduna bayan ta huta ne take tmbayan masu aiki akan
yaushe Muhammad Adnan ke dawowa gidan.?.

Amma anan taji bama ya kwanan gidan yyn da suka ce a daya gidan shi yake kwana.

Cike da dan mmki takejin komai wanda cikin rashin yarda da abun da zuciya n ta ke saka mata
ta nufi gidan da yake can.

Da shigan ta gidan nan ms'aikatan suka fara gaisuwa yyn da cike da gadara ta tambayesu inda
boss din nasu yake.

Yyn da jiki na rawa sukayi mata nuni,wanda da tafiyan ta jikin ma'akatan yayi sanyi kalau don
sun san yau da balai lallai xa ayita ta kare.

Kwance take tayi luff a jikin shi wanda take sanye da kalan kayan da yace irin su yake so ta
ringa sakawa.wato kananun kaya wanda suka mai data kaman wata balarabiya don kyau.

Shikuma ogan yana abun da yasaba yi mata don sam baya gajiya da dora kan shi a dan saman
cikin nata yana shafawa da kuma kissing.

Muryan Anisa ce ta dawo dasu daga abun da yakeyi.
Cikin karaji Anisa tace" mai xangani Muhammad?wai shin da gske ne abun da ido na ke
ganemun ko gixo ne,Adnan wacece watannan who is she...!!!
Ta fadi cikin wani irin karaji,wanda sai da ya firgita Mairo da jikin ta nan ya hau kerma.

Cikin wani irin murya ya bude baki ha'di da cewa my Aneessss
Keep up ur mouth Adnan mai xaka cemun yaushe kafara niman mata bansani ehhh im asking
you...?

Ae gadan gadan ta iso gaban Mairo ha'di da wanketa da wani mahaukacin mari wanda yasa ta
fara ganin haxoxo don axaba ga cikin ta da yake wani kulle mata don marin bakaramun shigarta
yy ba.

Cikin sauri Muhammad Adnan ya.......







Toh far tirkashin kenan

Ko yaxata kasance oho ke dai cigaba da bin alkalaman Maman teddy don ta warware maki
komai tun daga farko har karshe labarin.✍



A wannan shafin free page yakare don haka game bukatar cigaban labarin xai turo katin MTN
ma wannan number 08081202932/09137392680.


Idan VIP ne xaki biya #200 VTU ma #200 NORMAL kuma #100 only.
Idan kuma ha'di da na sauraro ne Wato wanda xa'a karanta maki zaki biya #300.







*#PLZ SHERE TO ANOTHER GROUPS*








Maman teddy ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login