Showing 1 words to 3000 words out of 29267 words

Chapter 1 - Masarautarmu Book 3 Complete Hausa Novel By Sumayya Takori Kabara .pdf


MASARAUTAR MU!.





3








SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
babbangoro2015@yahoo.com

SADAUKARWA
Ga 'yar uwar da muka rasa a TAKORITES. Allah ya jikan ki da rahma HASNA'U yasa aljannah
ce makomar ki. Ya bamu guzurin tadda ke. Takorites bazamu taba mantawa da ke ba. Da
zaman amincin da muka yi tare.Muna son ki Hasna.


JINJINA
Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin
MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah
ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah.

GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga
radio, youtube, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin
tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali.

MASARAUTAR MU 3
Cikin raunin murya marar amo da rashin karsashi kamar ta wanda ya sha duka sabida yadda
tayi kasa sosai, Yarima Sageer ya duka gaban mahaifin sa Askirama tamkar zai shige cikin sa,
ya soma magana cikin sanyin murya da hardewar harshe.
Allah Kawun jo (Allah ya baka yawan rai) amma me ya sa tun lokacin da na dawo daga
Amsterdam din, na kuma zo da bukatar auren Sultana baa tambayi raayi na a kan Saadatun
ba? Allah ya ja da ran ku da a ce kun bayyana min kudirin ku akan mu tun farko, tun a wancan

lokacin, a kan zabin da ku ka yi min, zan hakura ne da nawa zabin duk son da nake masa in
karbi zabin ku. Saboda na san duk wani hukunci da za ku yi a kaina alkhairi ne wanda ni duk
yawan shekaru na ba zan taba iya hangowa kaina ba!!!.
Sai hawaye suka fito sharr! Daga idanun Yareema Sageer, wadanda a yanzu Askirama ya
tabbatar na farin-ciki ne ba na komai ba; hawayen wani irin contentment da Dr. Sageer bai taba
ji a rayuwarsa ba.
Sai ya ji rayuwarsa a yau ta cika, ta zama cikakkiya, duk wani gibi dake cikin ta ya cika,
amma a baya incomplete yake jin ta somehow shattered. duk da tarin dimbin achievements din
da ke cikin ta. kamar akwai wani wawakeken gurbi a can kasan zuciyar sa da a da can, yake
jira a cike, gurbin da bai san ko na menene, ko kuma na wanene ba, ya samu aka cike masashi
yau unexpectedly. A yanzu ya gane cewa ya jima yana jiran shigowar Sa’adatu cikin rayuwar
sa, he'spatiently waiting for her to come to his life ba tare da ya sani ba, sai a yau ya gane
hakan.
A can baya kafin zuwan wannan ranar jin sa yake tamkar bashi da komai tamkar bai taba
mallakar komai a rayuwar sa ba, duk da ba abinda bai mallaka din ba a rayuwar tasa including
ASIAN WIFE.
Amma a yanzu da yake durkushe gaban Mai Askira yana yi masa wannan bushara sai yaji
tamkar Askirama ya mallaka masa dukkan mulkin matan duniya, da mulkin dake cikin duniyar,
mulkin da ya fi na garin Askira girma da ilahirin El-Kanem Borno Empire, da duk wani nau'in
farin cikin dake cikin duniya da dan adam ke burin samu da ya mallaka masa Saadatu diyar
Bilkisu da Mallam Hashimu.

Na gode da wannan gatan Mai Askira, Nagode ZAKIN Askira, ina mai rokon Ubangiji da ya fi
ni godewa, na kuma karba da hannu bibbiyu. Ina rokon Allah Ya sa daga yau ba za ku sake jin
wani abu a kaina wanda ya jibinci laifuffukana na baya ba.
Hakika na sani Askirama ni Sageer mai yawan laifi ne, mai saba muku ne, mai ketare
tarbiyyar da kuka yi masa, amma hakan bai sa kun yi fushi da ni ba, kullum burin ku da fatan ku
shine in dawo hanya madaidaiciya, wanda hakan yasa a kullum nake cikin tuba da neman
gafarar Ubangiji. Ina rokon Allah ya fidda ni kunyar ku, Ya ba ni ikon rike muku yar ku da
amana.
A yi min godiya wurin Fulanin Sarki (yana nufin Fulani Bilkisu), kodayake bari in je in same ta
da kaina.
Askirama sai gani ya yi Yarima Sageer ya mike cikin wata irin azama, jikin sa har bari yake,
gabadaya ya zama ba cikin nutsuwar sa ba, ya rude saboda excitement din da ya samu kan sa
a ciki. Wanda Mai Askira zai iya rantsewa bai taba ganin sa cikin kwatankwacin irin wannan
farin-cikin ba. Sai Askirama ya mika hannu ya kamo hannun sa, kada ya je ya yi abun kunya a gaban bayi
da kuyangin Fulani Bilkisu, kuma dai Fulanin ta gaya masa Saade ta dau fushi tun jiya ta kulle
kanta a daki. Wanda ke nuna ita bata murna da auren ko kadan. Kamar yadda nasa dan ke
neman shidewa sabida farin-cikin hakan. Zo zauna in kirawo Fulanin ka yi mata godiyar nan a gabana, kada ka je sassan ta yanzu har
sai bayan biki. Baa zuwa. Zuwa lokacin Saadatu ta huce daga laifin da muka taru muka yi mata.
Yareema ya yi murmushi yana sosa kai, laifi? Auren sa ne ya zamo laifi ga Saade? Kodayake

bai kamata hakan ya zamo abin mamaki ba a gare shi duba da cewa daga shi har ita respect ne
a tsakanin su, babu wata magana bayan wannan, koda ace akwai din ita a gareta babu komai
tunda bai taba furta mata ba, ko nuna wata alama da zata gane cewa he sincerely admires her
tun farkon rayuwar ta a gidan sa. A lokacin suka hada ido da mahaifin sa wanda ya kura masa ido kawai yana murmushi, yana
karanto duk abinda yake son karanta. Yareema Sageer yayi hanzarin dawowa daga duniyar
tunanin da ya fada cikin jin nauyin kaifafan idanun Askirama. Kada dai ya zamanto cewa Mai
Askira ya gane a rude yake gabadayan sa? Kuma already a rijiya yake? A rayuwar shi babu
farin cikin da ya taba ruda shi irin na yau, kai mawuyaci ne wani abu yasa ya kasa mallakar kan
sa amma yau? Saadatu a matsayin matar sa! Wani al'amari ne da bai zata ba. It comes
abruptly. And it touches him more than he can imagine. Wani abu ne da bai taba kawowa zai
samu da sauki haka ba, duk da zuciyar sa ta dade tana buri, kwakwalwar sa na kiyasta masa,
ruhin sa na kwadayi da mafarkin kasancewar hakan.
Ba don bashi da gatan samun ta ba, sai don yana ganin hes not worth enough ga mallakar ta
matsayin mata, in yayi laakari da tarin aibubbukan sa.

Maimartaba ya kira Fulani ta wayar hannun sa, suka yi magana ya aje, ya dubi Yarima wanda
jikin sa ke ta (tsuma) ya kasa nutsuwa a waje daya, ya zama very upset, bai taba ganin dan sa
Sageer cikin kwatankwacin irin wannan halin ba.. daga haihuwar sa har girman sa. Wanda ke
nufin....(already Sageer na son Sa'adatu)!!!
Ba abin da ya furta a zuciyar sa sai godiya ga Ubangijin talikai, ya ce da Sageer a hankali
cikin muryar sa ta girma da sanyawa dan adam nutsuwa, yana murmushin kasaita irin nasa ta
kyakkyawan gashin bakin sa da farin gemu ya zagaye;

Be a Prince!". (Wato ya koma Yariman sa).
Yareema ya dafe goshin sa yana yar dariya da jerarrun hakoran sa bakidaya a waje, wannan
ma wani abu ne da Mai Askira bai taba gani ba, iyakacin sa murmushi ga duk abinda yayi
impressing din sa, sannan ya kuma koma cikakken Yariman sa ta hanyar kokarin sarrafa kan sa
da komawa cikin nutsuwar sa. Sai ga sallamar Sarauniya Fulani Bilkisun Askirama cikin kwalliyar ta ta kasaita, ta shigo ta
kofar da suka saba shigowa bangaren Askirama ita da sauran matan sa, kowacce akwai kofar
da ta bulla unguwar ta, zuwa turakan Mai Askira. Takun ta kadai abin kallo ne ga mijin ta.

Yarima na ganin shigowar ta ya dukar da kai kamar tsohon da ya yi wa sarki karya. Surukuta
sosai yake nunawa yau ga Bilkisu. Bai taba jin kunyar ta matsananciya ba irin yau. Kafin zuwan
wannan ranar, jin ta yake kamar Yayar sa Yaa Maira, ba matar mahaifin sa ba.
Alal hakika yana son matar nan ba tun yau ba, sau-tari, mantawa yake kishiyar Ya Gumsu ce
sabida kirkin ta, mantawa yake da duk wani sabani da ke tsakanin ta da mahaifiyar sa sabida
son da yake mata da kulawar da itama take bashi. Ashe Allah ya rubuta Kakar yayan sa ce
masu zuwa nan gaba cikin kudurar Ubangiji. Jinin su ne zai zo ya cakude wuri guda ya kara binding din su together. A can gaba. Ya kara
dunkule su matsayin iyalin Sarki Yusufu Mai Askira. Ya kara nutsuwa a wurin da yake

tankwashe zaman Rakuma akan kafafun sa, sannan ya gaishe ta da sassanyar murya, bayan
ta zauna kusa da Mai Askira tana zolayar sa.
Ango! Ango ka sha kamshi.
In ji Fulani cikin murmushi.
Maimartaba ya juya gare ta yana tambayar ta,
“Fulanin Askira Me ku ke shiryawa ne game da biki?
Fulani Bilkisu ta gyara zama,sannan ta kaskanta murya cikin yanayin ladabin da Askirama
kadai take yiwa magana da shi ta ce.
Alanguburo, ai ni rabon da in ga Saade tun jiya da na gaya mata. Ta shige daka ta kulle
kofarta, watakila idan ta ji mutanen Tsanyawa sun zo ta bude, kuma dai dama bukukuwan gidan
nan Ya Gumsu ce ta ke tsara su ga shi kuma tana fushi da ni a kan laifin da babu ruwa na.
Maimartaba ya ce, Zan turo Yaa Maira (babbar yarsa) ku tsara komai, Murjanatu ma tana kan
hanya za su zo su same ki. Wannan kiran kuma na Yarima ne ba nawa ba, shi yake son
ganinki, zai bi ki unguwarki na ce ya bari in kirawo ki nan, na ga yana ta bare-baren jiki kada ya
je ya yi abin kunya a gaban bayi. Dariya Fulani ta yi, shi kuma Yarima ya kara dukar da kai, murya a raunane ya ce.

Fulanin Maimartaba, Allah ya baki yawan rai, na gode. Allah ya jikan magabata, insha Allahu
ba zan ba ku kunya ba. Na karbi auren Saadatu da hannu bibbiyu. Allah ya ba ni ikon yin adalci
a tsakaninsu.
Sosai Fulani ta ji dadin kalaman Yarima Sageer, suka wanke damuwarta kaso hamsin cikin
dari na tunanin Yarimazai wulakanta mata Saade tunda yar talaka ce kuma yana da mata
Baturiya, damuwar hakanta ragu daga ranta, don ba ta zaci haka zai karbi maganar ba with due
respect, tunda uwar shi ma ba ta so. Ta ce, Da kai da Saade duk daya ne a wurina Yarima, kamar yadda Askirama bai taba bambantata
da ku yayan da ya haifa ba. Rokona daya gare ka Yarima ina so ka raba musu gida, sabida
Saade ba za ta iya zama waje daya da Aisha - Sultana ba, shekarun su, tunanin su, akidunsu
da halayyar su ba zai taba zuwa daya ba. Ka ga kuwa zama da juna zai musu wahala. Ya saci kallon Askirama ta kasan idanun sa,sabida tsoron ko ya ji abin da Baggarar matar
san nan ta ke fadi? Sai ya ga hankalin shi ba ya kan su sam, waya yake yi ma da yar sa Yaa
Maira lokacin, wadda ke aure a masarautar Biu. Tana gaya masa cewa sun taso suna hanya
har sun wuce Maiduguri. Wani sigh of relief Yarima ya sauke da ya fahimci Askirama bai ji ta ba. A ran sa fadi ya ke na
tabbata sanda aka yi miki aure da Baban Saade baki yi girman ta ba kuma kin haifeta lafiya. A
fili kuma ya ce,
Insha Allah zan nema mata nata muhallin, daya bukatar kuma zan duba insha Allahu ran ki
ya dade. Ai ba abinda zai gagara.
Da wannan ya yi musu sallama ya mike zai fita. Sai Askirama ya sake yafito shi.
Be a man also, after being a Prince (ka zama namiji bayan zama Yarima) wanda ba mai
iya juya raayin sa, wanda ya san cewa mata da karkataccen haqarqari aka halicce su tunanin
su ba kamar na maza bane, ka san yadda za ka lallaba mahaifiyarka har ta sauko daga dokin
fushinta, ta karbi Saadatu matsayin diyar ta, ta sanyawa auren ku albarka. Tashi ka je ku tsara
komai kai da Awaisu. Allah ya yi wa rayuwarku ku duka albarka.

*****

Yaa Maira ta iso daga masarautar Biu kamar yadda mahaifinta ya kira ta don ta zo su yi
shirye-shiryen bikin dan uwansu. Haka Murjanatu ta taso dagaIstanbul tun jiya ta sauka Abuja.
Zata biyo connecting flight zuwa Maiduguri yau.
Kamar yadda Maimartaba ya yi mata umarni cewa, idan ta iso kafin ta shiga koina ta fara
ganinsa tukunna. Yaa Maira, ta bi wannan umarnin na mahaifin ta, ta yi saa babu kowa tare da
Mai Askira lokacin da ta shiga falon ganawarsa da iyalinsa.
Ta same shi yana cin abinci. Ita dai ta ji an daura wa kanin ta Yareema aure, amma ba ta san
da wa Askirama ya daura ba. Yanzu da ta ke durkushe a gabansa suna magana ta Da da
mahaifi, bayan ya kare cin abincin sa sun gaisa, ta fahimci ko wace ce Maimartaba ya zaba wa
kanin ta Yareema Sageer. Ba kowa bace face Saadatun Fulani Bilkisu!!! Yaa Maira, wadda sunan ta na sarauta kenan, tana da wata baiwa ta daban kamar yadda na
fada a baya ta sunsunar kaddara. Tun ganinta da Saadatu na farko jikinta ya ba ta wannan
yarinyar will some day become part of them, za kuma ta zamo wani jigo a rayuwarsu. Zubin
halitta da komai nata na Fulani Bilkisu ne, Bilkisun da ke juya zuciyar Maimartaba a halin yanzu.
Bilkisun da babu tauraruwa mai hasken ta a idanun Mai Askira. Sai ba ta yi mamaki ba ko
kadan da wannan zabin na mahaifin su domin BAGGARA matan manya ne. Abu daya ta ke so
ta tantance yanzu shi ne hakikanin alakar dake tsakanin Bilkisu da Saadatu.
Mai Askira sai bai boye mata ba, ya gaya mata hakikanin alakar da ta hada Bilkisu da
Saadatu.

Yar ta ce ta cikin ta!

Mamaki, alajabi da tuajjibi kamar ya zauta Yaa Maira, kodayake dama ta dade tana kiyasta
hakan, kawai sai ta ji ta karbi Saade da dukkan zuciyar ta matsayin suruka. Duk da aibanta ta
da Humaira ke yi duk sanda suka taru bata taba fadin wani mugun hali a tare da ita ba, in ka
fahimci duka kushen Humaira akan Saade to kishi ne na son da Askirama ke mata da daidaita
musu matsayi da yake yi lokacin suna makaranta. Sai ko taya uwar ta Yaa Hibbani kishi da
Fulani Bilkisu. Sai kuma kyawun Saaden da take cewa irin na shegu ne.
Ita ta sani uwar Saade mai nagarta ce, cikin matan gidan kaf babu mai kirkin ta, saidai kishi
ya hana aga hakan a kare da fadin aibun ta. Maimartaba ya sa mata albarka domin ta ce ta
karbi amanar Saadatu a dakin su, ita ce uwardakinta daga yau, za kuma ta yi duk irin kokarin da
za ta iya wajen ganin cewa mahaifiyarsu (Ya Gumsu) ta sauko ta sanya wa alamarin albarka. Da wannan ta bar falon Askirama zuwa unguwar Ya Gumsu. Tana tafe tana saka irin lallashin
da zata yi mata.
*****

Yaa Gumsu ta yi mamakin ganin Yaa Maira a daidai wannan lokacin, don dai ita da kanta ba
ta gaya ko dayan su zancen auren Yarima da Saade ba saboda tsananin kiyayyarta ga auren.
Yaa Maira ta kwaso gabadaya yayanta maza da mata sun taho, kallo daya ta yi wa Ya Gumsu,
ta tabbatar da abin da Askirama ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login