Showing 24001 words to 27000 words out of 30109 words
Chapter 9 - Masarautarmu Book 1 Hausa Novels Compelet By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf
ya zo masa gida da ita ta shan sigari, kuma ba jimawa yayi fata-fata da ita, ya
cigaba da dora shi a hanya ta hanyar tsawatarwa da jan sa a jiki, yana nuna masa illar smoking
ga lafiyar sa ta dan adam. Wani abu da bai samu daga iyayen sa ba sabida kawaici na masu
sarauta ga 'ya'yan su. Gara ma Maimartaba akan Ya Gumsu wadda babu wani kusanci ko
kankani tsakanin ta da dan nata, bata san me yake ciki ba, bata taba bincikar halayyar sa ba, ita
dai burin ta ya kasance cikin gata ya samu duk abinda yake so, ya girma ya gaje sarauta.
Cikin dan lokaci kankani Amb. Hassan ya canza da yawa daga baragurbin halayen Sageer
sai abinda ba'a rasa ba. Shima Awaisu a nasa bangaren yana iya nasa kokarin wurin ganin
Sageer ya canza munanan dabi'un sa zuwa na cikakken dalibin da ya san ciwon kansa.
A karshe Awaisu ya fahimci wani abu, zai iya nasarar raba Sageer da komai, amma ba zai
iya raba shi da 'yammata ba.
Mahaukatan kudin da sarki ke turo masa don yayi hidimar karatu, da wadanda Amb. Ke basu
lokaci-lokaci duk a hidimar 'yammatan sa yake karar dasu. Yana kuma da masaniyar cewa yana
branching da 'yammata a hotel ba da sanin Amb. Hassan ba.
Al'amarin ya kara kazanta ne lokacin da aka yiwa Amb. Hassan sauyin kasa, daga Egypt
zuwa Amsterdam akan aikin jakadancin sa. Suka tattara suka bar Egypt suka koma can. Inda
suka fara karatun doctorate degree dinsu a fannin da kowanne yake a babbar jami'ar
Amsterdam. Awaisu na karantar (Social Work) yayinda Sageer ke karantar (Pure and Applied
Chemistry).
A duka wadannan shekarun bai kara ganin kowa nasa ba, wadanda aka haifa baya nan bai
san su ba. Haka wadda aka aura a bayan sa wato Fulani Bilkisu. Bayan su akwai kwarkwarori
da yawa. Sannan elder sisters dinsa biyu duk sunyi aure sun hayayyafa: Ya Maira da Mairam
Murjanatu. Bayan su an haifi maza biyar, biyu Ya Gumsu, uku Ya Kirjinoma, sannan Hibbani na
da Humaira da Najaatu. Bayan kammala M. Sc din su dukkan su sun samu aiki a kasar
Amsterdam, Awaisu aikin asibiti yake yi yayin da Yarima Sageer ke aiki da wani mashahurin
kamfanin sarrafa kayan abincin gongoni na kasar.
Tuni sun manta daga gidan sarauta suka fito, sun karbi rayuwar gidan Amb. Hassan wanda
bazaka taba sanin ba shi ya haife su ba. Rayuwar kasar Amstedam ta karbe su sosai, sun tara
arziki nasu na kansu, ga aiki ga muhalli ga ababen hawa. Amma duk da haka a gidan Amb.
Suke zaune. Tun barin sa gida sai a shekarar baya ne maimartaba da Ya Gumsu suka kai masa ziyara,
bisa tsananin rokon Amb. Hassan don maimartaba yace shi har abada Sageer bazai dawo
masa gida ba, ya barwa Amb. Hassan shi duniya da lahira sabida gamsuwa da irin rikon da
yake musu shi da Awaisu, shi kansa Waziri bai taba bada shawarar su dawo gida ba. Sai kuma ga abinda Ya Gumsu ta zo da shi yau, na nema masa alfarmar zuwa gida yayi ko
sati daya ne.
Ya sake lumshe idon sa ya bude a hankali. A fili ya furta "nima ina kewar ka Muhammad
Sageer, tsoron abinda zai je ya zo nake. Ina tattalin mutuncin ka a idon al'ummarka. Duk da
Baban ka ya tabbatar min baka da matsala yanzu".
****
A shawarar da suka yi da Waziri ya karfafe shi akan ya bar Yarima ya zo gida, koda sati
dayan ne, tunda dai bazai dawwama a kasar da ba tasa ba, dole watarana zai zo gida, sannan
Amb. Hassan ya tabbatar musu komai lafiya a tareda Yarima. Awaisu ne dai da yafi kowa
kusanci da shi ya ce da Babansa Waziri da saura. Wazirin kuma bai gayawa sarki hakan ba don
ya samu nutsuwar barin dan sa ya shiga cikin 'yan uwan sa ko yaya ne. A gefe ya saka limamin
Askira da sauran malaman fada yin addu'a ta musamman akan zuwan Yarima Sageer, Allah ya
kintsawa mahafin sa shi a matsayin sa na magajin sa.
Da wannan sarki ya yiwa Yarima umarnin zuwa gida don yayi sati daya. A wannan lokacin
Amb. Hassan ya gama tenure dinsa na aikin jakadanci yana shirin dawowa gida gabadaya, don
haka tare suka soma shirin tahowa shi da 'ya'yan nasa Sageer da Awaisu, inda Amb. Hassan
zai sauka a kasar shi ta haihuwa Kanon Dabo, kafun ya koma Birnin Tarayya da zama. *****
"Na ga sai wani zumudi kake zaka je gida, kamar wani special abu ne zamu je mu taras
banda zafin Maiduguri, ni banda Ya Gumsu ta dage sai naje ai har abada na bar Askira kenan,
tunda Alanguburo baya son gani na".
Awaisu yayi murmushi yana ninke kayan Yarima yana jera masa cikin tsadaddiyar trolley din
sa. Bai yi niyyar bashi amsa ba sai da ya ji Yarima ya sake yin kwafa, "ni ko satin ma bazan cika
ba zan dawo, ka san nextweek akwai birthday din da na hadawa (Rose), kawai sai jin zancen
tafiyar nan na yi, da na san da ita da tun satin da ya wuce mun yi mun gama, she will be 26 by
next week". (Rose, yarinyar Yarima ce da yake ji da ita, 'yar asalin kasar Korea ta kudu), Awaisu
ya tamke fuska kamar bai ji shi ba, ya cigaba da jera masa kaya. Daga baya kuma ya ce "ayya!
Ai kawai ka tafi da ita Askira ka hada mata birthday din acan zai fi bada ma'ana" Yarima yayi
miskilin murmushin sa, ya ce "me kake ci na baka na zuba? Ka zuba ido zuwa shekaru biyu zan
kaita Askiran ne, amma a matsayin matata ba budurwa ta ba".
Awaisu ya dauka ya fada ne kawai don ya ji dadin bakin sa, ya manta da wani hali na Yarima
Sageer Yusuf Askira, duk abinda ya furta yana nufin sa ne har zuciyar sa. Amma akan zancen
Rose bayahudiya bai taba kawowa Yarima da gaske aurenta yake da niyyar yi ba.
A halayen Yarima in ka dauke son matan sa, sauran duka ababen sha'awa ne, Awaisu ba zai
daina kiran sa (his role model) ba. Mutum ne mai muhimmanta sallah da kiyaye lokutanta, mai
kirki mai kyauta, abun hannun sa bai taba rufe mai ido ba. Ga jin kan na kasa da shi, ga
girmama iyaye, sannan ga kokari wajen neman na kai kamar ba dan sarki ba. Bayan kamfanin da yake yiwa aiki yana kasuwancin automobile daga Amurka zuwa
Amsterdam. Duk da haka maimartaba bai taba fasa turo masa kudi duk karshen wata ba, shi
Awaisun shine akan komai na kasuwancin nasa kuma kyautatawar da Yarima yake masa a ciki
sai ka rantse su biyu suka mallaki jarin kasuwancin. Babban abunda ke burge Awaisu a halayen Yarima Sageer shine submissiveness, ya san shi
mai laifi ne a gurin Ubangiji, amma yana yawan ce da Awaisu ya kasa dainawa, kuma yana so
ya daina din, mata sun zame masa barin rayuwa da baya iya rayuwa daidai sai tare da su, don
haka kullum cikin istigfari yake yana fadin yana rokon Allah yasa kada ya mutu yana aikata laifin
da yake aikatawa.
Ko Awaisu ya soma wa'azi, baya arguing da shi, cewa ya ke ya sani babu kyau ya taya shi
addu'a. Sai Awaisu ya koma yi masa yakin karkashin kasa, don kuwa yarima tausayi yake
bashi, kana sabo ka san kana yi amma ka ce ba zaka iya dainawa ba, duk yarinyar da ya gani
tare da shi zai bi ta bayan idon sa ya ci mutuncin ta ya razanata akan tarayya da Sageer, wani
zubin har ya ce Sageer nada cuta, ga turawa da shegen tsoro, saidai Sageer ya nemi yarinyar
sa sama ko kasa ya rasa, a karshe saidai ya nemo wata, shi kuma Awaisu baya gajiya da
lalatawa, kamar yadda shima baya gajiya da sake nemowa.
Wannan itace rayuwar Yarima Sageer da dan uwan sa Awaisu a kasar Amsterdam. Tamkar
ciki daya suka fito, sha'awar su akan komai daya ce ra'ayin su daya, sannan zuciyar su
tsayayya ce akan junan su, saidai hali kowa nasa daban.
Jirgin su ya sauka a filin jirgin saman Maiduguri da asubahin safiyar Litinin, zaratan matasan
suka soma saukowa daga matattakalar jirgin 'AZMAN' cikin shiga ta barebarin usli, wadanda
fatar jikin su ta jiku da boko da kasar sanyi, kai da ganin su ka san sun fito ne daga sarauta ta
ainahi ko daga irin takun su da kasaitar su. Suna sauka motar 'Askira Emirate' na jiran su. Tun a Abuja suka rabu da Amb. Hassan da
Mama Laila wadanda suka hau jirgin Kano, su kuma suka hawo na Maiduguri.
Dogarawa bila- adadin duk daga motocin masarautar Askira, suka bude musu kofar motar
BMW wadda maimartaba kadai ke hawan ta a gidan. Daga nan basu bata lokaci ba suka kama
hanyar Askira da motar civilian mai dauke da wasu fadawan cike fal a cikin ta.
Yau tun safe masarautar Askira ta tashi da bushe-bushen algaita da kalankuwa da goge irin
na masarautar, baka jin komai sai tashin kirarin gidan sarautar Askira, maroka da makada daga
kowane bangare na garin sun barko sun cika kofar fada, haka tun jiya 'ya'yan sarki maza da
mata na nesa dana kusa sun hallara a gida dakunan iyayen su mata ba don komai ba sai don
marabtar Yarima Sageer wanda ya kwashe shekaru goma baya cikin masarautar gabadaya.
Mairam Murjanatu ce kawai bata samu halarta ba saboda ta yi nisa tana kasar Turkiya.
Naja'atu da Humaira kusan sun fi kowa zaquwa da murnar ganin Yariman domin sune basu
san shi ba, suna kanana sosai ya tafi, sai kuma jikokin gidan wato 'ya'yan Ya Maira su wajen
takwas. Lokacin da motocin su suka iso fada, sai kade'kaden da bushe-bushen ya karu. Wani
abu ne da Sa'ade bata saba ji a cikin masarautar ba in ba wani muhimmin abu ake ba, kamar
nadin sarauta ko bikin aure. Duka-duka ma dai tun zuwan ta Askira bai fi sau biyu ta ji irin
wannan ba, don haka ta gane akwai muhimmin abin da ke faruwa yau a masarautar.
Tana so ta san me ake yi, amma ta rasa wanda zata tambaya, don Fulani ma tun safe tasa
aka shirya Zarah suka wuce babban falon ganawar sarki da iyalin sa, inda sauran iyalin gidan
suka hallara, ko ta kanta bata bi ba. Fanna ma dai ta lura yau dukkan su busy suke a cikin gida
da girke-girken da iyalin gidan zasu ci da wanda za'a tarbi Yarima Sageer da shi. Don haka itama tun safe bata sa ta a idanun ta ba.
Sa'ade duk ta zama curious ga son sanin me ake yi haka cikin gidan, a ranta tace yau dai
zata yiwa Fulani laifi sau daya, dole taje ta baiwa idon ta abinci, iyakaci Fulani in ta kamata ta
murde mata kunne ko ta mare ta.
Da wannan tunanin ta dau mayafin ta, sadaf-sadaf ta fita daga sassansu, a falon daya raba
sassan Fulani da inda sauran bayinta ke shige da fice ta ci karo da wasu duk suka zubo mata
ido, bata ko kallesu ba ta daga kafa ta fice daga unguwar Fulani Bilkisu.
Mayafin ta ta janyo ta rufe rabin fuskarta, idanun ta kawai ake gani. Ta rasa ina zata dosa?
Dan ba sanin kan gidan tayi ba, daga bisani ta lura da inda bayi ke karakaina da manyan
farantai, kanta tsaye ta doshi wajen.
Wani babban falo ne ta ga bayin suna shiga da sundukan abinci da katon katon na lemukan
gongoni, ta bi bayan su a hankali har zuwa kofar falon, sai ta zagaya ta bayan tangamemeiyar
tagar gilashi ta falon ta leka a hankali. Ba zata iya shaida fuskokin data gani ba don tagar ta
baya ce duk sun juya bayan su, ta dai hango Alanguburo akan kujerar mulkin sa, zagaye da shi
kananan yara maza da mata har da matasan 'yammata kamar ta, a gefensa daura da shi bisa
kujerar da bata kai tasa ado ba wani zankadeden matashi ne, duk da bata yi nasarar ganin
fuskar sa gabadaya ba ta ga gefen fuskarsa, da dogon karan hancin sa, kalar bakar fatar sa
kamar ta mutanen kasar Morocco, hular sa ta nitse a cikin tarin sumar kansa sannan fararen
kayan dake jikin sa babu ado irin na sarauta a jikin su. Normal tsadadden yadi ne (filtex London)
mai taushi a idon mai kallon sa, sauran mata da mazan dake zagaye dasu duk bata ganin
fuskar su, amma ta shaida bayan uwarta Fulani da kalar tufafin dake jikin ta kasancewar ta san
ta da kayan. Wata zuciyar ta ce "yi ta kanki Sa'ade, idan Fulani ta kama ki a gaban kowa sai ta
yi miki dan banzan duka. Tunda dai kin gani taro ne suke yi nasu su-ya-su (family get together)".
Wata kyakkyawar mata ta juyo tana magana da wata dattijuwa, sai ta gane fuskar ta, tana
daga cikin wadanda suka je wa Humaira visiting har suka kira ta (Ya Maira). Salin-alin ta soma
ja da baya, sawun ta a likkafa, sannan ta juya da sassarfa akan kafafun ta ta koma inda ta fito.
Ko ba komai ta ba idon ta hakkin sa. Da Fanna ta fara cin karo ta saka bayin dake sassan a gaba tana ta yi musu fada don me
suka barta ta fita, sai gata ta shigo kamar an koro ta, da sauri Fanna ta doshe ta tana hamdala.
"Daga ina kike Sa'adatu?" "Kai Fanna, sai kace wata karamar yarinya zan bata a cikin gidannan
ne da wayo na da idanuna da komai?" "Ba cewa na yi zaki bata ba ranki ya dade, inda Fulani ta
shigo ta nemeki bata gan ki ba me kike so mu ce mata?" Sa'ade ta murguda baki tayi shigewar
ta ciki tana kunkuni.
"Haka kawai ayi ta kulle mutum a daki sai ka ce wani daddawa, su suna can suna jin dadin su
cikin jama'a, bata so a ganni don me ta haifo ni?"
Wunin ranar zungur bata ga Fulani ba, sai washegari da safe ta fito don ta gaisheta kamar
yadda ta saba duk safiya in dai tana garin, ta same ta ta hargitsa bayi suna ta gyare-gyare a
sassan wai Yarima zai shigo ganin Zarah, yau zai shiga kowanne sassa na gidan. Sama-sama
Fulani ta amsa gaisuwar ta sannan ta cigaba da bada umarni, ta juya cikin jin haushi, ta tsani
wannan rashin bata muhimmancin da Fulani take yi amma ba yadda zata yi.
Bakon da ake ta shirye-shiryen domin sa bai shigo sassan nasu ba sai bayan sallar la'asar.
Tana jin wani irin kirari yana tashi daga bakin bayi (Gyara kimtsi da kyau... Lafiya dan zakin
duniya. Lafiya dan malafar duniya. Lafiya dan mai fada da cikawa. Lafiya dan masha-sha.
Lafiyar ka dama da hauni mai nasara. Zauna dai-dai dan bawan Allah. Zauna dai-dai dan
waliyin Allah. Aminchinka rike linzamin ka dan bawan Allah....zauna dai-dai dan masu Alheri...)
daga bisani ta ji muryoyin mutane da alama ba shi kadai bane, mazane sun kai su biyar, bayan
Yarima Sageer akwai Awaisun sa, kannen sa maza su hudu tareda Ashgar duk da ba lafiya ce
da shi ba hannun sa na cikin na Yarima kamar zai maida shi cikin sa. Tana so ta yi leke tana
tsoron Fulani, sai ta zo bakin kofar dakin ta ta kasa kunne ita a dole sai taji me ake yi kuma su
wanene? Lol.
"Yarima in a hanya na ganka ai bazan taba gane ka ba, sabida a hoto kawai nake ganin ku
wajen Askirama, gara kai kana nan a bakin ka, amma Awaisu ya koma bature sak!" Inji Fulani.
Awaisu yayi murmushi ya ce "duk da haka gara ni ban manta Kanuri ba, amma wannan ko
Hausa da kyar yake yin ta, su sanya alkyabba kuwa tuni ya manta yadda ake yin su balle yadda
zai wara kafafu ya hau doki". Yarima ya harareshi a lokaci guda yana jijjiga Zarah dake hannun
sa, wadda tun ganin sa da ita jiya Allah ya sanya matsananciyar kaunar ta a zuciyar sa
musamman da ya ji cewa sikila ce, yayi kissing kumatun ta yace. "Ranki ya dade da fatan zaki bani Zarah in tafi da ita Amsterdam in kin yaye ta in sa ta a
makaranta?" Fulani ta ce "in ka yi aure ba? Kuma matar 'yar gida ka aura wadda bazata ji
kyashin rike maka diyar ba" Awaisu ya fashe da dariya da ya tuna wadda Yarima yake shirin
aure, dan kuikuiwo ne pet din ta dake biye da ita duk inda zata, ya ga yadda zata rike dan
mutum sukutum ko sallah bata yi.
Ta kasan ido Yarima ke kallon sa, shi kadai ya gane me yake nufi da kallon da yayi masan,
don haka ya ja bakin sa yayi shiru yana cigaba da dariya. Yarima ya dago manyan idanun sa
farare kal, ya sauke su a kan maridin dan uwan sa wato Ashgar, ya ce.
"Ashgar, ina labari?" Murmushi Ashgar