Showing 18001 words to 21000 words out of 30109 words

Chapter 7 - Masarautarmu Book 1 Hausa Novels Compelet By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf

da bata da tension din Humairah, kowa son ta yake a dakin su, kowa so yake
ace shi abokin ta ne. Ga hannun ta a bude, kyauta gare ta kamar 'yar siyasa. Kwakwalwar ta ta
bude a lokaci daya kamar kiftawar ido, take grasping ilmi na kowanne bangare wanda nan da
nan ya kara canza ta. Dama Alanguburo ya ce mata tunda ta kayar da mutum daya, to nan gaba zata kayar da
goma ne, to ba goman kadai ta kayar ba talatin ta kayar, ita ce ta dauki na goma a ajin su,
Raheema ta dauki na farko.
Don haka da karfin gwiwarta ta dawo gida wannan hutun. Amma har ta kwana ta wuni, bata
ga Fulani ba haka bata ji shigowar Alanguburo sassan su ba. Ta gaji da kallon kofar dakin
Fulani ta tambayi Fanna, sai Fanna tayi murmushi ta ce.
"Fulani ta tafi kasar India zata haihu".
Ta rasa a wane yanayi ta karbi zancen, haihuwa? Daman ciki gare ta? Tana farin ciki da jin
zata samu karin mutum a kusa da ita, amma wani gefen na zuciyarta yana kishi. Idan ta tuno
dama fa Fulani ba wai tana son ta bane, inaga ta samu dan kanta da ta haifa a gidan sarauta?

Ai wulakanci gareta zai koma mode activated.
Ta kyabe baki tareda cewa "Allah ya sauke ta lafiya".
Hutun nasu dama ba mai yawa bane, na sati biyu ne, har sati biyun ta cika Fulani bata sauka
ba balle ta dawo, suka koma makaranta zuciyar ta cike da kewar ta, bata san tana son ta har
haka ba, sai yau da ta nemi ganin ko inuwar ta cikin gidan ta rasa. Shima Alanguburo Fanna
tace yayi tafiya zuwa kasar Amsterdam (Neitherlands) shi da Ya Gumsu kaiwa babban dan Ya
Gumsu dake karatu a can ziyara.
Rayuwa ta mikawa Sa'adatu Hashim a makarantar EL-KANEMI da budi da nasara da cigaba
ta kowanne bangare. Wani sihirtaccen kyau ke bayyanarwa Sa'adatu wadda zuwa yanzu
Sa'ade ya bace bat da taimakon Raheema, dama itace in an tambayeta sunanta sai ta ce
Sa'ade Hashimu, bayan ba haka yake a rubuce a rijista ba. Raheema ta tsaya tsayin daka
wajen tabbatar da ta mantar da ita rayuwar ta ta kauye, ta yi adopting rayuwa mai cike da
cigaba, wayewa da aji daidai na shekarun su, kaunar su da juna abin akwai sha'awa da
burgewa a ciki.
Ranar wani visiting ne Raheema ta kira ta don ta gaisa da 'yan gidan su, fuska fal far'a take
gaida Abban Raheema da mamanta, Bakin Babarbare mai zanen bare-bari akan fuskar shi ya
sha manyan kaya na kamala, bayan sun gaisa ya sa musu albarka sai ya kasa dauke ido akan
Sa'ade yana tunanin inda ya san wannan fuskar. Tabbas ya san fuskar amma ya rasa ta inda ya
santan. Yana ta kokari ya tuna amma ya kasa. Har Sa'ade ta yi musu sallama ta koma cikin
dalibai 'yan uwan ta.
Su dama ba'a zuwa musu visiting daga ita har Humairah, aiken kayan abinci kawai ake musu
daga gida a kowanne visiting. Amma yau tana tsaye cikin daliban da ba'a zo musu ba ta hango
shigowar motar data bata mamaki, bakar 'Land Cruiser' ce mai tsayi dauke da rubutun 'Biu
Emirate'. Ba ta tafi wajen motar ba ta tsaya a inda take tana kallon su, don ta san ba wajen ta
aka zo ba sai dai ko Humairah.
Wasu hamshaqan 'young ladies' ke fitowa daga motar tare da kyawawan 'ya'yan su kanana
maza da mata, matan su hudu ne, daga inda take tsaye ta hango Humaira ta nufo su, duk jan
ajin ta yau sai da ta hada da gudu-gudu ta rungume babbar cikin su.

"Yaa Maira! Ashe da gaske zaku zo?"

Ya Maira itace babbar 'yar sarki Yusufu, sunan sarautar ta kenan 'YaMaira' a matsayin ta na
babbar 'ya. Sai mai bi mata a dakin Ya Kirjinoma wato Mairam Murjanatu, sai kanwar
Murjanatun Mairam Naja'atu 'yar Hibbani, wadda Humaira ke bi a haihuwa.
Ya Maira tana aure ne a masarautar Biu yayin da Murjanatu ke auren Ambasadan Najeriya a
Turkiya, ta zo ganin gida ne tareda 'ya'yan ta ta tadda Ya Maira ta zo daukar Naja'atu su zo wa
auta ziyara kamar yadda ta alqawarta mata, sai ta biyo su, don itama ta jima bata ga Humairan
ba. Wani kilishi mai taushi baiwar da suke tare ta shimfida musu, ta koma motar ta soma fiddo
sundukan abinci na alfarma da picnic coolers masu dauke da ababen sha masu sanyi. Nan
suka baje suna ta hira, kai bazaka ce 'ya'yan kishiyoyi bane sabida shaquwa da kaunar da ke
tsakanin su sabanin iyayen su da ke zaman kishin kwatar kai. Naja'atu ta juya idanun ta kan Humaira, "Hummy ina yarinyar da ake kawo ku tare ne 'yar

kalen dangin da kike cewa? Kin ji uwar rikon nata ta haihu ko?" Humaira tace "wai wannan 'yar
mutsiyatan nan, ni rabon da insa ta a idona tun ranar da muka dawo hutu, da yake an raba
mana daki". "Wace yarinya kuke magana ne? Menene kuma kalen dangi?" Inji Mairam
Murjanatu. (Mairam title ne na kowacce 'yar sarki). Humaira ta ce "yarinyar da Fulani Bilkisu ta
dauko riko, da fari cin uban ta nake yi as if na samu baiwa, sai kuma aka zo aka raba mana daki
aka barni da cizon yatsa".
Murjanatu tace "dadi na da ke Humaira baki da kirki, albarkacin zaman tare ai ko gaisawa kya
dinga yi da ita, ni na rasa inda kika dauko wannan fadin ran naki, na san dai ba daga Fulani
Hibbani ba haka ba daga Alanguburo ba". Dama can Murjanatu tafi kowa saukin kai cikin
'ya'yan sarki kai bazaka ce ita 'yar gidan bace. An raine su akan yiwa wanda ke sama da su
biyayya! Wannan ne ya sa Humaira ta kira wata junior din ta tace ta je ta zo mata da Sa'adatu
Hashim. Ya Maira bata ce musu komai ba. Sai dai itama tana son ganin 'yar da Fulani Bilkisu ke
rikon.
Suna tsaye itada wata 'yar ajin su Falmata wadda itama ba'azo mata ba, yarinyar da aka aiko
ta zo ta same su, tayi mata nuni da inda suke zaune tace "ki je in ji Princess Humaira".
Saida ta ji gabanta ya fadi don ita har ta manta da matsalar Humaira, tace da Falmata "ina
zuwa" sannan a hankali ta soma taku cikin nutsuwa zuwa inda suke zaune.
Tunda ta doso su taji gabanta na faduwa, duka fuskokin bata san su a gidan ba banda
Humaira amma ta gane iyalin Sarki ne. Haka suma suka zubo mata ido cikin tsananin mamaki a
fuskokin su, hatta gait (takun tafiyar ta) irin na Bilkisun Askirama ne. Is it possible dan kanwarka
yayi irin wannan kamar da kai har fiye da dan da za'a ce kai ka haifa? Har ta tsugunna ta soma gaishe su an rasa mai magana a cikin su, sai kallon ta suke with
astonishment, duk sun mata kwarjini irin na su na 'ya'yan Saraki ta kasa ko duban fuskokin su.
Ya Maira....ji tayi zuciyar ta na bugawa, tana da wata baiwa ta sunsunar kaddara. Haka kawai
jikin ta ya bata akwai wani babban al'amari da zai zo ya kasance tsakanin su da yarinyar nan
wanda bazata ce menene ko na menene ba.
So she became mute, kamar an dinke mata baki, ko gaisuwar Sa'ade bata iya ta amsa ba.
Murjanatu ce ta kawar da mamakin ta ta amsa mata gaisuwa, sannan ta ce Yaya karatu? Ina
fatan kina kokari? Kuma kina jin dadin makarantar taku?" Sa'ade tayi murmushin da ya fidda
beauty point a barin hagu tace "ina yi ranki ya dade, kuma ina jin dadin makaranta" tana ta
kallon yaransu cikin sha'awa kasancewar Allah ya sanya mata son yara kamar me, Murjanatu ta
nunawa baiwar da suke tare daya daga kulolin abincin da suka zo da su tace ta dauka ta bita da
shi har kofar hostel. Sa'ade tayi ta godiya, ba don yunwa take ji ba sai don karamcin Mairam
Murjanatu, a ranta tana fadin ashe akwai mai kirki irin Askirama cikin 'ya'yan sa, at the same
time tana ta karbar sakon harara mai zafi daga Humaira.
Har ta kule basu daina kallon bayan ta ba, Murja ta ce "Allah mai iko, dole Fulani Bilkisu ta
dauko yarinyar nan daga cikin dangin ta, ku dubi kama don Allah har zuba take" Humaira ta
kyabe baki ta ce "Ya Murja yanzu ne ta kile fa, da in kin gan ta ko kin ji maganar ta ko kin ga
yadda take tafiya sai kin kusa yin amai. Kawaye take bi kamar mayya suna kilar da ita, banda
haka bazaki so ki ganta sanda aka kawo ta makarantar nan ba".
Murjanatu tace "to ai sun taimaketa, yanzu wannan yarinyar ina ne baza'a shiga da ita ba ko
wanene ba za'a iya aurawa ba? Kin ce Alanguburo na son ta, ki zuba ido ki ga irin mijin da zai
zabo mata, kin san shi dai da so wa 'ya'yan sa da 'ya'yan rikon sa babban gida". Kishi ya kara

turnike Humaira tace "insha Allahu tsohon hakimi zai bata gidan kishiyoyi goma taci uban ta".
Ya Maira tace "ka so wa dan uwanka abinda kake so wa kan ka".
Haka suka maida Sa'ade da uwar ta topic of discussion har lokacin tafiyar su. A cikin hirar
tasu naji Murjantu na gayawa Humaira Fulani Bilkisu ta haihu 'ya mace, amma bakwaini, 'yar
tana cikin incubator har yanzu acan kasar India basu dawo ba.
Ya Maira tace "dama Alanguburo ya daina asarar kudin sa, sunan wannan din ma matacciya,
wadanda ta haifa lafiya ma basu zauna ba balle bakwaini mai cutar sikila.
Raheema ta shigo da nata kabakin abincin, nan ta ga abincin alfarmar dake gaban Sa'adatu,
tace "yanzu dama 'yan gidanku sun zo shine baki kira ni ba?" Sa'ade ta girgiza kai "ba waje na
suka zo ba, ni ban san su bama, arzikin Humaira na ci suka bani wannan din". Nan suka zauna
suka soma dibar garar dadin su. Yau kam sun wuni cikin farin ciki marar misaltuwa. A haka zangon karatun ya kare, akayi hutu suka dawo gida.
Wannan karon ma bata tadda Fulani a gida ba, Fanna dai ta ce mata ta haihu, bata dawo
bane don 'yar bata isa haihuwa ba aka haifeta sai ta yi kwari tukunna a asibiti.
Ta kasance cike da farin cikin jin labarin haihuwar nan, ashe itama zata samu dan uwa a
duniya, wanda zata kira "kanin ta". Babban abun farin cikin ma diya mace. Sai dai damuwa ta
biyo bayan farin cikin da Fanna tace 'yar mawuyaci ne ta rayu. Sai ta ji tausayin Fulani, yadda ta
lura Alanguburo na son ta, sai take musu fatan samun rayayyen Da a tsakanin su. Da tayi sallah sai ta samu kanta da daga hannu tana addu'a. "Ya Allah ka raya abinda Fulani
ta haifa".
Haka tayi wannan hutun ma cikin kadaici da kewar Fulani, amma da yake yanzu ta auri
littafan ta sai komai ya zo mata da sauki.
Tana son karanta littafan hikaya na turanci, duk da turancin nata baida karfin fahimtar
kowacce kalma, sai take yi tana duba kamus na hausa da turanci, haka ta karbo su kala-kala
daga library ta taho dasu gida musamman na ZAYNAB ALKALI da ABUBAKAR GIMBA.
A wannan hutun saida Sa'ade ta maida kanta 'yar karamar Farfesa a Ingilishi sabida karatu
da duba dictionary. Kullum Fanna ta shigo kawo mata abinci abinda zata tarar tana yi kenan.
Har ce mata take "ki dinga ajiyewa kina hutawa kada kan ki yayi ciwo". Sai tace da Fanna "da
haka ne zan kayar da kowa Fanna, idan na iya turanci, idan ka iya shi kowanne darasi zai zo
maka da sauki". Fanna sai tace "to ALLAH ya bada sa'a".
Har suka koma makaranta Fulani bata dawo ba.
In ka lissafa zaka ga cewa watanni masu yawa kenan basu ga juna ba, wanda hakan ya
sanya matukar kewar junan su a zukatan su. Ga Fulani, ba damuwa tayi ta ganta ba don ta san
tana lafiya amma somehow tana jin kewar ta a can kasan zuciyar ta. Saidai hankalin ta ya
dauku ga son rayuwar abinda ta haifa wadda ke tsakanin rayuwa da mutuwa, don haka bata
cikin kwanciyar hankali ko kankani. Shi kam Alanguburo ya gama fidda rai da rayuwar yarinyar
kamar sauran wadanda suka gabata.
Amma bai fasa karfafawa Fulani gwiwa ba kan tayi hakuri ta barwa Allah ikon sa. Da sun
haihu ko basu haihu ba, soyayyar da yake yi mata bazata taba raguwa ba, sannan ba ga
Sa'adatu Allah ya basu ba?"
Bata cewa komai idan ya fadi hakan, amma a ranta cewa take "yar Hashimu ce ba tawa ba,
da sannu Allah zai bar min tawa".
A sannu kuma sai Allah ya soma baiwa 'yar koshin lafiya sabida tsananin kulawar data ke

samu daga likitoci da adduar uwa, tayi bul-bul kamar ba bakwaini ba, amma still sikila ce.
Sun dawo gida ranar wata Lahadi, sati biyu da komawar Sa'ade makaranta. Nan aka yi ta
shigowa Fulani barka kamar za'a tsaga sassanta don yawan al'umma, kishiyoyin ta dake jiran
gumbar sadaka dole suma suka yi lullubi suka zo barka don ganewa idon su abinda ta haifo ba
don barkar ta Allah da annabi bace, "yarinya kamar Murjanatu" inji Ya Kirjinoma cikin al'ajabi.
Hibbani tace "wannan dan gajeren hancin ai na Ya Maira ne, Murjanatu mai dogon hanci zaki
hada da wannan burtuntunar, ai komai nata na Ya Maira ne" Ya Kirjinoma tace "in zaki tsoraci
Allah, Murjanatu ce sak wannan". Fulani tayi murmushi bata ce komai ba, amma burtuntuna da
aka kira 'yar ta ya sosa mata rai. Ta san kadan da aikin Hibbani, in ta kwabo maka magana ko
zaka mutu ita babu ruwan ta.
Amma abin mamaki Ya Gumsu bata shigo ba, tana can bakin ciki na neman kashe ta, don
bata taba zaton 'yar zata rayu ba.
Haka 'ya'yan gidan maza da mata na nesa dana kusa suka yi ta tururuwar zuwa barka har
wajen kwanaki talatin mutane basu tsagaita ba. Daki guda sai da ya cika taf da kayan barka na
uwar dana 'yar mai suna "Zarah"
Cikin kuyangin Fulani aka warewa Zarah masu kula da ita su biyu, dattijuwa da budurwa,
dakin Zarah yana jikin na Fulani, yayin da na Sa'ade ke kallon nasu.
Suka cigaba da rainon ta cikin tsananin kulawa.
*****
Kayan su suke hadawa itada Raheema kasancewar gobe hutu, suna yi suna hira, Sa'adatu
tace "wannan hutun ina duban hanyar ki, na san daga Fulani har Alanguburo in suna gida,
baza'a hanaki shigowa ba".
"To Allah yasa Abba ya barni, ya ce min ma shi kallon sani yake miki" Sa'ade tayi dariya, "ba
dole yayimin kallon sani ba tunda nima 'yar sa ce?"
Haka suka yi ta hira har suka kammala hada duk abinda suke bukatar zuwa dashi gida.
****





Yarinyar dake tsaye yau a gaban ta wata siririyar budurwa ce, cikin shekaru na tashen balagar
diya mace. In bata manta ba tana kamar girman ta aka yi mata auren fari, auren dolen da ya
zamo silar zuwan ta duniya.
Tana tsaye daga bakin kofa sanye cikin uniform din ta na makarantar sakandire, kyakkyawar
fuskar ta kunshe da sassanyan murmushi, wanda kai tsaye ta fassara shi da murmushin farin
cikin abinda yarinyar ta shigo ta tarar tana yi (breastfeeding her baby).
Ta tako a hankali cikin tafiyar data banbanta da ta SA'ADEN da ta sani watannin baya, mai
tafiya tana hada hanya, wannan Sa'adatun a nitse take tafiya. Her gait, her serene smiles duka
suna kara tabbatar mata da cewa, ta fito ne daga cikin mahaifar ta kwatankwacin diyar dake
rungume a hannun ta a yanzu, wato Zarah. Banbancin dake a tsakani shine; wannan soyayyah ce ta kaita ga haifar ta, yayin da waccan
kiyayya ce silar nata zuwan duniya.

Ta yi nisa a wannan tunanin har bata san lokacin da Sa'ade ta karaso gareta ba, kokari take
ta karbi 'yar daga hannun ta wadda ta saki nono tana kallon Sa'aden da kyawawan idanun ta.
Sa'ade blushing ta ke from ear to ear, ta dauka Fulani zata hana ta daukar diyar ta, amma ga
madaukakin mamakin ta sai ta ga ta sakar mata. Ta dauki kanwar tata tana ta murmushi. "Beautiful!" Ta fada cike da kauna. Fulani ta cigaba
da bin ta da kallo ba tare da ta sani ba, duk wani kankanin canji dake tare da Sa'aden a
watannin data kwashe bata ganta ba saida ta zaqulo shi cikin idanun ta.
"Ashe kilewar diya mace ba wuya muddin zata je makaranta!" Fulani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login