Showing 3001 words to 6000 words out of 30109 words

Chapter 2 - Masarautarmu Book 1 Hausa Novels Compelet By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf

bisu amma Malam Sale
yace ta zauna a ranar zasu dawo. Har kwana uku basu dawo ba, a kwanakin nan uku Sa'ade ta gama karewa a tsaye, bata ci
bata sha. A rana ta hudu kuwa tana gindin murhu tana hurawa Laure wutar tuwo taji ana fadin.
"Ku shigo da shi daga ciki, a kawo tabarmi.......". Sai ihu da kururuwar Laure. Tana fadin
"Malam ashe sa'i ya yi? Ashe rabuwar kenan?"
Fitowar Sa'ade a guje daga madafi yayi dadidai da shimfide gawar da aka yi a tsakar gidan
su. Da gudu ta karasa ta bude fuskar ta tabbatar Baban ta ne..... Ya rasu! Tafiya ta har abada
wadda babu dawowa........ Ji kake yiff! Ta fada kan gawar a sume bata kara sanin inda kanta
yake ba. *****
Ta farfado ne ta ganta a gidan su Hanne, Hanne na kuka Innarta na mata firfita. A lokacin ne
abinda ya faru ya dawo cikin kwanyar ta. Ta rushe da kuka tana fadin "Hanne da gaske ne
Babana ya rasu?" Innar Hanne ta rungumota jikin ta tana ta lallashinta tare da bata kalamai
masu dadi. Sai da aka kwana bakwai Sa'ade bata daina kuka ba, kulawa da kauna ta duniya
babu wadda iyayen Hanne basu gwada mata ba don dai su samu ta kwantar da hankalin ta ta
karbi reality na rasuwar Malam Hashimu.
Washegarin sadakar bakwai malam Saleh Baban Hanne ya kirata dakin sa, ya ce ta je ta

kwaso kayanta gabadaya, ta kuma yi sallama da Laure ta dawo. Zai cika wasiyyar da marigayi
ya bar masa suna hanyar zuwa asibiti. Zai dangana ta da mahaifiyar ta hannu da hannu....

A razane Sa'ade ta dago ta dube shi manyan idanun ta kamar sa fado kasa. Ya gyada mata
kai da murmushi a fatar bakin sa ya ce "maza je ki ki dawo, daga yau zuwa gobe, zan sadaki
da Innar ki da ta haife ki".
****
Tunda suka iso tasha Sa'ade ke rarraba idanu, wannan ne karo na farko da zata fita daga
garin Tsanyawa tun tasowar ta. Ita da Hanne rabuwar su mai taba zuciya ce. Tunda suka taso
basu taba rabuwa na kwana biyu ba, kullum suna tare dare da rana, yau an ce Jihar Kano zata
bari bakidaya ba garin Tsanyawa kadai ba. Zuwa inda bata sani ba, bata taba mafarki ba. Zuwa
wajen uwar da bata sani ba, bata taba gani ba.
Ko mahaifiyar tata ya zata karbe ta? Ko zata bata matsayin 'ya? Duba da cewa bata taba
sanin ta ba? Sai yau a dalilin mutuwa.... mai tonon asiri!
Tunaninnikan da Sa'ade ke ta yi kenan a lokacin da suka bar garin Tsanyawa cikin motar
Rake Akori-Kura, suka hau titi dodar! Wanda zai sada su da birnin Kano. Hanyar garin ba
kwalta a wancan lokacin don haka kura ta turnike idanun su a bayan akori-kurar, sai rufe
fuskokin su suka yi da mayafan su. A tashar unguwa uku aka sauke su, inda direbobin suka ce yamma ta yi, zasu yi dare, su
nemi waje su kwana in ya so washegari su yi asubanci su samu motar farko.
A rumfar wata mai tuwo malam Saleh ya roka mata ta kwana, shi kuma ya kwana a
masallacin tashar. Da asubah suna idar da sallah sune pasinjan farko a fasinjojin da zasu tafi
garin MAIDUGURI....

*****

"Tafiya yankin azaba".

Sa'ade ta fada a zuciyar ta. Sabida yadda ta wahala a motar. Kafin su isa Maiduguri sai
yamma lis, duk sun yi wujiga-wujiga daga ita har Baba Saleh. Sau biyu yana saya mata gurasar
masu balangu da pure water tana ci a hanya. Shi kam bawan Allah bata tunanin ko loma daya
ya saka a bakin sa. Aka sauke su a tashar BAMA, anan ma a tashar suka kwana, da Asuba suka bi mass transiet
wadda zata tafi kai tsaye zuwa garin ASKIRA.
Sa'ade ba zata manta da garuruwan da suka wuce ba, saboda akwai wani mutum mai yawan
surutu a motar tasu, duk garin da aka zo sai ya fadi sunan sa, sun wuce Damboa, sannan suka
bulla ta Chibok, sannan Uba, a karshe sai garin da ta ji an kira ASKIRA.

(A wancan lokacin ba insurgency, garuruwan Borno lafiya kalau suke).

Sa'ade ta daga kai tana kallon garin Askira, garin da aka ce wai anan ne zata ga mahaifiyar
ta, wadda ta haife ta, anan take raye. Babban gari ne wanda ya samu cigaban zamani kala-kala
a yankin Borno. Koda aka sauke su a tasha tana ji Baba Saleh na tambayar ta ina zai bi ya je

gidan Sarki?
Sa'ade ta tambayi kanta.
Me ya hada mahaifiyar tata da gidan sarki?
Bata samu mai bata amsa ba.
Da tambaya da kwatance aka kawo su har kofar tankareriyar masarautar Askira.
*****

















ASKIRA EMIRATE
Gidan sarkin Askira koko in ce masarutar Askira babban gini ne a tsakiyar gari, a unguwar da
ake kira "unguwar gabas". Tafkeken gida ne mai ginin sama da kasa. Dogarawa ne tun daga
zauren farko har zuwa ciki rukuni-rukuni, wasu a zazzaune wasu a tsaitsaye. Daga soron farko
za'a cire takalmi duk mai shiga gidan mace ko namiji, ginin farko dake tsakiyar gidan wani irin
gidan sama ne wanda ke dauke da kayataccen falo na sarauta wanda anan sarki ke ganawa da
bakin sa na nesa.
Balcony din dake gefen wajen shine wajen zaman sa tare da mahukunta (king-makers) in
ana wani muhimmin sha'ani kamar hawan sallah, nadin sarauta, bikin aure da sauran su. Akwai
wata doguwar baranda a kasa wadda anan ya kan zauna a kowanne yammaci ya gana da
jama'ar gari yayi musu maganin kukan su, alkalanci da zaman fada. Daga hannun dama na tsakiyar ginin akwai wata babbar kofar katako wadda in ka bi ta zai
kai ka barga (ma'ajiyar Dawakai). A kowanne yammaci kyakwawan Dawisu (Peacock) ne a
gaban gidan bila-adadin masu ado da ban sha'awa suna baza dogon bindin su cikin nuna
baiwar ado da kyau da Allah yayi musu wanda bai yi wa wani tsuntsu ko wata dabba a duniya
ba. Akwai fili fetal daga get din farko zuwa ginin farko na shiga ainihin zauren farko na
masarautar. Akalla zaka wuce zauruka shida kafin ka tarar da wajen zaman sarki na farko da
jama'ar sa na nesa, kafin ka isa wajen zamansa da mahukuntan sa, sannan ka yi tafiya mai
tsayi kafin ka shigo ainihin cikin gidan mazaunin iyalin sa.
Tsakanin inda sarki ke zama da 'barga' dakunan samarin gidan ne da yara maza da ake riko

a gidan, sannan kayi tafiya mai tsayi wadda zata kawo ka get din cikin gida.

Bangaren sarki zaka fara taddawa wanda ya hadu da get din cikin gida, kuma akwai kofofi da
ke hade da bangaren kowacce matar sa ta aure. Daga gaban ginin akwai baranda mai kama da
balcony a gaban kayatacciyar shigifar sarki inda anan ne ya ke ganawa da 'ya'yan sa, matan sa
da 'yan uwan sa mata. An fi yin wannan ganawa da yamma ko da daddare. A wannan shiyyar
babu mutane da yawa, kowa yana bangaren sa, sai bayi mata wadanda suma suke shige da
fice babu yawan surutu, kowacce tana bangaren data ke hidima suna kuma shige da fice daga
wannan sassa zuwa wancan na matan Sarki.
Sarki kan zauna a kofar shigifar sa da yamma, don gabatar da sallahr la'asar, maza in na jiki
ne suna iya shigowa nan, idan 'ya'ya ko jikoki suka shigo a daidai wannan lokacin saidai su rike
takalman su a hannu su sunkuyar da kai su wuce in har ba shine ya ce a kira su ba. Amma in a
barandar data raba shigifar sa data matan sa yake zaune, da 'ya'yan ko jikokin sun karaso zasu
zube gaban shi su kwashi gaisuwa.....
"Alanguburo" (Allah ya kara maka yawan rai) shine abinda ake cewa. Ba'a gaida sarkin
Askira da "ina wuni? Ko ina kwana?" Shi kuma ya amsa da "Allah Kawun jo" wato kamar ace
(Allah yayi albarka).
Akasari a wannan shiyyyar babu dogarai babu bayi, in ya ga dama ya kan ja 'ya'yansa da
jikokin sa da wasa, yayi musu tambayoyi akan rayuwar su a irin wadannan lokutan.
In ka wuce wannan shiyyar ne zaka hadu da bangaren matan gidan. Wato matan Sarki na
aure.
Kowacce da bangaren ta wadatacce ginin zamani mai manyan shigifu, wanda aka yiwa ado
da royal furnishing, babu abinda babu a ciki na jin dadin rayuwa, domin masarautar a
zamanance take sannan ilmi ya wadaci al'ummar masarautar, ba abinda zai hada kowacce da
'yar uwar ta in har ba ita ta neme ta ba. Daga bayan nasu bangaren ne na kwarkwarorin sarki
ya ke.

Ana kiran bangaren kowacce matar sarki da sunanta.....Unguwar Ya Gumsu (Fulani Babba),
Unguwar Ya Kirjinoma (Fulani Halima), Unguwar Fulani Hibbani (matar sarki ta uku) sai
unguwar Fulani BILKISU (amaryar sarki).
'Ya'yan gidan duk sun girma, mazan na wajen ayyukan su da masu karatu a garuruwa daban
daban, matan duk an yi musu aure a masarautu daban daban na jihar Borno, 'ya'yan Hibbani ne
kawai 'yan kasa da shekaru sha takwas. 'Yammata ne guda biyu: Naja'atu, da Humaira. Sune
kuma kadai ba'a yiwa aure ba a 'ya'ya mata. Kowacce cikin matan sarki tana da manyan 'ya'ya maza da mata, in ka dauke amarya Fulani
Bilkisu, wadda har yau take haihuwa suna mutuwa tun suna jarirai wato (wabi).
Wannan a takaice shine description na gidan sarkin Askira mai ci a yanzu, da bayanin tsarin
masarautar gabadaya. Masarauta ce mai farin jini da tarin arziki wadda aka yiwa shaidar adalci
da kyautayi ga talakawanta. Daidai gwargwado 'ya'yan sarki maza da mata sun wadatu da
ingantacciyar tarbiyya da ilmin addini da na zamani, duk da ba'a rasa masu fitina ba musamman
samarin maza. Kishin da ke tsakanin iyayensu mata bai hana su hadin kai a junan su ba, suna
matukar kaunar junan su. Sarki na da 'ya 'ya goma sha biyar, maza da mata da jikoki sama da
goma.

****
Baba Saleh ya koma gefe ya daga kai yana kallon wannan babbar masarauta da bai taba
mafarkin gani a zahiri ba, tun suna yara ya ke jin labarin masarautar Askira, irin tarin arzikin ta
da karfin mulkin ta, hannun sa cikin na Sa'ade, sun yi zuru-zuru sabida yunwa da gajiya.
Tunanin sa shine wa zai dosa ya ce yana son ganin BILKISU? Wadda marigayi Malam Hashimu
ya ce tana daga cikin matan gidan???
Bar ta wadannan dogayen dogaran dake shige da fice suna muzurai kamar sa ci babu, wasu
a tsaye kyam kamar an kafe su. Kai sai ka dauka babu bargo a cikin jikin su. Babban abinda ya
fi razana shi shine shirgegiyar kofar masarautar, irin kofar nan ce ta jan karfe da ake kira
mahdi-ka-ture. Ya ajiye kunshin kayan Sa'ade dake hannun sa a kasa yace da Sa'ade ta hau kai ta zauna,
shikuma ya zare sidadden silifan sa ya zauna akai ya kurawa kofar shiga masarautar ido yana
tunanin ta inda zai bullo.
Kafin ya farga sai ya ga Sa'ade na gyangyadi akan kunshin kayan ta sabida wahala da
gajiya.
Sai ji yayi wani Dogari ya buga musu gigitacciyar tsawa, "Kai tsoho! Me kuke nema anan?"
****

Baba Sale ya mike yana kakkabe kurar jikin sa Sa'ade ma ta yi firgigit ta farka daga
gyangyadinta, sai rarraba ido take gabadaya ta firgice. Cikin raunin murya Baba Saleh ya dubi
dogarin ya ce.
"Mu baki ne tun daga Tsanyawa ta jihar Kano, bawan Allah na zo garin nan ne takanas don in
ga Sarkin Askira, don Allah don Annabi ka taimaka mana".
Wani wulakantaccen kallo dogarin yayi musu sannan ya ce "ka san wa ka ke nufi kuwa?
Tsoho anya lafiya kalau kake?"
Baba Sale yayi murmushi mai ciwo irin wanda dan adam ke yi in yana son boye bacin ran sa,
ya ce "bani da alaqa da shi, kuma ban zo neman komai wajen sa ba, sakon dana ke dauke da
shi na matar sa ne, kaga kuwa bai yi daidai ba in nemi ganin matar sa ba tare da na fara neman
alfarmar sa da yardar sa ba. Ka taimaka mana ko don yarinyar nan da ke jin yunwa, marainiya
ce".
Dai-dai lokacin wani gajeren dogarin ya taso don ganin abinda ya tsayar da dan uwansa
wajen wadannan mutanen masu kama da korarrun jeji, "Buba me suke nema ne?" A raine ya
dube su sannan ya nuna su da bakin sa "wai maimartaba suke son gani" "amma shine zaka bar
su a tsaye ko wurin zama bazaka basu ba?" Ga dukkan alamu shi wannan din mai kirki ne, ya ce da dan uwan sa "maimartaba ya bada
damar duk mai son ganin sa ya ganshi cikin kasar sa, cikin aminci da girmamawa, don haka
barkan ku da zuwa Masarautar Askira, amma baza ku samu ganin maimartaba ba sai
washegarin gobe in Allah ya kaimu idan an fito fada". Baba Saleh yayi godiya sannan ya ce "don Allah ko zan samawa yarinyar nan wajen kwana?
Ba mu san kowa a garin nan ba, ni bani da matsala ko a nan wajen zan iya kwana".
Wanda aka kira da Adamu wato mai kirkin dogarin, ya ce "ta zo muje in kaita wajen matata ta
kwana, kai kuma ka biyo ni".
Matar Adamu itama baiwa ce a gidan, bangaren su yana daga can karshen masarautar,

unguwa ce guda duk bayi ne da iyalan su, amma yawanci basa wuni anan kowacce tana
sassan data ke aiki cikin masarauta, sai dare can suke komawa gidajen su.
Ta zubawa Sa'ade tuwo da miyar yauki ta kawo mata ruwa a kofin silba, Sa'ade ta tasar ma
tuwon nan kamar Allah ya aiko ta. Sai da ta ci ta koshi matar ta zuba mata ruwa a buta ta nuna
mata bayi, taje ta kama ruwa ta fito tayi alwallah ta shimfida mata tabarma anan dan tsakar
gidan ta, ta shiga rama sallolin da ke kanta. Ana idar da sallahr isha kuwa barci ya dauke ta
akan tabarmar data yi sallar, matar tayi mata shimfida a dakin ta ta tashe ta ta koma daki, ita
kuma ta cigaba da ayyukan ta.
Washegari ta bata koko da kosai ta karya kumallo, ta sa ta tayi wanka ta canza kaya cikin
nata dake kulle, Adamu bai shigo ba sai karfe goma na safe ya ce ta biyo shi. Tayi wa matar da
ta ji ya kira Kubra godiya sosai, tabi bayansa, anan waje suka hadu da Baba Saleh ya ji dadin
ganin ta cikin kyakkyawar kama, ya karbi kullin kayan ta suka bi bayan Dogari Adamu zuwa
fadar sarki.
Wuce wannan shigifa, tsallake wannan soro, wuce wannan falo har suka dangana da inda
Sarki ke ganawa da jama'ar gari a kowacce rana.
Dogarin ya ce su tsaya daga waje, ya shiga ya fadi yayi gaisuwa, sannan ya fadi sakon Baba
Saleh, Wazirin sarkin Askira yayi masa tambayoyi a kan su kafin aka amince masa kan ya shigo
da su.
Baba Sale ya shigo rike da hannun Sa'ade, ya fadi yayi gaisuwa yadda ya ga ana yi,
dogarawa suka ce "Sarki ya gaishe ka, ka yi gaggawar fadin abinda ke tafe da kai".
Baba Sale ya muskuta sannan ya soma koro bayanin sa cikin nutsuwa, wasiyyar da abokin
sa marigayi Malam Hashimu ya bashi a lokacin da yake cikin tsananin ciwo akan gargarar
mutuwa, na cewa ya kawo yarinya Sa'ade hannun BILKISU a masarautar Askira idan ta Allah ta
kasance da shi. Ya gaya mata cewa diyar ta ce da ta haifa tare da shi a garin Tsanyawa. Sarki Yusufu Bin AbdulHakimu (mai Askira), ya dan zamo daga cikin kujerar mulkin sa ya
tsurawa yarinyar ido, wadda ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login