Showing 15001 words to 18000 words out of 30109 words
Chapter 6 - Masarautarmu Book 1 Hausa Novels Compelet By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf
'yan dakin su cike da kewa suna fadi a ransu ai gara ta je gida ta huta da
wannan bautar data sha ta gimbiya Humaira, wasu kuma suka ce a ran su watakila har a gidan
ma irin bautar data ke mata kenan.
Kusan su ne na farko da aka zo dauka a washegari. Suna tsaye ita da Raheema a jikin
bishiya suna hira, Humaira na daga zaune a gefe akan jijiyar bishiya tana ta harare-harare irin
wanda ta saba da kallon kowa a wulakance. Zungureriyar mota kirar 4matic baka wuluk ta yi
parking a gefe, da rubutu baro-baro cikin ruwan gwal "ASKIRA EMIRATE". "Ma'assalam Raheema, an zo daukar mu"
Ta fada tana jan trollies din biyu dake gaban ta, nata da na Humairah, Raheemah ta daga ido
tana kallon inda ta nufa, tun kafin ta karasa dogarawa biyu suka yi wuf suka fito daga motar
suka karbi kayan hannun ta. Ta karanta rubutun ta sake karantawa "ASKIRA EMIRATE" Ashe
daga masarautar Askira suke, no wonder Humairah take mulkin data ga dama. Baban ta ya sha
basu labarin masarautar Askira da irin dimbin arzikin ta da shaharar ta a yankin Borno.
Ta karasa da gudu ta cimma Sa'ade, ta rike hanayen ta, tana murmushi ta ce "ki gaida mun
Fulani, i will give you a giant surprise insha Allah" Sa'ade ta yi dariya ta ce "Fulani zata ji, ki
gaida Mama dasu Sarina (kannen ta)".
Raheema na juyawa ta kusa karo da Humairah, da sauri ta bata hanya sabida mugun kallon
data sakar mata. Ta shiga gefen dama data saba zama dogarin ya rufe kofar. Ya zaga mazaunin
sa ya zauna suka ja motar zuwa get, inda suka cike takardun daukar dalibai sannan aka basu
dama suka wuce daga get din makarantar. Tun daga kofar gida kuyangin Humaira na tsaye suna jiran isowar ta. Cikin rakiyar su suka
wuce cikin gida kowacce ta doshi bangaren su. Fanna ta fara cin karo da a bakin kofar shiga
unguwar Fulani Bilkisu da alama jiran karasowar ta take, tana mata murmushi tace
"sannu da zuwa 'yar gida na, yaya hanya kuma yaya karatu?"
Tare da karbar jakar kayan ta wadda Humaira ta hana kuyangin ta su daukar mata.
Suka wuce zuwa ciki, tsakanin ta da sauran bayin Fulani sai ido, don ba'a basu damar alaqa
da juna ba, only Fanna. Ta kaita har dakin ta, ta hada mata ruwan wanka a bathtube sannan ta
fita don ta kawo mata abinci.
Sa'ade tayi wanka ta ji dadin jikin ta, ta sauya kayan makaranta zuwa doguwar rigar atamfa
exclusive mai hasken sararin samaniya, sosai tayi kyau, farar fatar ta ta yi tas, wanka da tsafta
sun kama jikin ta, ita kanta data tsaya a jikin mudubin dogon yaro ta kalli kanta sai da ta razana,
don gani tayi kuruciya kadai ce zai sa ta kasa cewa Fulani Bilkisu ce a cikin mudubin. Ta ga ta
kara tsayi, hancin ta da idon ta sun kara fitowa dara-dara, tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta.
Sai data ci abinci ta koshi tayi sallar data kufce mata sannan ta hau gado sai barci.
Cikin barcin ta ji an dala mata duka a cinya, ta zabura ta mike zaune, Fulani ce tsaye a kanta
ta ci gayu kamar mai shirin gasar sarauniyar kyau.
"Wa ya ce da ke ana barci bayan la'asar? Kidahuma kawai".
Ta zumburo baki tana mutstsikar ido. "Amma ko sannu da zuwa baki mun ba kin rufe ni da
fada, don Allah Fulani me na yi miki ba kya so na?" Ta saki kuka har da na shagwabar ganin
uwa, ba wai na zafin fadan da ta yi matan ba. She just felt relaxed by seeing her......after
missing her for over ninety days. Fulani ta saki baki tana kallon ta don bata ga abun kuka ba
don kawai tace ta daina barci bayan La'asar. Tsaki tayi tace "ba'a son naki, an ki a so ki din,
ubanki ya ja miki, banda alfarmar Askirama wallahi bazaki zauna mun a gida ba, Damaturu zan
kai ki". Sa'ade ta ida rushewa da kuka, it's painful uwar data haife ka ta bude baki tace bata son
ka sabida mahaifin ka komai kazantar laifin uban naka ai mutuwa ma na kunyar idon Da.
Balle in ta tuna Uban nata da akewa kiyayyar ba ya duniyar ma. Ita Fulani wace irin zuciya
gareta?
"Duk talaucin sa dai bazaki kankare cewa shi kika fara aure ba, tun da ga ni.....", sai bayan ta
furta kalaman wadanda a zahiri a zuciyar ta tayi niyyar fadar su, ta yi maza ta toshe bakin ta da
ta fahimci sun fito fili, amma ina! Already Bilkisu ta ji su.
Har ta kai bakin kofa gabadaya ta juyo, ta kankance idanu ta kai mata wani wawan mari,
Sa'ade ta kauce amma saida ta samu bayan kunnen ta, dan kunnen ta ya fice ya karce gefen
kunnen ta sosai jini ya kwanta a wurin tare da yatsun Fulani Bilkisu.
"Wannan ya zamo rana ta karshe da zan kara yin magana ki maida mun, mara kunyar banza!
Mai mugun hali irin na uban ta!"
Sa'ade na kuka wurjanjan Fulani ta bude kofar dakin ta fice.
Tana zuwa falon ta ja ta yi turus! Ganin Askirama a zaune yana jiran fitowar ta.
Ya sauke nagartattun idanun sa akanta, ma'abotan kamala da ilhama, a hankali ya ce.
"Koma ki kirawo min ita, na jiyo kukan ta".
Bata da damar yin musu, haka ta koma jiki a sanyaye tace daga bakin kofa.
"Ki zo Askirama na kiran ki".
Without giving her a second look ta fice ta bar dakin.
Sa'ade saida taje toilet ta wanke idon ta don dai ta boyewa Alanguburo cewa kuka take,
amma tana fitowa ta zauna a gaban sa idon sa bai sauka a ko'ina ba sai a bayan kunnen ta.
Ya kamo fuskar Sa'ade ya kalli ciwon sosai, yace "Sa'adatu ki yi hakuri kin ji? Ni na gaya miki
watarana in wani daban yayi miki haka, sai inda karfin ta ya kare".
Sa'ade tayi murmushi duk da idanun ta sun kumbura, a ranta tana tantamar zuwan wannan
ranar. Yau ta yarda da gaske Fulani ke kin Baban ta wanda shine mujazar nata kiyayyar. Amma
bata ga laifin ta ba, laifin kanta ta gani, da ta ke kasa tankwara zuciyar ta ta mayar mata da
magana. Wanda ko kusa bata cancanci hakan daga gareta ba. "Alanguburo ka taya ni bata hakuri don Allah, ni na bata mata rai".
Ya yi murmushi ya ce "babu komai ta hakura, amma nan gaba ko me zata yi miki kada ki ji
haushin ta, sannan kada ki tanka mata. Uwa ta wuce duk inda kike tsammani. Matsayin ta da
darajar ta daban yake dana kowa a wajen ubangiji. Sai da Ya ce abi ta.....a bi ta.....a bita... sau
uku kafin ya ce abi Uba. Ina fata kin fahimce ni?"
Hawayen nadama na zuba a idanun ta ta gyada masa kai, ta dago ta dubi Fulani da
appealing look, amma sai Fulanin ta kauda kai idanun ta jazur, ko kusa bata yi nadamar ciwon
data ji mata ba da jinin data fitar mata, ta ma so ya fi haka, tunda ita bata da kunya. Amma can
a karkashin zuciyarta ta ji wani sashe daban ya darsa mata tausayin yarinyar. Sanin cewa bata
da kowa da zata raba a rayuwar ta sai ita, amma duk kokarin ta ta kasa sanya ta a ranta.
Watakila sai ranar da Sa'aden da kanta ta yarda cewa ba laifin ta bane duk abinda take yi mata
akan baban nata. Ko kuma ranar da zuciyar ta ta gaji ta russuna ta karbi Sa'aden don kan ta.
"Je ki ki huta zan sa a kawo miki magani ki sha". In ji Alanguburo. Har ta mike sai kuma ta
dawo gaban sa ta durkusa. "Ka yi hakuri Alan....ban cika alkawarin dana yi maka ba, ban yi
kokari a makaranta ba, na yi duk iya kokarin da zan iya amma na kasa kamo kowa....a karshe
nice ta biyun karshe". Yana murmushi ya ce "to ai babu komai tunda kin kada mutum daya, a ta gaba na tabbata
goma zaki kayar, a ta can gaba ashirin, a ta gabanta talatin, daga haka har ya zamo kece a
saman kowa. Kada hakan ya karya miki gwiwa kin ji? Ba wanda aka haifa da iyawa, kowa a
hankali yake zama gwani, je ki kwanta ki huta sosai kafin a kawo maganin, ko talbijin ban yarda
ki kunna ba sai gobe".
Cikin jin dadi ta amsa tareda yi masa godiya, ta saci kallon Fulani ta ga harara kawai take
zabga mata, ta wuce su zuwa daki kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Barcin da ya ce ta yi, ta so ta yi amma ta kasa, duk tunanin ta na yadda zata dinga yiwa
Fulani biyayya ne, insha Allahu daga yau bazata sake bata mata rai da gangan ba.
*****
"Me ya kai ki? Me ya kai ki dora hannu a jikin marainiyar Allah Bilkisu? In da ya zo da
tsautsayi kin kurunta ta fa? Wallahi bar ganin ke kika haife ta, akwai hisabi tsakanin 'ya'ya da
iyayen su".
"Ku yi hakuri Askirama!".
Abinda ta iya furtawa kawai kenan, ya mike cikin bacin rai mai tsanani ya ce "ni kam ba
abinda kika yimin sai kyautatawa, balle ki bani hakuri, tunatarwa ce kawai nake miki domin tana
amfanar da muminai. Amma tunatarwar da kullum sai an maimaita maka ita, ban ga amfanin ta
ba. Daga yau bazan kara yi miki magana akan 'yar ki ba, na tabbata kin fi ni son ta. Saidai bana
bayan zulunci, ni shugaba ne mai adalci wanda Allah ya damkawa amanar duk wani talaka da
ke cikin garin Askira babba da yaro, balle wanda ke cikin gida na karkashin iyali na don haka
bazan lamunci duka ba, in kin so ko dakin ta ki daina shiga wannan ya rage naki, amma duk
ranar da kika sake kai hannu a jikin ta zaki ga bacin rai na Bilkisu".
Ta tabbatar yau ta kure hakurin mai Askira, dole ta kwantar da kai tayi ta bada hakuri.
Tsakanin mace da miji sai Allah balle Bilkisu da Sarki Yusufu mai Askira. Soyayyar su wata ajiya
ce daga Allah. Wadda babu irin ta a wannan zamanin, soyayyar mazan jiya masu dattako da
sanin yakamata. Fanna ta kawo mata magani ta sha, arashin sanin ta har da maganin barci a ciki. Haka tayi ta
barci kuma Fanna bata tashe ta ba saida lokacin sallah yayi.
****
Kwanansu bakwai da dawowa hutu, Sarki Yusufu da Fulani Bilkisu da Fulani Hibbani suka
tashi zuwa kasa mai tsarki domin gabatar da aikin Hajji na wannan shekarar kamar yadda suka
saba duk shekara, yana daukan mata biyu ne cikin matan sa su tafi da kwarkwarori biyu.
Harkokin gidan suka cigaba da gudana kamar yadda suke gudana in sarki baya gari karkashin
kulawar Wazirin gari Ibrahim.
Kadaici ya kara yi wa Sa'ade sallama, bata ganin kowa sai Fanna, bata zuwa koina daga
dakin ta sai falon Fulani na karshe wanda babu mai shigar shi in ka dauke Fanna. Ta kagu a
koma makaranta ko ta hadu da Raheemar ta su yi ta karatun su ya fiye mata wannan jin dadin
mara 'yanci. Domin kafin Fulani ta tafi ta ja kunnen ta sosai akan kowa na gidan koda kuwa bayi
ne, bata yarda ko magana ta hada ta da kowa ba sannan bata yarda ko kofar unguwar ta ta fita
ba. Ko me take so ta gayawa Fanna zata yi mata.
Satin su Fulani biyu a kasa mai tsarki, rannan da Fanna ta kawo mata abincin rana ta hado
mata da wata wasika da aka rubuta da fensir, tace "sakon ki ne daga kawar ki".
Tun kafin ta bude takardar ta gane rubutun Raheema wadda ta rubuta sunanta a bayan
takardar. Raheema Kyari. Jikin ta har rawa yake wajen warware takardar. Ga abinda Rahima ta
rubuta.
"Hi Sa'adatu,
Ni ce Raheema, na zo tun daga Maiduguri as i promised to surprised you, an hana ni ganin
ki, don an ce ba'a bada umarnin ki ga kowa ba, sannan Fulani bata gari balle a nemi izninta.
Ina fatan ba za kiyi ta kallon talbijin ba, zaki yi ta bitar littatafanki ne kina koyar da kanki kafin
mu koma hutu, na so in kwana uku tare da ke don muyi karatu sosai in koya miki mathematics,
Allah bai yi ba, musamman Abba ya bada mota aka kawo ni, dana gaya masa masarautar
Askira ne bai hana ba. Na so mu hadu, na so in ga Fulani, na so in gan ki, but some other time
insha Allah. Mama da Sarina suna gaishe ki.
Yours sincerily,
Raheemah Kyari.
Har hawaye ta yi na bakin cikin rashin ganin Raheema, ta yarda Raheema mai son ta ce, mai
kaunar ta ce. Tunda har ta iya biyo ta tun daga Maiduguri har Askira. A karshe ta dauki
shawarwarin Raheema, ta daina kunna talbijin, ta mayar da littafanta da darussanta na baya
ababen debe mata kewa kuma abokan hirar ta. Sosai take tsintar abubuwa masu muhimmanci,
sannan ta dinga tisa haddar ta, Fanna ta kawo mata 'yar radio tana sauraren karatun
Abdurrahman Sudaith a ciki. Cikin haka har Allah yayi wa Fulani da maimartaba dawowa daga
aikin hajji ana saura kwana biyu su koma makaranta.
Suna dawowa shirin komawar su aka fara, aka yo musu provision har fiye dana wancan
hutun, babu wanda Fulani bata yiwa tsaraba ba cikin unguwarta (sassan ta). Banda Sa'ade. Ko
tsinke bata sayo mata ba.
Ita Sa'ade bata san ma an yi rabon tsarabar ba tunda tana cikin daki kullum, ta dai daidaici
sanda Fulani take zaman falo ita kadai ta je ta yi mata sannu da zuwa. Tare da tambayar ta "an
dawo lafiya?"
"Lafiya kalau, alhamdulillahi"
Kawai ta ce, ba tare da ta tambayeta komai ba, kamar lafiyar ta ko yadda ta sameta, wannan
abu ya sosa ran Sa'ade, ta wuce daki tana share hawaye da bayan hannun ta.
Kamar Maimartaba ya san za'ayi haka, da daddare sai ga kyawawan akwatuna manya guda
biyu Fanna ta shigo mata dasu, tace tsarabarta ce inji Alanguburo. Ta ce Fanna ta bude mata.
Tsala-tsalan dogayen riguna na 'yammatan larabawa ne a ciki kala-kala harda masu ado na
sarauta a jikin su, takalma da jakunkuna na yammata masu karshen tsada a daya akwatun
kalar kowacce daga cikin dogayen rigunan.
Ta cire biyu a ciki ta bawa Fanna, amma sai Fanna tace bazata karba ba Fulani ta basu irin
nasu. Wadannan 'ya'yan gidan kawai suke sanya su. Don haka sai ta dauki guda uku a ciki tasa
a kayan ta na tafiya makaranta da zummar zata kaiwa Raheemah a matsayin nata tsaraban.
Tunda suka dawo hutu wajen kwana arba'in bata kara sa gimbiya Humairah a idanun ta ba,
sai yau a cikin mota da zasu koma makaranta. Da ta gaisheta ko amsawa bata yi ba don Fulani
Hibbani ta kara ja mata kunne akan mu'amala da ita, ta gaya mata duk abinda Alanguburo ya
sayo mata a Saudiyyah irin wanda ya saya mata ne ko banbancin kala babu. Wannan ya kara
rura wutar kishin Sa'ade a zuciyar Humairah, ta kudiri aniyar kuntata mata wannan zangon fiye
da na baya.
****
Da Allah ya tashi taimakon Sa'ade, satin su biyu da komawa aka yiwa dalibai canjin dakunan
kwana, inda aka dauke ta daga dakin su Humaira kuma cikin ikon Allah ba'a kaita kowanne
hostel ba sai na su Raheema.
Murna wajen su abin ba'a cewa komai, a daren ne ta samu ta baiwa Raheema tsarabar data
ajiye mata, ita kuma ta bata labarin zuwan ta Askira, tace ta damu baban ta da labarin ta ne ta
yi ta rokon sa kan ya sa a kaita, shi kuma ya amince, amma cikin rashin sa'a sai bata samu
ganin ta ba. Nan aminci ya kara kulluwa, suka hade kai suka zama kamar 'yan biyu, gasu dama tsayin su
daya, sai dai Raheema baka ce sosai cikakkiyar Kanuri, yayin da Sa'ade take jajawur kamar
Fulani Bilkisu.
Kawancen Sa'ade da Raheema ba karatun Sa'ade kadai ya taimaka ba, ya taimaka mata a
sauran fannoni na rayuwar diya mace, tsafta, kwalliya, da iya magana, hatta tafiyar ta Raheema
gyara mata take don tace tana tafiya gaba-gadi babu tsanaki. Ta koya mata magana a hankali
cikin nutsuwa da yadda zata dinga gyara da kula da sassalkan gashin kanta na Shuwan usli.
Rayuwar Sa'ade ta yi ta samun cigaba islamically, educationally, socially and morally a
makarantar EL-KANEMI COLLLEGE OF ISLAMIC THEOLOGY.
Balle yanzun