Showing 9001 words to 12000 words out of 30109 words

Chapter 4 - Masarautarmu Book 1 Hausa Novels Compelet By Sumayya Abdulkadir Takori .pdf

taba
bayarwa ba". "Sai kuma mutuwa ta yanke muku dukkan kudirin ku ke da shi, akan baiwar Allah, wannan ya
isa ya nuna muku cewa karfin kudura da irada naShi ne, bawa bai isa ya tsarawa kansa rayuwa
ba, face abinda Ubangiji ya tsara masa".
Mai martaba ya fada mata a tsanake.
Ta sunkuyar da kanta, tana wasa da yatsun hannun ta, bata ce komai ba.
"Ki gaya mini duk abinda yakamata na sani akan yarinyar nan, tunda dai kin yarda sunnah ki
kai kika haifeta, kada ki zama azzalumar Uwa, wallahi Allah bazai bar ki ba".
Fuskarta tayi jajawur kafin hawaye su cicciko idon ta.
"Ran ka ya dade bana son tuna labarin nan, bana so. Ba abun fade a cikin sa, me kake so ka
ji? Yes, aure na yi na haife ta, amma ban taba son uban ta ba! Sau daya ya taba kwanciya da ni
bisa fin karfi har na samu cikin ta. Kana so ka ji cewa Babana biyan bashi yayi wa ubanta da ni?
Ya aura masa ni a matsayin filin sa da yake bin sa bashi?" Maimartaba ya nuna abin bai bashi mamaki ba, a fuska da muryar sa babu komai, yace "to
ita yarinya meye laifin ta? Bata zo duniyar ba lokacin, balle ta san laifin da babanta ko baban ki
yayi miki da zaki rama a kanta. Ki yi a hankali, 'ya'ya amanar Allah ne a hannun mu, bar ganin
ke kika haifeta, wallahi hakkin ta zai iya kai ki wuta. Ba kya tunanin hakkin ta ne yake hana
wadanda kike ta haifa rayuwa? Tunda itama baki ji kanta ba a lokacin da Allah ya baki ita?"
Bata ce komai ba amma tabbas kalaman sa sun shige ta, daga zaunen da yake ya kamo
hannun ta. "Bilkisu ki karbi amanar da Allah ya baki da hannu bibbiyu, na yafe jin labarin auren
ki da mahaifin ta tunda na lura yana tono miki bacin rai ne, wanda kika riga kika manta. Abu
daya nake so ki rike a ranki shine wannan yarinya dolen ki ce, bata da sauran gata sai ke, wani
dan uwan baban ta da kika ce akwai a Damaturu ba shi shari'ah ta bawa rikon ta ba kasacewar
ta mace, kuma kina raye, sannan kina da halin rike ta. Ni na karbi yarinyar nan kamar sauran
'ya'ya na..... idan ni da nake kishin Baban ta ya riga ni samun ki, na karbi 'yar sa zan rike da
amana, ke mai zai hana ki kwatanta tausayi da adalci irin na UWA ki karbi marainiyar Allah???"
Sai ta fada jikin sa tana kuka sosai, jikin ta yana tsuma, ya rike ta sosai a jikin sa yana cigaba
da lallashin ta, Fulani Bilkisu ta san maimartaba yana son ta, amma bata zaci son ya kai har
haka ba, duk da bata taba haife masa rayayyen Da ba. Shi gashi yau ya karbi nata da hannu
bibbiyu, wanda bai taba sanin da wanzuwar sa ba. Idan bata yi masa biyayya ba kuwa, hakika
ta cika butulu, wadda bata godewa ni'imomin Ubangiji gareta ba.
"Zaki kula da ita ko Bilkisu? Zaki bata kaunar duk da ya kamata ki bata?"
Ta gyada masa kai, ba tare da ta ce komai ba. Sai rungume shi data yi sosai a jikin ta.
"Ka yi min alfarma Askirama kar ka gayawa kowa cewa 'ya ta ce, don Allah, kace 'yar
kanwata ce na karbo, ina gudun gorin kishiyoyi, tunda cikin su babu wadda ta san na taba aure
kafin na zo gidannan".

"In don wannan ne kada ki damu, amma akwai wadanda sun riga sun ji a fada, zan
gargadesu don duk na san su".
"Nagode.... Nagode Askirama. Alanguburo (Allah ya kara maka yawan rai)".
****

Duk da haka sai da ta kwashe kwanaki uku bata nemi Sa'ade ba, bata shiga dakin ta ba, bata
nemi sanin halin data ke ciki ba. Fanna dai ta gaya mata tana nan lafiya kuma tana kokarin
koyar da ita tsafta da sauran abubuwa.
Sarki Yusufu ya san halin kafiya irin na Bilkisu, don haka bai gushe ba yana cigaba da
lallashin ta akan Sa'ade. Tana nuna masa komai lafiya, alhalin bata kara sanya yarinyar ma a
idon ta ba.
A rana ta hudu sai gashi ya kara dawowa da kansa da safe kafin ya fita zuwa zaman fada.
Tana karya kumallo ita kadai a 'dining table' din falon cin abincin ta. Ta mike cikin girmamawa ta
same shi a kujerun da suka kawata falon, suka gaisa kamar yadda suka saba cike da kewar
juna kasancewar ba ita tayi girki ba, kwana biyu kenan basu hadu ba, cikin hikima irin ta manya
ya ce,
"Yaya kike cin abincin ke kadai babu 'yar tayin hira? Maza kirawo min ita mu gaisa, sabida ita
na shigo".
Fuska a turbune tace "bata tashi daga barci ba"
"A taso ta"
Ba yadda ta iya dole ta juya cikin kasaitaccen takunta ta nufi dakin da ta san ta ce a ajiye
mata Sa'aden kamar wani kayan wanki.
Ta murda kofar ta shiga a hankali ba tare da ta bari sauti ya fita ba, akan darduma ta same ta
tana sallah, tana wani karatu a fili "basim-mi'ara, alu ambaki wau-zal, wa'aluba ilallan
haakuri"..... sannan ta tafi sujjadah ba tare da ta yi ruku'u ba. Fulani ta mutu a tsaye, sujjadar
ma guda daya tayi ta sallame sallahr. Kamar jikin ta ya bata da mutum a dakin, da sauri ta juyo,
suka hada ido da matar data ke kwana tana wuni da ita a ran ta.
Da kyar Fulani ta hada sautin muryar ta waje daya, ta ce "sallahr me kike yi?"
"Asubah ce Inna"
"Asubah? Wa ya ce miki yanzu ne lokacin sallar asubah karfe goma na safe har ta wuce?"
"Ai i yanzu nake yin ta kullum, wataran ma sai na dawo daga talla ma nake hadawa da
azahar inyi kafin Baba ya barni na fara zuwa makarantar A-BA-CA-DA".
Takaici ya hanata magana kawai ta juya a fusace tare da cewa "biyo ni".
Suna shigowa falon taga maimartaba a zaune cikin rawanin sa da jabba, da sauri ta tafi
gareshi ta zube a gaban sa, ta lura shi mai kirki ne ba irin matar sa ba mai kama da mala'ikun
daukar rai. "Baba ina kwana" yayi murmushi yana kallon ta da tausayi "Anan ba'a cewa Baba
diyata. "Alanguburo" ake cewa. Tayi kokarin maimaita kalmar amma ta kasa. Yayi dariya kadan
cikin tausayi yace "kina son makaranta?" "Sosai Alan...." sai ta yi shiru. Ya karasa mata
"......guburo" ta maimaita a hankali "Alanguburo" "masha Allah! Makaranta wacce kike so? Ta
kwana ko ta jeka ka dawo?" Ta saci kallon Fulani Bilkisu ta ga yadda take hararar ta, sai ta ga ai
gara mata ta zabi makarantar kwana akan zama ita kadai cikin daki da idanun Innarta masu
razanata. A hankali ta ce.
"Na fi son makarantar kwana Alanguburo"

"To shikenan tashi jeki abun ki, nan da sati biyu za'a kai ki, amma bazakiyi nisa da gari ba,
nan cikin garin Maiduguri zan sa a nema miki mai kyau, ince ko kina kunna talbijin kina kallo?"
"Menene talbijin Alanguburo?" Ya nuna mata ita da hannu, ta ce "ai babu a dakin dana ke" ya
ce "Innar ki bata kyauta ba, yau zan sa a kawo miki taki a jona miki a dakin ki". Ta hau murna
sosai ta ce
"Nagode Alanguburo"
Yace "Allah Kawun jo".
****
Duk yadda ta so ta wuni cikin sukuni a ranar ta kasa, sallahr Sa'ade da karatun sallahrta
kawai take tunowa. Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, wai dan musulmi ne yake irin wannan
ibadar, me ake da rayuwar jahilci.
Ta so ta share, don a ganinta tunda Askirama ya ce zai kaita makaranta ta san zata koya a
can, amma sati biyun da zata cigaba tana irin wannnan sallahr zuwa lokacin da zata koya din
shin idan ta bari Allah ba zai tambaye ta ba? Tunda har ya nufe ta da gani, tamkar umarni ne ya
bata kan ta yi mata gyara tana so ko bata so, ita ba jahila bace ta san muhimmancin sallah ga
dan musulmi, balle wanda ka haifa a cikin ka.
Ta kira Fanna da zata wuce kai mata abincin dare, tace "kira min yarinyar can ta same ni a
dakina yanzun nan". Fanna ta yi matukar mamaki don banda ita Fannan ba mai shiga dakin
Fulani Bilkisu, itama gyara ne kawai yake kai ta shima ba kullum ba, sai lokacin da Fulanin ta
bukata. Har dakin ta kawo Sa'ade, sannan tayi bankwana ta juya, don ta gama aikin ta na daren sai
kuma gobe.

A wannan lokacin ne Fulani ta yi mata kallo na sosai, tana durkushe gabanta kamar yadda ta
ga Fanna na yi, da can a fizge take kallon ta, a 'yan kwanaki hudun kacal data yi cikin gidan har
ta fara washewa, kamannin ta da ita sun gigitata, kallo daya zaka yiwa yarinyar ka san ita ta
haifi abar ta, kamar ta yi kaki ta tofar. Anya akwai wanda zai yarda in aka ce ba 'yar ta bace? Ko
dai ta bari Askirama ya fadi gaskiya ne? Amma in ta tuna gorin da zata sha wajen Ya Gumsu
(most senior wife ta sarki) kuma wadda suke buga mugun kishi da ita fiye da sauran matan sarki
sabida yadda take jin kanta matsayin uwar manyan 'ya'yan sa, amma ya zo yana fifita Bilkisu
akan ta, wanda hakan ya haifar da zazzafan kishi a tsakanin su, sai ta ga gara ta bar ta a 'yar
kanwar ta ce, ai is normal dan dan uwanka yayi kama da kai.
Ta yi ajiyar zuciya tareda dauke kanta daga kallon yarinyar tana jin kirjin ta na wani irin
bugawa, inta kalli yarinyar sai ta tuno sanda Hashimu ya daure ta a jikin karfen gado ya haike
mata, ko ta so ta ji tauayin ta abinda take tunawa kenan ta ganta bakikkirin a idanun ta, duk da
an ce ya mutu, bata jin nan kusa zata yafe masa, ta hadiye wani kullutu daya tokare ta a kahon
zucci, tana mai kautar da kanta ta ce mata.
"Kin yi sallahr Isha?"
"A'ah Inna, bari nayi sai can dare, an ce sallah cikin dare tafi lada"
Ta galla mata harara tace "inji uban wa? Ni kar ki sake ce min Inna".
Sa'ade ta yi shiru tana kikkifta ido. Ta nuna mata hanyar toilet da hannun ta "muje ki yi
wankan sallah da alwalah akan idona na gani"
Sa'ade ta zaro ido.

"Kina nufin a gaban ki zan yi timbir?"
Ta sake galla mata harara cikin tsawa tace,
"Rufe min baki! Ko kin ga ana yi min musu a gidannan? Zaki wuce ko sai na hankada ki?"
Sum-sum-sum Sa'ade ta wuce ita kuma ta bi bayanta.
Da kyar Sa'ade ta iya cire riga a gaban Fulani, tana yi tana kare kirjin ta, tace tayi wankan
tsarki tana gani. Ai yadda ake normal wanka da soso da sabulu haka Sa'ade ta yi, alwala kuwa
ba'a zancen ta. Fulani Bilkisu ta ji kwalla ta tarammata, ba na tausayin yarinyar bane na tunanin
wai gudan jinin ta a duniya ne wannan ba arabi ba boko. Zama tayi akan masai ta dinga gaya mata yadda zatayi wankan tsarki don ta tambayeta
cewa ko ta fara ganin jinin al'ada ta tabbatar mata ta fara, sannan ta koya mata alwala, suka fito
ta bata mayafi tace ta tsaya ta lura sosai da yadda take sallah. Sannan tasa ta tayi tana kallo.
Akwai improvement sosai duk da haka wani abun sai kyalewa ta yi, ta san a hankali zata kara
gyarawa.
Sannan ta zaunar da ita a gaban ta ta koyar da ita fatiha, falaki da nasi da ikhlas, cikin 'yan
mintuna Sa'ade ta karanta mata su tiryan-tiryan, daga nan ta gane tana da saurin daukar abu
muddin zata samu kulawa.
Sai karfe goma na dare ta sallameta. Bayan ta gaya mata wannan karatun data koya mata
yanzu ta karanta ta tofa a hannayen ta ta shafe jikin ta da shi.
Daga ranar kuma bata kara nemanta ba, sai bayan sati guda, shi din ma kayane akwati uku
maimartaba ya aiko mata dasu, atamfofi, lesuka da shaddoji na alfarma, ta sa telar ta tazo har
sassan ta ta gwada yarinyar a gabanta, don har zuwa ranar ko kofar falo na biyu bata bari ta fita
ba, Allah Allah take ma satin ya zagayo a kaita makarantar kwanan ta huta. Ta manta cewa magana bata buya a gidan sarauta, abinda bata sani ba kuyangi suna
magana a junan su cewa yarinyar nan da aka kawo daga kauye tun ranar da ta zo basu kara
ganin ko inuwarta ba kuma basu san daga ina aka kawo ta ba ko aikin me ta zo yi. Har tsakanin
kuyangin sauran matan sarki suna zancen har zance ya kai kunnen su Ya Gumsu, Ya Kirjinoma
da Fulani Hibbani cewa Fulani Bilkisu ta dauko rikon 'ya daga kauye. Ya Gumsu tace "matar so
an gaji da zaman kadaici an buge da tsinto 'ya'ya". Ita kuwa Hibbani cikin hila ta tambayi
Askirama ko ya san da batun 'yar da Bilkisu ta dauko riko? Ba tareda ya bata hankalin sa ba ya
ce 'yar kanwarta ce, kanwar tata ta mutu". Haka ta je ta fesawa Ya Gumsu, ita Ya Kirjinoma
dama bata shiga sha'anin su, daga ita sai 'ya'yan ta take harkokin ta, tana da kamun girma
sosai.
A cikin sati biyun kafin tafiyar Sa'ade makaranta akwai cigaba sosai a tare da ita, sallahrta ta
gyaru, ga wanka ya kama jikin ta, Fanna ta koya mata yin Brush sau biyu a rana, safe da dare,
ta zama kamar Yayarta. Har hira suke yi sosai in Fulani ta tafi girki Turakar Sarki. Tana kara
gyara mata kome ta ga ta yi ba daidai ba, har dige-digen data ke yi a fuskarta da kwalli Fanna
ta hana ta.
Sannan ta kiyaye umarnin uwargijiyarta da gaskiya na cewa kada ta bari kowacce kuyanga ta
zo inda Sa'ade ta ke, bata yarda tayi alaqa da kowa cikin sassan ba bayan ita Fannar.
Ana i gobe sati biyun da Sarki yayi alkawari ya sake shigowa sassan nasu, wannan karon da
daddare. Ya samu Fulani da kuyanginta kusan su duka goman ana bata labarai tana
murmusawa. Yana shigowa duk suka mike, fadi suke in chorused "...zauna daidai mai Askira...
takawar ka lafiya Askirama!"

Suka fice akan layi, shikuma ya zauna sannan ya soma yiwa Fulani fada.
"Haka kawai kin kama yarinya kin kulle a daki don mugunta, kin hanata ko zama cikin
kuyangin ki, to wadanda kike gudun su san da zamanta sun riga sun sani, gara ma ki sakarwa
yarinya mara ta yi fitsari".
Ita dai bata ce komai ba sai "Allah ya huci zuciyar Askirama (mai Askira).
Bai amsa ta ba ya ce "kira wo min Sa'adatu". Ta tashi tana tafiyarta cikin yauki na halitta ta
nufi dakin Sa'ade.
"Ke ki zo ana kiran ki".
Ta ce da Sa'ade wadda ke luntsume tsakiyar gado ta kafawa talabijin ido tana kallon diramar
larabawa. Irin yadda ta saki baki da hanci tana kallon ba karamin haushi ya baiwa Fulani ba.
Kamar tayi fiffike ta shige cikin akwatun talbijin din a yi da ita. Ko maganar Fulani bata ji ba, sai
da ta taka ta kashe soket din talbijin din, tayi firgigit tace "haba don Allah Inna ya zaki kashe
mini.....?" Sauran maganar ta makale mata a makoshi sabida mugun kallon da Fulani ta jefe ta
da shi. "Na ce ki zo, ko ke kurma ce ne?" Sa'ade ta sauko daga gadon ta bi bayan ta don tuni
har ta fice, tana shigowa falon ta yi arba da Sarki, ai tuni ta washe ta daina fushin kashe mata
talbijin da Fulani ta yi ta nufi wajen sa cikin tsananin murna.
"Alan....ina wuni?" Yayi murmushi ya yafito ta da hannun sa. "Zo nan kusa gare ni Sa'adatu"
ta rarrafa gabansa ta zauna ya ce "Ah! Masha Allah, da alama Fulani tana kula da ke, gashinan
kin yi haske kin yi kumatu" ta saci kallon Fulanin, hararar data ke mata yasa ta kasa fada masa
abinda ta yi niyya, cewa ita bata wani kula da ita, Fanna ce take kula da ita, ita sai tayi kwanaki
bata ko ga inuwar ta ba. Aka soma shigo da kwalaye da katon katon na kayan masarufi ana
jibgewa a gefe. Daga ita har Fulani Bilkisu bin kayan suka yi da kallo don basu san ko na
menene ba.
"An samo makarantar Sa'adatu, an gama komai, gobe za'a kaita, ita da zuwa gida sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login