Showing 24001 words to 27000 words out of 31076 words
Chapter 9 - HAUWAU KULU Yar Cikin Badala 3 BY TAKORI.pdf
yau ta ji duk duniya ba wanda ta ke jin kunya sai Dr. Sarham, kasa amsawa ta
yi, gashi yana kara karfin matsar da yayiwa hannunta da nasa hannun mai tsananin taushi, ya
ce, "Ina gaishe ki Maiji....”.
Ta dan motsa baki cikin dabarar son janye hannunta daga nasa, sabida kasalar da taushin
hannun nasa ke saukar mata, da kyar ta iya ta ce,
"Ni ya kamata in gaishe ka ai Yaya Sarham, ina kwana?"
Bai yarda ya saki hannun nata ba duk da yadda ta ke son zameshi cikin dabara, ya ce,
"Na kwana ina tunanin cikin halin da ki ka kwana yau ba tare da Inna ba.
Na fi ki damuwa da rabuwa da Inna, amma wannan ita ce 'reality' din kowacce diya mace,
cewa ita din yar gidan wasu ce kin ji, mai lafiya ko mara lafiya in dai ta isa aure to Allah ya yi
umarnin iyayenta su yi mata, ko a birnin Sin ne, so ko ba ni ba ki sa a ranki wai don rashin ido
ba za ki dauwama a gaban Inna ba matukar Allah ya kawo miki mijin da ya dace dake yake
kuma son ki tsakani da Allah, amma banda Jamilu, ba don komai ba sai don kwanciyar hankalin
ki da zaman lafiyan iyayen ki da hakan zai wargaza. Ki yi hakuri kin ji???
Ni na san na saka gaggawa a cikin aurenmu, amma dai ai ba yau muka san juna ba ko
Maijidda, kuma in har na kara jan lokaci bayan wanda Ubangiji ya ara min, Jamilu ba zai rabu
da ke ba, da gaske yake.
Ni kuma ba zan taba barin wani abu ya kara taba zuciyar Inna ba da izinin Allah, balle
aurenki da Jamilu wanda shi ne babban tashin hankalinta”.
Hauwa bata san sanda ta katse Sarham ba, cikin rishin kukan da ya taso mata.
"....... Yaya Sarham, kana kokarin gaya min ne cewa saboda Inna ka aure ni kai, saboda
kwanciyar hankalinta daga Baba Zakari, don ka raba ni da Yaya Jamilu, amma ba don kai a
karan_kanka kana sona ba ko?"
Maganar Hauwa ta firgita Sarham yadda bai yi zato ba, don a tunaninsa Hauwa ba ta ma san
wani abu wai shi SO ba. kuma bata da tsinkaye mai zurfin haka.
Shirun da ya yi ne ya ba ta damar zare hannunta daga cikin nasa a hankali, tareda matsawa
gefe daga jikin sa, ta ce cikin dauriya da hadiye kuka.
"Na san ka aure ni ne saboda kana jin tausayina, kana kuma son ka wanke dattinka da ke
cikin raina, sannan don ka dorar da dangantakarka da Innata. Amma kayi mantuwa, ka manta
cewa ka riga ka gina zuciyata a kan wani ilmi na kada nakasa tasa in dauki kaina abar tausayi,
ko inferior, ko mara amfani a cikin al’umma, ko wadda matsayinta bai kai ga samun kaza ba
saboda nakasarta. Ka hore ni ne akan in zama jajirtacciya, cikakkiyar mutum, kuma in nemi
ilmin da isheni hada kafada da kowa, ka koya min tsayuwa da kafafuna, in haka ne aurenmu
cikin gaggawa ka yi ne don wani abu daban, amma ba don SO ba.
In haka ne ai da ka bar ni a gaban Inna ta, na ci gaba da bin koyarwarka as my Pacesetter,
na ci gaba da rayuwa da iyayena a gefe na. Koda kuwa ban auri Yaya Jamilu ba zan iya cigaba
da rayuwata daidai, saboda ba'a aure babu soyayya a iya sanina.
Ashe shiyasa ko amincewata baka tsaya nema ba kafin ayi mana auren, Yaya Sarham ba ka
taba tambayata ina so ko bana so ba, tunda ka san da ka furta Inna da Baba amincewa za su yi
koda basa so.
Hakan bai yi kama da fin karfi ba? Tunda ni dai ban ce inaso a aure ni don a taimakeni ko a ji
tausayina ba?".
Hauwa ta saka fuska cikin tafukanta tana kuka mai tsuma rai, tana fadin, "Yaya Jamilu ba don
tausayi ya yi niyyar aurena ba, ba don ya taimakeni ko ya sani a makaranta ba, zai aure ni ne
saboda So, da gittawar Kalmar so da kauna, da kuma niyyarsa ta gyara gurbataccen zumuncin
iyayenmu, shi ne ka yi maza ka hana shi, ba don kai din so na ka ke yi ba.
Already you have your life and your love, kana da macen da kake so daidai kai; wadda tayi
daidai da rayuwar ka, meyasa nima baka barni na auri daidai ni ba? Na gina nawa gidan kamar
yadda ka gina naka da so da kauna, a maimakon inda za'a dan raba ni da sunan tausayi da
taimako?? Sabida bana gani? Ko saboda iyayena sun ce neman kai suke da ni? Ko kuwa saboda ni
ban cancanci a so ni so na soyayya kamar sauran mata?" Ta kara tsananta kukanta harda jiniya
kamar tayi masa tumami a kasa.
Yau dai Hauwa na shayar da Dr. Sarham matsanancin mamaki, wonders shall never end!
Wato abin mamaki baya karewa. Mamakin ma irin wanda bai taba sha a kanta ba. Rikicin sosai
yau Hauwa ta tubure tana yi masa, akan don me ya aureta ya rabata da mai sonta na hakika,
tana kuka tana sharbe tana da ya barta ta auri Jamilu ya fiye mata alkhairi. Haka ya tabbatar masa da cewa Hauwa ta San 'yancin ta, nan gaba kadan in ta kara
shekaru da zurfin ilmi ba za ta taba yarda a danne mata hakki wai don tana makauniya ba.
Ya nisa ya sake nisawa, a wahalce ya ce, "Meji... Maijiddah don Allah ki saurare ni, Maijidda
nine fa, Ya Sarham dinky, kin san dai babu namijin da zai auri macen da ransa ba ya so ko
kadan.
Tukunna ma ki gaya min wane irin so ne wannan da ki ke ikirarin ni ba na yi miki? Sai kin
gayamin kowanne iri ne kuma a ina kika san shi?"
Ya tsattsare ta da ido kamar tana kallonsa, sosai taji idanun sa a jikinta kamar suna mata
bulala, kuma wai sai ta ji duk kunya ta kamata, ta rufe ido ta ki budewa, har zai kama hannunta
ya kai kirjinsa, don ta ji yadda kirjinsa ke bugawa akan rigimarta da rikicinta da ya daga masa
hankali, da yadda kalamanta suka firgita shi, sai kuma ya fasa. Baya so ya zamo touchy a
kanta. A ganinsa Hauwa ta yi kankanta ya zauna yana bayyanar da ‘inner feelings’ dinsa gareta
bari dai ta kara hankali zuwa can gaba, watakila shi ma zuwa lokacin ya samu ya fahimci kansa
da kansa, don shi kansa a halin yanzu bai san wane irin so ne zuciyarsa ke yi wa Hauwa ba, bai
san alqiblarsa ba, ya san dai ba irin na Madina bane, ba kuma irin na Sumayyah kanwar da
suka fito ciki daya ba kamar yadda yake kuskuren ikirari.
Ganin ta rasa inda zata sa kanta don kunya don ya dage shima sai ta gaya masa wane irin
so ne take nufi da baya yi matan. Shi bai san wane iri bane. Mikewa ya yi yana ce da ita,
"tunda bazaki gayamin ba bari in tafi sabgogi na. Zan shiga AKTH Haj. Soyayya, na rantse
sai kin gaya min da bakinki wane irin so ne wannan don ni ban san shi ba ko ba yau ba, akwai
abin da ki ke so in zan dawo in taho miki da shi?"
Hauwa ta kara kuluwa, tunda kuwa abin da ta ke son ji din daga bakinsa Sarham bai fade shi
ba har zuwa lokacin. Sannan ya maida zancen rainin sense. Bai kuma musanta kalamanta na
cewa ba don Inna ya aure ta ba, har ila yau, bai musa cewa don yana jin tausayinta ya aure ta
ba, haka bai ce ba don kada Jamilu ya aure ta ne ya sa shi yin gaggawar aurenta ba, haka bai
yi mata karyar da take son ji ba, wato ya karkace kai yace da ita yana mata so ne irin wanda
Jamilu ke mata ko fiye, wato na zallar ‘I LOVE YOU’.
Hakan ya sa Hauwa ta kara tsananta sautin kukanta. Don ta tsani a raina mata hankali.
"Cry more!" In ji Sarham. Yana takawa zuwa kofa. Tunda ni din dai da ba ki so ni Allah ya bai
wa ba Jamilun da ki ke so ba, wanda ya iya kalaman I love you da ni ban iya ba".
Ya dawo ya russuna daidai fuskarta har tana iya jin sanyin numfashinsa a saman fuskarta
kamar zai sumbaci hannayen da ta rufe fuskar da su, sai kuma ya fasa. “Kiss”. Abu ne mai
nauyi da sai da Madinah kadai yake iya shi. A ganinsa Hauwa is too young a yanzu ya tsaya
yana sumbatarta. Tunda kuma ta yi masa gorin Jamilu ya fi shi sonta, ya kara sanya shi shiga
taitayinsa da ita, yasa a ransa ba zai barwa Hauwa kofar sanin zuciyarsa a kan kowaccen su ba
ita da Madinah, wadda tun ba'a je ko ina ba ya gane Hauwa irin matannan ne masu son
soyayya, da son miji ya zauna yana gaya musu yadda yake son su a ran sa, koda karya zai
musu to yafi musu dadi akan ya ki furtawa, shi kuwa duk wata kalma ta ‘I love you’ da ire-irenta
da dangoginta ai ya gama fadawa Madinah su a can baya, ‘in his twentieth’ ba yanzu da ya fara
zama Uba ba.
Har yanzu yana nan a kan bakansa na cewa, ba auren soyayya ko son sauke sha'awa yayi
da Hauwa-Kulu ba, a'ah, auren dalili ne, kuma auren jihadi da kawo maslaha cikin rayuwarta
data iyayenta.
"Sai na dawo Maijidda, me zan kawo miki?"
Hauwa tayi masa shiru, tana jan hanci, ya ce. "Ko kina son ‘ice cream?"
A nan ne ta ce a dan fusace, "Ban san shi ba, kuma ban iya sha ba".
Ya ce, "Zan sayo ki koya?".
Da sauri tace.
"Wallahi bana bukata".
Murmushi ya yi, a ransa yace "oho dai, ba zan ce I love you din ba". Ya juya zai fita, sai ga
Sumayyah na shigowa dakin.
Ya ce, "Summy, na ce zan sayo muku ‘ice cream’, sarkin rigima ta ce ba kwa sha".
Sumayyah ta yi dariya ta ajiye tray din da ke hannunta a gaban Hauwa, ta ce, "Bhaiya, ka fa
yi babbar mantuwa, shin ka kawo kazar amarci ne kafin ice cream din? Ko ka fara zuwa zance
ka kafa gwamnatin ka yadda ya kamata???
Sarham ya shafa ‘man’s pride’ din shi (sajen shi) yana gyada kai, kafin yace “wato akace
dama sai hali ya zo daya ake abota, yau kam na yarda da wannan zaurancen”, ya gyada kai ya
fice yana cewa,
"Lallai Sumayyah kin raina ni da yawa. Watakila ma ke kike koya mata. Ke da ita ki gayamin
me ye marabarku? Ai ni kanwa nake da Maijiddah, don haka na girmi kazar amarci da wani
zuwa zance".
Wannan magana ta kara kular da Hauwa-Kulu, yadda baya zato, Sumayyah na ta dariya ya
fice ya rufo musu kofar.
Bayan fitarsa Sumayyah ta takura mata sai ta ci abinci duk da fushin da ta samu kanta tana
yi dole ta ci abincin tare da Sumayyah, sai da suka kammala Mama ta shigo tana jaye da
akwatuna daya bayan daya ta shigo da su har guda shida, ta ce,
"Sumy ga nan lefen Hauwa'u ne, da Babanta ya hana a kai. Da ma na ce sai ta zo nan zan
ba ta da kaina".
Kan Hauwa na kasa sabida nauyin Mama da ta ke ji. Sai Sumayyah ce ke yi wa Mama
godiya. Ta soma bubbudewa tana fiddo su, kaya ne masu daraja, tsala-tsala kowanne a
diddinke da mayafi mahadinsu, sai akwatin takalma da jakkuna duka flat shoes ne, da karamin
akwatin kayan shafa dana wanka, Mama da kanta ta zabo kayayyakin don haka komai ya bada
kala da ma’ana.
Mama ta zauna tare da su suna magana da Sumayyah kan sha’anin makarantarta da
abubuwan da ta ke bukata da za'a hada mata na komawa, dama duk sanda zata koma hutu sai
ta sayi abubuwan bukata da babu a Jeddah irin su maggi da sauran kayan girkin kasar Hausa,
don tare za su koma ita da Sarham, ta canza booking dinta ya koma daidai da nasa. A nan ne Sumayya ta ji hukuncin da aka yanke daga bakin Mama, cewa Hauwa ba za ta bi
su ba. Tana tare da Mama, makaranta za ta fara zuwa itama.
Sumayyah ba ta so hakan ba, amma sai ta ga Abba ya fi su hikima da tunani mai kyau. Ina
Hauwa ina iya zama da Madinah? Ita kanta ta san ba wai mugunta ke da Madinah ba, ba boka
ba malam, amma wutsiyar rakumi ce ta yi nesa da kasa, kuma Hauwa ba za ta taba sakewa a
tsakaninsu shida Madinah ba, haka Sarham din ko yadda yake kula Hauwa a yanzu, a gaban
Madinah ba za ta samu hakan ba. Sai ta ga Mama da Abba sun fi su gaskiya, gara Hauwa ta
zauna a tsakaninsu inda za a kula da ita ta kara ilmin zama da Madina koda watarana Allah zai
hadasu zama tare.
A rana Sarham ya kan shigo dakin Sumayya wajen sau uku don kawai ya ga Hauwa, ko
wannan yana faranta ran Sumayyah, amma tun ranar da ya ce ita da Sumayyah ba maraba bai
kara ganin murmushin ta da kalar hakorinta ba. Ko Madina sanda aka kawo ta gidan bai yi
zaryar dakin Sumayyah irin wadda yake yi a yanzu ba saboda Hauwa na fushi dashi kadai.
Yadda ya kasa samun ko murmushi bayan gaisuwa daga bakin Hauwa, duk irin zaman da zai yi
a dakin da irin lallashin da zaiyi mata bazata tank aba abun yana damunsa. Shi ba abun ya
kwantar da kai ta hanyar janyota jikinsa ya lallasheta ba, girman kansa bazai bari ba, kada ta ga
gadon barcinsa tun yanzu.
Ga shi jibi insha Allah za su tashi zuwa Jeddah shi da Sumayyah. Amma har zuwa lokacin ya
kasa samun kan Hauwa.
Ana i-gobe zai koma Jeddah ya zo ya same su ita da Sumayyah a kitchen wai girki suke yi
tare. Amma sumayyah ta kafa mata kujera ta zauna suna hira tana daga zaune tana yanka
mata salad. Ta sha wani tsadadden cotton lace mai laushi ruwan jinin kare riga da zani da aka
kawo kasan lace din aka yi adon wuyan rigar da shi. Sosai Hauwa ta yi wani irin kyau, sai
kyallin amarci take ga daurin kan yayi mata cif-cif a kai, kai ba za ka ce babu idanun ba, don har
mascara Sumayyah ta zizara mata. Ta yi mata daurin kallabi mai tsari.
Sanda Sarham ya sako kai kitchen din ya ji Hauwa na ce wa sumayyah, “Gaskiya in kun tafi
zan yi kewarki Aunty Sumayyah, tunda Aunty Surayyah ba ta zama a gidan nan”.
Sumayyah ta ce, “Ta fi son zaman gidan kakarmu tuntuni, ita ta raineta, amma Mama ta gaya
mun yau za'a dauko miki ‘yar Baffanmu na Shanono mai suna Mardiyyah, yarinyar na da
hankali, na tabbata sai kin fi jin dadin zama da ita fiye da Ya Surayya”.
Kamshin turaren Sarham ne ya sanar da Hauwa shigowarsa kitchen din, sai ta nutsu, ta
daina maganar da ta ke yi. Wayarsa ya mika ma Hauwa ya ce, “Ga nan Inna na miki sallama
sun sauka a kasar Ghana lafiya. Saura ki min kukan naki”.
Ya sa mata wayar cikin hannunta, jikin Hauwa har rawa yake jin muryar Inna. Ta kankame
wayar tana kiran sunan Inna, sai ta sa kuka.
Inna ta ce, “Shi ya sa fa tuntuni na ki yarda likita ya hada ni da ke, na ce sai mun sauka
lafiya. Don na san hakan ce za ta faru.
Likita Sarhamu ya saya mana tikitin da ya kawo mu Kumasi, Hauwa ba ki ga gidanmu ba
masha Allah, yayi ukun namu na Kano, ki yi biyayyar aure Hauwa, ki yi biyayya ga iyayensa da
shi kansa, su ma iyayenki ne. ki gode wa Allah da ya hada ki da surukai na arziki ki zauna lafiya
da kowa. Kin ji Hauwa-Kulu na?".
Hauwa ta gyada kai kamar Inna na kallonta. Inna tace "madallah, ya gaya min a nan gidansu
zai barki tareda Mamansa, za ki fara makarantar jami'a, hakan ya fi min kwanciyar hankali fiye
da kina tare da kishiya alhalin babu idanu a tare da ke. Allah ya zama gatanku, Ya jibinci
al’amarinku. Allah yayi muku albarka”. Malam Bilyaminu ya karbi wayar, shi ma nasiha sosai ya yi mata, kafin su yi sallama har
lokacin Hauwa ba ta bar share hawaye ba.
Mama