Showing 27001 words to 30000 words out of 31076 words
Chapter 10 - HAUWAU KULU Yar Cikin Badala 3 BY TAKORI.pdf
ta shigo kitchen din tana cewa, har yanzu ba su gama girkin ba? Me ya samu Hauwa’u
ta ke kuka haka?”
Sarham ya juya zai fita don shi ma zuciyarsa ta tabu da hawayen Hauwa, har sai da ya
gwammace da ya sani bai hada ta dasu Innar ba.
Da kyar Mama ta samu ta yi shiru, ta saka hannu aka karasa abincin yau har dakinta ta ja
Hauwa, inda suka zauna daga ita sai Hauwa.
Mama ta ce, “Na san ba zan maye miki gurbin Inna ba, amma zan kula da ke kamar yadda
nake kula da nawa yaran.
Na san ana cewa iyayen miji basu da kirki, but I want to be an exception!
Ki bani damar zama Uwa a gareki Hauwa, saboda inason Sarham, inason duk abinda zai
zama kwanciyar hankali a gareshi, ki ga yadda zan zame miki uwar goyo da zani”.
Da ire-iren wadannan kalaman Mama ta lallashe ta suka ci abinci a dinning har da ita.
Sarham na idar da sallar la’asar ya soma hada kayan tafiyarsa. Haka Sumayyah tun jiya ta
hada nata kowannensu jiki a sanyaye, kuma ba don komaijikinsu yayila’asar ba sai don barin
Hauwa da zasu yi ita kadai sai Mama dake wuni a chamber.
Bayan isha ne Sarham ya zo yin sallama officially again da Hauwa. A lokacin ita har ta yi
shirin bacci. Sumayyah na can falo suna kallon talabijin da iyayensu.
Hauwa na karanta addu’ar kwanciya ta ji zaman Sarham a gefen gadon, har jikinsa na gugar
kafafunta. Koda ma can turaren shi da sallamarshi sun riga shi isowa gare ta.
Da wayo da dabara ya kama hannunta ya dora bisa saitin zuciyarsa.
Hauwa na iya jin yadda kirjinsa ke dagawa yana sauka. "To haka fushinki ke azabtar dani
kwana da kwanakin nan Nana Hauwa'u. Ba zan dai iya bayyana miki bane don kin yi kankanta
kuma kinga nan gidanmu ne, banida sakewa a cikinsa".
Wannan kyakkyawan kawaicin na Dr. Sarham har gobe yana tare da shi, ba ya hada girman
iyayensa da girman idanunsu da komai na rayuwarsa.
“Maijidda zan tafi, ba zan samu dan abin da zan ke tunawa da irin wannan lokacin ba? Dana
tafi na bar mata ta HAUWA karkashin kulawar aurena da iyayena ba? Ko da kuwa sallama mai
kyau ta fatar baki ce???
Na san kina fushi da ni, amma exactly ina son sanin laifin da na yi miki Maijidda. Honestly
speaking bansan laifina ba”.
A hankali Hauwa ta janye hannunta daga saman kirjinsa, don ta kasa jure sauyukan da hakan
ke haifar mata cikin jikinta da ruhinta, da kyar ta ce,
“ni ba ka yi min laifin komai ba, hasali ma sai tarin alkhairi ni da iyayena, irin wanda baki ba
zai iya furtawa ba. Sannan babu kalaman da za su isa godewa. Ina rokon Ubangijiya fini
godewa.
Idan har na yi fushi da kai a kan wani abu Yaya Sarham, to ya zama rashin adalci da butulci
irinna an adam, domin ka yi min komai and beyond, da ya cancanci in gode maka ba inyi fushi
da kai ba.
Kawai in na tuna cewa ni ba SO ne ya sa ka aure ni ba, tausayi ne da son kyautata rayuwata
sai in ji komai na duniya ya daina yi min dadi…, burikana na shekara daa shekaru sai inji sun
fita kaina”.
Sarham ya ce cikin daga murya, “Shi tausayin ba SO ne yake yin sanadinsa ba?
Ko kuwa in tausayi ne ashe duk masu lalurar ido na aibitin Murtala na Kano dana yiwa aikin
ido sai in bisu in aure su, bana son ki zan kawo ki cikin gidanmu, in hada ki cikin iyalina
Maijidda?
Bana sonki zan miki takwara da diyar cikina? Tun ma baki zama matata ba?”
Kawai sai Hauwa ta ji kukan dadi ya kwace mata, ta sa tafukanta ta rufe fuskarta tana yinsa
riiiii-riiiii.
A hakan ba ta yi aune ba ta ji numfashin Sarham daf da fuskarta, ya ce, “kin yi kankanta in
tsaya ina gaya miki abinda kike son ji daga gareni. Amma duk da haka ina so ki saka a ranki, ba
wai furta kalmar so ne kadai yake sakawa a yi aure ba, sannan aure ba ya taba samun muhalli
a inda babu so. Ko na ce, ko ban ce ba Maijiddah, ba zan aure ki alhalin ba ki da muhalli ko
yaya a zuciyata ba.
Da wannan nake cewa. Maijiddah ki yi hakuri ki bani lokaci, ki taya ni mu taru ni dake mu
raini wannan burbushin SOn, wanda dalilai da hujjoji suka fi shi karfi, daga ni har ke ba mu san
me gobe za ta haifar ba, Allah daya halicce mu shi kadai ya san sirrin da ya boye a tsakaninmu.
Ina fatan ki taya ni rainon wannan burbushin son, har zuwa sanda zai girma ya zama
mashahuri, abin buga misali beyond our expectations”.
Sarham ya yi shiru yana nazarinta hawaye sun ki tsayawa a idanunta, amma ta kare fuskarta
da tafukanta. Ta sani cikin abubuwan da yake fada duka babu karya, gaskiyar zuciyarsa yake
gaya mata,
“suyi nurturing dan burbushin son tare har ya girma ya zama mashahuri”.
Wanda ita kuma gaskiyar ce ta ke mata daci, ta cewa ita an aure ta ne ba don so ba, sai don
wasu dalilai masu karfi.
Sarham ya fada ya maimaita a kunnenta, ya fada har a bayan idon ta, wanda shi a wurinsa ba
komai ba ne face gaskiyar da ke zuciyarsa kasancewarsa frank person, kuma a wurinsa ya
girma da yin karya, wai don ya farantawa mace.
Bai sani ba, ita wannan gaskiyar bakanta shi ta ke yi a zuciyarta, har gara ya barwa ransa ita,
koda kuwa bai yi mata irin zancen da ta ke son ji din ba kamar na Jamilu mai nuna tsantsar
tsagwaron soyayyah muraran.
Duk yadda Dr. Sarham ya so su yi kyakkyawar sallama abu ya faskara, shi kuma yana jin
nauyi da pride din ya rungumo ta cikin jikinsa ya lallashe ta irin lallashin da yake yiwa Madina in
ya bata mata rai, Madinah ai sa’arsa ce, ta kuma mallaki hankalinta, sannan soyayyar ce zallah
ta hada su. A wautarsa Hauwa-Kulu ba ta san da irin wannan duniyar ba, ba kuma zai koyar da
ita ba balle har a zo gejin da wani abu makamancin nasa da Madinah zai samu mabubbuga
tsakaninsa da Hauwa.
Hauwa za ta ci gaba da cin matsayinta na tudu biyu, na kanwarsa kuma matarsa.
Yayin da Madina ke kan tudun muntsira na masoyiyar romansiyya.
Matsayin da ya bata na kanwa kuwa ai ya fi na masoyiyar soyayya, tunda matsayin kanwar
jini ya ba ta, kuma dai Hausawa suka ce jini ya fi ruwa kauri, wato soyayyar jini da yake yi wa
Hauwa-Kulu kaurin ta yafi na romantic soyayya tasiri, irin wadda ke tsakaninsa da Madinah.
Sallamar dai ta ki dadi tsakanin Sarham da Hauwa, ta ki kula shi, ta ki daina kuka. Ta ki yafe
furucinsa. Har cewa tayi cikin subutar baki.
"Ita da ma ya barta tare da su Inna sun tafi Ghana, ya fi mata alkhairi a kan wanan
kaddararren auren nasa, (wadannan kalaman da ya gama gaya mata yanzu sun mata da
banzan ciwo), na cewa da yayi ta taya shi su yi nurturing ‘yar burbushin soyayyar da yake yi
mata, su girmar da ita tare, har su samu ta zama mashahuriya, wanda in anbi salsala
kalamansa na nufin ba ta da muhallin soyayya a zuciyarsa.
Wannan ya kara tunzura kuka da rikicin Hauwa. Abinda bata sani ba harda na kewar
tafiyarsa.
Abin da ba ya son yi wato rungumar Hauwa ya lallasheta shi ya yi a bisa dole, jikinsa yana
’yar kyarma ya hade jikinsa da nata wuri guda suka dunkule cikin ‘tight hug’. Hauwa tana sakin
kuka a hankali bata daina ba, wani abu tamkar 'electrical shocking' ya bakunci jiki da zuciyar
Hauwa, dana Sarham as well, ta yi kokarin janye jikinta daga cikin nasa, amma yaki saki, ya
tallafo fuskarta da hannu daya, kallon hawayen da ke bilbila daga kyawawan idanunta suna
sauka akan kundukukinta sumul sumul dashi kawai Sarham ke yi, kafin ya kai dan yatsansa
manuni yana kawar dasu one by one daga kan kuncinta, sai kuma yasa fuskarsa a cikin tafukan
Hauwa, wato ya tallafi fuskar shi da hannuwanta biyu ya sanya fuskarsa a tsakiyar tafukanta,
murya na dan rawa kamar yadda ilahirin jikinsa ke shaking and vibrating da ya hadu dana
Hauwa, Sarham ya ce.
“Zan tafi Hauwa-Jiddah, sai nazo, ban san yaushe zan samu dawowa ba. Anyway ki
kula da kanki, ki kula da ibada kin ji?”
Kai kawai ta gyada masa don dai ta samu freedom daga rikon kazar kukun da yayi mata, zai
sumbaci tafukanta da ke kan sajensa, idanunsa a lumshe, Hauwa kamar ta san hakan zata faru
ta yi maza ta janye hannayenta daga sajen fuskarsa, tsigar jikinta na tashi amma a wannan
lokacin ji take bata bukatar irin wannan rarrashin yaje can yayiwa matar so. Duk yadda Sarham yake so sallamar tayi dadi da armashi tsakaninsa da Hauwa, ta yadda
bazai tafi tana ajje dashi da kalamansa a ranta ba, hakan bata samu ba, Hauwa ta dauki fushi
mai ban mamaki wanda shi a iya saninsa bai da dalili. Meye laifi don ya gaya mata hakikanin
gaskiyar da ke zuciyarsa cewa ba soyayya ce ta sa ya aure ta ba? Dalili ne, kuma har gobe zai
kara maimaitawa dalili ne mai kwari da karfi ya yi mujazar auren nasu. Ta tayashi su raini
wannan dalilin har ya koma ingantaccen SO, Shima zai so hakan. Ko don ya zamo mai adalci
tsakanin ta da Madinah. Ya gama gane Hauwa so ta ke ya zauna yana mata karerayin samari
‘yan I love you? Ya karkace kai yana ce mata ‘I can’t do without you, bayan Madinah ce kawai
‘he can't do without’.
A ganinsa ya wuce wannan ‘stage’ din tun a can baya, kuma ba zai iya maimaita shi da
kowacce mace a yanzu ba, bayan Madinah.
Ya tsura ma Hauwa ido daga tsaye, hannayensa biyu zube cikin aljihunsa, ya kasa fita daga
dakin, kalma kuma ta kare masa don ta ki tsaida hawayen idanunta, kukan da bai ga dalilin yin
sa ba, don ba za ta ce don kewarsa ta ke yin shi ba. Don yana da tabbacin Hauwa bata wani
saka shi a ranta ba.
Lokaci na ta tafiya, Hauwa na sheshsheka, wadda ke saka Sarham tsuma daga tsaye, kukan
nata na huda shi sosai, ya kasa fita daga dakin har sai da Sumayyah ta dawo, ba ta san cewa
har lokacin yana dakin ba.
Ta yi niyyar komawa da baya ganin yanayin da suke ciki, ya ce murya na sarkewa “Summy,
kina iya shigowa, wucewa zan yi in kwanta, kin san gobe asubanci za mu yi.
Ina fatan kin sayo ma Maijidda duk abin da za ta bukata din wanda zai yi mata akalla
watanni uku?”
Sumayyah ta idasa shigowa dakin cikin sanyin jiki na yanayi mara dadin data gansu aciki, ta
ce, “Ba abin da ban sayo mata ba, duk da cewa akwai komai a cikin akwatin lefenta, irin su pad,
macleans da listerine na karo mata da sauran tarkacen da babu cikin akwatunan".
Sarham ya soma taku daya, biyu zai bar dakin har zuwa lokacin hannayensa biyu cikin
aljihunsa ya ce, “Maijidda sai mun yi waya, take care”. Da wani irin karfin hali ya bar dakin ba
tareda ya jira jin amsarta ba.
Hauwa ta ce, “Allah ya tsare, Allah ya sauke ku lafiya”.
Wani irin tausayi mai tsanani ya kama Sumayyah ganin cewa, ai Sarham ba irin sallamar da
ya dace a ce ya yi da Hauwa ba kenan, za ta iya rantsewa in Madina zai tafi ya bari a wata kasa
ba irin sallamar da za ta samu kenan ba.
A halittarsa ‘he's very romantic’ ga matar aurensa. Me yasa yake ja baya da Hauwa?
Ta hade rai sosai cikin taya Hauwa kishi, ta yi kwafa ta bi shi da harara yana ficewa.
Sumayyah ta zauna a gefen Hauwa wadda ke gyara filo don ta kwanta, ta ce, “Aunty Hauwa
saboda Allah haka ake sallama da miji ana cin magani ana faman sharar hawaye da sharbe
majina?
Da me zai tuna ki ya yi dokin sake zuwa gare ki?
Hauwa sai fa kin sake lale, in ba haka ba wallahi za su kai ki su baro a ‘yar jiran dakinsu.
Ki tashi ki kwato wa kanki ‘YANCIN SO, dana lura anaso a take miki da gangan, don ni ban
ga soyayya a wannan auren naku ba, ya fi kama da zallar ‘yan uwantaka.
Ni ko yadda na ga ana magana da Madinah ana kashe murya da Ido ba haka na ga ana
magana da ke ba.
Ke ni fa bana karbar ‘defeat’ na a so wata mace ‘yar uwata fiye da yadda za a so ni, don ban
yarda ta fi ni da komai ba, dukkanmu mata ne a halitta, sai dai a ce kowacce da kalar tata fatar.
Amma da irin kissar ta, na rantse mai mata irin Madinah, sai kin yi da gaske kafin ki samu
gurbin da ya dace da ke a hannunsa, don wallahi Madina ta gama shan gaban Bhaiya daga
sama har kasa, har kudu da arewa”.
Hauwa ta ce, “Aunty Sumayyah kenan, ta ya ya zan zo in same shi da matarsa in ce lallai sai
na hada kafada da ita a zuciyarsa?
Nasan irin gwagwarmayar da sukayi tare kafin su kai ga wannan matakin? Kamar zan fi
yarda da nasa ‘perception’ din fiyeda naki, da yace in taya shi mu raini nawa son har in samu ya
girma a zuciyar sa.
Soyayyah ta Allah ce, ba’a mata dole, shi yake sanya ta a zuciyar da ya ga dama, ni ba wani
‘effort’ da zan yi don a so ni, ban da maida al’amurana ga Allah da yin abin da zai amfane ni
duniya da lahira.
Ban shigo rayuwarsu don in hada kafada da ita a komai ba kamar yadda ban taba tsarawa
kaina aure da mai mata ba. na shigo ne ta hanyar kaddarata.
To amma ya zanyi tunda Yayanki Allah ya rubuta min? Kuma shi iyayena suka zaba min? Na
shigo gidansa ne da sunan shi ne mijin da Allah ya zabar min, kaddara kuma ta rubuta min, ba
ruwana da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da matarsa”.
A takaice Sumayyah ta gama gane Hauwa, sune irin matan da ake kira ‘naive and innocent’ a
zamantakewar aure. Ba ta da wani ‘proper experience’ na zama da miji balle da kishiya, don
haka duk yadda za ta kwatanta mata ta tashi tsaye ta kwaci soyayya a zuciyar Sarham ba za ta
gane komai ba. Ita kuma sai inda karfinta ya kare wajen kwato wa Hauwa ‘yancin so, sannu-sannu ba ta
hana zuwa aka ce sai dai a dade ba a je ba. An yi mai wuyar ai tunda har Hauwa ta amshi
sadakin Sarham, shi kuma ya amince ta amsa sunan matarsa, har ya bata dafin Mrs. Shanono.
Babban abin da ya taba zuciyar Sumayyah ko irin dokin nan na amarci babu a tare da shi, a
tsayin zamansu da Hauwa za ta iya tuna ko sau nawa ya kira ta a waya daga sanda ya mallaka
mata wayar hannu. Amma Madinah fa?
Sanda aka kawo ta gidan bata manta ba Sarham baya awanni biyu bai kira ta a waya ba, ga
wani munafikin ‘midnight’ call da suke yi kullum dana yammaci da yake tafiya bakin layinsu yayi
duk don tana cikin gidansu ba tare dashi ba, har sai da suka bar gidan zuwa inda suka fito,
sannan suka samu lafiyar su. Duk wannan ba ya gaban Hauwa, ba don komai ba sai don cewa Sarham bai koya wa
Hauwa soyayya ba, bai bi matakan da suka dace wajen aurenta ba, don ko tadi bai taba zuwa
officially ba, kalmar so ba ta taba giftawa tsakaninsu kamin su yi aure ba, haka ba ya jin wai a
gaba za ta gifta. Duk abin da yake nema a diya mace yana da shi a Madina, don haka aurensa
da Hauwa ba zai daina kiransa da auren dalilai da sanadi masu yawa ba.
A daren Sumayyah ta koya wa Hauwa amfani da abubuwa na tsaftace jiki kamar su mouth
wash da mouth freshner, wanka da bath gel maimakon sabulu. Turarukan lefenta ta jere mata
su a kan madubinta, ta nuna mata yadda za ta dinga amfani da komai har abubuwan toiletries