Showing 15001 words to 18000 words out of 31076 words
Chapter 6 - HAUWAU KULU Yar Cikin Badala 3 BY TAKORI.pdf
Sumayya. Amma likita a yi haka? Yaushe rabon ku gaisa da mutuniyar taka
idan ka zo? Daure ka je ka lallashe ta don Allah, don ni dai tun jiya da uban ya zaunar da ita ya gaya
mata gobe daurin aurenta da kai ta daina kula ni, ta kuma kwana tana kuka.
Hauwa ta ina za ta gane cewa ba yinmu ba ne mu duka, wannan auren yin Allah ne,
alkawarinsa ne tun fil azal ba na kowannenmu ba? Na fi kowa son kada a yi mata aure ka sani".
Idanun Inna suka ciko da kwallah, ta yi shiru don har ta fara jin kewar Hauwa a cikin jikinta,
tun ma kafin a yi batun kai ta gidan miji.
Sarham ya sunkuyar da kai kasa yana jin wani iri a ransa da ganin hawayen Inna. Ya san irin
shakuwar da ke tsakaninta da Hauwa. He can feel for her, na irin kewar Hauwa da za ta yi,
amma hakan ne kadai abin da zai yi ya zama maslaha akan rayuwar HAUWA-KULU da ta
iyayenta, hakanne kuma kadai abinda zai dorar da dangantakar su, musamman da aka yi sa'a
ya lura Sumayyah na son Hauwa, ya tabbatar za ta taya shi kula da ita, kai dai bar Sumayyah
da ra'ayin ta na rikau akan abin da ranta yake so da wanda ba ya so.
Ya ce, Insha Allah Inna ki sa a ranki ko kin koma Ghana Hauwa na hannunku ne, bana jin
Mamana, bana kuma jinsu Sumayyah, za ta taya mu kula da Maijidda. Adduarki za ta bi
Maijidda duk inda ta ke.
Don Allah don Annabi ki cire damuwar wai Hauwa wulakanta za ta yi a hannun mijinta,
wannan shi ne babban dalilina na auren Hauwa, don in tsare mata mutuncinta da martabarta in
kuma kula da ita, rayuwar ta bakidaya da ilminta.
Ba ni da haufi a kan kowa nawa. Babu Mai cutar da HAUWA cikinsu, Inna za mu rike Hauwa
ne da amana da amincewar Ubangiji kamar tana gaban ku".
Sumayyah ta shigo tana cewa, "Bhaiya, wannan lallashin fa sai kai, Hauwa ta ki yin shiru duk
irin lallashin dana yi mata".
Ta zauna a kusa da Inna.
Inna ta ce, "Je ka ka ji Sarhamu, lallashe ta, mace tafi son lallashin mijinta sama da na kowa, ta
ci albarkacina ba don halinta ba".
'Yar dariya Dr. Sarham ya yi, kamar Inna ta san tun ranar da ya ganta suna tadin soyayya ita
da Jamilu yake jin haushinta, ya kuma fita sabgarta bakidaya, babu gaira babu dalili ya tsani
ganin da yayi mata da Jamilu. Ko ta gaisheshi sai ya ga dama yake amsawa.
Amma yau ji yake duk haushin nata da yake ji akan Jamilu ya kau. Sosai yake jin tausayinta
don ya san rabuwa da Inna ga Hauwa ba wasa ba.
Sallamar Sarham a dakinta ya sa ta wani irin saurin dagowa, kamar a firgice. Ta watsa masa
manyan idanunta harrrr! Kamar tana ganinsa da suke jike jagab da hawaye.
Dr. Sarham ya tsaya 'standstill' daga bakin kofa hannayensa duka biyu zube cikin aljihunshi,
as ango as he is, ko makiyinsa ya san ya yi kyau har ya gaji kamar ranar farkon aurensa, ya
koma kamar yaro matashi dan 27 kai ba za ka taba cewa ya ajiye hamshakiyar mace kamar Dr.
Madinah Sorondinki a gida, har da albarkar 'ya ba. Hauwa tana iya jin idanun Sarham na bin
jinin jikinta, don haka ta kasa jure kallon hararar da ta sa gululun idanunta yi masa, ta sunkuyar
da su kasa. Ta kuma lumshe su duk a lokaci guda.
Sarham ya tako cikin dakin ya zauna a kujera kwalli daya da ke dakin, karonsa na farko da
shigowa dakin Hauwa, tun dawowarsu sabon gidan. Saidai ya dan leko daga kofar daki I zai
wuce gida.
Cikin rishin kuka Hauwa ta ga ya dace ta gaida Dr. Sarham, ko da kasancewar mugun
haushinsa ta ke ji yanzu, nayi mata katsalandan cikin rayuwa, amma Dr. Sarham na da muhallin
gaisuwa daga gare ta (no matter what), wato cikin kowanne yanayi. Hauwa ta sa habar hijabinta
ta share fuskarta, ta kuma bar fuskar a cikin tafukanta da hijabin nata ta ce (kamar wadda aka
yiwa dole sai ta gaishe shin), “Masa'ul Noor”.
Sarham bai yi gaggawar amsawa ba, don ya raina ‘yar gaisuwar tata mai kama data rowa,
ganin irin kukan da ta ke yi kuma, bayan furta gaisuwar ya san takura kanta tayi ta furta ta
tamkar kuma ta kwace abarta ta mayar cikinta, ya yi kwafa cikin jin wani maqaqi a ransa na
rashin son da ya lura Hauwa na yi masa, ya ce, "Shin wannan kukan na mene ne Maijidda? Tsakani da Allah auren da ni ne ba ki so ko? Na
tabbata da wancan yaron dan polo ne yau Inna ta aura miki, da yanzu kin takarkare kina shafa
hoda don tarar zuwansa matsayinsa na angonki.
Amma da yake nine dube ki don Allah, a haka wai amarya ce mai shirin tafiya dakin miji, da
wani zurmemen hijabi kamar mai zuwa fadar limamin jihar Kano".
Hauwa ta tale baki ba ta ce komai ba, ya ce, "To ya ishe ni kukan nan haka Malama, ki tashi
ki yi sallah raka'a biyu ki roka mana duk wasu alkhairai na duniya da lahira da zaman lafiya, har
da jikoki masu yawa da albarka ga Inna da Malam".
Ai Hauwa ba ta san sanda ta sake barkewa da sabon kuka ba. Ya dai tabbata ta zama matar
likitan nata yau, ba mafarki ta ke yi ba, ba kuma dan uwanta Jamilu data ke so aka aura mata
ba. Dr. Sarham ne.
Hauwa ta yi kukanta mai isarta ta goge ido, Sarham da ya lura ta gaji da kukan sai ya mika
mata farin hankicinsa cikin tafin hannunta yana fadin.
“Ki yi kuka ba zan hana ki ba, don dole ne a wurin mai uwa irin Inna yayi kuka, in aka ce ga
ranar rabuwarsu ta zo. Amma ki sa a ranki ba hannun makiyanta ta kai ki ba, ko inda ake son ta
da tozarta da wulakanta kamar yadda ke ki ka fi so (hannun su Zakari).
Na san duk wannan kukan don ba shi ne mijin ba, ni da ba ki so din ni Allah ya baiwa
HAUWA, sai inga mai kwace mini, don haka ga hankici na baki, ki yi kukan da zai jika shi jagab,
ki gama ki fara shirya goya 'ya'ya na, ki haifa mun su da yawa kamar dozen su zama kannen
Waheedah takwarar ki, kin ji ko Maijidda?” Daga haka ya koma lallashinta, da kalamai masu taushi da alkawarin bai aureta don ya
wulakantata ba, bai aureta don y araba ta da farin ciki ba, bai aureta don ya raba ta da iyayenta
ba, lallashi dai irin na namiji mai wayo, ilmi, wayewa da dabarar a saurareshi, har ya samu
Hauwa ta yi shiru da kukan. Ta ki karbar hancikin da yake bata, amma kuma ta gyada kai kan
nafilar da ya umarce ta da yi, sannan ya yi mata sallama kan zai koma gida a shirya mata dakin
da za ta zauna kafin a gama yi mata visar tafiya tare da shi da Sumayyah zuwa Jeddah.
Da ya kai bakin kofa sai ya juyo yace "ki cigaba da kwalliya, da shafa hodar dana taba gani
kinayi a asibiti, tayi min kyau ranar, ina son gayu fa ni Maijidda dan gayu ne, matata ma ‘yar
gayu ce sai kin shirya da zama 'yar gaye". Yayi murmushi cikin kallonta, ta saki baki da kunne
tana jin sa, sannan ya fita da murmushin a fuskarsa. A ranta tace ba hodar da zan shafa, inna
gumbuda tayi yawa ba lallai a gayamin ba. Karshenta ma sai dai yayi min dariya shi da Inna.
Allah yasa matar tasa balarabiyace karewa kenan. Ji take da dai Jamilu ne da kuwa tayi duk
abinda yake so ba hoda kadai ba.
Tayi maza tayi istigfari akan wannan tunanin don ta san yanzu akwai igiyar aure a kanta.
***** ****** ******
MADINAH
Bayan Usman ya dauko ta. A kan hanyarsu ta zuwa gidan iyayenta daga filin jirgi kawai ta samu
kanta da canza shawara. Ta ce a ranta macen kwarai ba ta yaji. Tsayawa ta ke ta fuskanci
‘challenges’ din gidanta dana mijinta ‘in general’ komai tsaurinsu in masu gyaruwa ne ta gyara.
Zuciya mafi rinjaye na gaya mata Sarham wasa yake yi, domin ba zai taba iya hada ta da wata
mace a zuciyarsa da duniyarsa ba. Da wannan tunanin Dr. Madina ta canza shawara, ta ce da Usman ya wuce da ita gidanta ba
gidansu ba. Tana gaya wa kanta wataqila akwai ta inda ta ragi Sarham tunda har ya fara yi
mata wasan son karin aure.
Abin da ya kamata ta yi shi ne ta tsaya ta binciki ta ina wannan gibin nata yake, ta yi
gaggawar cike shi. Ta ga dai ko aiki bata yi duk don ta samu lokacin sa da kyau shi da diyarsu.
Ba kuma za ta gane ta ina ta rage shi din ba idan ba ya bude baki ya gaya mata ba.
Ta sa a ranta za ta yi magana ta gemu da Sarham din idan ya dawo, ta ji ta ina take kuskure
shi da har tunanin karin aure ya yi crossing mind dinsa, dole ruwa ba ya tsami banza.
Da wannan Madinah ta baiwa kanta nutsuwa ta shiga gidanta ta bude ta soma gyare-gyare,
bayan sun yi sallama da Yayanta Usman da cewa ya gayawa Hajjah Ramlah sai wajen gobe za
ta shigo gidansu. Ta kawo sakonnin Hajjah Ramlah da ta taho da su daga Kano ta ba shi.
Amma me? Bayan ta manta da komai ta ci gaba da harkokinta cikin gidanta tana share-share
da goge-goge, tana kuma kula da Waheedah, sai ga wayar kanwar Sarham wato Surayyah ta
shigo mata.
Madinah ta amsa wayar Surayyah tana tsokanarta da amaryar Engnr. ta Aliyu ba da kanki a
sare".
Tun daga nan Surayyah ta fahimci Madina ba ta san me ake ciki ba, don muryarta ras! Babu
alamun damuwa a cikinta. Surayyah ta ce, cikin damuwa.
"Aunty Madinah kina ina?"
Madina ta amsa, "Na koma Jeddah Surayyah".
Surayyah ta ce, "Ga dukkan alamu ba ki san me ke faruwa da ke ba, kuma ni ba zan iya shiru
ba, duk da an ce babu ruwana.
Ta nisa. "Aunty Madina ba zan taba manta tarin alkhairinki gare ni ba, har ma da wannan
butulalliyar Allahn Sumayyah, hakika kin mana alkhairi mai yawa don haka ni ba zan ga inda
za’a cuce ki in yi shiru ba.
Gaban Madina ya yi mugun faduwa, amma haka ta daure ta ci gaba da sauraron Surayyah
ba ta katse mata hanzari ba, duk da a tsarinta ba a kawo mata gulma, kamar yadda ba ta zama
ta yi gulmar wani ita ma, amma yau ta kasa tsayar da Surayyah sabida curiosity da ya ziyarceta
irin na dan Adam. "Yaya Doctor ya yi aure!".
Wadannan kalamai sune 'shock of her life' duk da cewa ta yi anticipating dinsu ko
makamantansu, bayan zuciyarta ta gama karyata su daga bakin da ta tabbatar bai taba yi mata
karya ba wato (bakin Sarham din da kansa).
Surayyah na jin irin numfashin da Madinah ke yi, sai taji tsoro, amma haka ta ci gaba da
cewa, "Aunty Madinah, I am sorry to say, kuma yar talakawa fa ya dauko miki irin ‘yan cikin
Badalar nan ‘yan tallan abinci, makauniya, almajira, basu da cin yau basu da na gobe sai
abinda ya dauko ya basu, don talauci ubansu ya gudu ya barsu shekaru bakwai. Suka koma
sayar da abinci a Tasha. Ko gidan zama ba su dashi, shi yake ciyar da su tun da jimawa.......".
maganganu dai na gulma rututu
wadanda Madinah ba ta iya ta karasa ji ba ta saki wayarta a kasa ta rabe gida biyu.
Surayyah a can bangarenta ta ce, "Allah ya bi miki hakkinki Aunty Madinah, karshen
wulakanci da kaskanci Yaya Doctor ya gama yi miki".
Mama ta gama shirin karbar amarya a dakin Sumayyah inda Madinah ma a nan aka karbe ta,
don Malam Bilyaminu ya ce, ko kare kada a gayyato masa don biki, ya aurar da Hauwa ne ba
don ya gaya wa duniya ba, sai don cika umarnin ubangiji na in 'ya'yanku sun kai munzali ku
aurar da su. Ya kuma gaya wa Abba Prof. duk wani abu na kayan daki da ake yi wa ya mace a bashi
muhalli, zai yi wa Hauwa. Sai Abba ya ce, Sarham bai gama ginin gidansa na Kano ba har yau,
za ta zauna tare da su ne kafin wucewarsu Jeddah. Sai dai ya bari sai can gaba, wato ranar da
suka dawo kasar Kano da zama gaba daya sai ya saka mata kayan dakin. Amma hakika wannan abu da Malam Bilyaminu ya fada na sayawa Hauwa kayan aure ya
kara sayawa Hauwa mutunci a idon Abban da Mama, shi abu daya ke bata masa rai, in ya tuna
Hauwa da uwarta sun sayar da abinci a tasha. Wannan kalma ta ‘yar tasha ya kasa daina ganin
su Hauwa da ita. A cewar Sarham hakan yana cikin kaddarar su, sannan ba kowa da ya zauna
ko yake sana'a a Tasha bane mutumin banza. Duk da haka dawowar Malam Bilyaminu a daidai
wannan lokacin ya yi wa aibunsu wanka da soso da sabulu a idanun Farfesan.
Mama ta shirya masu zuwa taho da Hauwa kanwarta dake aure a Kaduna da kanwar Prof.
Daga Shanono, amma Malam Bilyaminu ya ce don Allah su koma, Sarham ya zo ya tafi da
matarsa da kansa shi wannan ne policy dinsa. Ba ya son kowacce irin bidi'a a auren
Hauwa-Kulu albarka kawai yake nema mata. Bai ki ba bayan kai ta gidan in sun so su yi walima kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya
koyar.
Daren yau ne ya kama Sarham zai tafi dauko Hauwa, tun safe yake gwada wayar Madinah ta
ki shiga. Yana so ne yaji lafiyarta ya kuma gaya mata komai ya tabbata kafin Hauwa ta tare, ya
kuma tabbatar yayi mata lallashin da za ta fahimce shi a kan aurensa da Hauwa. (Bai san tuni
Surayyah ta kwaba masa aiki ba). Duk da haka Madina ba ta bar gidanta ba, saboda a wurin ta karshen tozarta aure shi ne
"yaji". A wurinta yaji ga macen aure wadda ta san abin da ta ke yi zubewar aji da zubewar kima
ne.
Ita kuma Madina duk abin da zai zubar mata da aji da kima da martaba tana gudunsa a sittin,
exactly yadda ta ke kallon auren da Sarham ya yi yanzu da makauniya ‘yar tasha, ‘yar talakawa
ya zubar mata da aji, ya zubar mata da kima ya kaskantata ya wulakantata a idon tsararrakinta
da duniya bakidaya. A duniyar Subhana ta san tana son Dr. Sarham Abbas, tana kuma da wani irin kishi mai
radadi a kansa, wanda hankali da tunani ba zai dauka ba, amma yau ji ta ke SON bakidayansa
yana narkewa, yana zagwanyewa yana dalala kamar narkakkiyar dalma a kasa yana bin rariya.
Sai dai abu daya da ba zata yarda ta taba yi ba a rayuwar aurenta shi ne, "YAJI". Za ta jure ta
zauna har Sarham ya dawo, in ya so in ta tabbatar da abin da Surayyah ta labarta mata a kan
matar da ya aura daga bakinsa, to fa zamanta da Sarham ya kare. Ita ba ta saurin yanke
hukunci a kan abin da ba ta da hujja kuma bata tabbatar ba. Wato dai bata yanke hukuncin one
sided (daga bangare daya).
Wane irin makauniya irin yaran cikin BADALAR Kano da ke sayar da abinci a Tasha ana
zaune kalau, miskiniya ce kenan ko Musaka? Duk ba wannan ba Makauniya fa? Shi kuma daga
likitancin ido sai ya bige da auren makauniya, ‘yar talakawa? Shi kuwa Sarham me yake nema
a rayuwarsa wannan faduwa kasa har yaushe??
Madinah ji take kamar ta dora hannu aka tayi ta kururuwa ita kadai. Sau tari tana jin ana
fadin. Wani namijin in ya tashi karo aure in kayi duba da irin matar da yake da ita a gida, sai ka
dauka hau ce ta hau kansa.
Madina ta yarda da Sarham matukar yarda, ta amince da shi da soyayyarsa iyakar
amincewa, don haka wannan auren nasa da aka kara maimaita mata ya zama 'shock of her life'
kuma in har Sarham ya tabbatar mata da hakan da bakinsa, to fa ta taho daga rakiyar duk wani
Da namiji, ba Sarham kadai ba.