Showing 30001 words to 31076 words out of 31076 words
Chapter 11 - HAUWAU KULU Yar Cikin Badala 3 BY TAKORI.pdf
din duk ta koya mata amfani da su. Tun a daren suka yi sallama da Sumayya cike da kewar juna, haka Hauwa ta kwana cikin
sake-saken yadda rayuwa za ta kasance mata a gidan iyayen mijinta babu mijin, babu Sumayya
mai debe mata kewar Inna.
Sarham da kanwarsa Sumayyah, sun tashi zuwa Jiddah a washegari. Gida ya rage daga
Mama sai surukarta Hauwa da yarinyar da aka dauko mata daga Shanono.
Hauwa na jin dadin zama da Mardiyya, nan kasan kafafun gadonta Mardiyya ke saka
katifarta ta kwanta. Duk wani motsi da Hauwa ta yi za ka ga Mardiyya ta mike tana tambaya,
“Aunty Hauwa kina son wani abu ne? ko bandaki za ki shiga in taimaka miki?”
In bandaki za ta shiga sai ta ce, “Ai ba sai kin raka ni ba Mardiyya, ko ma barcinki zan iya kai
kaina”.
Mama koyaushe in ta dawo aiki sai ta fara shigowa dakin da Hauwa ta ke, ta zauna su yi hira,
tun Hauwa ba ta sakewa har ta gane Mama fa ba ta surukuta da ita. In Abba Prof ya dawo
kullum Mama cewa ta ke, Mardiyya ta fito da Antinta falo ta ji labaran tara, su daina kulewa a
daki su kadai. Surayyah tuni ta bar musu gidan, ta koma gidan Hajiyar Gadon Kaya.
A kullum abincin Hauwa na musamman Mama ke sa wa a shirya mata, kuma sai ta zabi abin
da za a dafa mata. Mama ba ta dawowa gida ba tare da ta kawo wa Hauwa tsaraba ba,
musamman da ta gane tana da son cin gugguru (popcorn) kullum sai ta sawo mata shi.
Kafin ka ce me ye wannan, wata irin shakuwa irin ta Uwa da Da mai ban mamaki da ban
sha'awa ta samu muhalli tsakanin Mama Mai Shari'a da surukarta Hauwa.
A wasu lokutan Barr. Haj. Maimuna Shanono in tana hira da kawayenta na jiki su Barr.
Hannatu a chamber dinsu, za ka ji Mama tana fadin musu, “ita kam yanzu ne ta san Sarham ya
yi aure daidai da shi. Inda zai fada aji, inda ba'a raina arzikin shi ba. Yanzu ne ta san ta yi
surukar da in ta ce ta yi kaza za ta yi ba girman kai ba dagun kai, ita yanzu ta san ta yi suruka
da take da ‘high influence’ a kanta".
Kuma in za ka tsire ta ka ce meye aibun Madinah Sorondinki, kome tayi mata da har gobe
bata bata yardarta da amincewarta 100% ba, kamar yadda ta bai wa Hauwa-Kulu farad daya,
zaka tarar Mama ba ta da amsar ba ka.
Bata da wata hujja kwakkwara ta son Hauwa fiyeda Madina. Daidai gwargwado Madina ba ta
gaza da su ba, ko bata musu biyayya ko tana da wani nakasu da za'a iya bugun gaba a soketa
da shi ba, illa hakan halin Dan Adam yake musamman a inda soyayyar miji ta kasa boyuwa
akan mace, wasu iyayen mijin nada halin dan Adamtaka in ‘ya’yansu na mutuwar son matansu,
to su kuma za ka samu ko me matar za ta yi ba zai burge su ba. Kuma a kasan ransu suna jin
zafinta, babu gaira babu dalili.
To hakan ce tsakanin Mama da Madina. Koda bata taba nuna mata Hakan ba. Balle dama
Madina wadda tun asali tana da fenti a idon Mama na wulakancin da mahaifinta ya yi musu duk
da cewa (eventually) ya yi (repenting), ita kam har gobe in ta tuna sai da ya fara bada ta ga
maikudi irin su, ya rasa shi, sannan ya nemo Sarham ya manna masa abin yana ragewa
Madina tagomashi a idanunta.
Musamman data san cewa auren da Madina tayi bai rage komai daga soyayyar da Sarham
ke mata ba.
Maganar auren Sarham da Hauwa kuwa, Mama ta dade da sakawa a ranta, watarana zai
faru. Duk da Sarham ya yi ittifakin ba son Hauwa yake ba a gabanta, amma ita ta dade da sanin
akwai babbar kaddara a tsakaninsu. Tana biye da al’amarinsu tun daga ranar da ya yi wa
Hauwa aikin ido, har zuwa yau. Mama ta yarda ta zama uwar Hauwa, tunda har Sarham ya rabo ta da uwa da ubanta,
alhalin babu idanu a tare da ita. Tana lura da cewa, tun tafiyarsa bai kara kiran Hauwa a waya
ba, sai dai ita in ya kira ta ya ce a gaida masa Maijidda.
Wannan abu yana yi mata ba dadi, ita kuma ba ta taba ce masa don me ba ya kiran Hauwa
‘direct’ tunda yana da lambarta ba? Ko musuluci bai yarda da wannan ba, kuma hakan tauye
‘yanci ne. Ta kwana da sanin Sarham ba zai iya kiran wata mace alhalin yana tare da Madinah
ba. Abin da ba za ta taba kira tsoro ba, don a policy din Sarham ba shi da tsoro ba shi da shakka
tun yana dan karamin sa, don haka ba ta san dalilinsa na kin kiran Hauwa ba, bata masa fatan
soyayyar da yake yi wa Madina ta kai ga matakin tsoro, tunda ai yana fita, zai iya kiranta in ya
fita in ma idon matarsa yake gudu, bata fatan soyayyarsa da Madinah ta yi yawan da za ta saka
shi zabar tashi ranar lahira da shanyayyen barin jiki na tauyewa Hauwa hakki.
A karshe ta gode wa Abba Prof. da bai bari Sarham ya tafi da Hauwa Jiddah ba, hakika da ta
ga rainin wayo, da rashin adalci, amma ai ba za'a dauwama a haka ba tunda Hauwa-Kulu, ko
da ta ke makauniya, aurenta ake kamar yadda ake auren kowa.
Lokaci Mama ta bashi don ganin kamun ludayinsa a kan auren Hauwa, don ba zai yiwu ya
auri ‘yar mutane a gaban shaidu ya bata sadaki sanan ya maida ita kanwarsa ta jini Sumayyah
ba.
(Da a ce Mama ta san halin da Sarham ke ciki tun bayan komawarsa Jiddah hakika da ta
tausaya wa masa, data ji tausayin tilon dan nata namiji daya tamkar da maza dubu, wato (Likita
SARHAM)!!!