Showing 18001 words to 21000 words out of 31076 words

Chapter 7 - HAUWAU KULU Yar Cikin Badala 3 BY TAKORI.pdf

Maganar tafiya daga gidansa alhalin bai sake ta ba, ba shi ne solution ba, gara ta zauna su
fuskanci juna idan ya dawo, don ta san matsayinta. Ta kuma tambayeshi hakikanin menene
flaws dinta data cancanci wannan tozarcin.
Yanzu kam bayan ta ji irin matar da ya aura din, sai ta ki yarda wai gazawarta ta wani
bangare ne ya sa Sarham yin wannan auren, za ta fi yarda in ya ce kawai ya daina sonta ne
(short and simple).
Amma shin anya soyayya irin tasu wadda aka yi shekaru goma cur ana fafutukarta ta kuma
samu actualizing ba jimawa don ko shekaru biyu ba su rufa da aure ba, za ta iya karewa a
farau-farau din banza irin haka cikin dan lokaci???
Yanzu dai ta yarda ba gazawarta ba ce, ba kuma aibinta bane ko wani gap data bari, duba da
irin matar da aka ce ya auro din.
Madinah a wannan gabar, ta kasa jure wani irin bakin ciki da ke cin ranta, tun farkon maganar
bata ji kuka yazo mata ba sai yau, ta kifa fuska cikin tafukanta ta soma rera kuka na sarewa a
kan mijin nata, dama duk wani da namiji mai numfashi, tana yi tana karyata soyayyar maza ko
wacce iri ce, a yau Madina ta la'anci duk wata yarda da soyayyar da ta yi wa Sarham tsayin
shekaru goma sha daya a baya.
**** **** ****
Maimakon irin shigar da angwaye ke yi ta manyan kaya ranar tarewar amarensu, abokai kuma
su rako su dakin amarya. Dr. Sarham nasa salon daban ne, don wata farar T. Shirt ya saka
samfurin 'Burberry' da bakin wandon 'Givenchy Jeans' mai kauri matuka, ya kuma taje sumar
kansa sosai ya shafe ta da man da yake amfani da shi na musamman (Argan Oil for men),
kowa ya san a dabi’arsa dama bai cika yin askin sumar kan shi ba sai tara suma da kykkyawan
sajen (man’s pride) da baya gajiya da kula dasu. Sai kamshin turarensa na (Oud Abyad) da
‘Sandalia' na musamman yakeyi.
Dakin Mama ya fara zuwa ya same su ita da Sumayyah suna shirye-shiryensu su ma, ya ce,
"Mama zan je in zo da ita yanzu, ina fatan Sumayyah ta gama gyaran dakin?"
Mama Mai Shari'a ta daga kai ta dubeshi, sai ta ga Baban na Waheedah ya koma mata yaro
sabon jini, kuruciyar sa ta karu, kamar yanzu ne aka daura masa auren fari, wani boyayyen
annuri ya fito sarari ya kayatar da idanun sa.
Da karsashi Sumayyah ta amsa,
"Komai fa ya kammala Bhaiya, har abincin da za ku ci na dare na kammala, na gasa maka
kazar amarci da wani irin ‘french grill’ mai ruwa-ruwa dana koya online, sai jiran isowar kanwata,
amarya, Hawwa-Jiddan Bhaiya, Yaya Sarham mai Jidda mai Madinah, bari in je in turare dakin

da turaren 'hawii' yanzun nan”.
Murmushi kawai Sarham ya yi yana mamakin Sumayyah, in ya tuna tsiyar da ta shuka masa
lokacin auren Madinah.
Mama ta ce, "Ai Sumayyah ko ita aka auro wa Hauwa sai haka, yau ko na minta daya ba ta
zauna ta huta ba, duk abin da ta san Hauwa'u za ta bukata ta nemo ta ajiye mata a dakin nan
har brush da maclean ba ta manta ba.
Sarham ya fadada murmushin sa zuwa dariya, ya ce, "Summy, mai abun mamaki, wanda
ranta yake so ya ji dadinsa!".
Duk zancen nan da suke yi Surayyah da ke toilet din Mama tana jinsu, waya ta ke da
Madinah a bandakin tana gaya mata cikin takaici mai yawa "Anti Madinah yanzu Yaya Doctor
zai je ya dauko makauniyar nan fa, anya kin dauki matakin da ya dace? Ga ‘yar banzar yarinyar
nan Sumayyah sai rawar kafa ta ke kamar ta fi shi son auren ma". Madina ta kasa shiru wannan karon sabida a rayuwarta ta tsani gulma da daukar zance, ta
kuma fahimci Surayyah halinta kenan, ta ce, "Surayyah please, in kin sake kirana mu yi magana
wadda ta shafe mu, kada ki kara yi min zancen auren Sarham ko na yarinyar da ya aura, I may
be intolerant, besides, is none of my business, in ba so kike kuma in samu ‘heart attack’ ba. Ni wannan ba taimako na kike yi ba cutar da ni kikeyi a zuciyata da kwakwalwa ta".
Daga yadda ta ke maganar muryarta na daukewa sama-sama kamar mai fama da ciwon
asthma, sai da Surayyah ta ji tsoro. Madina ta kashe wayarta daga nata bangaren, ta koma ta
jingina da fuskar gadonta, ta lumshe ido tana ambaton sunan Ubangiji da neman daukinsa, na
sanyayawa da tausasawa a gareta cewa ta ke a fili, idanu a rufe, hannu dafe da kirji; "Ya Salamu-Sallim".

**** **** ****
A nan layin shiga gidan Malam Bilyaminu ango Sarham ya kashe motarsa, ya dan zauna a
ciki kadan na wasu mintuna dafe da sitiyari yana karanto addu'a a zuciyar sa, addu'ar Allah ya
sa aurensa da Hauwa shi ne alkhairin da kullum yake nema a wajen Ubangijin sa da neman
zabinSa da yayi ta yi kafin ya furta amincewa da yin sa. Ya kuma bashi ikon yi mata adalci
tsakanin ta da matarsa.
Ya fito ya shiga gidan da kyakkyawar sallama a bakinsa da murya mai karsashi, Malam ne ya
amsa daga dakinsa, ya kuma fito suka hade su duka a falon Inna.
A lokacin Inna tana can dakin Hauwa tana tsaye a kanta tana fama da ita a kan shiryawa da
sabuwar atamfar da ta dinka mata, dinkin doguwar riga akayi mata daidai jikinta. Hauwa ta kasa
tsaida hawayenta haka ita ma Inna amma duk da haka bata fasa karfafa kanta tana lallashinta
ba, lallashi irin wanda ba ta taba yi mata ba. Babbar damuwar Hauwa ita ce, jin cewa nan da
kwanaki uku Babanta da Innarta za su koma kasar Ghana su barta a Kano hannun mijinta,
wannan abu shi ya fi komai daga hankalin Hauwa fiyeda auren da ake ikirarin an yi mata da
likita Sarham.
Malam ya leko dakin Hauwa yana fadin, "Har yanzu ba a gama shiryawar ba ne? Ko
bankwanan bai kare ba tsakanin Hauwa da Innar ta? Naga dai jiya baku rintsa ba kuna hirar
bankwana. Har gashi angon ya iso, tun dazu yana jiranku".
A lokacin Inna ta yi wa Hauwa lullubi da sabon mayafin da ya shiga da atamfarta ta fesa mata
turaren Binta Sudan, ta kamo hannunta suka fito falon. Inna da kanta ta saka hannun Hauwa

cikin na Sarham tana faman kokawa da hawayenta.
Addu'a ta musamman Malam Bilyaminu ya karanto duk suka shafa, ya baiwa Sarham
amanar Hauwa kamar yadda ya baiwa Abba Prof, Inna kuma da aka zo jin ta bakinta cewa ta yi
ita ta san in dai Sarham ne ba sai ta jaddada masa amanar Hauwa ba, ita Hauwan ta ke baiwa
amanar danta (SARHAM), don ta santa wani lokacin hutsuwa ce, musamman (in ka nemi raina
mata wayo), tace ta yi masa biyayya fiye da wacce take yi musu don yanzu aljannarta ta tashi
daga yardarsu su iyayenta ta koma kasan dugadugansa.
Kan Sarham a kasa, hannun Hauwa cikin nasa, ya rike hannun sosai da riko mai karfi, suka
fito daga falon Inna, Malam da Inna suka raka su har bakin motarshi ya budewa Hauwa ta shiga
gidan gaba, ya maida kofar ya rufe, shima ya zaga ya shiga mazauninsa ya tada motar a
hankali suka bar BADALAR KOFAR NA'ISA. Hauwa na jin 'feeling' na rabuwa da mahaifarta, inda ta rayu shekarun rayuwarta gabadaya,
ba’a jikinta kadai take jin kewar BADALA ba, har a cikin zuciya da ruhinta take jin kewar.
**** **** ****
Suna tafe a hanya jin kukan na Hauwa ya ki karewa Kuma yana taba masa zuciya ba kadan
ba. Dr. Sarham sai ya samu gefen titi ya tsaya ya kashe motar, ya kuma yi sama da glassan
motar wadanda dama tinted glasses ne.
Hauwa jin ya tsaya tsayin lokaci ya kashe mota kuma ko tari bai yi ba, bayan kashe motar da
yayi, sai ta rage sautin kukan nata, har daga karshe ta yi shiru gaba daya tana ajiyar zuciya.
Sarham yayi kyacci, ya ce, "Maijiddah kin san me? Wannan kukan da ki ke ta yi mun yau, da
wanda aka ce kin kwana yi, yafi min kama da irin kukan nan na an miki auren dole.
Ni na tabbata da Dan Polonki aka aura miki ya daukoki zai kaiki gidan Baba Zakari, ba za ki
yi ta yin wannan banzan kukan ba.
A'ah, inada yaqinin farinciki zakiyi tayi na kin auri wanda kikeso yake son ki, wanda har
masoyanki sai sun taya ki wannan farin cikin. Sai gashi ni din da ba ki so kuma kike kullace dani
sabida wani dalili naki na rashin Tawhidi ni Allah Ubangiji ya ga damar baiwa.
Don haka ki ci gaba da kuka son ranki Maijidda, ina taya ki bakin cikin auren tsoho, mai mata,
har da 'ya, ba yaro dan Polo sabon jini ba".
Hauwa ta dauke numfashi, ta daina hadiyar zuciyan da take yi don tana iya karantar irin
(bitterness) din da ke cikin muryarsa akan Jamilu da halin da ya shiga a sanadin kukan nata a
sautin cool muryarsa. Me ya sa yake son yi mata wannan fassarar da wannan habaicin ne
kullum a kan Yaya Jamilu? A ganinta koma dai yaya ne, zancen ta da Jamilu ne koma waye) ya
wuce, tunda an riga an daura musu aure itada shi, ai zance ya zama past, tana so ko ba ta so,
sunanta matar Sarham yanzu, bai kamata ya yi ta yi mata gori, yarfe da mita a kan Jamilu ba.
"Ka yi hakuri". Kawai ta iya cewa cikin dusassar muryar data gaji da kuka.
Ganin kamar ban hakurin nata bai gamsar ba, domin har zuwa lokacin bai ja motar sun
cigaba da tafiya ba, ta cigaba da sauke ajiyar zuciya sannan ta dora da.
"kayi hakuri don Allah. Na daina kukan Yaya Sarham, kuma ba don shi nake yin kuka ba, a'a,
don kewar Malam da Inna ne.
Kada ka manta fa kasar zasu bari gabadaya babu ni".
Ta fada cikin rauni, da jin kamar cewa ta zama ita kadai kwal ta rage a fadin duniya tunda babu
Inna jagorarta, wadda itace garkuwarta, karfinta, sannan kwarin gwiwarta a kan komai tun
bayan da ta rasa idanunta.

Sannan babu Baba a tare da ita yanzu, wanda shima ta kwashe shekaru ba tareda shi ba,
bata mori komai na dawowarsa ba an yi mata aure, wannan tunanin ya sa wani sabon kukan ya
dawo mata ta soma kokawa da shi ta hanyar toshe bakinta kada ta kara laifi wa Sarham.
Sarham ya rasa inda zai sa ransa, sabida kuka irin wannan musamman na mace na kassara
shi ba dan kadan ba, koda kuwa ace baida alaqar komai da ita, da hannunsa biyu ya bugi
sitiyari sannan ya kifa kansa akan sityarin, yana sauraron yadda Hauwa ke rera kukanta wanda
ya zarta na rabuwa da iyaye yanzu kuma, ya koma na tunanin yadda rayuwa zata kasance
mata a gidan surukai da kishiya in general, alhalin bata da idon ganin su, kuka take tukuru, mai
fita tun daga kasan ruhinta.
A baya ya saka a ransa Hauwa ba abun tausayi ba ce, Hauwa za ta iya yi wa kanta jagora a
duk inda ta samu kanta saboda karfin halinta da ki-fadinta, ya san ita ko lalube irin na makafi da
son a taimaka a kamata a yi mata jagora ba ta cika yi ba, saboda zuciyarta dakakkiya ce,
tsayayya kwarai, ya san Hauwa na da taurin zuciya mai sawa ta ji cewa za ta iya komai da mai
lafiyar ido zai iya, amma wannan kukan da ta ke yi a yau, da iyayenta suka damka ta hannun sa
bisa igiyar aure ya karyata duk wata jarumtakar ta, da duk abinda ta yarda da shi akan karan
kanta. Ta koma ganin bazata iya komai ba yanzu tunda babu Inna. A yau ta yarda duk wani mai
nakasa yanada rauni, da dole wani lokacin sai ya bukaci kusanci da tallafin wani nasa.
Ya yarda Hauwa abun tausayi ce yanzu, tana bukatar tausayinsa, kaunarsa da adalcinsa, da
kauna daga iyayen sa da dukkan ahalinsa da sadaukarwar su suma, hakan ne kadai zai
karfafeta daga karayar data yi a halin yanzu.
Ya lura ta gama karaya da nakasarta yanzun, ta gama sarewa da rashin Inna a tare da ita. Ta
gama sarewa da cewa ada tana da confidence. (tabbas aure yakin mata).
Dr. Sarham ya ja motarsa a hankali, suka ci gaba da tafiya sannu sannu, yana mai kokawa
da zuciyarsa da ke cewa, dole ya koyawa kansa soyayyar HAUWA. Tunda aure ya riga ya gitta
kuma babu jin qai a cikinsa idan babu soyayya ko yaya take, zai kuma tsaya wa rayuwarta daga
yau kamar, koma fiye da da yadda Inna ta ke kula da ita, zai kula da ita ya tsare mata mutunci
da martabarta wadanda sune makasudin dalilan da suka sa ya aure ta. Abun da zai mayar da
hankali akai yanzu shine koyawa zuciyarsa soyayyar wata macen bayan Madinah a inda hakan
ya zama dole.
A kofar flat din gidan su Sumayyah suka tarar tsaye tana jiran isowarsu. Daga isowarsu bakin
Sumayyah ya gaza rufuwa, ta karasa ta bude barin Hauwa, sannan ta kama hannunta ta fito
daga motar fuskarta rufe ruf cikin mayafinta.
Har dakin Mama Sumayyah ta isa da Hauwa, Mama Mai Shari'a ta daga ido a hankali tana
kallon Hauwa-Kulun, Kuluwa, AKA Maijidda (ta bakinsa), HAUWA'U kuma Hauwa-Jidda tana
shigowa dakinta, da tafiyarta cikin nutsuwa da tsentseni, duk da ta rufe fuska da mayafi za ka
gane akwai nutsuwa mai yawa a tattare da ita. Har gefen gadon Mama Sumayyah ta kai ta, Mama ta yi murmushi ta ce, "Barka da zuwa
cikinmu Hauwa'u, cikin iyalin Abbas Shanono, nan gidanku ne, don haka bude fuskarki ki daina
kukan haka. Ajiye mayafin ki sha iska kin ji? Mu duka nan yan uwanki ne da iyayenki daga yau.
Ga abincin barka da zuwa kannenki sun shirya miki, sauko bisa ledar cin abinci mu ci abinci
tare har Sarham din kin ji? We are family, insha Allahu ba za ki yi nadamar shigowa cikinmu ba".
Hauwa sosai ta ji dadin maganganun Maman Sarham, taji duk rabin damuwarta ta yaye nan
take, a lokacin Sarham din ma ya shigo dakin ya zauna a kujerar da ke fuskantar gadon

Maman, Sumayyah ta sauke mata lullubin sai Mama ta samu damar ganin kyakkyawar fuskar
Hauwa sosai. Da manyan fararen idanunta masu kama da an diga musu zaiba ma'abota
kayatar da idanun duk mai kallonta.
Mama ta yi tazbihi cikin ranta, ta kuma tabbatar bayan son taimako, shakuwa da son yin
jihadi ga rayuwar HAUWA KULU, danta Sarham zai iya auren Hauwa (on the ground) na so da
kauna, domin ta isa mace ga kowanne namijin da ba kyale-kyale yake so a macen aurensa ba.
Sumayyah ta zaunar da Hauwa kusa da Mama a kan ledar cin abincin. Ita kuma ta zauna
gefen Sarham. Sannan ta zauna tayi serving kowannensu, Surayyah cewa ta yi cikinta na ciwo,
don haka za ta je ta sha magani ta kwanta, ba ta jin yunwa.
Kwarai kyawun Hauwa ne da kamalarta har ma da kwarjininta ya razanata, duk da
kasancewar ta 'yar talakawa din bata zaci ko kusa ilhamarta ya kai haka ba, hakika Surayya ta
razana da ganin Hauwa don haka ta ki zaman dakin Mama ta kuma kasa cin abincin taredasu,
duk da yunwar take ji ta yi karyar ciwon cikin, gulma na cinta kamar me. Tana so kwarai ta kira
Madinah a wannan lokacin ta labarta mata yadda taga Hauwa da yadda Mama ke rawar jiki da
ita sannan ta gargadeta kan ta sake lale, tayi babbar dammara in har tana son korar HAUWA
sai ta yi da gaske ba kamar yadda ta bata labara kafin ta ganta ra’aayal aini ba, sai ta mike
akan Sarham da Mama, kada wankin hula ya kaita dare, domin gabadaya yadda suka zaci
abubuwan da Hauwar kanta a kalar 'yan tallen cikin gari ba haka take ba, a nitsenta take, ta
tuna gargadin da Madinah ta yi mata na cewa, kada ta kara yi mata zancen Sarham, ko na
matar da Sarham ya aura. In ba so take ta samu (heart attack) ba.
Da kyar Mama da Sumayyah suka lallaba Hauwa ta ci abincin da suka shirya dominta, amma
kadan ta iya ta ci, sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login