Showing 21001 words to 24000 words out of 31076 words
Chapter 8 - HAUWAU KULU Yar Cikin Badala 3 BY TAKORI.pdf
Mama ta kai ta dakin Sumayyah har bisa gadon da yaji shimfidar
sabon zanin gado da sabon quilt, inda a can suka shirya mata sauka.
Ta barta tare da Sumayyah, ita kuma ta hada mata ruwa mai zafi a toilet ta ce ta shiga ta yi
wanka ta ji dadin yin barci, ta kamata ta kai ta har bandakin ta nuna mata duk abin da za ta yi
amfani da shi har saida ta gane kan komai na bandakin, sannan ta fito.
Sau biyu Sarham yana lekawa dakin don yayiwa Hauwa sallama zai je ya kwanta, Sumayyah
na cewa ba ta fito daga wanka ba. Ita kuma Hauwa sulbi da taushin kumfar da kuma kamshin
'bath gel' na 'Fà' da kamshin turaren wankan da Sumayyah ta zuba mata a cikin ruwan wankan
su suka sa ta kasa daina wankan, yi take tana sakewa jikinta na santsi don ba ta taba jin
kamshi mai dadi irin su ba. da sabulun da ke dirje fata ta fita sumul kamar wannan ba. Su
turarensu ita da Inna daga Dan Duala ne sai Binta Sudan. Sabulunsu kuma dan yanka ne
wanda har wanki da shi suke yi, shi ya sa ta dauki lokaci tana saba jikin tana karawa, tana jin
kamar bata taba yin wanka a duniya ba sai yau.
Ta kwashi wajen mintuna sittin kafin ta gamsu cewa fatar jikinta ta fita sumul, ta lalubi tawul
faffada wanda Sumayyah ta aje mata ta ce shi za ta daura a jikinta in ta gama wankan, ta kuma
rufa karaminsa a kanta ta tsane kai dashi ta fito.
Sumayyah na jin motsin fitowarta ta mike ta kamo hannunta zuwa stool ta taya ta goge ruwan
jikinta da karamin tawul din.
Gashi daman Maman Salele ta rangada mata sabon kitso kanana da ake kira (weeving) a
gashinta baki mai cika, na asalin Hausawa-Kanawa.
Sumayyah na taba jelunan kitson da sha'awa tana ce da Hauwa.
"Hauwa Jidda kina da kai mai cika, haka kuma mai karfi, wanda baya breaking, amma kamar ba
ki taba saka masa 'relaxer' ba".
Hauwa ta ce, "Umh, can baya ina yarinta na taba karambanin saka masa danjangabu da
sunan zanyi shamfo gaba daya gashin ya sauka kasa, tun daga lokacin ban kara gwadawa ba,
don kaina tal kwabo ya koma Aunty Sumayyah".
Sumayyah ta dinga dariya, wait tal kwabo, ta ce, "Danjangwabo ai 'traditional relaxer' ne, wa
ya aike ki?
Insha Allahu da mun sauka a Jiddah zan kai ki saloon din dana ke zuwa a yi miki na amarci
wanda zai burge Bhaiyana".
Hauwa ta rufe ido tana jin kunya. Sumayyah tace "ah toh! Don in gaya miki gaskiya Bhaiya
Dan kwalisa ne na gani kasheni, kuma yana so ‘yar kwalisar matar shi".
Sumayyah ta dauke mata damuwa da hirarrakinta masu ban dariya, duk na Sarham da irin
gayunsa, nan da nan ta rage mata kewar Inna.
Sabuwar rigar barci fara kal, tsayinta iya kauri Sumayyah ta dauko ta bata ta saka, ta bata
lotion mai kyau na neutrogena tana shafawa tana mata hira.
Sosai Hauwa ta sake da Sumayyah, ta jita (at home) don Summy ta maida kanta sa’ar
Hauwa, duk da cewa ta girme ta da shekaru uku kwarara.
Mama da Abba na babban falo, Abba Prof. na cin abinci, Sarham na gefensa suna hira shi ya
sa ya kasa tsallake su ya je don ya ga yaya Hauwa ta ke coping a gidansu, ya san dai zuwa
yanzu ta fito daga wankan. Sumayyah kuma bazata barta ta nemi komai ta rasa ba.
Sarham duk da kasancewarsa dan bokon zamani hakan bai cire masa dattaku da halin
kawaici akan mata irin na manya ba. Bokonsa bai cire masa wasu daga halayen kawaici irin na
mazan da a gaban iyayensu ba, duk kuwa da kasancewar iyayen nasa yan zamani ne kuma
'yan boko suma. Banbancin tashin yaro a kasar musulunci irin Saudiyya da kasashen turawa
kenan
Abba ke tambayarsa ko yaushe 'annual leave' din nasa zai kare? Kuma yaya ya tsara zaman
iyalin nasa? Kafin Sarham ya shirya amsar bashi kuma yace.
In zaka bi shawarata, to Hauwa ka barta tare damu a nan, ta fara karatun degree a nan BUK
tunda tana da WSSCE certificate, Jamb kawai zata zana a samar mata gurbi a duk tsangayar
da take so”.
Abba Prof. ya kara da cewa, “bana so ta je Jeddah mata biyu su hada maka zafi, a
matsayinka na likita mai bukatar nutsuwa wajen gudanar da ayyukan sa, Hauwa na bukatar
(special care) in kun tafi kullum kana asibiti, matarka na jego, wa zai kula da ita? Tunda
Sumayyah a makaranta ta ke zaune ba'a gidanku ba, don haka in har shawarata kake nema, to
Hauwa'u ta zauna tare da mu a gidannan, Mamanku ta kula da ita, ni kuma in sa ta cikin jami'a
zuwa gaba kadan mu ga me Allah zai tsara muku. For the mean time".
Sarham kansa na duke a kasa ya kasa dagowa balle Abba ya ga irin yanayinsa, da irin
karbar da yayiwa shawarar sa. A da kam ya so ne ya tafi da Hauwa. Amma shawarar Abba
Prof. ma abar dubawa ce, bai auri Hauwa don yayi rayuwa ta soyayya da ita ba, ko don biyan
bukatar ransa, ko don ya yi auratayya da ita nan kusa, har gobe kallon kanwa yake yi wa
Maijidda kanwar ma ta jini abar kulawa a gareshi, cikin dalilan da suka sa ya aureta harda dalilin
zamowarsa sanadin nakasar idonta, da har gobe ya kasa yafewa kansa da kuma sauran dalilai
masu tarin yawa, da bazau lissafu ba, ciki har da kaunar sa ta hakika ga Inna, da kuma
alkawarin da yayiwa kansa na gina rayuwarta positively da tallafar ilminta koda idonta bai gyaru
har abada ba.
Da kyakkyawan burinsa na ganin cewa ta zama wani abun amfani ga alumma, kuma abin
alfahari ga iyayenta da duniyar masu nakasa. He wants to become HER PACESETTER in life!
In haka ne kenan shawarar Abbansa tana kan hanya, kuma ita ta fi dacewa da Hauwa.
Bai auri Hauwa don sha'awa ko soyayyarbukatar gangar jiki ba irin wadda za’a kasa
controlling ba, ya auri Hauwa ne don ya tallafi rayuwarta ya zame mata, ya ginata ta kowanne
bangare ya kuma nema mata lafiya.
Da wannan tunanin Dr. Sarham ya amince da shawarar Abbansa na zai tafi Jiddah ya bar
Hauwa tare dasu, ya dago a hankali ya ce, "Abba na amince da shawararka. Hauwa ta zauna
karkashin kulawar ku, na tabbata sai tafi samu kulawa har fiye da a hannunmu".
Abba ya ce, “To masha Allah lelan Abba, haka nake so ka dinga fahimtata a komai, yanzu sai
a samar mata karamar yarinya daga Shanono cikin yaran family dinmu, wadda za ta zama mai
aikinta ita kadai ta kuma dinga raka ta cikin makaranta kullum, ko’ina ya zama suna tare, ko ni
in zan fita in fita da su in kai su department dinsu. In yaso sai su dinga dawowa da kansu in ta gama lectures su dawo gida tare da mai aikin
nata. Zan yi wa Babanku na Shanono magana ya bamu aron 'yar sa Mardiya tunda ba su kai ga
yi mata aure ba.
Yarinyar nan Mardiyya na lura tana da hankali sosai ga nutsuwa.
Har suka gama hira shi da Abba Sarham bai tsallake su ya je dakin Sumayyah gun Hauwa
ba. Har sai da Abba ya tashi ya shiga turakar barcinsa, bayan ya gaya masa sati mai zuwa zai
koma Jeddah, hutun nasa next week zai kare, kuma zai sayo mata (JAMB form) ya cike mata
komai kafin ya koma in sha Allahu, don a lokacin Mama ta ke gaya musu an fara sayar da jamb
form na wannan shekarar.
Bayan wucewar Abba bedroom dinsa ya rage daga shi sai Mama suka ci gaba da hira. Mama
ta ce,
"Yanzu da gaske iyayen nata jibi za su koma Ghana? Su kuwa me yayi zafi hana da
bazasuyi hakuri su zauna a mahaifar su ba?"
Ya ce, "Eh Mama, ni ma abun yana tayar min da hankali sosai don wallahi na saba da Innar
Hauwa yadda ba kya zato. Saidai ko ke kika ji cikakken labarin Malam Bilyaminu da dan
uwansa Zakari, zaki bi bayan hukuncinsa na yin nisa dashi shine mafi alkhairi gareshi da
iyalinsa, ga dukkan alamu arzikin sa yana can". Ya ba ta labarin irin yadda Inna ke sonshi da kula da cikinsa da abincinta mai dadi da tsafta,
da yadda ta ke yawan yi musu addu'a su iyayensa ba dare ba rana. Da halin da Zakari ya janyo
musu na shan wahala da sayar da abinci a tasha, sakamakon rushe gidansu da yayi, ya ce,
“Mama, in na tuna hakan sai in ga hukuncin da Malam Bilyaminu ya yanke na barin Kano ya fi
masa alkhairi fiye da ci gaba da zama da irin wadannan ‘yan uwan, kuma a haka dan sa na
cikinsa ya dage ya kafa kahon zuka sai sun aura masa Hauwa.
Wallahi Mama ban yi niyyar auren Hauwa ba Allah ya sani, wadannan dalilan da wasu masu
yawa suka sa na yanke shawarar auren nata kawai, don Jamilu da gaske yake auren Hauwa
zai yi ko ta halin kaka, ya manta da ko waye ubansa garesu".
Mama ta jinjina kai, abun ya tsuma ta, a karshe kuma ta yi ‘yar dariya ta ce,
"kenan Jamilu ya tado tsohuwar boyayyar soyayya daga barci, kishi ya sa an yi gaggawar yin
abin da ya dace".
Sarham ya yi wani basakkwacen murmushi, ya yamutsa fuska ya ce,
"Mama ni fa, ni fa in zan gaya miki ki yarda ba son Hauwa nake ba, I mean so na soyayyah,
Mama ni Hauwa kanwa nake kallonta har gobe, kwatankwacin yadda nake kallon Sumayyah
cikin idona".
Mama ta tsuke fuska sannan ta mike tsaye don tatsuniyar tasa ta fara isar ta, ita bazata taba
yarda wai namiji zai iya kashe kudinsa da lokacinsa ya auri macen da baya so ba, ta ce,
"ka je ka gayawa wani maho din wannan tatsuniyar kanzon kuregen naka, ba ni mai shari’ah
Maimunatu ba".
"Mama ki yarda da ni, ban taba yi ma wata mace kallon so bayan Madinah ba, ba don so
kadai maza irina ke aure ba Mama. Dalilai da yawa sun fi komai saka maza kashi 90% yin aure
ba soyayya ba, wallahi Mama dalilai ne suka rinjayi zuciyata na yi wannan auren amma ba so
ba". Mama ta ji wani irin babu dadi a ranta, kamar ita ce ta haifi Hauwa, mijin da ya auri Hauwan ya
tareta yana gaya mata haka, ta kuma ji matsanancin tausayin Hauwa ya kama ta kan abinda
Sarham ke fada a kanta.
Tun daga wannan lokacin Mama Mai Shari'a ta kudiri aniyar zata taimaki Hauwa-Kulu,
za ta zame mata UWA kamar Inna, amma ba uwar miji ba, zata zame mata Uwa, kamar yadda
Innarta ta zamewa Sarham ba tareda su sun sani bama. Ko albarkacin abincin da ta dinga
bashi. An ce mai Da wawa…inda ake son dan sa anan yake. Mama tace a ranta. Insha Allahu watarana sai Sarham ya furta SON nan da yake ta musawa
da bakinsa. Sai ya so ta kamar, ko ma fiye da yadda yake son Madinah dinnan.
Mama ta mike ta ce masa, "Ma'assalam Sarham zan shiga daga ciki, don na ga tatsuniyar
taka ta yau ba mai karewa ba ce, mu kwana lafiya.
In kun yi waya da “MATAR SO” din ka ce ina gaida Waheedah, tun safe nake gwada layinta
(tana nufin Madinah) na kasa samu, in ya shiga sai ya katse, ban san me ya samu wayar tata
ba, kwatakwata an daina samun ta. Naso ne dama in rarrashe ta akan maganar auren ka da
Hauwa. Ina fatan ka lallashe ta da kyau Sarham, ka san mu mata a irin wannan lokacin lallashinku da
hakurinku da juriyar ku kan canjin halinmu da dabi’unmu kowanne iri ne kadai muke bukata, ka
yi hakuri da dukkansu, ka kuma zamo mai adalci a tsakaninsu.
Kada ka kara fada min wai dalili ne yasa ka auri Hauwa, raina baci yake yi".
Mama ta dade tana yi masa nasiha mai ratsa jiki da bargo, akan zama da mata biyu, sannan
suka yi sallama ta bi bayan Abba. Shi kuma har zai wuce dakinsa sai kuma ya taka zuwa dakin
Sumayyah don ya yi wa Hauwa sai da safe, ya kuma ga halin da ta ke ciki, ya san har yanzu
tana nan cikin kukan nata na shagwabar an rabo ta da Inna. Amma ga mamakinsa a kan stool din madubi ya same ta cikin farar rigar barci mai kyan
gaske wadda Sumayyah ta bata ta saka, ta dau wanka tayi wani irin fresh da ita, bai taba ganin
ta zahirin irin yau ba da tsabar kuruciyarta ta ‘teenager’ data fito fili, sannan bai tsammaci
wannan yanayin a tare da ita ba, dakin sai kamshin amarci mai dadi da sanyi yakeyi, kanta da
ya sha ‘weeving’ yiri-yiri babu kallabi, ta gama shafa lotion wanda ya sa fatarta yin taushi sosai.
Tana daga kan stool Sumayyah na daga gefen gado suna ta hira suna dariya, fararen hakoranta
a warwaje kamar mai tallan sensodyne.
Bai taba ganin Hauwa-Kulu cikin kyakkyawan yanayi da kyakkyawar shiga irin wanda ya
ganta ciki a yanzu ba.
Ita Sumayyah ta ga shigowarshi, da yake kofa take fuskanta, amma ba ta fada wa Hauwa ba.
A lokacin Hauwa na tambayar Sumayyah, "Karatun likitanci nada wahala?”
Sumayyah ta dubeshi tayi murmushi mai sauti ya kasha mata ido, ta ce mata, "Aah babu, ba
wani wahala".
Sai ta ce, "Kin ga da idanuna ba su rufe ba, da a bude suke kamar na kowa har yanzu, nima
da irin karatun Yayanki zan yi, Ina sha'awar inga ana aikin fidar ido, kasancewar sa wani kwayar
halitta mafi hatsari da muhimmanci ga jikin dan adam, ba ki san yadda likitoci suke burge ni ba,
shi ya sa har wasu lokutan nake DAKACEN ina ma… in ga Yaya Sarham! Inama in ganshi cikin
kwayar idona, in ga yadda kamanninsa na zahiri suke? Ko daidai suke da yadda nake kintata
shi ina fasalta shi a raina?
Anti Sumayyah wallahi haka kawai kyawawan kalamansa SUNA BURGENI!!!”.
Sarham sai kawai ya juya da baya cikin mutuwar jiki, tare da yi wa Sumayyah alamar kar ta
ce ya shigo.
Yana shirin kwanciya kamar yadda ya saba ya samu kansa da yin addu'ar Allah ya cika wa
Hauwa burinta watarana ta sanya idanunta cikin nasa, ya gaya matai do da ido shima tana
burge shi”.
Yana addu’ar Allah ya bashi ikon yi mata adalci ta kowanne bangare, ya kuma ba shi tsawon
ran da zai sauke duk alkawururruka da kudirin da ya dauka a kan rayuwarta na zame mata
PACESETTER.
Sai washegari ya shiga dakin Sumayyah suka gaisa, ya baiwa Sumayyah kwalin waya, ya ce,
ta hada wa Hauwa.
Sumayyah har ta fi Hauwan murnar mallakar tsaleliyar wayar nan. Nan da nan ta hada ta, ta
saka layin da ya hado da shi na mtn, ta saka a caji tana gaya wa Hauwa sunan wayar da
Bhaiya ta saya mata.
Hauwa wadda kanta ke sunkuye tun shigowarsa dakin, tana iya jin idanunsa all over her, da
kyar ta iya furta masa kalmar godiyarta gajeriya.
A lokacin bata dade da yin wanka ba. Mama ta kawo shadda dinkakkiya dakakkiya 'yar Mali
ta bata ta sanya, shaddar orange colour, tasa ta yi sharr da ita, amarya sosai mai jini a jika.
Sumayyah ta fice daga dakin don dai ta ba su wuri su gaisa, ganin cewa tun jiya basu gaisa ba.
Sarham ya tako ya zauna a gefen Hauwa. Dab da kafadunta. Hauwa na iya jin sanda ya
zauna din, da kamshin balaraben turarensa 'sandalia' daya nasheta, ta lumshe ido ba shiri,
inama zata gan shi a lokacin, hakika da ta kara godewa Allah a bisa ni'imar da yayi mata na
bata Dr. Sarham Abbas a matsayin mijinta kuma abokin rayuwar ta na har karshen rayuwa.
Wani sassaukan yadi ya sanya mai matukar tsada ruwan Madara shara-shara da shi har kana
iya hango sabuwar farar singlet dinsa dake ciki. Sannan yadin baida nauyi ko kadan sai tsada.
Hannun Dr. Sarham Hauwa ta ji ya ratsa a cikin hannunta na dama for the first time a
rayuwarsu, wanda hakan yasa ta dan firgita, tsigogin jikinsu gaba daya suka tashi a lokaci guda.
Sarham ya yi crossing fingers nashi da na Hauwa tareda rufesu da daya hannun nasa yana
murmushi ya ce,
“Maijidda matar likita ina kwana? Yaya kuma kwanan bakunta? Ina fatan kinyi barci mai
ni'ima kin warware gajiya”.
Hauwa, wadda