Showing 18001 words to 20550 words out of 20550 words

Chapter 7 - KUNDIN ALAJABI Book 1 By MANSUR USMAN SUFI.pdf

ba za su samu nasarar kawar da su

Ayumul-barƙas, sannan ma inda kizo ke saƙar shine idan sun yi nasarar ta ya ya ɗayansu zai
iya haƙura ɗan uwansa ya mallaki KUNDIN AL'AJABI tare da kubar Miftahul-sihir, daga can sai
wata dabarar ta faɗo masu, dabarar kuwa ita ce su yaƙi junan su, idan ɗaya daga cikin su ya yi
nasara sai ya shiga kogon Garul-shammar ya hallaka mahaifina, ya mallaki KUNDIN AL'AJABI
da kubar Miftahul-sihir.
Koda gama tunanin hakan sai sarkin aljanu baƙaƙen fata ya ɗaga hannunshi izuwa
sama, sai ga wani makami mai kama da zarto mai tsini da kaifi tamkar takobi ya bayyana gare
shi, koda ganin hakan sai sarkin aljanu fararen fata ya zare wani makami na sihiri a jikinshi mai
kama da Adda mai KAIFI DA TSINI. A lokaci guda tamkar haɗin baki suka ɗaga makamansu suka yi ɗauki kan juna suna ihu da
kururuwa mai firgitarwa, suna haɗuwa suka rungumtsume da azababben yaƙi mai matuƙar
kwarjini da ban tsoro, duk sa’adda makamansu suka haɗu da juna sai a kwatsama wata irin
razananniyar ƙara gami da tsawa, tamkar za’a kece da matsanancin ruwan sama. Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce. “Idan ana babbakar Giwa
wa yake jin ƙaurin ɓera” kuma tabbas “Sawun Giwa ya take na raƙumi”.
Sa’adda waɗannan GWARAZAN SARAKAI biyu suka fara bawa hammata iska sai suka tashi
hankalin duk wata halitta dake wajen, ba shiri dakarun dake daf! Da inda suke fafata artabun
suka dinga yin ƙaura domin tsira da rayukansu daga sharrin shuwagabannin na su.
Al’amarin mahaifina kuwa lokacin da ya shiga cikin wannan ƙofa dake ƙarƙashin wannan
macijiya mai kawuna uku, sai kwatsam ya tsinci kanshi a cikin wani makeken waje mai ɗauke
da manyan duwatsu, bishiyu gami da sarƙaƙiyar duhuwa, haka abbana ya ci gaba da tafiya a
cikin wannan duhuwa har ya zamana ya shafe tsawon daƙiƙa ɗari uku, a dai-dai wannan lokaci
ne kishi da yunwa suka addabi mahaifina, kuma dama ga shi ya jefar da jakar guzurin shi tun a
wajen da ya fafata yaƙi da wannan macijiya.
Yana cikin wannan hali ne ya hango wata bishiyar tuffa can nesa kaɗan da inda yake, cikin
matuƙar farin ciki ya durfafi inda take, yana isa ya sanya hannunshi ya tsinki guda ɗaya ya kai
bakinshi da nufin ya ci. Kawai sai ya ji an daka mashi tsawa, wacce ta sanya hantar cikinshi ta
kaɗa da ƙarfi. Abbana ya waiga gabas, yamma, kudu da arewa bai ga kowa ba. Al’amarin da ya yi matuƙar bashi mamaki kenan, kawai sai ya sake kai tuffar bakinshi karo na
biyu domin ya ci, amma sai aka sake daka mashi tsawa, a wannan karon sai da firgita ya jefar
da tuffar dake hannunshi.
Kwatsam! Sai ga wata BAƘAR INUWA na ketowa daga cikin gajimare, lokacin da ta
kammala sauka sai ta rikiɗa izuwa wani zabgegen maridi.
Maridin ya kasance narkeke tamkar basamude yana da tafkeken kai irin na bil’adama, mai
ɗauke da ido guda ɗaya jal! A tsakiyar goshinshi, ƙofofin hancinshi manya ne tamkar mazirari,
yana makeken baki tamkar mazirari, ƙirjinshi makeke ne ya tara ƙwanji tamkar duwatsu aka
cusa mashi a ciki, sangalalon hannayenshi da ƙafafuwanshi masu kauri ne tamkar bishiyar
kuka, Kuma yana sanye cikin gagarumar shigar shigar yaƙi ta baƙin sulke mai matuƙar kwarjini
da ban tsoro, a gadon bayanshi yana rataye da waɗansu zaratan adduna biyu masu kaifin tsiya.
Kaico! Haƙiƙa wannan maridi ya cika GAGARABADAU, komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi
arba da shi, dole ne ya ɗimauce ya yi nadamar wanzuwar shi a doron ƙasa.
Sa'adda mahaifina ya yi arba da maridin, nan take ya ɗimauce jikinshi ya kama tsuma ya ja da
baya.

Maridin ya tako lafta-laftan ƙafafuwanshi ya durfafi inda mahaifina yake, duk sa’adda da ya ajiye
ƙafarshi ɗaya idan akan dutse ne sai kaga ya nutse izuwa cikin ƙarƙashin ƙasa, ya yin da ya
rage saura taku biyar tsakaninsu sai ya ja ya tsaya ya ƙarewa mahaifina kallo tun daga ƙasa har
sama, nan take mahaifina ya zamto tamkar an ajiye ƙyanwa a gaban raƙumi, saboda matuƙar
tsawon maridin.
Daga can sai maridin ya wangame bakinshi cikin kakkausar murya mai kama da gurnanin zaki
ya dubi mahaifina ya ce “ya kai Yasiran ka yi sani cewa fiye da shekaru dubu uku a cikin halarar
tsafina na gano cewa kai ne bil’adama mau tsananin sa'a da zai iya shiga cikin kogon dutse na
Garul-shammar kuma har ya samu nasarar ɗauko littafin KUNDIN AL'AJABI. Bisa wannan dalili
ne ya sanya na yi GABA DA GABA da kai domin na canja wannan ƙaddara taka, saboda haka
yanzu ina so ka miƙo min kubar Miftahul-sihir, cikin ruwan sanyi domin na yi maka kisa mafi
sauƙi, ta hanyar tsinka gaɓoɓin jikinka, ba tare da ka sha wata azaba ba”;
Koda jin wannan batu sai mahaifina ya bushe da dariyar ƙarfin hali, sannan daga bisani
ya haɗe rai ya dubi maridin ya ce “ya kai wannan rafkanannan halitta ka yi sani cewa
GWARZON DUNIYA ba ya taɓa gudu a filin fama, ballantana ya miƙa wuya ga abokin gaba,
face ya yi GWAGWARMAYA domin ya yi MUTAWAR JARUMTA”. Koda jin wannan batu daga bakin abbana sai maridin ya fusata ainun, jikinshi ya kama tsuma
yana ƙyarma, idanuwanshi na fitar da wani tiririn baƙin hayaƙi.
Kawai sai ya yi wuri! Ya zare waɗansu zaratan Adduna biyu a gadon bayanshi ya kaiwa
mahaifina wani bahagon sara da nufin tsinke mashi wuya, cikin baƙin zafin nama ya wurƙila ya
zamewa harin, sannan ya afkawa mahaifina suka rugumtsume da azababben yaƙi mai matuƙar
kwarjini, muni da ban tsoro. Duk sa’adda maridin ya kai mashi hari idan ya goce, duk abin da ya sara koda dutse ne sai
kaga ya yi bindiga ya tarwatse, amma sai ya zamana cewa maridin ya ƙi yarda kubar
Miftahul-sihir ta taɓa jikinshi.
Sai da daƙiƙa ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi tsakanin GWARAZAN
JARUMAN biyu, tamkar jikkunnansu ba su kasance na jini da tsoka ba, lokacin da sa’a biyu ta
shuɗe nan take sai ya zamana cewa abbana ya fara galabaita saboda ƙishi da yunwa da suka
adda be shi. Koda maridin ya fahimci halin da mahaifina ya shiga sai kawai ya shammace shi ya gabza
mashi naushi a fuska, saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da abbana ya yi sama tamkar an
janye shi da ƙugiya, sannan daga bisani ya faɗo ƙasa tim! Da rubda ciki a matuƙar galabaice
yana aman jini ta baki da hanci, amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta GAGARABADAU
sai ya ƙi yarda ya saki kumar Miftahul-sihir daga hannunshi”.
Sa’adda jaruma Sulaiza yar mafarauci Yasiran yazo nan a labarin ta sai hawaye suka
kwaranyo daga idanuwanta zuwa kan kuncinta.
Al’amarin da ya sanya ni da Raudatul-abyad da sauran tawagarmu muka kamu da matuƙar
tausayinta kenan har ƙwalla ta cika mana idanu.
Daga can sai Sulaiza ta share hawayenta sannan ta ci-gaba da cewa.
“Tabbas mahaifina ya sha matuƙar wahala a cikin kogon Garul-shammar kafin ya ɗauko littafin
KUNDIN AL'AJABI, wanda har ta kai cewa ya rasa dukkan idanuwanshi. Bayan ya fito ne sai
yaƙi ya ɓarke tsakanin sarakunan shida, da zarar wannan ya ƙwaci kundi da kuba, sai wancan
ya yi mashi fin ƙarfi ya ƙwace.

Koda aljani Zaruhul-Amwat da ya ɗauko mahaifina da sarakuna huɗu ya kawo su gaɓar kogon
Garul-shammar ya ga halin da mahaifina ke ciki, kuma ya tabbatar da cewa zai iya rasa
rayuwarshi sai tausayin shi ya kama shi, kawai sai ya ɗauke shi ya kawo shi izuwa bakin
kubbarmu ya ajiye, sannan ya tashi izuwa sama yq ɓace ɓat! A cikin gajimare, Tsananin iskar fuka-fukan aljani Zaruhul-Amwat ta sanya muka yi tsammanin harin sumame aka
kawo mana, sai daga bisani muka lura cewa a she mahaifina aka ajiye a daf da mu.
Cikin matuƙar tashin hankali muka fito daga bukkar muka rugo izuwa gare shi, muka rungume
shi, yana mai bamu labarin irin butulci da sarakunan duniya huɗu suka yi mashi. Bayan ya
kammala bamu labarinne idanuwanshi suka ƙafe, jikinshi ya sandare komai ya daina motsi,
alamar rai ya yi halin shi, baƙin cikin rasuwar abbana ya sanya mahaifiyata ta faɗi ƙasa matacce
ko shurawa bata yi ba.
Nan fa na sake fashewa da sabon matsanancin kuka ina mai kiran sunayen mahaifana, ina mai
jijjiga su ina cewa, ku tashi kar ku mutu ku barni, amma babu wanda ke saurare na ballantana
ya kawo min ɗauki, har da muryata ta disashe, idanuwana suka yi jajur tamkar garwashi, bayan
na haƙa ƙabari na binne mahaifana, kullum sai na tsugunna a gaban ƙaburburan iyayena ina
kuka gami da karanto baitocin bege a gare su.
Haka rayuwata ta kasance cikin maraici da ƙunci, kullum sai ya fita farautar abin yin kalaci.
Daga wannan rana na sha alwashin ɗaukar fansa akan sarakunan duniya huɗu”;
Lokacin da jaruma Sulaiza ta zo nan a labarin ta sai ta fashe da matsanancin kuka mai
tsuma zuciya daban tausayi.
Nan take dukkaninmu muka ƙara kamuwa da matuƙar tausayinta, hatta aljani Jauharul-layal da
bai kasance bil’adama ba sai da ƙwalla ta zubo mashi saboda matuƙar tausayin Sulaiza.


BABI NA GOMA

Lokacin da boka Matawus ya zo nan a labarin shi, sai ya ɗago kai ya dubi sarki
Sabrul-marhut, nan take ya ga ƙwalla na zuba daga idanuwanshi, bakomai ne ya sanya shi
hakan sai bisa mutuƙar tausayin jaruma Sulaiza yar mafarauci Yasiran.
Matawus ya yi ajiyar zuciya sannan ya ja dogon gwauron numfashi ya ajiye sannan ya ce “ya
kai Sabrul-marhut ka yi sani cewa “mun sha matuƙar wahala sosai a domin isa fadar Sarkin
bokaye, wanda dukkanin mu babu wanda bai rasa wani sashi a jikinsa ba, kuma nine kaɗai na
samu nasarar fitowa daga fadar sarki bokaye a raye bayan na samu nasarar tone shirin tsafin
da aka yiwa mahaifinmu na tawo da shi, domin na koma zuwa birninmu, na yi kukan baƙin ciki
bisa mutuwar Raudatul-Abyad tare da jaruma Sulaiza yar mafarauci Yasiran, bayan na samu
nasarar kama hanya domin komawa zuwa gida, na ci karo da sauran ‘yan uwana in da suka yi
min abin nan da masu iya magana ke cewa kura da shan bugu gardi da ƙawace kuɗi, suka
yaudare ta hanyar bayyana min nadamar su akan ƙiyayyar da suke yi min, tare da alƙawarin
cewa za su goya min baya na haye bisa karagar mulki, amma sai suka soka min takobi a gadon
bayana suka jefar da ni ƙasa a tunanin su na mutu. Mahaifinka Maigirma Marhut shine ya ɗauke
ni a wannan hali a lokacin da ya fitowa farautar ƙarshen shekara da ya saba yi, ya ceto rauwata,
ya yi jinyar raunin dake jikina har na warke sumul, har na samu nasarar komawa izuwa
birninmu, amma abin mamaki koda na isa sai na tarar dukkanin ‘yan uwana sun rasa
rayukansu, domin ashe yaƙi ya kaure a tsakanin su domin hawa karagar mulki, amma abin da

ya bani farin ciki shine mahaifinmu ya samu lafiya, kowa ya yi farin ciki da dawowa ta bayan an
cire rai cewa bana raye, ‘yan majalisar sarki suka sake naɗani sabon sarkin Romaniya.
Ya kai Sabrul-marhut ka yi sani cewa wannan abun alheri da mahaifinka ya yi min ban manta da
shi, dare da rana ina binciken hanyar da zan saka masa da abin da ya yi min sai a halin yanzu.
Ya kai Sabrul-marhut ina so ka kwantar da hankalinka, ka sani cewa za ka samu magaji da zai
zamo halifanka, sai dai ina so ka saurari jawabin da zan yi maka, a halin yanzu uwar gidanka na
ɗauke da juna biyu har na tsawon watanni takwas, ba tare da ita kanta ta sani ba, ni ne wanda
ya ɓoye junan biyun ta hanyar shiri domin kawar da idanu da bakin maƙiya daga sharrin
matarka, junan biyun ba zai bayyana gare ta ba sai a daren da naƙuda zata kama ta, ina so da
zarar ta haife abin da ke cikinta ka ɗauke sa ka sanya sa a cikin akwatin baƙin ƙarfe tare da
TAKOBIN SARAUTA daka gada a wajen mahaifinka. Ka ɗora su abisa kenan doki a can bayan
gari ka tafi ka barsu, abin da aka haifa maka zai dawo gare ka cikin aminci a lokacin da
dukkanin maƙiyanka na ɓoye da fili za su bayyana. Sai dai zan gargaɗe ka koda ita matarka kar
ka kuskura ka sanar da ita wannan sirri, ballantana waninta”.
Sa’adda boka Matawus ya zo dai-dai nan a zancen sa sai sarki Sabrul-marhut ya cika da
ɗumbin al’ajabi gami da farin ciki, bai sa’adda ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa ga Matawus ba.
Koda ya tashi tsaye ya buɗe ba ki da nufin ya ce wani abu, sai ya ga boka Matawus ya zama
wani koren haske ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa wanzuwa ba. Take dukkan dakaru da barorin
gidan sarautar da suka kamu da barci suka wartsake.
Nan fa sarki Sabrul-marhut ya sake cika da matuƙar mamaki, yana ta juya wannan hikaya da
umarni da boka Matawus ya yi masa, ya kasa zaune ya kasa tsaye ya wanzu yana kai komo a
cikin turakarsa, a haka har a alfijir ya keto.
Kamar yadda boka Matawus ya labartawa sarki Sabrul-marhut haka al’amarin ya
kasance. Kwanaki na bin kwanaki mako bayan mako, wata ranar asabar lokacin sulusainin
dare naƙuda ta kama uwar gidan sarki wato gimbiya Nadirat, al’amarin da ya yi matuƙar
dugunzuma hankalin Nadirat kenan, ta yi zaton ko cutar ajali ce ta zo mata, domin ta san bata
ɗauke da wani abu da nuna cewa tana ɗauke da juna biyu, a wannan lokaci dukkanin kudancin
dake turakar a ɗimauce suke, tamkar a ce ƙyat! Su cika wandon su da iska. Kwatsam! Sai sarki
Sabrul-marhut ya kunno kai cikin turakar, cikin matuƙar tashin hankali ya durfafi inda take,
lokacin da kuyangin suka ja da baya suka zube ƙasa gami da kwasar gaisuwa.
Sarki ya daf da ita bisa ƙasaitaccen gadon sarautar, sannan ya sanya hannunsa ɗaya a tallabo
kanta, ɗayan hannun kuma yana shafa gashin kanta, cikin lallausar murya sai ɗauke raɗaɗin
ciwo ga masoya ya ce “kwantar da hankalinka ya abar bege na dare da rana, kuma uwar
‘ya’yana ki yi sani cewa a halin yanzu za ki haife abin da ke cikinki, wanda ke kan ki ba ku san
cewa kina ɗauke da shi ba, boka Matawus ya bayyana min cewa ya ɓoye wannan juna biyu na
ki ne domin kawar da idanun maƙiya.

Mu haɗu a book 2 na kuɗi ne domin jin cigaban wannan kayataccen littafi.
Za a biya kuɗin littafin ta wannan hanyar

₦400
Account Number: 0084279025
Account Name: USMAN UMAR MANSUR
Bank: Access Bank Nigeria

Sai a tura shaidar biya ta wannan number
08137237071

Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
08137237071

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login