Showing 6001 words to 9000 words out of 20550 words

Chapter 3 - KUNDIN ALAJABI Book 1 By MANSUR USMAN SUFI.pdf

daf da ni ta
tsugunna ta ajiye wannan akushi da salkar ruwa sannan ta juya ta nufi ƙofar fita har ya sanya
ƙafarta ɗaya a waje sai dattijon ya dube ta ya yi gyaran murya ya ce "ya sha'afa ban faɗa miki
sunan baƙonmu ba da abin da ke tafe dashi, amma magana a bakin mai ita tafi daɗi bari ki ji
daga gare shi.
Koda jin hakan sai na buɗi baki na ce da farko dai suna Matawus ibnu Sahibul-Sihir, kuma na
fito ne tare da 'yan uwana domin zuwa fadar Sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar duk wanda ya
samu nasarar tone sihirin da aka yiwa mahaifinmu shine zai gaji karagar mulki. A wannan tafiya
tawa ne hanya ta biyo da ni ta nan, kuma zan zauna tare da ku wani lokaci kafin na samu
damar haye kogin dake gaɓar wannan tsibiri.
Sa'adda nazo nan a jawabi na sai kyakkyawar budurwar ta juyo ta dube ni tare da ƙura min
idanu ko ƙiftawa ba ta yi, sai daga bisani ta gyaɗa kai sannan ta juya ta fice batare da tace ƙala
ba".
Dattijon ya dube ni ya ce "ya kamata nima na sanar da kai sunan mu ni da 'yata, ni suna
na Abu-Raudat 'yata kuma ana yi mata laƙabi da Raudatul-Abyad.
Daga wannan batu ne kowa ya yi shiru na buɗe wannan akushi da aka kawo min na shiga
kintsa cikina.

Babi na huɗu

Kashe gari tunda duku-dukun safiya bayan mun kammala kalaci sai muka yi ɗauki kayan
aiki muka nufi gona tare da Raudatul-Abyad, yau ma kamar kullum fuskarta rufe take da rawani
kuma tana sanye da baƙaƙen tufafi a gadon bayanta tana ɗauke da wata zabgegiyar takobi,
shigar da ta yi matuƙar yi mata kyawu.

Tafe muke cikin hanzari ta gaba ina biye da ita a baya, tsawon daƙiƙa ɗari biyu muna cikin
wannan hali babu wanda yace ƙala. Sannu a hankali har muka iso wata makekiyar gona mai
ɗauke da alkama mai tsawon hetta goma. Koda muka iso ɗin sai Raudatul-Abyad ta miƙa min
fartanyar dake hannunta gami da lauje na karɓa sannan ta yi min nuni da na fara aiki batare da
buɗi baki ta ce min uffan ba, kawai sai ta durfafi gindin wata itaciya ta kwanta bisa wata
tabarmar kaba mai haɗe da matashi, kawai sai na duƙufa na fara aiki, wasa-wasa sai ga shi na
shafe tsawon sa'a ɗaya a cikin wannan yanayi, koda na ɗaga kaina na duba aikin da na yi sai
naga ashe bai huce kunya goma ba, a wannan lokaci hasken rana ta fito ta fara zafi ainun.
Al'amarin da ya sanya kishi ya fara damuna, kuma gadon bayana ya fara ciwo. Lokacin da
sa'a biyu ta shuɗe ina cikin wannan hali kwatsam! Bazato babu tsammani sai na ga waɗansu
masifaffun kibiyoyi suna sauka a dajin, cikin wani irin zafin nama na dinga zillewa kibbau ɗin
tare da falfalwa da azababban gudu izuwa inda Raudatul-Abyad ke kishingiɗe domin na bata
kariya, a wannan lokaci barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita, koda ya rage saura taku biyar
na isa daf da ita kwatsam ba zato babu tsammani sai waɗansu irin samudawan dakaru suka yi
fitar burgu daga duhuwar dajin,
Dakarun suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, fuskokinsu
a rufe suke da hulunan ƙarfe, a hannayensu suna ɗauke da miyagun makamai dangin Gatari,
sungumi, majaujawa, al'amudi da sauran su. Adadin su ya kai dubu ɗaya da ɗoriya, kafin nayi
wani yunƙuri sun yi min ƙawanya suna muzurai tamkar za su ci babu. Lokacin da aka fara kallon-kallo tsakaninmu sai na lura wani badakare ya ɗora KAIFIN TAKOBI
akan wuyan Raudatul-Abyad.
Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan kallon-kallo, daga can sai wani narkeken ƙato ya fito daga
cikin su, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da cewa shine shugabansu saboda hular kwanon
da ke kanshi da takobinshi da ta kasance ta musamman,
Sannu a hankali yana takawa da ƙafafuwanshi har iya isa daf! Da inda Raudatul-Abyad take ta
yadda suna jin numfashin juna. Kawai sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta tamkar ba
zai daina ba, daga bisani kuma sai ya turɓune fuska tamkar an aiko mashi da SAƘON
MUTUWA, sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da haniniyar doki ya dubi
Raudatul-Abyad ya ce "ya ke Raudatul-Abyad 'ya ga tsoho Abu-Raudat kiyi sani cewa dama na
faɗa miki in dai kere na yawo zabo na yawo wata rana za su haɗu, kuma rabon kwaɗo baya
hawa sama koda ya hau zai sakko.
Yau ga shi kin faɗa tarkona wanda ya za ki iya tserewa ba, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba zan
kashe wannan baƙo naki a gaban idanuwanki sannan na tafi dake a matsayin sabuwar
amaryata…".
Kafin narkeken ƙaton ya gama rufe bakinshi ya gama rufe bakinshi Raudatul-Abyad ta tari
numfashin shi tana mai daka mashi tsawa ta ce "Dawazul-kiryan kayi sani cewa haƙiƙa ka tafka
babban kuskure da rafkananniyar zuciyarka ta yaudare ka cewa za ka ci galaba a kaina, ka sani
cewa har abada ƘARYA DA GASKIYA ba za su taɓa zamtowa abu guda ba, ni MURUCIN KAN
DUTSE ce ban fito ba sai da na shirya. Kuma ni ƙadangaren bakin tulu ce..
Shawarar da zan baka ita ce ka gaggauta miƙa wuya gare ni wata ƙila ka samu tsira da
ruhinka";
Dawazul-kiryan ya bushe da dariya a karo na biyu sannan ya ce "haƙiƙa ƙi faɗin ki tana matuƙar
burgeni domin masu iya magana na cewa wai matsoraci baya zama gwani. Amma kar ki manta

cewa alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, kuma koda ba a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza.
Kuma dai SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI.
"Haƙiƙa ka makara wajen cimma wannan burina naka, amma ko ba komai an ce ba a
ƙwacewa yaro garma. Kuma inda babu ƙasa nan ake gardamar kokowa"
Raudatul-Abyad ce ta yi wannan furuci cikin matuƙar fushi.
Dawazul-kiryan ya ce "ai zuwa a makare yafi zuwa a makara, kuma duk mai nema yana tare da
samu".
Koda gama faɗin hakan sai yaran Dawazul-kiryan suka yi wuf suka zare makaman su suka
yi ihu da kururuwa sannan suka yi ɗauki izuwa kaina.
Yayin da naga hakan sai na zare takobina ya ruga gare su domin tarar juna,
Lokacin da aka haɗu sai a kayi KARON MAZA, aka ruguntsume da azababban yaƙi mai
matuƙar kwarjini da ban tsoro, ana fara wannan artabu ne na fara gane cewa shayi ruwa ne ba
abinci mai nauyi ba.
Nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, ihun mazaje ta cika dodon kunne, duk sa'adda na kaiwa dakarun
hari sai ka ga sun kare tare da mayar da martani, in da ba don ina da matuƙar zafin nama ba da
tuni sun murƙushe ni saboda yadda suka yi min rubdugu tamkar yadda dandazon ƙudade ke
yanyame ƙwallon mangwaro. Lokacin da rabin sa'a ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi kuma na fahimci cewa idan aka
cigaba da wannan artabu a haka wankin hula zai kai ni dare kuma dakarun za su samu nasarar
kashe Raudatul-Abyad.
Koda na zo nan a tunani na sai na fusata ainun na sake dage damtse ina kai sara da suka cikin
matuƙar zafin nama, gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya canja dole rawa ma ta
canja, faruwar hakan ke da wuya sai na fara samun galaba akan dakarun, yazamana cewa duk
inda na sanya a gaba sai dai kaga fili fetal dakarun na zubewa ƙasa matattu tamkar ana
sassabe a gonar auduga.
Al'amarin da ya fusata sauran mayaƙan kenan suka sake yin ɗauki izuwa kaina, kafin shuɗewar
daƙiƙa ɗari kacal na kashe fiye da rabin dakarun. Nan fa JINI DA ƘASA suka cakuɗu waje
guda.
Lokacin da rabin sa'a ta shuɗe ana wannan artabu na zubar da dukkan mayaƙan a ƙasa
hatta badakaren da ya ɗora KAIFIN TAKOBI akan wuyan Raudatul-Abyad, illa shugaba
Dawazul-kiryan ne kaɗai a tsaye fuskarshi a murtuke tamkar an watsa mashi garwashin wuta
akan ta. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakani na da Dawazul-kiryan na wani lokaci daga can sai ya dube
ni cikin kakkausar murya mai tattare da fushi ya ce "ya kai wannan jarumi ma'abocin taurin kai
da shisshigi kayi sani cewa zaki koda ya mutu gawarshi abar tsoro ce, KARO DA GOMA
kalacen safe in ji masu iya magana, kuma masu iya magana na cewa kaɗe mage ba yanka wa
ba ne.
Saboda haka idan ka miƙa kan ka izuwa gare ni, zan yi maka kisa mafi sauƙi ta hanyar datse
gaɓoɓin jikinka ɗaya-bayan-ɗaya ba tare da kasha wahala ba.
Idan kuwa ka ƙi to zaka gwammace wa aya zaƙin ta";
Kafin ya gama rufe bakinshi na tari numfashin shi ina mai daka mishi tsawa na ce "ya kai
wannan tsohon AZZALUMI kar ka manta cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Kuma
shi zalunci baya ɗorewa a doron ƙasa, don haka sai ka shirya ga maza nan bisa kan ka.

Koda gama faɗin sai na ɗaga takobina na durfafi inda yake tsaye ina kururuwa koda ganin
hakan sai Dawazul-kiryan ya yi wuf ya zare wani zabgegen gatari a gadon bayanshi ya yi ɗauki
kaina, muka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
Koda fara wannan artabu sai Raudatul-Abyad ta koma gefe guda ta harɗe hannaye tana kallon
yadda gumurzun ke wakana.
Nan fa muka wanzu muna kai wa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA
BAJINTA irin ta GWARAZAN JIYA. kaico! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce
artabun gwani da gwani daɗin kallo gare shi, kuma idan BABBAR GIWA ta fito filin fama babu
wanda yake yin fito-na-fito da ita face GWARZON ƘARNI. Kuma masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce duk wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka
tashi. Ana fara wannan ɗauki ba daɗi ne ma fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi
ba. Kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana.
Ga wanda ke kallon yadda gumurzun ke wakana zai fahimci cewa Dawazul-kiryan ya nunka ni a
ƘARFIN DAMTSE sau uku. Domin kuwa duk ya kai min hari da gatarinshi idan na kare da
takobina sai na durƙushe ƙasa, cikin ƙanƙanin lokaci na fara galabaita ya zamto ba na iya
mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kaina, ana cikin wannan hali ne Dawazul-kiryan ya
shammace ni ya makamin ƙotar gatarinshi a akaina saboda ƙarfin dukan sai dai kan ya tsage
jini ya yi tsartuwa, saboda matuƙar zugi da raɗaɗi ban san sa'adda na kurma ihu ba na yi
taga-taga zan faɗi amma sai na turje, sai dai kash! Kafin na dawo cikin hayyacina ya sake
samun nasarar makamin a wuya. Nan take na sulale ƙasa magashiyan ina nishin wahala.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai Dawazul-kiryan ya bushe da dariyar mugunta
sai da ya yi ta ishe shi sannan ya murtuke fuska ya dube ni ya ce "ai da ma na faɗa maka a juri
zuwa rafi wata rana tulu zai fashe" kuma komai tsananin duhun dare gari zai waye".
Yanzu ga shi kana kusa da baƙuntar barzahu za ka yi mutuwar wulaƙanci, alfarma ɗaya zan yi
maka ita ce ka rubuta wasiyyarka kafin na zare maka ruhi daga gangar jiki".
Duk wannan abu dake wakana sai Raudatul-Abyad na tsaye a gefe guda tana kallo.
Dawazul-kiryan na gama faɗin hakan sai ya durfafi inda nake kwance ya raba ƙafafuwanshi
biyu a kaina yana mai yi min murmushim mugunta, kawai sai ya ɗaga gatarinshi domin ya datse
min wuya, kawai sai wata hikima ta faɗo min na damƙi ƙasa a hannuna na watsa mashi a fuska.
Kafin ya wartsake na miƙe tsaye zumbur na sanya takobina na sare mashi wuya take kan yi fitar
burgu jini ya yi feshi gami da tsartuwa gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica!.
Nan take na faɗi ƙasa bisa gwiwoyina cikin matuƙar galabaita.
Cikin matuƙar kaɗuwa Raudatul-Abyad ta rugawa izuwa inda nake ta rungume a ƙirjinta tana
mai fashe da kuka mai tsuma zuciya duk da kasancewar ina cikin mawuyacin hali sai da naji
sanyi a raina gami da farin ciki. Bisa jin Raudatul-Abyad a daf da ni.
Sannan daga bisani ta janye jikinta daga gare ni muka fuskanci juna cikin alamun matuƙar
tausayi ta dube ni kana ta buɗi baki cikin zazzaƙar murya mai ɗan-karen daɗi tamkar alagita ta
ce "ya kai wannan jarumi ma'abocin sadaukantaka haƙiƙa na yaba da sadaukantakar ka kuma
ma yarda cewa kai mai amana ne, kai ne irin namijin da ya dace ya zamto abokin rayuwata. Ina
mai matuƙar farin cikin sanar da kai cewa za ka cimma nasara.
Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-Abyad sai na cika da matuƙar farin ciki
maral-musaltuwa.
Daga wannan furuci ne kuma ta shiga bani kulawa inda ta tashi tafaɗuna muka isa ƙarƙashin
itaciya ta zaunar da ni sannan ya ɗauko salkar ruwa ta buɗe murfin ta ta sanya hannunta ta

tallafo wuyana ta kafa min a baki na shiga kwankwaɗar ruwan har na ƙoshi, kana ta buɗe wata
jakar fata dake sanye a kwiɓin cinyarta ta buɗe ta ɗauko wani gashasshen naman barewa ta
shiga bani a baki ina ci cikin matuƙar tsantsar soyayya da tausaya wa.
A iya tsawon rayuwata ban taɓa sanin cewa haka so yake da daɗi ba.
Haƙiƙa so shine sinadari mafi girma dake sanya zuciya da ƙarfafa garkuwar jikin ɗan Adam.
So shi ne linzami da yafi ƙugiya ƙarfi wajen sarrafa bil'adama a doron ƙasa.
Haƙiƙa so kan sauya duniyarmu daga kowanne ƘARSHEN KARNI izuwa SABON ƘARNI mai
cike da abubuwan ban mamaki.
Tabbas so shine ni'ima mafi daraja a cikin dukkanin wata al'umma.
A wannan rana haka muka kasance tare da Raudatul-Abyad tana ba ni kulawa mai cike da
tsantsar bege da soyayya.
Sai da la'asar sakaliya sannan muka nufi komawa izuwa gida, da yake a wahale nake sai ya
zamana daƙyar nake iya takawa domin haka kafin mu isa gida duhun dare ya kawo kai. lokacin
da muka samu nutsuwa sai Raudatul-Abyad ta kwashe dukkan labarin abin da ya faru da damu
ta zayyanawa mahaifinta Abu-Raudat daga farko har ƙarshe. Koda jin wannan labari sai farin ciki ya turnuƙe shi bai san sa'adda murmushi mai taushi ya
suɓuce mashi ba ya dube ni cikin murya mai tattare da dattijantaka ya ce "ya kai Matawus kayi
sani cewa kai ne matashi na arba'in da biyar da suka zo gare ni domin na bayyana masu
hanyar da za su haye tekun dake gaɓar mu domin su isa izuwa fadar Sarkin bokaye
Bazzagul-Nadiyar.
Babu wani mahaluki ɗaya a cikin su da ya samu nasarar cinye jarabawar da na yi masu sai kai,
'ya ta Raudat ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance da babu wani ɗa namiji da zai yi tozali
da ita face ya kamu da matuƙar sha'awar ta, amma gashi ka keɓance da ita ba tare da ka haike
mata ba, Sannan kana da halin da za ka ƙi ceto rayuwar 'yata a lokacin da dakarun sumame suka
farauce ta.
Tsawon lokaci ina jiran zuwan jarumin da zan damƙawa amanar 'yata a hannun nagartaccen
namiji, kuma GWARZON ƘARNI amma sai a yau na cimma burina. Kasancewar a halin yanzu
shekaru na sun ja tsufa ya kamani kuma cutar da nake fama da ita a koda yaushe rai zai iya yin
halin shi, domin hakan dole na miƙa ragamar abar kaunata kuma farin cikina ga wanda zai bata
farin cikin rayuwa har abada.
Ina mai farin cikin sanar da kai cewa za ka cimma nasara akan abin da ka fito nema".
Lokacin Tsoho Abu-Raudat yazo nan a zancen shi sai ya sanya hannunshi ya ɗaga gefen
shimfiɗar da yake zaune ya ɗauko wata jemammiyar fatar barewa ya miƙa min sannan ya ci
gaba da cewa "wannan ita ce taswirar da zata kai ka izuwa fadar boka Bazzagul-Nadiyar da
dukkan bayanan kowacce ƙofa da dokokin shiga fadar. Sannan ina mai damƙa maka amanar 'yata ka riƙe min ita cikin aminci, bana sa rai za ku dawo
ku same ni a raye.
Zan haɗa ku da hadimin da zai yi maku rakiya a cikin wannan tafiya har ku cimma nasara.
Koda gama faɗin hakan sai Abu-Raudat ya miƙe tsaye ya durfafi ƙofar fita daga bukkar cikin
hanzari ni da Raudat muka rufa mashi baya.
Ya yin da muka fito ne sai Abu-Raudat ya buɗe bakinshi yana mai karanto waɗansu ɗalasimai
da shi kaɗai ya san me ya ke furtawa.

Yana gama rufe bakinshi sai ga wata shirgegiyar halitta tana keto wa daga cikin gajimare sannu
a hankali wata irin iska mai ta karaɗe wajen, wacce ta haddasa kaɗawar rassan bishiyu sai da
halittar ta sauka a bisa turba sannan komai ya samu dai-daituwa ita dai halittar takasance wani
narkeken ƙaton aljani mai girma da munin tsiya, yana rusheshen kai mai ɗauke da 'yan
mini-minin idanu jajur tamkar garwashin wuta, hancinshi mai girma ne ƙofafin masu faɗi tamkar
mazirari, bakinshi tafkeke ne tamkar ƙofar gari mai ɗauke da waɗansu wargatsattsun haƙora
babu kyawun gani.
Yana ɗauke da manyan fuka-fukai guda goma a kowanne kwiɓin hammatarshi, gaba ɗaya
jikinshi cike yake da wani irin baƙin gashi buzu-buzu.
Babban abun da ya ƙara mashi muni shine wani zabgegen gemun shi mai tsawon kamu shida.
Kaico! Haƙiƙa babu wata halitta mai numfashi da za ta yi tozali da wannan aljani face ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login