Showing 12001 words to 15000 words out of 20550 words
Chapter 5 - KUNDIN ALAJABI Book 1 By MANSUR USMAN SUFI.pdf
a tunanin shi, sai kawai ya cire kai ya dubi sarki Ayumul-barƙas,
sannan ya yi gyaran murya ya ce "na amince zan biya maku wannan muhimmiyar buƙata amma
ina buƙatar ku bani lokaci na yi nazari".
Koda jin wannan batu daga bakin abbana sai sarakunan suka sake duban juna gami da
yiwa juna murmushi mai tattare da tsantsar mugun tanadi.
A can dajin Harbul-zawat kuwa ina zaune tare da mahaifiyata cikin tashin hankali, sai mu kaji
abbana ya yi gyaran murya ya tura ƙofar hujjar, koda muka yi arba da shi sai muka riga izuwa
inda yake suka faɗa kan ƙirjinshi ya rungume mu, muna masu fashewa da kuka.
Sai daga bisani ne ya janye jikinshi daga namu ya dube mu fuskarshi cike da annuri, nan take
ya zayyane mana abin da ya wakana tsakanin shi da sarakunan tun daga farko har ƙarshe.
Koda jin wannan jawabi sai mahaifiyata ta cika da matuƙar farin ciki, amma kuma sai hankalinta
ya dugunzuma ainun, abin da ya dugunzuma hankalin nata shine shin akwai tabbacin cewa
abbana ba zai rasa rayuwarshi wajen shiga tekun Bahar-rum ba?
Sannan wata shaida gare shi dake tabbatar da cewa sarakunan ba su ci amanar shi ba?
Cikin alamun matuƙar damuwa mahaifiyata ta dubi abbana ta ce "haƙiƙa nayi matuƙar farin ciki
bisa jin wannan gagarumin aikin ceton al'umma da zaka yi,
sai dai ina matuƙar tsoron ka rasa rayuwarka a wannan hali, sannan kar mutanen da ka aminta
da su suci amanarka".
Koda jin wannan batu daga bakin ummina sai mahaifina ya yi murmushi a gare ta ya ce "ki
kwantar da hankalinki babu wani sharri da zai same ni, kar ki manta cewa NASARA DA
ƊAUKAKA na tare da ma'abocin gaskiya da riƙon amana, kuma ciki da gaskiya wuƙa bata huda
shi. ke dai ki kasancewa mai yi mani fatan alheri a kodayaushe. Koda jin wannan batu sai muka sake rungume shi cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
Babi na shida
A ranar da tafiya kogon GARUL-SHAMMAR ta zo mun sha kukan baƙin cikin rabuwa da
mahaifina, tamkar ba za mu ƙyale shi ya tafi ba.
Tun daga wannan rana ummina ce ke ɗawainiya da rayuwata, kullum cikin kewar abbanmu
nake, wasa-wasa sai gashi ya shafe tsawon mako uku ba tare da mun ji ɗuriyar shi ba,
al'amarin da ya sanya mahaifiyata ta fara tsammanin ko ya rasa rayuwarshi ne.
Al'amarin abbana kuwa tun sa'adda mu kayi bankwana muna masu zubar da hawayen
rabuwa da juna, sai kawai ya kunna kai izuwa cikin daji yana tafiya cikin hanzari, tafiyar daƙiƙa
hamsin kacal ya yi ya iske su sarki Fitinatul-muluk zaune a bisa kan wani narkeken aljani mai
matuƙar kwarjini muni da ban tsoro shi kaɗai suke jira, ba tare da wani ɓata lokaci mahaifina ya
haye bisa kan aljanin ya zauna kamar yadda sarakunan suka yi.
Cikin kuzari aljanin ya buɗe manyan fuka-fukanshi ya luluƙa izuwa sararin samaniya yana mai
keta gajimare cikin matuƙar sauri tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.
Tafiyar sa'a uku kacal aka yi aka iso tekun Bahar-rum, cikin hanzari aljanin ya saki fuka-fukanshi
ya yi ƙasa luhh! Ya sauka a dai-dai ƙofar shiga kogon, cikin hanzari sarki Ayumul-barƙas ya fara
sakkowa sai Fitinatul-muluk, Hubaizu, Abul-uyum mafarauci Yasiran ne a ƙarshe.
Ba tare da wani jinkiri ba sarakunan suka zira hannayensu a aljihun rigar su sai ga shi
kowannen su ya fito da ɓarin kubarshi, fuskokinsu cike da murmushin mugunta suka haɗa su a
waje guda, faruwar hakan ke da wuya sai aka kwantsama wata tsawa da walƙiya a sararin
samaniya, kubar ta kammala jikinta baki ɗaya. Fuska a murtuke babu annuri sarki Fitinatul-muluk ya miƙawa abbana kubar ya sa hannu ya
ƙarba, sannan ya dube shi fuskarshi babu yabo babu fallasa ya ce "ya kai Yasiran kayi sani
cewa wannan kuba ta Miftahul-sihir da muka baka da ita ne zaka buɗe kofar wannan kogon
dutse har ka samu nasara ɗauko KUNDIN AL'AJABI daga cikin shi". Koda jin wannan daga bakin Fitinatul-muluk sai mahaifina ya yi jim! Tamkar mai tunanin wani
abu, koda ganin halin da mahaifina ya shiga sai sarakunan suka bayyanar da murmushi akan
fuskokinsu, da ganin hakan sai abbana ya ji ya samu nutsuwa kawai sai ya juya ya durfafi ƙofar
kogon GARUL-SHAMMAR yana isa ya sanya kubar a cikin wani kwaroron rami da ke jikin
makekiyar ƙofar kogon da aka yi ta da zallar mulmulallan baƙin ƙarfe, ya murɗa kubar sau huɗu
da dukkan ƙarfin shi, take sakatun suka shiga ƙara, zuwa can sai ƙofar ta yi wani ƙara da ya
cika dajin baki ɗaya, sannan ta buɗe kanta, wani irin tururin hayaƙi ya surnano daga ciki, ba tare
da wani tsoro ko fargaba ba, mahaifina ya kunna kai izuwa cikin kogon tare da sanya kubar
Miftahul-sihir a cikin aljihunshi, lokacin da ya kammala shiga sai ƙofar ta mayar da kanta ta rufe
ruf!.
Daga ciki kogon GARUL-SHAMMAR ya kasance makeke mai matuƙar tsawo da faɗi, yana
ɗauke da saƙarƙaƙiya da lunguna, gaba ɗaya gine ginen dake ciki an yi su ne da waɗansu
manyan duwatsun wuta masu ƙwarin gaske, gaba ɗaya kogon dutsen a haskake ta yadda koda
allura ce ta faɗi a ƙasa da ya duba zai gani, kuma a ƙasa a zube akwai kwarangwal ɗin
bil'adama da wasu halittu gasu nan birjik.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, inda a ce abbana ya san abin da zai faru da bai
ya gangancin kutsawa kai cikin kogon ba, domin abin da bai sani ba shine, waɗannan
kwarangwal ɗin sun kasance tarin miyagun aljanu.
Lokacin da ya zamana ya iso tsakiyar kwarangwal ɗin, nan take ruhikansu suka fara dawo
jikkunansu kuma surar tana haɗuwa, kafin cikar daƙiƙa hamsin baki ɗaya halittun sun miƙe
tsaye.
Aljanun sun kasance gabza-gabza masu ƙirar samudawan farko, jikkunansu irin na bil'adama
ne amma kawunansu irin na tsuntsun batoyi ne, idanuwansu jajur suke tamkar garwashin wuta,
a ƙugunsu suna maƙale da wata murtukekiyar jela irin ta kada, sannan dukkanin suna shirye
cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini muni daban tsoro, a hannayensu suna ɗauke
da waɗansu irin makaman yaƙi masu kama da zarto.
Haƙiƙa Waɗannan aljanu sun kasance ababan tsoro da razani ga duk wata halitta mai
numfashi.
Lokacin da mahaifina ya yi arba da halittun sai jikinshi ya kama tsuma yana kyarma saboda
matuƙar tsoro, amma sai ya yi wuf! Ya zare takobinshi aka fara kallon-kallo tsakani, tsawon
daƙiƙa arba'in ɗayan su bai yunƙurin afkawa abokin gwamin shi ba.
A lokaci guda tamkar haɗin baki dakarun suka ɗaga makamansu suka yi ɗauki kan Yasiran
suna ihu da kururuwa mai firgitarwa, tare da kai mashi miyagun hare-hare cikin matuƙar zafin
nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance. Take mahaifina ya tare su aka ruguntsume da
azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, a lokacin da dakarun suka yanyame shi
tamkar yadda dandazon ƙudaje ke yanyame ƙwallon mangwaro.
Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce inda babu ƙasa nan ake
gardamar kokowa, kuma KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka saba gwagwarmaya a
filin fama, nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe da ihu da hargowar dakarun aljanun ta cika kogon
baki ɗaya, kuma kogon ya ɗauki zafi ainun, tamkar zai yi bindiga ya tarwatse, sai da aka shafe
tsawon sa'a ɗaya da daƙiƙa ɗari uku ana wannan ɗauki ba daɗi.
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa aljanun kai kenan kuma ya ba su mamaki, domin fiye da
shekaru dubu biyu suna gadin wannan kogon na GARUL-SHAMMAR ba su taɓa ganin halitta
mai matuƙar zafin nama da ƙwarewar yaƙi tamkar na mahaifina ba.
Al'amarin mahaifina kuwa lokacin da ya fahimci cewa babu alamun nasara, kuma koda alamun
gajiya babu a tare da dakarun sai hankalinshi ya dugunzuma ainun ya faɗa izuwa kogin tunani
domin samun mafita, koda samun mafitar sai kawai ya mayar ta takobinshi izuwa cikin kube, ya
yi wuf ya zaro kubar Miftahul-sihir ya shiga dukan dakarun da ita da dukkan ƙarfin shi. Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce, idan kiɗa ya canja dole ne
rawa ma ta canja, nan fa abbana ya gano lagon tsuntsayen ya zamana cewa duk wanda ya
daka da kubar sai kaga ya kurma wawan ihu ya tarwatse, nan fa ihu da kururuwar shaiɗanu ta
ƙara cika kogon, kafin shuɗewar rabin sa'a, nan fa dakarun suka ɗimauce suka kama guye-guje
da ifice-ifice, wasu suka shiga ƙoƙarin ƙwace kubar Miftahul-sihir daga hannun abbana, wasu
na kai mashi sara da suka cikin matuƙar zafin nama, domin ganin sun kai shi ƙas.
Ana cikin wannan artabu ne wani daga cikin aljanun ya shammaci mahaifina ya kafta mashi
sara a cinya, take inda ya yanke shin ya dare jini ya yi tsartuwa, abbana ya kurma ihu
sakamakon zafi da raɗaɗin da ya ji amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta JARUMAN
DUNIYA sai ya ci gaba da yaƙin a haka ba tare tsaida zubar jinin ba, haka ya ci gaba da yaƙin
jiri na ɗibar shi a wasu lokutan har yanke jiki yake ya faɗi ƙasa amma sai ya miƙe tsaye zumbur
ya ci gaba da yaƙin a haka.
Kaico! Haƙiƙa jarumtaka baiwa ce daga Ubangiji, dukiya, mulki basu bayar da ita face baiwa
daga Allah, komai hassadar mutum idan ya ga yadda mahaifina ke ragargazar dakarun cikin
baƙin zafin nama da kafin tsiya, dole ya jinjina mashi ya tabbatar da cewa ya cika gwarzon
mayaƙi mai ƙarfi na Allah ya isa. Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA YAFI SARKIN ƘARFI qna cikin wannan
artabu ne mayaƙan suka samu nasarar kai abbana ƙasa suna niyyar hallaka shi, koda ya ga
irin mawuyacin halin da yake ciki da yake tsakanin RAYUWA DA MUTUWA, bai san sa'adda ya
buga kubar Miftahul-sihir a ƙasa ba, faruwar hakan keda wuya nan take wani farin haske ya yi
fitar burgu daga kubar, ya shiga sassan jikkunan sauran aljanun, nan take suka kama ci da
wuta suna ihu da kururuwa neman taimako, kafin wani lokaci mai tsawo baki ɗayan su sun
sheƙa barzahu.
Cikin matuƙar farin ciki abbana ya miƙe tsaye da ƙyar ya sake kunna kai izuwa cikin kogon,
Tsawon daƙiƙa ɗari huɗu yana tafiya sannu-sannu,
lokacin da rabin sa'a ta shuɗe a dai-dai lokacinne ya iso wani waje mai matuƙar sanyi, hatta
durakun dake wajen na dusar ƙanƙara ne, babu wani waje da mutum zai ajiye ƙafarshi face
dusar ƙanƙara ce.
Sa'adda mahaifina ya tsinci kanshi a cikin wannan hali sai hankalinshi ya dugunzuma ainun,
domin baya sanye ɗauke da rigar kariya daga sanyin.
Cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi mai zafi ya kama mahaifina jikinshi ya kama ƙyarma, tun yana iya
takawa da ƙafafuwanshi har ya zamana ya zube a ƙasa magashiyan nunfashin shi na fita
daƙyar.
Yana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai kawai wani irin ƙatuwar
halitta tayo fitar burgu daga dusar ƙanƙarar ta fito waje, Ita dai halittar takasance wata
shirgegiyar macijiya mai kauri tamkar bishiyar kuka, jelar murtukekiya ce, bayan ƙaton kanta
tana ɗauke da ƙarin wasu guda biyu, na farko yakasance na zaki, ɗayan kuma na raƙumin
dawa.
Kaico! Wannan halitta ta kasance mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, babu wani jarumi da zai yi
arba da ita face ya yi nadamar wanzuwar shi a doron ƙasa.
Babi na bakwai
A can bakin ƙofar shiga kogon GARUL-SHAMMAR sarakunan duniya huɗu suna tsaitsaye
suna jiran fitowar mahaifina fuskokinsu a murtuke babu annuri cike da matuƙar kiyayyar juna.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai suka ga sararin samaniya ta yi duhu dunɗum! Tamkar
DARE UKU ne ya haɗu waje guda mutum koda tafin hannunshi baya iya gani.
Sannu a hankali duhun dake sararin samaniya ya fara raguwa, sai ga waɗansu halittu masu
tarin yawa suna ketowa daga cikin gajimare suna sauka a kan tekun Bahar-rum.
Koda ganin hakan sai sarki Fitinatul-muluk da sarki Hubaizu suka yi wuf suka fito da maduban
tsafin su suka shiga gudanar da bincike, koda kammala binciken sai suka taƙarƙare suka bushe
da dariyar mugunta, ba komai suka gani ba face halittun da suka bayyana sun kasance
rundunar sarakunan duniya biyu, sarkin aljanu baƙaƙen fata da farare. Sun turo tawagar ne domin su ƙwaci KUNDIN AL'AJABI da kubar Miftahul-sihir da zarar
mahaifina ya samu nasarar ɗaukowa.
Sarki Hubaizu na birnin Hindu ya katse shirun da ya wanzu a q hanyar duban sauran 'yan
uwanshi fuskarshi a murtuke babu annuri ya ce "yaku manyan abokan gaba a gare ni ku yi sani
cewa waɗancan dakarun aljanu da suka bayyana ba su ba ne face Tawagar sarakunan aljanu
da suka zo domin ɗaukar kubar Miftahul-sihir haɗe da KUNDIN AL'AJABI, saboda haka yanzu
dole mu haɗa kai mu kawar da waɗannan sabbin abokan gaba, idan ya so daga baya kuma sai
a raba rai tsakanin mu ga wanda zai zamo zakara a, da zai zamo mamallakin KUNDIN
AL'AJABI".
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Hubaizu na birnin Hindu sai sauran sarakunan uku
suka zare makaman yaƙin su suka yi ɗauki kan dakarun aljanun, koda ganin hakan sai aljanun
suka tare su suna ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
***
A cikin kogon GARUL-SHAMMAR kuwa kafin mahaifina ya yi wani yunƙuri wannan macijiya ta
kafta masa sara a hannayenshi da ƙafafuwanshi, nan take nunfashin shi ya fara sarƙewa kuma
ya faɗi ƙasa magashiyan".
Lokacin da kyakkyawar baƙuwar jaruma ta zo dai-dai nan a labarin da take bamu sai
hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta.
Al'amarin da ya sanya jikinmu ya yi sanyi ni da Raudat har ƙwalla ta zubo mana.
Cikin alamun matuƙar tausayi na dubi jarumar na ce "haƙiƙa labarin mahaifinki cike yake da
abun tausayi darasi da abubuwan al'ajabi. Kuma ya cancanta ki ɗauki ko wane mataki domin
daukarwa mahaifinki fansa, duk da cewar ba mu ji ƙarshen abin da ya faru tsakanin abban ki da
manyan sarakunan duniya huɗu ba, duk da cewar da farko mun nufi mu yaƙe ki, amma a halin
na ji a raina ni da abokiyar tafiyata za mu taimaka miki ki cimma wannan buri na ki. Amma bisa
sharaɗin cewa ba za ki cutar da wani mahaluki ba idan har kin samu nasarar mallakar
makaman yaƙin sarkin bokayen duniya".
Sa'adda na zo nan azance na sai fuskar baƙuwar jarumar ta faɗaɗa da murmushi mai taushi, ta
dube mu sannan ta yi gyaran murya ta ce "ya ku waɗannan jarumai haƙiƙa nayi matuƙar farin
ciki da wannan taimako da za ku ba ni, kuma ina mai tabbatar maku da cewa ba za ku same ni
da wani abu na cin amana ko yaudara ba. Kuma a halin yanzu ba zan iya ci gaba da ba ku labarin mahaifina ba sai dai anan gaba, sai dai
ban sanar da ku suna na, mahaifna na kira da suna Sulairat bintu Yasiran".
Sa'adda Sulairat yar mafarauci Yasiran ta zo dai-dai nan azancen ta sai na yafito aljani
Jauharul-layal dake tsaye a gefe guda da hannu da ya iso inda muke, taku ɗaya kacal ya yi ya
iso gare mu ba tare da wani jinkiri ba Raudat, Sulairat suka haye gadon bayan shi, take na yi
koyi da su ina mai zama da daf da inda suke yazamana tazarar dake tsakaninmu bata huce
kamu ɗaya ba,
A halin yanzu tafiya ta sauya salo daga mutum biyu izuwa uku, wato ni Raudatul-abyad sai
jaruma Sulairat.
Sai da muka shafe tsawon sa'a huɗu muna keta gajimare cikin matsanan gudu na keta sa'a, ɗa
ya daga cikin mu bai ce uffan ba, a wannan lokaci ne Raudatul-abyad ta lura da cewa Sulairat
na satar kallo na lokaci zuwa lokaci, koda ganin hakan sai ta daka mata wata harara dake nuna
tsantsar kishi da soyayya. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai mu ka ga aljani Jauharul-layal ya tsaya cak! A
sararin samaniya, cikin fushi Raudatul-abyad ta dube shi tana mai daka mashi tsawa ta ce "ya
kai Jauharul-layal shin ina dalilin wannan tsayuwa ta ka bayan ka san cewa muna so mu isa
fadar sarkin bokaye Bazzagul-nadiyar cikin sauri ? Koda jin wannan tambaya sai Jauharul-layal ya risina cikin ladabi ya ce "ki gafarce ni ya
shugabata bakomai ne ya sanya na dakatar da tafiya ba face bisa jiyo ƙanshin 'yan uwana
aljanu a daf da mu, hakan ya tabbatar min da cewa akwai waɗanda ke biye da mu…"
Karfin jauharu ya gama rufe bakinshi kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu ka ga tawagar
waɗansu zaratan aljanu kimanin dubu hamsin, sun bayyana a suna masu yi mana ƙawanya, su
dai aljanun sun kasance bakaƙe wuluk, masu girma, kwarjini da munin gaske, fuka-fukansu irin
na mikiya ne, a gadon bayansu suna ɗauke da wani ƙusumbi da ya tamkar duwatsu aka saka
masu, duk sa'adda da suka buɗe bakunan sai wani ruwa mai yauƙi mai warin gaske ya zubo.
Baki ɗayan su suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, kuma
girman kowannen su ya ninka na aljani Jauharul-layal sau goma.
Wohoho! Haƙiƙa waɗannan tawagar ifritai ta cika abar tsoro ga duk wata halitta mai numfashi,
nan fa muka zo tamkar an ajiye kyanwa a gaban garken raƙuma.
BABI NA TAKWS
Lokacin da boka Matawus yazo dai-dai nan a hikayar da yake bawa sarki Sabrul-marhut
sai ya ja dogon goron numfashi sannan ya ɗora da cewa.
Lokacin da aka fara kallon-kallo tsakanin mu na tsawon daƙiƙa arba'in sai daga bisani ne
shugaban tawagar ifritan aljanun ya ratso ta tsakiyar ya matso daf da mu ya dube mu da
turɓunanniyar fuskarshi da ninka