Showing 15001 words to 18000 words out of 20550 words

Chapter 6 - KUNDIN ALAJABI Book 1 By MANSUR USMAN SUFI.pdf

ta sauran muni, cikin wata irin kakkausar murya mai kama da
saukar aradu ya ce "ya ke Raudatul-abyad tare da tawagarki kiyi sani cewa yau tsawon shekaru
dubu da ɗoriya ina jiran zuwan wannan rana da zan karɓi taswirar fadar sarkin bokaye daga
hannunki, tsawon shekaru ina bibiyar mahaifinki domin ya mallaki taswirar amma saboda sirrin
dake tare shi ban samu wannan dama ba sai a yanzu".
Koda jin wannan batu daga bakin shugaban tawagar sai Raudat ta tari numfashinshi tana
mai daka masa tsawa ta ce "ya kai wannan rafkananne kuma tsohon AZZALUMI ka yi sani ce
wa, ire-iren ka ba za su taɓa cimma buƙatar su domin mallakar wannan taswira ba, domin
shimfiɗa BAƘIN ZALUNCI, shawara ɗaya zan baka ita ce ka janye waɗannan 'yan tsakin
mayaƙan na ka, idan kuwa ba haka ba zaka yabawa aya zaƙinta…".
Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-abyad sai shugaban tawagar ya fusata ainun
jikinshi ya kama tsuma ya ƙyarma tamkar mazari, idanuwanshi suka kaɗa suka yi jajur, ya buɗi
baki a karo na biyu cikin matuƙar fushi har wani irin tururin baƙin hayaƙi na fita daga ƙofofin
hancinshi, baki da kunnuwa ya ce " kaicon ki yake wannan ƙaramar ƙwaruwa haƙiƙa kin tafka
babban kuskure, wanda ba zan iya yafe miki ba face na shayar dake gidauniyar azabata da
dukkanin abokan tafiyar ki, sai dai kafin hakan akwai buƙatar na sanar dake wane ne ni, da
farko dai suna na ifritu Sulsainil-auman ibn Turbus, shugaban ifritan aljanun duniya baƙaƙen
fata. Da wannan nake yi miki bankwana ga maza nan bisa kan ki".
Koda shugaban ifritai Sulsaini ya zo nan a zancen shi sai ya yi ihu da kururuwa mai firgita
GWARAZAN JIYA a FAGEN FAMA ya afka Raudatul-abyad, take sauran yaran shi suka afka
mana ni da Sulairat da Jauharul-layal.
A can ƙololuwar sararin samaniya inda Allah (SWT) ya yiwa dukkan halittu iyaka kuwa,
anan ne uwar mayu Ummul-sharri ta kafa fadarta domin gudanar da ƙasaitaccen mulkinta,
A wannan lokaci Ummul-sharri tana zaune a bisa karagar mulki a cikin gawurtacciyar fadarta,
Ita dai fadar ta ƙasaitacciya tamkar gari guda, gaba ɗaya ginin fadar an yi shi ne da zallar
waɗansu irin duwatsu masu ƙwari gaske suna sheƙi da ƙyalli tamkar gilashi, duk inda mutum zai
ajiye ƙafarshi wani irin koren gilashi ne mai kama da darduma, idan mutum ya kalla yana iya
ganin surarshi, gefe guda kuwa 'yan majalisa na jinsin mutum da aljan na zaune bisa ƙayatattun
kujeru na alfarma, a kowa ce kusurwa a fadar dakarun tsaro ne na jinsin mutum da aljan ɗauke
da miyagun makamai suna kai komo domin tabbatar da cikakken tsaro, a bisa wata matattakala

mai hawa goma anan aka ajiye karagar mulki da aka yi ta da sallar jauhari, kai tsayawa masalta
tsaruwa da ƙawatuwar fadar ya huce hankali, kai wani abun ma ko jin sunan shi bai taɓa yi ba,
kana gani ka san aiki ne na sihiri.
Shiru ne ya mamaye wajen tamkar mutuwa ta kawo ziyara, uwar mayu Ummul-sharri ce
ta katse shirun da ya wanzu ta hanyar sanya hannunta a aljihun rigarta ta ɗauko madubin
tsafinta da girmanshi bai zarce faɗin tafin hannuna ba, ta shafe da hannunta na hagu gami da
runtse idanuwanta ta karanta waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama furtawa sai ga taswirar
gumurzun dake wanzu tsakanin tawagar ifritu Sulsainil-auman da su jarumai Raudatul-abyad ya
bayyana a kan madubin.
Koda ganin hakan sai uwar mayu ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, mai kama da
haniniyar dawakai, sautin ta ya mamaye fadar baki ɗaya, al'amarin da ya firgita wasu daga cikin
jama'ar fadar kenan cikinsu ya ɗuru ruwa, domin sun san cewa duk sa'adda uwar mayu tayi
wannan dariya to za ta zartar da wani baƙin zalunci, tsawon daƙiƙa arba'in tana cikin wannan
hali sai daga bisani ta murtuke fuska tamkar an aiko mata da WASIƘAR AJALI, kawai sai ya
mayar da madubin izuwa ma'ajiyar shi, kana ta dawo da dubanta zuwa ga wani mummunan
aljani daga cikin 'yan majalisarta, tamkar ya san abin da take nufi kawai sai ya miƙe tsaye ya
matsa daf da karagar mulki ya zube ƙasa ya yi sujjada a gare ta, sannan daga bisani ya ɗago
kanshi a ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da haushin kare ya ce "gani gare ki ya
SARAUNIYA MAI DUNIYA, gajimare kike mai shayar da duniya mugunyar annoba.
Guguwar musiba mai share TAWAGAR ZARATA.
ina gagararre ko hatsabibi ya zo ga GAWURTACCIYA uwar matsafan dunya"
Kin ci dubu sai ceto kin yi KARO DA DUBU kalacen safe, ina mazan suke ne ga sa gudu
maganin ƙi gudu"
ANNOBA ƊARI kike duk wanda ya ja dake zai baƙunci barzahu".
Lokacin da ɗan majalisar ya zo nan a kirarin na shi sai uwar mayu ta yi murmushi mai
kama da yaƙe da ya ƙara tona asirin munin fuskarta, bisa jin daɗin kirarin da yake yi mata.
Sannan ta buɗe tafkeken bakinta mai ɗauke da waɗansu wargatsattsun haƙora baƙaƙe babu
kyawun gani ta ce "an gaishe ka ya kai Darmanu maganin ƙananan ƙwari abin da nake so a
gare ka shine ka tafi cikin hanzari izuwa gaɓar dajin Zarutul-shammar domin ka ƙwato min
taswirar fadar sarkin bokaye a hannun jaruma Raudatul-abyad, ina mai farin cikin sanar da kai
cewa burina ya kusa cika na shiga fadar sarkin bokaye domin na gaje komai nashi, sirrikan tsafi
da kayan yaƙinshi, dole ne duniya ta zamto a tafin hannuna, na juya ta tamkar yadda ake
sarrafa waina a tanda,
Wannan ita ce dama ta ƙarshe a gare mu domin shiga fadar sarkin bokaye don haka ina mai
gargaɗarka ka kula sosai kar a samu kuskure a cikin wannan aiki”.
Sa’adda Uwar mayu Ummul-Sharri ta zo nan a jawabinta sai aljani Darmanu ya risina ya ce “an
gama ya shugabata wannan aiki abu ne mai sauƙi a gare ni tamkar cire silin gashi daga cikin
tandun mai”.
Ummul-Sharri ta ce “tsafi ya baka kariya ka dawo cikin aminci ya kai Darmanu”.
Koda gama faɗin hakan sai Darmanu ya risina ga uwar mayu sannan ya rikiɗa izuwa wani baƙin
haske ya ɓace ɓat daga fadar tamkar bai taɓa wanzuwa ba.
Wannan shi ne abin da ya wakana a fadar uwar mayu ta duniya matsafiya Ummul-Sharri.

Lokacin da muka kacame da azababban yaƙi tsakaninmu da shugaban ifritai Sulsaini da
yaranshi sai muka wanzu muka kaiwa juna hare-hare cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA
BAJINTA ta gaban kwatance, ana fara wannan artabu ne dukkaninmu suka fara gane cewa
shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin matuƙar zafin nama gami da ƙarfin damtsen ifritan
ya ninka namu sau biyar, babban abin da ya dugunzuma hankalinmu shine yadda duk sa'adda
makaman yaƙinmu suka sari jikkunan ifritan sai mu ji tamkar dutse muka sara, ko gezau ba sa
yi sai dai tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara ƙal! Ƙal!.
A duk sa’adda makaman yaƙinmu suka haɗu da juna sai ka ji an kwantsama wata tsawa gami
da walƙiya, nan fa sararin samaniyar ya cika da ƙarar karafniyar ƙarafa, ihu gami da hargowar
MAZAJEN DUNIYA.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu da goma ana wannan ɗauki ba daɗi babu sassauci.
A cikin wannan artabu ne na fahimci Sulairat tafi mu ƙarfin damtse da salon dabarun yaƙi,
domin a hankali yanzu tana iya samun nasarar yankan jikkunan ifritan, koda suka fahimci irin
ɓarnar da Sulairat ke yi masu sai suka yanyame ta suna kai mata sara da suka gami da yakushi
da faratansu. A ɓangaren aljani Jauharul-layal kuwa ya wanzu yana kai FARMAKI da fuka-fukanshi, bakinshi
gami da faratan hannunshi, cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance.
Lokacin da shugaban ifritai Sulsaini ya ga cewa sa'a ɗaya ta shuɗe ana wannan baƙin
artabu sai ya fusata ainun zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone, ya fahimci cewa
wankin wula zai kai su dare, wani abu da ya fusata shi shine tun da yake yin GABA DA GABA
da jarumai bai taɓa haɗuwa da bil’adama masu matuƙar zafin nama da ƙarfin damtse tamkar
mu ba.
Lokacin da sa'a ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi, sai ƙarfin damtsenmu ya
fara raguwa yaran ifritu Sulsaini suka fara galabaitar da mu, faruwar hakan ke da wuya sai
Aljani Sulsaini ya yi ƙara luhhh! Domin ya zillewa ifritan, amma sai hakan ya faskara domin
kadoni ya kai ga hakan wani daga cikin ifritan me nacin tsiya ya kafta masa sara a kafaɗarshi,
saboda matuƙar ƙarfin sara sai da Jauharul-layal ya kurma wawan ihu, saboda raɗaɗi da zugin
da ya ji.
Sa’adda jaruma Sulairat taga halin da muke ciki, kuma ta fahimci cewa a koda yaushe
ɗayanmu na iya raya rayuwar shi, sai kawai ta shiga amfani da ƙarfin shirin tsafi amma ya zamo
a banza, domin da idan ta yi TSATSUBA ta turawa ifritan Kibbau na huta da zarar sun doshi
inda suke sai suka zama farin haske su ɓace ɓat! Ana cikin wannan wannan fafatawa ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga sararin
samaniya tayi duhu dunɗum! Tamkar DARE BIYU ne ya haɗu waje guda, kuma aka dinga
kwantsama tsawa da walƙiya kai ka ce za’a kece da ruwan sama tamkar da bakin ƙwarya.
Daga can sai aka ga wata shirgegiyar halitta ta bayyana a sararin samaniya, halittar tana da
matuƙar girma fiye da aljani Jauharul-layal, tana ɗauke da fuka-fukai goma a tsakiyar kanta tana
ɗauke da wani zabgegen ƙaho mai kama da na rago, batun munin fuskarta kuwa sai abin da
idanu suka gani kawai, a gadon bayanta tana ɗauke da wata sharɓeɓiyar takobi. Kaico! Haƙiƙa
wannan halitta ta cika abar tsoro ga duk wata halitta mai numfashi, ba wata ba ce wannan
halitta ba face aljani Darmanu manzon uwar mayu Ummul-Sharri, wanda ta tura domin ya
ɗauko mata taswirar fadar sarkin bokaye Bazzagul-nadiyar.
Sa’adda kowa ya yi arba da aljani Darmanu sai aka tsayar da yaƙi kallo ya koma kanshi.

Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan kallon-kallo sai daga bisani aljani Darmanu ya
taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta mai kama da saukar aradu wacce ta ɗimauta duk wata
halitta dake wajen hatta ifritu Sulsaini da yaranshi, a lokaci guda ya tsuke bakinshi ya fara
magana cikin wata irin kakkausar murya mai kama haniniyar doki yana mai cewa “Ya ku waɗannan ƙananan halittu ma’abota ƘARAR KWANA ku yi sani cewa ban zo nan domin
kallon fafatawar da kuke yi ba, face sai domin ya karɓi taswirar fadar sarkin bokaye domin na
kaiwa uwar matsafan duniya Ummul-Sharri, kira na a gare ku shine ku gaggauta miƙo min
taswirar cikin ruwan sanyi domin na yi maku kisa mafi sauƙi ba tare da kun sha wahala ba, ta
hanyar da daddatsa sassan jikkunanku.
Kafin Darmanu ya gama rufe bakinshi ifritu Sulsaini ya yi ƙarfin hali ya tari numfashin shi yana
mai daka masa tsawa ya ce “ ya kai wannan maƙetaci kuma wanda rarraunar zuciyarshi ke
yaudarar sa ka ji sani cewa ka tafka babban kuskure, da kake tunanin za ka ƙwaci taswira daga
hannun Jaruma Raudatul-abyad, bayan muna gab da mallakarta, wato kura da shan bugu gardi
da ƙwace kuɗi”.
Koda jin wannan batu daga bakin ifritu Sulsaini sai aljani Darmanu ya fusata ainun,
idanunshi suka kaɗa suka yi jajur, gashin jikinshi ya mimmiƙe, kawai sai ya miƙa hannunshi
izuwa sama sai ga wata zabgegiyar takobi ta bayyana ta haske, take ya yi ɗauki izuwa kan
Sulsaini da tawagarshi, ana haɗuwa aka yi KARON BATTA, nan fa aka garƙame da sabon
gumurzu mai matuƙar muni ban tsoro gami da tashin hankali, a wannan karon sai artabun ya
canja salo, domin a wannan karon duk inda aljani Darmanu ya sanya a gaba sai dai kaga yaran
ifritu Sulsaini na sheƙawa barzahu, takobinshi na raba sassan jikkunansu.
Nan fa muka shiga raba idanu domin ba su san wane ɓangare zamu shigarwa yaƙin ba, tun da
dukkanin su abokan gabarmu ne.
Muna cikin wannan hali ne wata dabara ta faɗo min, koda samun mafitar sai kawai na yiwa
aljani Jauharul-layal inkiya ta wutsiyaar idanu, koda ya fahimci abin da nake nufi sai ya faki
idanun TAWAGAR ABOKAN GABA ya kaɗa fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuu! ya keta cikin
gajimare ya fara tsala azababban gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya muka ɓace ɓat!
Har muka daina hango so.
Lokacin da muka shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu suna gudun tsira da rayuka, sai ƙarfin
gudun Jauharul-layal ya fara raguwa ainun saboda gumurzun da aka sha, domin hakan sai aka
yanke shawarar mu yada zango domin mu huce gajiyar dake tattare da mu, cikin hanzari
Jauharu ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuu! Ya sauka a turba, inda muka saukar ya kasance
daji mai tattare da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, duwatsu, ƙoramu gami da sarƙaƙiya, muna
sauka ne dukkaninmu kowa ya sha jinin jikinshi, domin da ganin dajin ba a rasa miyagun halittu
masu cutarwa ba.
Da yake akwai inuwar bishiyu sai ya zamana cewa bamu kafa tanti ba, aka fito da abin kalaci
kowa ya shiga kimtsa cikinshi.
A wannan lokaci ne jaruma Sulairat ta duba mu tayi gyaran murya sannan ta ce “tun da a halin
yanzu dukkaninmun mun samu natsuwa zan cigaba da baku labarin abin da ya wakana da
abbana tare da manyan sarakunan duniya uku, inda ta ɗora da hikayar kamar haka:-


BABI NA TARA

Sa’adda abbana ya yi arba da macijiyar sai jikinshi ya kama tsuma yana ƙyarma saboda
matuƙar firgici, domin a iya tsawon rayuwarshi bai taɓa ganin halitta mai matuƙar kwarjini da
muni tamkar macijiyar ba.
Kafin ya yi yunƙuri ta kafta masa sara a dukkan sassan jikinshi, ya faɗi ƙasa magashiyan yana
mai aman jini ta baki da hanci, kuma wani zazzaɓi mai zafi ya kama shi ya kama ƙyarma tamkar
zai sheƙa barzahu.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai macijiyar ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta,
dariyar ta ta ta haddasa wata irin gagarumar iska. A lokaci guda ta tsuke baki tamkar an aiko
mata da saƙon mutuwa, sannan ta buɗe bakinta dake maƙale a jikin kanta mai siffar gwaggwan
biri cikin wata irin kakkausar murya ta dubi abbana ta ce “ya kai wannan bil’adama ka yi sani
cewa haƙiƙa kai mutum mai matukar sa'a da rabo a rayuwarshi, domin kai ne mahaluki na farko
da ya shigo wannan kogo fiye da shekaru dubu uku domin ɗaukar littafin KUNDIN AL'AJABI, sai
dai ina farin cikin sanar da kai cewa kai ne bil’adama na ƙarshe da zai sake shigowa wannan
waje, yanzu ba tare da wani ɓata lokaci ba zan rugurguza ƙasusuwanka ka yi mutuwar
wulakanci”.
Koda tazo nan a zancenta sai ta sake bushewa da dariya a karo na biyu, kawai sai ta sanya
jelarta ta kanannaɗe mahaifina ta ɗaga shi izuwa sama, sannan ta buɗe bakinta ɗaya ta jefa
abbana ciki tayi loma ɗaya da shi ta rufe rufe! Tamkar ta haɗiye ƙwallon dabino.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu. In da ace wannan macijiya ta san abin da zai faru da
bata haɗiye abbana ba, domin kuskuren da ta yi shine ta haɗiye shi tare da kubar Miftahul-sihir.
Sa’adda mahaifina ya tsinci kanshi a cikin macijiyar sai nan take ya ji dukkan zazzaɓin dake
jikinshi ya rabu da shi, tamkar a cire silin gashi daga cikin tandun mai, kuma ya samu ƙwarin
jikinshi, nan take wata hikima ta faɗo mashi ya ɗauki kubar Miftahul-sihir ya shiga dukan sassan
cikin macijiyar. Kaico! Nan fa macijiyar ta shiga mawuyacin hali domin duk sa’adda abbana ya
daki wani ɓangare a jikinta sai ta ji tsananin azaba tamkar da wuta ake ƙona ta.
Nan fa ta shiga guje-guje da ifice-ifice a cikin kogon saboda matuƙar azabar da take sha, take
ta shiga ƙaƙari ta amayo mahaifina daga cikinta ya faɗo ƙasa tim! Kafin shuɗewar daƙiƙa
hamsin jikin macijiyar ya sandare ya daina motsi, kuma wata ƙofa ta musamman ta bayyana a
ƙarƙashinta, hatta tsananin sanyin dake kogon dutsen ya ɗauke. Cikin matuƙar farin ciki mahaifina ya miƙe tsaye cikin ƙwarin gwiwa ya kunna kai izuwa cikin
wannan ƙofa hannunshi ɗauke da kubar Miftahul-sihir.
A can gaɓar tekun Bahar-rum kuwa manyan sarakunan duniya haɗu da na aljanu gami
da rundunoninsu sun wanzu suna bawa hammata iska. Nan fa manyan sarakunan huɗu,
Abul-uyum, Ayumul-barƙas, fitinatul-muluk da sarki Hubaizu suka zamto tamkar GOBARAR
DAJI a tsakiyar mayaƙan, duk inda ɗayan su ya sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa
ƙasa tamkar ana sassabe a gonar auduga, sun haddasa fili fetal.
Nan fa gagarumar walima ta ɓarke a tsakanin halittun dake ƙarƙashin tekun, suka shiga
watanda da sassan jikkunan dakarun.
Babu abin da zai bawa mutum mamaki kuma ya ɗaure mashi kai face yadda gwarazan
sarakunan huɗu ke fafatawa tamkar jikkunnansu ba su kasance na jini da tsoka ba.
A ɓangaren sarakunan aljanu kuwa, koda suka ga irin ɓarnar da su sarki Ayumul-barƙas ke yi
masu sai suka fusata ainun, kuma suka faɗa izuwa kogin tunani, abu na farko da ya faɗo masu
a rai shine matuƙar basu canja salon yaƙin su ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login