Showing 12001 words to 13155 words out of 13155 words
Chapter 5 - KANGIN BAUTA Book Complete by Mansur Usman Sufi .pdf
yarima da
sarkin yaƙi su fahimci wani abu sai
Kawai ya shiga sakar wa su hilwas murmushi mai taushi,
Amma har a lokacin zuciyar shi bugawa take da karfi tamkar zata faso cikin kirjin shi ta fito waje,
Abin da bai sani ba shine kamar yadda ya kamu da tsoron haka yarima da sarkin yaƙi su ka
kamu dashi,
Yayin da ya zamana an iso daf da juna sai sarki shardasu ya dubi su hilwas cikin annurin fuska
tamkar wanda aka bawa SARAUTAR DUNIYA ya buɗi baki yace "lale marhaban da zuwan
JARUMAN DUNIYA sai a yau ne na tabbatar da cewa kun cika MAZAJENI DUNIYA kuma
GWARAZAN JIYA da babu kamar ku a wannan KARSHEN ƘARNI,
yaku waɗannan jarumai kuyi sani cewa a yau ne zan cika muku alqawarin da na ɗaukar muku
na baku yanci da mahaifan ku daga KANGIN BAUTA a karkashin iko na,
Don haka yanzu sai ku danƙamin sandar sihiri da ƙoƙon kan boka Mannaf,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki shardasu sai hilwas ya murtuke fuska tamkar an aiko
masa da wasikar mutuwa ya dubi Sarki yace " ya shugabana ni da yan uwa mun amince zamu
damƙa maka abubuwan da ka buƙata amma bisa sharaɗin cewa bazaki yaudare mu ba,
Idan kuwa har ka saɓa alkawarin zamu bar ka tare da wannan jaruma ta yanke maka hukunci
dai dai laifin da ka aikata,
Kuma sai mun rushe mulkin zaluncin ka daga doran ƙasa,
Koda jin hakan sai sarki shardasu yace na amince da sharaɗin ku,
Da jin haka sai hilwas ya ciro sandar sihirin boka kimraz tare da ƙoƙon kan boka Mannaf ya
miƙa wa sarki shardasu ya sa hannu ya karɓa zuciyar cike da matukar farin ciki,
Kawai sai ya nuna dakarun dake bayan sa da ɗan yatsan shi na hagu take su ka ɓace ɓat kuma
sasarin ɗaya daure mahaifan su hilwas ya ɓace a daga jikin su,
Cikin matukar farin ciki maral misaltuwa hilwas, Kahzib da Sharwas, suka ruga izuwa in da
mahaifan su suke domin tarar juna.
Yayin da ya rage saura kamar taku goma sha biyu a tsakanin su sai sarki shardasu ya yi nuni
da hannun sa izuwa wajen take wata ƙarama ta tafasasshiyar darma ta bayyana a tsakanin su
ta yadda babu damar su haɗu da juna,
Sannan sarki shardasu ya ɗauki ƙoƙon kan boka Mannaf ya sanya kansa take ya ya zauna a
kan tamkar ya saka hular ƙarfe.
Ya riƙe sandar sihirin a hannun sa gami da bushewa da dariyar mugunta, Yarima kinzaru da
sarkin yaƙi su ka yi koyi dashi,
Daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya dubi su hilwas a
lokacin da hawayen takaici ke zuba daga idanuwan su,
"Haƙika yaro man kaza ne bai san wuta ba sai ta nar ka shi, kuma tabbatar duk tsuntsun da ya
ja ruwa shi ruwa kan doka,
Yanzu kuna tsammanin cewa zan barku a raye ne,
Ku sani cewa a halin ku da mahaifan ku baku da wani amfani a waje na,
Yanzu batare da ɓata lokaci zan hallaka waccan jarumar da kuke takama da ita,
Koda Gama faɗin hakan sai sarki shardasu ya daga sandar sihiri izuwa sama ya kwarara
wawan ihu sannan ya falfala da azababban gudu izuwa kan jaruma Husnat,
Koda ganin hakan sai bawa hilwas ya riga izuwa kan yarima kinzaru, Kahzib da Sharwas kuwa
suka tari sarkin yaƙi hatyal, rike da makaman su,
Lokacin da aka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini
daban sha'awa.
Ɓangarorin uku suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da
bajinta tagaban kwatance,
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan gwani da gwani suka haɗu a
yaƙi juriya da bajinta suka game waje guda dola ne yaƙi ya zamo tashin hankali daban tsoro.
Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya cur ana wannan artabu,
Tabbas a wannan rana Allah ya nuna ikon sa domin Husnat ta samu nasarar hallaka sarki
shardasu ta hanyar karya masa waya,
Amma ita ma tasha matuƙar wahalar gaske,
Hilwas da Kahzib suma sun kashe abokan gabar su,
Amma sai da Husnat ta kai musu ɗauki bisa taimakon Ubangiji,
Tabbas inda ace mutum yana tsaye a wannan waje zai ga yadda gawar sarki shardasu ke
kawance a ƙasa cikin ƙaskanci da wulakanci dole ne ya gode wa Allah bisa ganin yadda ya
kawo KARSHEN ZALUNCI da azzalumai.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai wannan ƙorama da ta raba tsakanin su hilwas da
mahaifan su ta ɓace ɓat tamkar bata taɓa wanzuwa ba.
A sannanne su hilwas suka ruga izuwa inda mahaifan su suke suka rungume juna suna masu
zubar da hawayen farin cikin.
Al'amarin da ya sanya Husnat dake tsaye a gefe guda ta kamu da matukar tausayin su kenan
har kwalla ta zubo mata,
Daga can sai ta taka da kafafun ta har zuwa inda suke ta durƙusa kasa bisa gwiwar ta ta dube
su cikin tausaya tace "yaku waɗannan jarumai kuyi sani cewa a yanzu ne zan cika alkawarin da
na ɗaukar muku na warkar da mahaifan ku bisa taimakon Ubangiji na,
Koda Gama faɗin hakan sai Husnat ta fito salkar ruwan ta ta kofa ayatul-kursiyyu da falaƙi da
nasi,
Ta umarci mahaifan su Kahzib maza su shanye ruwan. Haƙiƙa tsarki ya tabbata ga Ubangiji
maɗaukakin sarki,
Faruwar hakan ke da wuya sai idanun mahaifin hilwas suka buɗe garau yana iya ganin komai,
Mahaifin kahzib kuwa bakin ya buɗe ya dawo yana iya magana tar-tar.
Sharwas kuwa duk kuturtar dake jikin mahaifin shi ya warke jikin sa yayi kyau sumul,
Batare da bata lokaci ba su hilwas da mahaifan su suka karɓi kalmar shahada a wajen Husnat
Sannan aka dunguma izuwa cikin birnin Baitul-na'im aka musuluntar da kowa dama sun gaji da
mulkin sarki shardasu,
Bayin dake kurku kuwa aka fito dasu aka basu yanci. Nan fa gari ya kaure da shewa da murna,
Kashe gari tun da duku-dukun safiya aka shiga shagalin nadin sarautar bawa hilwas a matsayin
sabon sarkin birnin Baitul-na'im,tare da auren sa da gimbiya lashmira,
Kahzib a matsayin waziri, hilwas a matsayin sarkin yaƙi tare da daura auren su, Kahzib da
gimbiya shuraima yar sarki Husubul-Dinar,
Sharwas da jaruma Husnat, daga wannan rana aka rushe KANGIN BAUTA kowa ya samu
'yanci gaba ɗaya jama'ar birnin suka kasance cikin matukar farin ciki maral misaltuwa,
Hasken musulmi ya mamaye ko ina a nahiyar baki ɗaya
Alhamdulillah
Ƙarshe
Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin marubutan Yaƙi
08137237071