Showing 3001 words to 6000 words out of 13155 words
Chapter 2 - KANGIN BAUTA Book Complete by Mansur Usman Sufi .pdf
JININ da na yi miki tabbas ban yi hakan
domin kaskanta daraja da martabarki ba sai domin kare zuciyar ki daga kudurun da ke tattarc a
al'adar.
ki yi sani ccwa na san ba wani abu ne ya fito da ke a cikin wannan dare ba fuskantar tsananin
soyayyar bawa Hilwas da ta addabi zuciyarki.
Tabbas, matsalarmu irn daya ce, domin ni ba komai ne ya fito da ni a dai-dai wannan lokaci ba
sai bisa kamuwar da zuciyata ta yi da kyau kaunar bawa Kahzib, irin son da ban taba yuwa
wani da namiji ba,
Saboda haka kinga yanzu tsakaninmu sai dai mu hada kai domin saduwa da masoyanmu kafin
wayewar gari.
Koda jin wannan doka daga bakin gimbiya Shuraima sai Lashmira ta saki tattausan murmushi,
a gare ta sannan ta budi baki cikin annurin fuska ta ce
"Ya ke Shuraima ki yi sani cewa tabbas na gamsu da dukkan bayaninki domin na san a cikin
sarakunan da suka halarci GASAR JARUMTA mahaifin ki ne kadai ba shi da wani mummunan
kudiri a zuciyarsa a kaina da abbana.
Amma sai dai kafin mi ci gaba da tafiyar mu ina so ka amsa mini tashin tambayoyi kamar haka:
-
Shin kuna yakinin cewa bawa Kahzib zai amince da soyayyarki?
Tambaya ta karshe ita ce a ina ki ka samu irin tufafin da na sanya?
Adabi24.com.ng
Da jin wannan tambayar sai Shuraima ta yi murmushi ga Lashmira sannan ta dube ta ta hanyar
gyaran lallausan muryar ta kawo gwauron nunfashi ta ajiyc ta ce,
"Game da tambayarka ta farko, ki yin sani cewa duk da cewa bawa Kahzib bai furta min cewa
yana kaunata ba tabbas na ga alamun hakan a kan fuskarsa,
a lokacin da muka hada idanuwa da shi a filin gasa,
kin san masu iya magana na ccwa LABARIN ZUCIYA a tambayi
fuska Sannan game da tufafin da na sanya mai kama da naki kuwa labari ne mai tsawo,
akwai bukatar mu samu lokaci mu zauna. Sa'adda Lashmira ta ji amsar wadannan tambayoyin
sai mamaki ya turnuke ta ta ce a cikin ranta.
"Shin wace alaka ce ke tsakanin tufafina da na gimbiya Shuraima,
Kawai sai ta bar abin a cikin ranta su ka ci gaba da tafiya suna masu sakc rufe fuskokinsu da
rawanin har suna hira kamar sun dadec da sanin junansu har suka iso masaukinsu,
bawa Kahzib ba su hadu da wata matsala ba, sai da kyar da sidin goshi suka sadu da
masoyansu.
Wato bawa Hilwas da Kahzib kuma suka samu damar taron a ranar, ashe su ma da kyau Sun
sun kamu da soyayyarsu.
Kashe gari tunda duku-dukun safiya fadar sarki Shardasu ta cika ta batse da jama'a,
duk in da mutum ya kalla kawunan bil'adama ne rututu babu masaka tsinke Babu abin da zai
bawa mutum mamaki kuma iya daure masa kai fuska ganin yadda sarakunan da suka halarci
taron ba su yi wani jinkirin fitowa ba,
da yawa daga cikin jama'a a nan suka same su.
Ana cikin wannan hali ne sai aka jiyo bushin algaita hade da bugun tambura,
alamun sarki Shardasu na kan hanya.
Kwatsam! Sai aka hango sarki Shardasu da tawagarsa sun shigo fadar sarki ne a kan gaba,
gimbiya Lashmira tsaye aɓangaren hagu yarima Kinzaru a dama dukkansu sun caba ado mai
girma daukar hankali, dakaru rike da kyau na take musu baya.
Koda ganinsu sai gaba daya jama'ar da ke fadar suka mike tsaye domin girmamawa a gare su,
Adabi24.com.ng
domin masu iya magana kan ce ba a sarki biyu a masarauta daya,
sai da sarki da su yarima suka zauna a wajen da aka tanadar musu sannan kowa ya zauna,
fadar ta yi shiru kamar mutuwa ta kawo Ziyara.
Aɓangaren da aka tanadarwa sarakuna kuwa
sa'adda sarki Hukubul Ansab ya yi arba da tufafin da ke sanye a jikin sarki Shardasu sai takaici
da bakin ciki suka suka mamaye zuciyar shi ya ji kamar ya kurma ihu daboda takaici.
Ba wani abu ya sanya shi hakan ba face bisa ganin wannan dukkan kayan sarakunan
masarautar daya sace a dakin masarauta domin ya samu nasar yiwa sarki Shardasu JUYIN
MASARAUTA sarki Shardasu na sanye dasu wato alkyabba, kambu, takalmi da sauransu.
Sarki Hukubul Ansab ya ce a ransa Shin yanzu duk wahalar da na sha ta tashi a banza, tabbas
sarki Shardasu ya cika hatsabibi a ilimin tsafi, kuma wannan shi ne masu iya magana ke cewa
kifi na ganiqnka mai jar koma. Sa'adda sarki Hukubul Ansab ya zo nan a tashinsa sai
hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe.
Kamar hadin baki sarakunan da suka gabatar a bayyane suka mike daga kan kujerun zamansu
suka je suka zube a gaban sarki Shardasu suka kwashi gaisuwa,
sarki Shardasu ya karbi gaisuwar fuskarsa babu yabo babu fallasa.
Duk wanda ya kalla daga cikin sarakunan sai ya ji hantar tasiri ta kada, ya sunkui da kansa
kasa shi kuwa sarki Shardasu sai ya yi guntun murmushi a gare shi,
sarki Husubul Dinar ne kadai bai ji wani abu a ransa ba har ya mayar wa da sarki Shardasu
martanin murmushin,
KANGIN BAUTA
Rubuta labari
MANSUR USMAN SUFI
08137237071
Sarakunan suka sake mikewa tsaye suka koma wajen zamansu suna yiwa junansu wani irin
kallo mai tattare da kyayyar juna.
Bayan kamar shudewar dakika talatin sai aka hango su bawa Hilwas sun shigo fadar dakaru na
dauki musu baya,
su duka ukun shigar korayen tufafi suka yi farin rawani, farin takalmi.
Shigar da tayi kyau fito da tsantsar kyawunsu. Koda shigowarSu ya zauna gaba daya fadar ta
ruɗe da shewa masu tafi da jinjina na yi su Hilwas na daga musu hannu, sai da suka zauna a
wajen zamansu bayan sun kwashi gaisuwa ga sarki Shardasu sannan fadar ta sake yin shiru
A karo na biyu, sarkı Shardasu ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar miƙewa tsaye ya
fuskanci jama'a Sannan ya yi gyaran murya ya ce,
"Hakika na girma jin dadi bisa ganin yadda jama'a suka bayar da hadin kai wajen halartar
wannan fada mai albarka, domin ganin yadda za a bayar da manyan kyaututtuka ga jaruman da
suka samu nasarar lashe gasar gasa rukuni uku da aka sake a jiya.
Yanzu sai kowa ya saurara, domin ya ji sauraran bayanı. "Gama fadin hakan sai sarki ya koma
kan kujerarsa ya zauna sarkin yaki Hatyal ya miƙe tsaye ya yi gyaran murya ya ce," Da farko
yanzu muna bukatar ganin jarumi Hilwas wanda shi ne ya lashe kallon yaki da takobi, bayan ya
samu nasara a kan abokin gwaminsa yarima Kinzaru.
"Koda jin an ambacı Hilwas sai fadar ta rude da ya Koda hayanıya magoya bayansa na yi masa
jinjina, har sai da je ya tsaya a da akc bukata.
Koda tsayawar ta shi sai wani badakare va iso da wata madaidaiciyar akwatu ta bakin karfe ya
ajiye ta gaban sarkin yaki a bisa tcburin da ke gabansu.
Adabi24.com.ng
Sarkin yakı ya bude akwatun ya dauko wata takobi da aka yi ta da zubar daji haɗe da wani
kambu ya je ya risina a gaban sarki ya miƙa masa ya karba, shi kuma ya mike tsaye ya
sanyawa bawa Hilwas kambun kuma ya damka masa takobin,
Sannan ya rike hannun hilwas ɗayan ya saka a nasa ya daga sama.
Nan take fadar ta rude da shewa gami da tafi, wasu ma har da kida da rawa, domin nuna farin
ci kınsu bisa ba wa gwaninsu KAMBUM JARUMTA na gwarzon shekara. A bangarcn gimbıya
Lashmira kuwa saboda tsananin muna ba ta san sa'adda ta mike tsaye ba tana yıwa masoyinta
tafi da jinjina.
Al'amarin da ya harzuka zuciyar yarima Kinzaru ke nan takama tafarfasa kamar zuciyar tasa za
ta ƙone
ya ji kamar ya zare takobi ya sare wuyan bawa Hilwas.
Fadar ba ta samu nutsuwa ba sai da sarkı Husubul Dinar da sarki Hulbaru suka ba wa Hilwas
kyutar dukiya mai yawa da adadinta ya kai dinare miliyan shida da ɗoriya sannan yaje ya zauna
a kan kujerarsa a cikin yan uwansa Sharwas da Kahzib Sannan sarkin yaki Hatyal ya yi gyaran
murya ya dora demunsa a kan takardar da ke magana game da shi,
Jarumai na Kahzib da ya lashe zaben harbin KWARI DA BAKA, sai arumi Sharwas da ya lashe
kallon jifa da mashi A lokaci guda tsakanin Kahzib da Sharwas suka mike tsaye suka nufi in da
karagar mulki take sai nan take fadar ta sake kaurewa da shewa da tafi, gimbiya Shuraima
kuwa farin cikin da ke zuciyarta ba a tonawa bisa ganin abin Kaunarta bawa Kahzib.
Sa'adda ya rage bai fi sauran taku uku ba da girma da karagar mulki sai suka zube kasa suka
kwashi gaisuwa ga sarkı Shardasu sannan wannan mummunan halin ya sake daukar manyan
akwatu guda biyu ya ajiye su gaban sarkin yakı Hatyal,
shi kuma ya bude ya dauko wata kasaitacciyar KWARI DA BAKA a cikin akwatu daya ya sake
mikawa sarkı Shardasu shi kuma ya dankawa Kahzib, sannan sarkın yakı ya sake bude akwatu
ta biyu ya dauko wani dogon mashi mai bakı biyu mai kyau launi da daukar ido ya mikawa sarki
a karo na biyu, shi kuma ya damkawa Sharwas.
Take fadar ta sake rudewa fiye da ko yaushe, a wannan lokaci ne Kahzib ya hango gimbiya
Shuraima 'yar sarki Husubul Dinar,
kawai sai ya ga ta jefe shi da wani inn tattausan mumushi mai tattare da tsantsar so da Kauna.
Adabi24.com.ng
Ai kuwa shi ma bai san sa'adda ya mayar mata da maratanin murmushin ba.
Kahzib da Sharwas suka juya domin komawa wajen zamansu suna gaisawa da masoyansu
Wasu kuma na ɗaga musu hannu,
har suka isa in da kujerunsu suke suka sake zama, zuciyoyinsu cike da farin cikin farin ciki
Maral
Bayan komai ya samu dai daita sai kuma tsala tsalan Isalan mutanan kuyangi suka shigo fadar
dauke da farin ciki da nau'ikan kayan abinci mai rai da lafiya.
nau'i daban-daban Wadansu na dauke da tulunan giya,
Nan take aka shiga hidimar ciye ciye da tanɗe-tanɗe,
wani abu da zai bawa mutum mamaki kuma ya, daure masa kai shi ne duk tarin tsananin yawan
jama'ar da suka halarci bikin sai da suka yi wadata da abıncı da abin sha har suka bar shi,
sannan taro ya watse kowa yayi kama gabansa, baki suka koma masaukinsu
Adabi24.com.ng
kahzib, Hilwas da Sharwas na zaune a cikin turakarsu suna hira a tsakanınsu domin debewa
juna ƙewa.
A cikin hirar ta su ne Sharwas ya dube su fuskarsa cike da tsananin damuwa ya ce "Ya 'yan
uwana ku yi sani cewa wannan farin cıkı da muke a yanzu,
kawai ina nuna shine ba dan zuciyata tana so ba, ta wata fuskar ma wannan farın cıkin ba shi
da wani amfanı.
Cike ma maganar mamakI Hilwas ya dubi Sharwas cikin murmushi ya ce, "Ya abokina shin ina
dalilin wannan furici naka?"
Sharwas ya sake haɗe rai ya ce, "Sanın kanku ne ke cewa mahaifanmu na raye kuma mun
rabu da su tun muna yara kanana, to ina amfanin farın cikın mu tunda ba mu san halin da suke
cikı ba.
Ko da jin wannan batun daga bakın Sharwas sai hankalın Hilwas da Kahzıb ya dugunzuma
ainun har kwallar takaici a zubo masu Hilwas ya buɗi baki da ƙyar fuskarshi cike da damuwa ya
ce,
"Haƙiƙa abokina ka sosa mini in da yake yi min Kaikayı.
ka sani cewa a yau yau kafin wayewar gari sai mun gano in da mahaifan mu suke mun gana da
su.
Hakika mahaifa sune ginshiƙin rayuwar dukkannin wani ɗa na gari.
Sa'adda Hilwas ya zo nan a zancensa sai ya fashe da kuka, al'amarin da ya narkar da zuciyar
Kahzib da Sharwas ke nan suma suka fashe da kukan,
Marubuci
MANSUR USMAN SUFI
08137237071
KANGIN BAUTA 8
Marubuci
Mansur Usman sufi
08137237071
Sai da suka shafe tsawon lokaci a cikin wannan hali sannan Hilwas ya share hawayen da ke
fuskarsa ya mike tsaye zumbur ya fice daga cikın turakar Kahzib da Sharwas na bıye da shi.
Da ya ke lokacı ne na dare sai suka huce kai tsaye izuwa kurkukun kasar,
Duk in da suka huce sai dai ka ga kuyangi da bayı nayi musu musujina gamı da miƙa gaisuwa.
Su kuwa ko kallonsu baa yi suna masu fice daga gidan sarautar,
Tafiyar daƙiƙa hamsin kacal suka yi suka iso kofar kurkukun wadda ta kasance murtukekiya da
aka yi ta da zunzurutun bakın karfe,
duk in da mutum ya kalla a sama da ƙasan kofar tarin muggan dakaru ne shırye cikın shigar
yakı.
Hannayensu suna rike da miyagun makamai sai mazurai suke yi suna kai komo kamar za su ci
babu,
haƙiƙa komai dakewar zuciyar jarumi da rashin tsoronsa idan ya yi arba da dakarun dole ne ya
firgice saboda kwarjininsu.
Koda shugaban da ke kula da kofar wani garjejen basamuden kato ya hango su Hilwas sai ya
tako da katafunsa ya tare su ya risına a gare su cikin girmamawa.
Hilwas ya dubi basamuden ya ce, "Ya kai Zamaru ka yi sani cewa ba komai ne ya kawo mu nan
ba sai domin ka sanar da mu shin ina ne mahaifanmu suke.
''Da jin wannan tambaya sai idanun Zamaru suka zazzaro ya dubi Hilwas cikin alamun tsananin
tsoro ya ce,
"Ya shugabana na roƙe ka da ka yi min rai. ka sani cewa ba zan iya sanar da kai in da sarki
Shardasu ya boye mahaifanku ba, domin ina ina tsoron ka da ya halakar da ni
Sa'adda Hilwas ya ji wannan batun sai ya fusata ainun har idanunsa suka kaɗa suka yi jawur,
ya dakawa Zamaru tsawa wacce ta sanya hantar cikin Zamaru ta kaɗa, ya dube sa ya ce "Na
rantse da rayuwar mahaifan mu idan ba ka sanar da mu in da aka ajıye mahaifanmu ba sai mun
yi maka kısa mafi muni ka bƙkunci barzahu.
Nan fa hankalin Zamaru ya dugunzuma ainun ya rasa abin da yake yı masa dadɗiA.
Abuna farko da ya faɗo masa a rai shi ne, shin yanzu idan ya sanar da su Hilwas in da aka ajıye
mahaifansu yana da tabbacın cewa sarkı Shardasu ba zai gane cewa shi ne ya sanar da su ba.
Sannan abu na biyu shi ne tabbas idan bai sanar da Hilwas abin da ya ke bukata ba zai rasa
rayuwarsa a yanzu take,
Wannan fa shi ne masu iya magana kan cewa gaba tsini baya siyaki.
Wata zuciyar kuma ta ce da shı koma dai dai zai zai faru gwara ka sanar da Hilwas abin da ya
bukata.
Domin ka TSIRA DA RAYUWAr ka a yanzu. Koda barde Zamaru ya zo nan a tunanin sa sai ya
dubi Hilwas da turɓunanniyar fuskarsa kai ka ce murmushi bai taba wanzuwa a kanta ba. Ya
buɗe tafkeken bakınsa wanda ya fi kama da kofar gari ya ce, "Ya shugabana sarkı ya ajiye
mahaifan ku maza ne a can Wani gida na musanman,
bayan ɗauke su daga kurkuku, domin ka da ku yi yunƙurin zuwa in da suke.
Shi dai gidan ya kasance a cikin kasa, wanda i dan har aka shigar da mutum baya taɓa fitowa
face dai mutuwarsa.
Gidan ya kasance a can ƙarshen gidan sarauta.
Mahaifan ku mata masu suna a zaune a gidan horar da mata sana'o'i domin samar wa da sarkı
dukiya mai tarin yawa,
Ko da jin wannan bayani daga bakin barde Zamaru sai bawa Hilwas, Kahzib da Sharwas suka ji
sun kamu da sananın tausayin mahaifansu bisa jin matsanancin halin KANGIN BAUTA da suke
ciki".
Ba tare da ɓata lokaci ba Hilwas ya umarci barde Zamaru ya kawo musu ingarmun dawakai,
sannan suka kama musu linzami, suna masu tsala azababban gudu Kai tsaye gidan karkashin
kasa suka nufa da ke karkashın gidan sarauta domin su fara saduwa da mahaifansu maza,
Tafiyar rabuwa sa'a da daƙiƙa hamsin kaɗai suka yi suka iso ɓangaren tun kafin su karaso bakin
kofar wajen suka fara fafata yaƙi da dakarun da ke tsaro.
Lokacin da suka iso bakin kofar kuwa sai suka cika da matukar mamaki,
Abin da ya ba su mamakin kuwa shi ne duk da irin yadda sararin samaniya ta mamaye da duhu,
Amma ko ina a wajen haskake yake da wani haske na musamman wanda in da allura za ta faɗi
a kasa da zarar mutum ya duba zai ganta Kai da gani ka san aiki ne na sihiri.
Dakarun da ke wajen kuwa sun kasance ababan tsoro saboda kwarjininsu sai ka rantse ka ce
ba su kasance bil'adama ba, tsananin yawansu kuwa ya huce musali.
Yayin da suka bayyana suka yı arba da su Hilwas sai suka