Showing 6001 words to 9000 words out of 13155 words
Chapter 3 - KANGIN BAUTA Book Complete by Mansur Usman Sufi .pdf
zare makamansu suka tare su aka
kacame da KAZAMIN GUMURZU mai matuƙar muni, ban tsoro da ban al'ajabi.
Ana fa wannan gumurzu ne dakarun suka gane shayi ruwa ne ba abinci mai nauyı ba, yawansu
ya zamto banza,
domin duk in da su Hilwas suka sanya gaba sai dai ka ga gawarwakin su na zubewa kasa, jini
kuwa ya dinga feshi, fantsama yana malala a kasa.
Nan fa ya zamana cewa bangarorin biyu sun wanzu suna kawai juna sara da suka cikin
matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta ban al'ajabi.
Ana cikin wannan yaki ne wani daga cikin yanayin ya shammaci bawa Hilwas ya kawo masa
wani nagartaccen sara da takobinsa wanda zai canza masa hannu.
cikin bakin zafin nama Hilwas ya sanya takobinsa domin ya kare harin amma sai saran
badakaren ya rinjaye shi ya kadɗe takobin Hilwas ta yo kasa za ta fadi. Kafin badakaren ya
sake wani yunkuri Hilwas ya dunkule hannun sa ɗaya ya gabza masa wawan naushi a fuska,
kuma ya miƙa ɗayan nasa ya cafo takobinsa saboda tsananin karfin naushin sai da badakaren
ya banke 'yan uwansa dakaru mutum shida,
suka zube kasa magashiyan. Tabbas jarumta da SADAUKANTAKA baiwa ce daga Allah, dukiya
mulki ba sa bayar da ita face Allah. Kuma duk wanda Allah ya ba shi jarumta ya huta.
In da a ce mutum zai ga yadda Hilwas, Kahzib da Sharwas ke ragargazar dakarun suna yin
MUGUWAR HALAKA dole ne ya jinjina musu. Sai da aka shafe sa'a daya ana fafata baƙin
artabu.
sannan kuma Hilwas suka samu nasarar halakar da dakarun ba ki ɗaya,
suka kutsa kai izuwa cikin gidan a nan amma sai suka yi GWAGWARMAYA da dakaru masu
tarin yawa sannan suka samu shiga cikin ƙarƙashin ƙasa.
Lokacin da suka shiga sai suka kama kalle-kalle da dube-dube suna masu duba dakunan da ke
cikı domin su ga in da mahaifansu suke amina shiru babu labari sai fursunoni da suke gani
maza da mata,
Da ƙyar da sidin goshi suka gano a cikin mahaifan nasu suke a cikin waɗansu kejina na karfe
hannayensu da kafafunsu ɗaure da sarƙoƙi.
Cikın matuƙar farin ciki maral musaltuwa su Hilwas suka ruga izuwa in da kejinan suke Koda ya
rage bai fi saura taku uku a tsakanınsu ba kwatsam ba zato ba tsammani sar wani wawakeken
rami ya bayyana a gabansu
wata irin gagarumar wuta na ci ganga-ganga a cikin ramin.
Kuma wata irin kakkausar murya ta kece da dariya cike cike da matukar fushi da ɓacin rai
Hilwas, Kahzib da Sharwas suka waiga bayansu domin su ga wanda yake dariyar.
Ai kuwa koda waigawar tasu sai suka yı turus.
Ba wani suka gani ba face sarkı Shardasu shirye cikin gagarumar shigar shigar yarima Kinzaru
na tsaye a ɓarin hannun sa na dama, sarkın yaƙi Hatyal na tsaye a hagu.
Waɗansu gabza-gabzan samudawan dakaru na kewaye da su cıkın shigar yaƙi mai matuƙar
kwarjini, hannayensu rike da muggan makamai
Sai da sarki Shardasu ya yi dariya ta ishe shi sannan daga bısani ya murtuke fuska kamar an
aiko masa da WASIKAR MUTUWA, ya dubi Hilwas, Kahzib da Sharwas sannan ya buɗi baki
cikin kakkausar murya ya ce, "Ya ku jarumai masu dauke da KAMBUN JARUMTA ku sani cewa
tun daga lokacin da kuka fice daga cikin masaukinku har kawo izuwa nan na ga dukkannin abin
da ya faru gare ku.
Ina so ku yi sani cewa ku da mahaifanku gaba ɗaya kuna karkashin iko na ne har abada ɗaya
daga cikin ba zai sadu da mahaifansa ba face ya amince da biya mini wata mahimmiıyar bukata
ta.
"Koda gama fadin hakan sai sarki Shardasu ya yi nuni da hannun sa na hagu izuwa bangaren
bangon yamma da ke wajen.
Yana mai karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, gama rufe bakinsa ke da wuya sai hoton
mahaifansu Hilwas mata ya bayyana suna zaune a cikin wani gida suna aika ce aika ce Duba
ɗaya za ka yi musu ka fahimci cewa suna cikin damuwa
Domin sun rame matuƙa sun yi baki tufafin da ke jikinsu ya yi datti sosai duk ya yayyage, babu
wanda zai gansu a cikin wannan hali face ya kamu da tsananin tausayinsu
Sa'adda Hilwas, Kahzib da Sharwas suka yi. Arba da su a sannan ne mahaifin Kahzib da
Sharwas da ke zaune a cikin wannan kejin suka fara zubar da hawaye.
duk da mahaifin Hilwas idanuwansa a makance suke baya gan abin abin da ke faruwa, amma
da ya ji kukan ɗan sa Hilwas da abokanan Rauzil da Hasham sai shi ma ya fashe da kukan.
Sai da suka shafe wani lokacı a cikin wannan hali yarima Kinzaru na yi musu dariyar mugunta.
sannan sarki Shardasu ya sake nuna bangon a karo na biyu hoton bat! Kuma ya sanya wani
duhu tsakanin su da su Rauzil ya zamana ba sa iya ganin 'ya'yansu.
Sarki Shardasu ya saki guntun murmushi ga su Hilwas da har yanzu hawaye ke zuba daga
idanuwan su Sannan bushe da dariyar mugunta, kana ya murtuke fuska kamar an aiko masa da
WASIKAR MUTUWA, ya ce, "Ya ku wadannan ZARATAN MAYAKA ma'abota karfin damtse ku
yi saji cewa idan har kun ɗaukae mini Alkawarin da za ku samo mini abin da nake ji Bukata to
zan 'yantaku tare da iyayenku ba za ku kara bauta a gare ni ba. Idan kuwa ku ka bijirewa buƙata
ta ku da mahaifan ku za ku kasance a cikın KANGIN BAUTA har ajali ya riske ku,
Yanzu dai shawara ta rage ga mai shiga rijiya. Koda jin wannan batun daga bakın sarki
Shardasu sa hankalın Hilwas, Kahzib da Sharwas ya dugunzuma ainun,
kuma su duka ukun suka faɗa kogin tunani don samun mafita.
Abin da ya faɗo musu a rai shi ne shin wace irin bukata ce za su biyawa sarkı Shardasu? An ya
kuwa ba yaudararsu zai yı ba?
To yanzu kuma idan ba mu amince mun biya masa bukatarsa ba za mu ci gaba da zama a cikın
kuncin rayuwa, tare da mahaifanmu? Amsar tambayoyın da suka kasa bawa kansu ke nan take
hankulansu suka sake dugunzuma fiye da ko yaushe.
Hilwas ne ya katse shirun da ya wanzu a tsakanınsu ta hanyar buɗar bakı ya sanya hannu ya
share hawayen sa sannan ya ce "Mun amince za mu bıya maka buƙatar matsawar za ka ba mu
FANSAR RAYUKAN mahaifanmu.
Shin mece ce ake buƙatar taka?" Sarkı Shardasu ya yi murmushi a karo na biyu ya ce, "Abın da
kawai nake buƙata shi ne za ku tafi izuwa gidan boka Kimraz domin ɗauko mini SANDAR
SARAUTAR shi
Kafin ku isa gidan za ku tarar da miyagun dazuzzuka guda huɗu masu matukar haɗari.
Daji na farko ya kasance mallakin wani gawurtaccen matsafin dodo da ake yi masa masa laƙabi
da suna Zamzaru.
Dodo Zamzaru ya kasance gwarzon mayaki, kaifi da tsini ba ya tasiri a kansa,
A wannan ƙarni ba ki ɗaya, domin saboda hatsabibancinsa ne ya zamana sarakunan da ke
makwabtaka da dajin suka yi kaura suka bar yanayin.
Kuma an ce shi kadai ne yake rayuwa a dajin. Daji na biyu ya kasance na waɗansu irin
tsuntsaye ne masu kama da tsuntsun batoyi, babu wani nau'in makami da yake tasiri a kansu
face tsagwaran KARFIN DAMTSE da basirar mutum.
Masana da bokaye sun tabbatar da cewa adadin tsuntsayen ba zai kidayu ba,
Domin kullum kara yawa suke yi.
Daji na uku na waɗansu fatalwoyi ne na haske, mutum ba zai taba samun nasara a kansu ba
face ya kashe shugabansu kuma dukkanninsu suna da kamanni iri daya sak!.
Babu yadda za a yi mutum ya iya gane wane ne shugabansu.
tsakanin zafin namansu kuwa ba zai musaltu ba sai dai abin da ido ya gani.
Na karshe kuwa ya kasance daji ne na waɗansu zakunan sihiri da wani shu'umin boka ya ƙirƙira
mai suna Sultan ibn Hammar. Bayan kun samu nasara shiga gidan boka Kimraz kun dauko mını
sandar tsafinsa sai kuma ku huce izuwa wanı daji da ke ıyaka da gidan ku ɗauko mini ƙoƙon
kan boka Mannaf da ke ajiye a cikin wata tsohuwar rijiya dake fadar Sarkin bokaye na duniya, Sa'adda sarki Shardasu yazo nan a zancen sa sai hankalinsu Hilwas ya dugunzuma ainun,
Sharwas dubi sarki ya ce, "Ya shugabana a wace nahiya dazuzzukan suke?" Sarki ya ce, "Me
ku ke ci ne na baka na zuba? Ai zan haɗa ku ne da wani hadimin aljanina ya yi muku jagora."
Koda gama fadin haka sai sarki Shardasu ya rintse idanunsa ya kırawo sunan aljaninsa, wata
irin kakkarfar iska ta mamaye wurin wacce ta haddasa gashin kansu bawa Hilwas da rigunan
jikinsu kaɗawa.
Daga can sai ga wani narkeken aljani ya bayyana tsum! Tamkar an jefoshi daga sararin
samaniya.
Aljanin ya kasance mai matuƙar tsaho, muni, girma gami da kwarjini.
Domin duk dakewar zuciya irin ta su jarumi Hilwas sai suka firgita da ganin aljanın
Shi kansa sarkin yaki Hatyal da yarima Kinzaru sun razana matuka.
sarki Shardasu ne kadai bai tsorata ba. Aljanin ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa ga sarki
Shardasu.
Sarki ya dube sa ya ce, "Ya kai Kubuzul Haiman ka yi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai
domin ina sai ka yiwa waɗannan jarumai rakıya izuwa dajin Darul Hashawar. Wannan shi ne
abin da nake bukata."
Koda jin wannan batun sai aljani Kubuzul Haiman ya risina ya ce, "An gama ya shugabana. Ba
tare da wani ɓata lokaci ba Hukubul Haiman rankwafa gadon bayansa bawa Hilwas, Sharwas
da Kahzib suka hau kan kansu suka zauna tare da dawakansu sannan Kubuzul Haiman ya
yunkura ya tashi izuwa sararin samaniya.
Kafin kiftawar ido ya ɓace ɓat a cikin gajimare, nan take sarki Shardasu, yarima Kinzaru da
sarkin yaki Hatyal suka bushe da dariyar mugunta.
Wannan shi ne dalilin barowar jarumi Hilwas, Sharwas da Kahzib daga birninsu na Baitul Na'im,
domin su ɗaukowa sarki Shardasu sandar sihiri da kokon kan boka Mannal.
SHIN WADANNE IRIN MIYAGUN MUSIBU SU HILWAS ZASU FUSKANTA A WANNAN TAFIYA
TASU SUNA SAMUN NASARAR KETARE MIYAGUN DAZUZZUKA HUDU HAR SU ISA GIDAN
BOKA KIMRAZ?
KUMA SUNA SAMUN NASARAR DAUKOWA SARKI SHARDASU SANDAR TSAFI DA
KOKON KAN BOKA MANNAF DOMIN FANSAR RAYUKAN MAHAIFANSU?
SHIN YA SHURAIMA 'YAR SARKI HUSUBUL DINAR DA GIMBIYA LASHMIRA ZA SU
KASANCE NA KEWAR MASOYANSU HILWAS DA KAHZIB?
TSAKANIN YARIMA KINZARU DA GIMBIYA LASHMIRA WAYE ZAI GAJI KARAGAR MULKIN
SARKI SHARDASU?
INA LABARIN SARKI BARSUS, Sarkin marubutan yaƙi ANSAB DA SARKI HULBARU DA
KOWANNENSU YA SHIRYAWA SARKI SHARDASU BAKIN TUGGU DOMIN RABA SHI DA
KARAGAR MULKINSA, AMMA YA TSIRA DAGA SHARRINSU?
SHIN A WANE HALI MAHAIFANSU JARUMI HILWAS YA ZA SU KASANCE NA RABUWA DA
'YA'YANSU?
Mu hadu a 10 KANGIN BAUTA domin jin ci gaban wannan labarin nayataccen labari.
Lokacin da su jarumi Hilwas suka yi cirko cirko a kofar shiga gidan boka kimraz
Cike da matukar damuwa bisa halin KANGIN BAUTA da suka baro mahaifin su a ciki.
Sai suka shafe tsawon daƙiƙa arba'in Batare da ɗayan su yace uffan ba.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai suka hango wani mahayi bisa
ingarman doki fari.
Ya rataya wata sharbebiyar takobi a gadon bayan sa ya durfafo inda suke gadan gadan.
Sai dukkanin su suka ƙura wa mahayin idanu suna jiran ƙarasowar sa. Sannu a hankali
mahayin ya ci gaba da kusanto su,
Har yazmana tazarar dake tsakanin su bata huce taku biyar sannan yaja linzamin dokin sa ya
tsaya cak
Yayin da suka yi arba da mahayin sai suka cika da matukar mamaki.
Abu na farko da ya basu mamaki shine yadda mahayin ya yaksance ya mace ba namiji ba,
Sannan ya akayi ta iya ketare miyagun dazuzzukan dake baya
Wato dajin fatalwoyi na haske, dajin dodo zamzaru da kuma dajin zakunan sihiri masu ɗauke da
fuka -fukai ,
Wanda su kansu sai da suka sha bakar wahala sannan suka samu nasarar ketare dazuzzukan.
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan
Shi kuwa Sharwas sam bai ma san da wannan zancen ba,
Domin tuni ya shagala da kallon kyakkyawar budurwar, domin lokacin da ya fara arba da ita sai
yaji zuciyar sa ta buga wa karfi wani abu ya soki ya soki zuciyarsa a karo na farko yaji ya kamu
da matukar kaunar ta a zuciyar sa,
Tsawon daƙiƙu ana wannan kallon kallo tsakanin su Sharwas da Mahayin,
Sannan daga bisani hilwas yayi karfin hali yayi gyaran murya ya dubi budurwar yayi gyaran
murya yace" yake wannan budurwa shin wace ce ke ?
Kuma ya akayi kika ƙetare miyagun dazuzzukan dake baya har kika iso nan?.
Sannan mene ne ke tafe da ke izuwa gar mu.
Sa'adda budurwar taji wannan batu daga bakin hilwas dai tayi gyaran murya cikin tattausar
murya mai daɗin sauraro tace" yakai hilwas ɗan makaho rukaisu kayi sani cewa da farko dai ni
suna na Husnat bintu abu-husein
Na fito ne daga gabashin duniya a wani birni da ake yiwa lakabi da Darul--imfidal,
Game da amsar tambayar ka ta biyu kuwa shine,
Na samu nasarar ketare dazuzzukan dake baya ne bisa taimakon Ubangiji mahalicci,shine
wanda ya halicci duniya da Abin da ke cikin ta,
Amsar tambayar ta karshe ita ce bakomai ne ke tafe dani izuwa gare ku sai domin na taimaka
muku da izinin Ubangiji na domin ku samu nasarar abin da kuka fito nema.
Kuma na kuɓutar da mahaifan ku daga makircin azzalumin sarki sharadi,
Sa'adda Kahzib, hilwas da Sharwas suka ji wannan batu daga bakin Husnat sai suka cika da
ɗumbin al'ajabi da mamaki,
Kahzib yace "yake wannan jaruma taya ya za ki iya taimaka mana wajen cimma burin mu bayan
cewa mu ɗin Jarumai ne zamu iya nasara akan dukkan abinda muka sanya a gaba,
Sannan naji kin ambaci wani Ubangiji shin dama akwai wani abin bauta bayan namu?.
Husnat tayi ƙaytaccen murmushi da ya ƙarawa fuskar ta kwarjini sannan tace " na yar da cewa
tabbas ku sadaukai ne kuka kuma zaku iya cimma nasara akan abinda kuka sanya a gaba
Amma ina so ku sani zan taimaka muku ne wajen mallakar abin da kuka fita nema cikin ruwan
sanyi batare kun sha wata wahala ba,
Sannan ina so mu haɗa karfi da ƙarfe wajen rushe mulkin zalunci na sarki shardasu domin ku
sani cewa koda mallaka sa abubuwan dake bukata sai ya ci amanar ku bazai taɓa baku fansar
rayukan mahaifan ku ba,
Sannan zan roƙi Ubangiji na ya warkar da lalurar dake samun iyayen ku,
Amma sai idan kun ɗaukar mini alkawarin cewa zaki bayar da gaskiya ga Ubangiji na
Sa'adda Sharwas, Kahzib da hilwas su ka ji wannan batu daga bakin Husnat sai jikin su yayi
sanyi,
Suna masu zurfafa izuwa cikin Kogin tunani
Daga bisani sai
Sharwas yace "Ɗan bamu Lokaci zamu tattauna da yan uwa na,
Koda gama faɗin hakan sai shaewas da yan uwansa suka koma gefe guda suka yi ƙusƙus a
junan su sannan daga bisani suka dawo izuwa inda Husnat take,
Hilwas ya dube ta yace" yake Husnat haƙiƙa mun amince zamu zamu karbi addinin ki,
Matukar kika cika alkawarin da kika ɗauka na taimaka mana wajen mallakar abubuwan da
muka fito nema,
Sannan idan har Ubangijin naki ya warkar da mahaifan mu,
Munyi miki alkawarin cewa zamu taimaka miki wajen yaɗa addinin ki a wannan nahiya baki
ɗaya,
Koda jin wannan batu daga bakin hilwas sai jaruma Husnat ta cika da matukar farin ciki maral
misaltuwa,
Kawai sai ta kama linzamin dokin ta ta sauko ta durfafo ƙofar gidan boka kimraz
Da isar ta sai kawai ta sanya hannun ta akan Mabudin kofar tayi bismillah ta tura ƙofar bisa
mamaki sai gashi ta buɗe
Al'amarin da yayi matukar bawa su hilwas mamaki kenan kuma ya ɗaure musu kai,
Domin dai ko da a tarihi basu taɓa ganin jarumin da yayi wannan bajin ta ba.
Domin kofar tana da kaurin gaske wacce in da za'a sanya karti majiya karfi mutun sattin ba za
su iya ture ta ba,
Batare da fargabar komai ba, Husnat ta zare sharbebiyar takobin dake gadon bayan ta ta kunna
kai izuwa cikin gidan tana mai yafito su hilwas da hannunta tana nuna su biyo bayan ta,
Batare da gardamar komai ba hilwas ya zare takobin sa ya bi bayan ta da sauri,
Kahzib na rike da mashin sa mai baki biyu,
Sharwas na rike da kwari da bakan sa suka shige izuwa cikin gidan,
Wannan shi ne abinda ya faru da su bawa Hilwas akan hanyar ta zuwa gidan boka kimraz
domin ɗauko wa sarki shardasu sandar sihiri.
Acan birnin baitul-na'im kuwa al'amarin gimbiya lshamira da gimbiya shuraima yar sarki
Husubul-Dinar kuwa,
Tun sa'adda suka ji abinda ya da yafaru da masoyan su wato bawa Kahzib da hilwas,
Sai suka kasance cikin tsanin damuwa yana zamana cewa sun kamu da rashin lafiya domin ko
abinci basa iya ci,
Koda sarki Husubul-Dinar yaga abin