Showing 9001 words to 12000 words out of 13155 words

Chapter 4 - KANGIN BAUTA Book Complete by Mansur Usman Sufi .pdf

05 Aug 2025

340

da ya samu yar sa sai ya yanke shawarar ya tafi izuwa
Birnin sa domin yi mata magani,



Amma sai sarki shardasu yace yayi hakuri har zuwa lokacin da zasu samu lafiya ayi musu
magani tare da gimbiya,



Al'amarin mahaifan su Kahzib maza da mata a cikin kurkuku kuwa sun kasance cikin kinci da
damuwa dare da rana bisa tunanin halin da ya'yan su ke ciki.

Suka ji sun tsani sarki shardasu fiye da komai a rayuwar su .



Wannan shi ne abin da yafaru da su gimbiya lshamira da mahaifan su Kahzib.







Mu haɗu a KANGIN BAUTA Littafi na 11 domin jin cigaban wannan kasaitaccen labari.



Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe


Lokacin da su jaruma Husnat dasu bawa Hilwas suka shiga izuwa gidan boka kimraz,

Sai suka tsinci kansu a wani makeken fili mai tarin rairayi,

Sai suka ci gaba da tafiya Husnat tana mai dawo bayan su,

Saboda ta lura yadda Sharwas ke satar kallon ta a fakai ce,

Yayin da taga hakan sai ta dube sa ta sakar masa tattausar murya a lokacin da ya waigo ya
haɗa idanu da ita ɗin.

Koda yaga irin murmushin da Husnat ke yi masa sai yaji zuciyar sa ta buga da karfi,

Kawai ya mayar da duban sa zuwa kan hanya yana mai tambayar kansa a cikin ran sa yana
mai cewa shin Mene ne ma'anar wannan murmushi da Husnat tayi mini shin ko ita ma ta kamu
da soyayyata ne.

Amsar tambayar da Sharwas ya kasa bawa kansa kenan.

Haka dai aka cigaba da tafiya sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana tafiya batare da an haɗu
da wani abu mai cutar wa ba,

Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu irin dakaru na
taso wa daga cikin rairayin tamkar yadda danshi ke tsattsafowa daga cikin ƙasa,

Dakarun sun kasance girɗa-girda tamkar samudawan farko suna dauke da siffa guda biyu,

Tsagin jikin su na dama na karfe ne tsagin hagun kuwa na na haske ne

Suna dauke da miyagun makamai masu barazana ga rayuwar bil'adama,

Suna dauke da idanuwa jajur kwaya ɗaya jal a tsakiyar goshin su,

Hancin su da bakunan su irin na gwaggwan biri ne,

Haƙiƙa waɗannan dabaru sun kasance munana kuma ababan tsoro,

Babu wata halitta mai numfashi walau mutum ko aljan da zayi arba da miyagun dakarun face
tayi nadamar wanzuwar ta a doran ƙasa,

Sa'adda su jarumi Hilwas sukayi arba da dakarun sai suka ɗimauce,

Tamkar ace kyat su zura da gudu,amma saboda juriya irin ta zaratan Jarumai sai suka dake,

Jaruma husnat ce kaɗai bata razana ba ita ma saboda tana karanta sunayen Ubangiji tsarkaka
ne a cikin ran ta yasa hakan,

Yayin da dakarun suka kammala yiwa su hilwas ƙawanya sai aka fara kallon-kallo tsakanin su,

Daga can sai dakarun su ka zare makaman su suka yi ihu da kururuwa mai firgitar wa suka
ruga izuwa kan su.

Ko da ganin hakan sai jaruma Husnat ta zare takobin ta ta kwala kabbara da karfi ta ruga izuwa
kan dakarun,

Sharwas, Kahzib da hilwas sukayi koyi da ita ta hanyar zare makaman su,

Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini muni daban
tsaro,

Kowa ne ɓangare su ka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare hare cikin matuƙar zafin nama
juriya da bajinta tagaban kwatance,

Wohoho ana fara wannan artabu ne wani abun mamaki ya fara guda domin kuwa duk irin zafin
nama na su jarumi Hilwas yazama abanza,

Domin kuwa duk sa'adda suka sari jikkunnan dakarun da makaman su sai suji tamkar dutse
suka sara domin wani irin tartsatsin wuta ne yake tashi gami da kara marar daɗin sauraro.

Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin su kenan suka fahimci cewa idan aka Cigaba
da wannan artabu a haka dakarun zasu iya samun nasarar hallaka su.

Abangaren jaruma Husnat kuwa tuni labari yasha bambam,

Domin kuwa Husnat ta zamo gagarabadau a tsakiyar dakarun,

Duk in da ta sanya a gaba sai dai kaga dakarun na zubewa ƙasa matattu tamkar tana sassabe
a gonar auduga.

Tabbas jarumtaka baiwa ce daga Ubangijin halitta ba'a siyan ta kuɗi ko mulki,

Komai hassadar Mutum idan ya ga Yadda Husnat ke ragargazar dakarun doka ne ya jinjina
mata ya tabbatar dacewa ta cika mace mai kamar maza kuma jarumar Asali,

Nanfa ƙarar karafniyar ƙarafa,ihun mazaje haɗe da kururuwar dakaru ta cika dodon kunne,

Sassan jikkunnan dakarun suka dinga shawagi a sararin samaniya suna zubowa ƙasa tamkar
ana ruwan su ne daga saman,

Jini kuwa ya dinga kwaranya, tsartuwa gami da feshi yana zubar a ƙasa tamkar an balle Teku,

Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan fafatawa babu sassauci,

A sannanne dakarun suka fahimci cewa Husnat tayi musu muguwar barna.

Domin ta kashe fiye da rabin su,

Nan fa hankalin su ya dugunzuma ainun,kuma suka fusata ainun zukatansu suka dunga
tafarfasa tamkar zasu kone,

Kawai sai suka zage damtse suna cigaba da kaiwa Husnat hare hare ta ko ina,

Al'amarin su Bawa hilwas kuwa sa'adda su ka ga irin gagarumar bajintar da Husnat ke yi sai
suka cika da matukar mamaki suka ce a cikin ransa anya kuwa Husnat bil'adama ce,

Taya ya za'ayi ce zaratan Jarumai kamar mu mun kasa samun damar hallaka koda badakare
ɗaya amma Husnat ta kashe fiye da rabin su,

Lokacin da sa'a biyu ta shuɗe ana wannan fafatawa a dai dai wannan lokacin ne Husnat ta
hallaka ba ki ɗaya dakarun dake gaban ta,

Kuma ta hango irin mawuyacin halin da su Bawa hilwas ke ciki,

Domin dakarun sun galabaitar dasu basa iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kansu.

Wasu lokutan idan dakarun suka kawo musu hari suka kare da makaman su sai kaga sun faɗi
ƙasa magashiyan,

Amma saboda juriya irin ta zaratan Jarumai sai suka muƙe tsaye aci gaba da yaƙin,

Koda ganin hakan sai ta falfala da azababban gudu izuwa kan su

Tana mai kwala kabbara da ƙarfi tare da yiwa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama salati,

Domin ta kai musu ɗauki,

Cikin daƙiƙa hamsin bisa taimakon Ubangiji mahalicci ta samu nasarar hallaka dakarun baki
ɗaya,

Faruwar hakan ke da wuya sai gaba ɗaya gawarwakin dakarun da makaman yakin gami da jinin
da ya cakuɗa da ƙasa suka ɓace ɓat tamkar basu taɓa wanzuwa ba,

Nan take filin ya rikiɗa izuwa wata ƙasaitacciyar faɗa,

Da aka kawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya,

Bisa wani zagayayyan tudu da aka shimfiɗe sa da wata irin Koriyar Darduma anan aka ajiye
wata ƙasaitacciyar sanda wace akayi ta zallar zinare kuma aka yi mariƙin ta da zubardaju,

Sandar tana canza launi lokaci zuwa lokaci

Kai da gani kasan aiki ne na sihiri.

Koda Husnat tayi arba da sandar sai ta dubi Bawa hilwas tace"sai kayi hanzari ka ɗauko mana
waccan sandar sihiri domin mu tafi izuwa dajin kushuful-fannar domin ɗauko ƙoƙon kan boka
Manaf.

Ko da jin wannan umarni daga bakin Husnat

Sai hilwas ya taka da kafafun sa har izuwa wannan gayayyen tudu yake ya dauki sandar
sannan ya dawo izuwa inda su Kahzib ke tsaye.

Kawai ya shige gaba ya durfafi kofar fita daga gidan,

Sharwas, Kahzib na biye dashi jaruma Husnat ce a karshe,

Lokacin da suka fita sai suka hango dawakan su acan gefe suna cin ciyayi,

A sannanne Husnat ta lura cewa lokacin sallar la'asar ya giya,

Don haka sai tayi istigfari sannan ta cire salkar ruwan ta ta ɗaura alwala,

Bayan ta kammala ne ta fuskanci gabas ta tayar da sallah,

Sa'adda Hilwas, Kahzib da Sharwas suka ga yadda jaruma Husnat ke gudanar da ibadar ta nan
take suka ji addinin musulunci ya kayatar dasu,

Domin ba su taɓa ganin addini mai tsafta da nutsu tamkar addinin Husnat ba,

Nan take Sharwas yaji soyayyar Husnat ta daɗa mamaye zuciyar sa,

Da yake yamma tayi liƙis duhun magariba ya fara kawo kai sai hilwas ya bayar da shawarar a
kwana a dajin idan ya so da safe sai a durfafi dajin Kushuful-fannar,



Mu haɗu a KANGIN BAUTA Littafi na 12 domin jin cigaban wannan kasaitaccen labari,



Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe



Marubuci



MANSUR USMAN SUFI

Wthapp number &;call

08137237071

KANGIN BAUTA
Marubuci
MANSUR USMAN SUFI
Wthapp&call
08137237071





Kamar yadda jarumi Hilwas ya bayar da shawara haka al'amarin yakasance,

In da aka kwana a wajen da duku-dukun safiya bayan jaruma Husnat tayi sallar asuba anyi
kalaci kowa ya kimtsa cikin sa,

Sai kowa ya kama dokin sa ya hau ya sakaasa linzami aka cigaba da tafiya,

Hilwas, Kahzib da Sharwas suna tafiya a jere kusa da juna,

Husnat na biye dasu har a wannan lokaci fuskar ta rufe take da rawani idanuwan ta kaɗai ake
gani,

Nan fa aka wanzu ana ratsa duwatsu, koramu tsaunuka haɗe kwazazzabai gami da sarƙaƙiya,
cikin matsanancin gudu ma keta sa'a ,

Wasa-wasa saka gashi an shafe tsawon Sa'a uku ana wannan tafiya,amma ba'a haɗu da wani
abu mai cutar wa ba,

Koda kuwa miyagun yan fashi da dakarun sumame,

Lokacin da Sa'a huɗu ta cika a dai dai lokacin aka shigo dajin kushuful-fannar,

Nan fa kowa yasha jinin jikin sa bisa ganin yadda dajin yaksance dole ne a samu miyagun
halittu a cikin sa,

Kuma yakasance cikin shirin ko ta kwana

Tsawon tafiyar Sa'a aka yi sannan aka hango wata rijiya a can nesa,

Don haka sai aka ƙara azama domin isa, lokacin da aka isa sai kowa yaja linzamin dokin sa ya
kama ya sauka ƙasa,

Ita dai rijiyar an gina ta ne da zallar dawatsun wuta masu kwarin gaske,

Tana ɗauke da murfi guda ɗaya jal, da aka yi shi da zallar mulmulallan karfe,

In da za'a sanya karti majiya karfi mutun sattin ba zasu iya buɗe murfin ba,

Nan fa aka yi cirko-cirko aka rasa wanda zai buɗe murfin rijiyar.

Daga can Kahzib ya matsa izuwa bakin Rijiyar ya sanya hannun sa ɗaya domin ya buɗe murfin
amma sai yaji tamkar Dutse ya rike, sai da ya tara gumi ya jiƙe sharkab amma murfin ko gezau
bai yi ba,

Amma sai da hilwas, sa Sharwas suka gwada tasu dubarar amma murfin bai buɗe ba,

Duk wannan abu dake da wakana jaruma Husnat na tsaye a gefe guda tana gani bata ce ƙala
ba.

Koda taga kowa ya kasa buɗe wa sai ta matsa daf da rijiyar ta karanta ayatul-kursiyyu tare da
yiwa Annabi s'a'w salati.

Ta sanya hannun ta ɗaya ta buɗe murfin tamkar ta yaye tufafi,

Hilwas, Kahzib da Sharwas basu san sa'adda su ka dunga dalalar da yawu daga bakunan su ba
saboda matukar al'ajabi.

Koda murfin ya buɗe sai akaji wani irin mahaukacin gurnani na fitowa daga cikin rijiya,

Daga can sai aka ga wani ɗan wadan aljani yayo fitar burgu daga cikin rijiyar tamkar an janyo
shi da ƙugiya.

Aljanin yakasance baƙi mummuna yana ɗauke da fuka -fukai irin na jemage, Du du du tsawon
sa bai huce kamu biyu ba,

A hannu ɗaya ana rike da wani ƙoƙon kai, ɗayan kuwa yana ɗauke da wani zabgeegen Gatari
na zinare yana sheƙi da walwali,

Aljanin ya bushe da dariyar mugunta tamkar bazai daina ba

Daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya ce"

Kaicon ku yaku waɗannan bil'adama ma'abota taurin kai da GAJEREN KWANA,

kuyi sani cewa haƙiƙa kun tafka babban kuskure da kuka kuke tsammanin cewa zaku iya
ɗaukar ƙoƙon kan mai girma Mannaf kuma har ku fita a raye,

Ina mai tabbatar muku dacewa dayan ku bazai fita a raye ba,

Kafin aljanin ya gama rufe bakin sa Husnat ta tari numfashin sa tana mai daka masa tsawa tace

"Kai tsohon maketaci kuma azzalumi la'anannan Allah kayi sani cewa,

Ka sani cewa ai babu mai kashe wa face Ubangijin musulunci,

Da yardar sa zamu ga bayan ka sannan samu abinda muka fito nema.

Sa'adda ɗan wadan aljanin yaji wannan batu daga bakin Husnat sai ya fusata ainun idanun shi
su ka kaɗa su ka yi jawur, gashin jikin shi ya mimmiƙe ya dubi Husnat yace "Na rantse da
gemun mai gidana boka Mannaf sai nayi gunduwa-gunduwa da sassan jikin ki ta yadda
ƙananan tsuntsaye zasu ji daɗin tsatstsagar naman ki,
Domin hakan ya zamo darasi ga bil'adama masu tsarin idanu irin ki,

Kafin Husnat ta sake cewa wani abu Aljanin ya ɗaga gatarin sa izuwa sama ya falfala da
azababban gudu izuwa kan ta yana ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAKA

Komai tsakanin yawan su,

Koda ganin hakan sai Husnat ta kwala kabbara da ƙarfi tare da zare takobin ta ta ruga izuwa
gare shi,

Su na haɗuwa suka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini daban sha'awa,

Su duka biyun suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da
bajinta tagaban kwatance,

Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan gwani ya haɗu da tsohon
ƙashi , juriya da jarumtaka suka game a waje guda dola ne artabu ya zamo tashin hankali,

Gaskiyar masu iya magana da suka ce fadan da yafi karfin sai ka koma ɗan kallo,

Hakan ne yafaru da hilwas, Kahzib da Sharwas domin koda suka ga cewa Manyan
GWARAZAN JIYA sun kacame da azababban yaƙi sai suka koma izuwa inda dawakan su suke
suna hangen abinda ke wakana,

Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan fafatawa amma aljanin bai samu nasarar taɓa
jikin Husnat ba,

A zahiri ga wnada yake kallon yadda artabun ke wakana sai tabbatar da cewa aljanin ya nuna
ka Husnat a karfin damtse,

Sai dai ita ta fi shi salon kwarewar yaƙi,

Al'amarin da ya fusata shi kenan ya kaiwa Husnat wani bahagon sara da gatarin sa sa nufin
tsarga ta gida biyu,

Cikin wani irin baƙin zafin nama Husnat ta wurkila tare da zamewa,

Gatarin aljain ya sari iska, koda aljanin yaga cewa yakasa samun nasarar hallaka ta sai ya
shiga aika mata miyagun sihiri kamar ,kibbau, duwatsu,mashi da sauran su,

Amma Dazarar sun doshi inda take sai su narke su zama ruwa su ɗige a ƙasa,

saboda addu'o'in da take karantawa na neman tsari a a gare sa,

Da kyar da siɗin goshi ta samu ta hallaka aljanin ta hanyar soka masa takobi a ƙahon zuciyar
sa.

Kuma ta ƙone shi ƙurmusa ta hanyar karanta masa ayatul-kursiyyu,

Haƙiƙa su Bawa hilwas sun ga iko da ƙidira ta Ubangijin talikai bisa ganin yadda Husnat tayi
masara akan aljanin,

Bayan an fito da abin guzuri an yi kalacin rana. Sai kowa ya sake kama linzamin dokin sa ya
hau ya sakar masa linzmai a ka cigaba da tafiya domin fi cewa daga dajin kushuful-fannar.

Mu haɗu a Littafi na 12 don cigaban wannan labari



Marubuci

MANSUR USMAN SUFI

mansurusmansufi@gmail.com


Kangin Bauta 14

Rubuta labari

MANSUR USMAN SUFI

08137237071





A wannan karon da aka fara wannan tafiya sai fira ta ɓarke tsakanin su jarumi Hilwas,

Domin a wannan karon sun samu nutsuwa a zukatan su cewa jaruma Husnat za ta cika musu
dukkan burikan su bisa taimakon Ubangijin ta,

Gaskiyar masu iya magana da su ka ce sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a je ba,
sai gashi an shafe tsawon kwanaki ashirin da uku ana wannan tafiya,

A ranar kwana na ashirin da huɗu ne da la'asar aka iso birnin Baitul-na'im,



Tun daga nesa aka hango kofar birnin cike da miyagun dakaru ɗauke da miyagun makamai,
Al'amarin da ya sanya su hilwas su ka sha jinin jikin su kenan,

Domin da gani ruwa baya tsami banza, don haka sai hilwas ya ɗauki sandar sihiri ya sanya ta a
kirjin sa ta yadda babu komai wanda zai iya gane ta,

Kuma ya ɗauki ƙoƙon kan boka Manaf ya sanya shi a cikin wata jaka ya rataya a gadon bayan
sa, Sannan ya zare takobin sa. Da ganin hakan sai Kahzib ya zare kwari da bakan sa,

Sharwas ya ciro mashin sa ya rike a hannu, Husnat riƙe da takobin ta aka durfafi kofar birnin
Baitul-na'im,

Yayin da ya rage saura taku talatin tsakanin su da kofar birnin. Sai kawai aka ji wani ƙara daga
cikin birnin sai kofar ta buɗe, Sai ga sarki shardasu, yarima kinzaru da sarkin yaƙi hatyal,
Waɗansu irin girɗa -girɗan dakaru na take musu baya,

Bisa tsakiyar dakarun mahaifan su hilwas me maza da mata sanye cikin sararin baƙin ƙarfe
hannu da ƙafa,

Koda ganin hakan sai su hilwas suka ja linzamin dawakan su suka sauko ƙasa, Suka durfafi in
da su sarki shardasu suke domin tarar juna,

Sa'adda sarki shardasu yarima da sarkin yaƙi suka yi arba da jaruma Husnat sai hantar cikin su
ta kaɗa da karfi tsoro ya ka masu.

Sarki shardasu ya tambayi kansa a cikin ran sa shin wace ce wannan bakuwar jaruma?



Shin ya akayi halarar tsafi na bata bayyana mini ita ba a lokacin da na gudanar da bincike akan
su hilwas ɗin,

Amsar tambayar da sarki shardasu ya kasa bawa kanshi kenan, Amma saboda kada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login