Showing 1 words to 3000 words out of 18096 words

Chapter 1 - FATAUCIN BAYI Book Complete Book Written by Mansur Usman Sufi .pdf

05 Aug 2025

543

FATAUCIN BAYI











MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071





Haƙƙin mallaka
Mansur Usman Sufi
Shekarar bugu
2023

GARGAƊI

Ban yarda wani ya sarrafa min littafi ba ta hanyar yaɗa shi a soshiyal midiya, karantawa a
rediyo ko manhajar YouTube, website da sauran su ba tare da izina na ba, yin hakan zai kai mu
zuwa ga hukuma a kiyaye.
Ko kuwa zuwa babban mai sakamako Allah (SWT).

Sako daga
Sarkin Marubutan Yaƙi



GODIYA

Ta tabbata ga Allah SWT bisa iko da ya ba ni na rubuta wannan littafi mai taken
FATAUCIN BAYI.
Tsira da amincin Allah ya ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi
Wasallama da iyalanshi tsarkaka.

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan littafi ga dukkanin masoyan Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi
Wasallama a ko ina suke a faɗin duniya.


Bugawa da yaɗawa SUFI PUBLISHING COMPANY
R/lemo Kano state Nigeria
08137237071





BABI NA ƊAYA


Ƙasaitaccen jirgin ruwa ne da aka cika shi maƙil da fursunoni maza da mata, manya da
yara, gaba ɗaya an ɗaure hannayen da waɗansu irin murtuka-murtukan sarƙoƙi kuma an haɗa
da katakon jirgin an ɗaure tamau, ta yadda babu mai iya tserewa daga cikin su.
Duba ɗaya za ka yiwa fursunonin ka fahimci cewa sun kasance jama'ar ƙabila ɗaya, abin
da zai tabbatar maka da hakan shi ne yanayin ƙirar jikkunansu da kamanni gami da tufafin su
iri ɗaya ne sak!
A wannan lokaci jirgin ruwan na tafiya ne a saman wani makeken teku, a kowace
kusurwa a jirgin an zuba dakaru masu tarin yawa, suna shirye suke cikin gagarumar shigar yaƙi
hannayensu ɗauke da miyagun makamai, suna ta kai komo domin tabbatar da cikekken tsaro.
Sai da jirgin ya shafe tsawon sa'a biyu da daƙiƙa ɗari biyu yana tafiya a saman tekun ba
tare da watsala ba, shi dai tekun ana yi mashi laƙabi da Baharul-sawara.
Ana cikin wannan tafiya ne wani garjejen ƙato daga cikin dakarun ya dubi wani badakare
wanda da alama shine shugaban su ya risina a gare shi sannan ya buɗi baki ya ce "ya shugaba
na ina ganin ya kamata a kwance waɗannan fursunonin a basu abinci domin sun galabaitu
ainun, haƙiƙa a koda yaushe za su iya rasa rayuwar su, kuma sanin kan ka ne cewa mutuwar
ɗaya daga cikin fursunonin tamkar rasa rayukanmu ne baki ɗaya''.
koda jin wannan batu daga bakin badakare Sharkar sai shugaba Yasiran ya dube shi
cikin alamun matuƙar damuwa cikin wata irin kakkausar murya mai tattare da jarumtaka ya ce
"ya kai Sharkar tabbas ka zo da shawara mai kyau, amma fa wani hanzari ba gudu ba, shin ba
ka tsoron kwance fursunonin zai bada matsala a tare damu? Koda jin wannan tambaya sai Sharkar ya bushe da dariya ya ce ''haba ya shugabana
ka duba fa ka ga irin tsananin yawan mu, ta ya ya kake tsammanin cewa akwai wanda ya isa ya
tsere mana.
Yanzu mafita ɗaya ce ta rage mana, ko dai mu bawa waɗannan fursunonin abinci domin su
rayu, ko kuma mu ƙyale su yunwa da ƙishirwa su zamo ajalin su".

Sa'adda shugaba Yasiran ya ji wannan batu daga bakin Sharkar sai ya ce "tabbas
zancen ka dutse ya kai Sharkar ya zama wajibi mu yi amfani da wannan shawara da ka kawo".
Yana gama faɗin hakan ya umarci waɗansu dakaru mutum arba'in suka kwance
fursunonin mutum ɗari biyu, sannan suka rarraba masu wata bushasshiyar gurasa gami da
wani ruwa mai yauƙi a matsayin abin kalacin su.
Dakarun na cikin aiwatar da hakanne wani badakare ya miƙawa wata yarinya gurasar.
Kafin hannunshi ya kai inda take, sai kawai ta shammace shi ta ciri wata siriyar wuƙa a damtsen
shi ta soka mashi a marainanshi, sannan ta sanya ƙafafuwanta biyu ta daki a ƙirji, take ya
hantsila izuwa cikin tekun yana mai tsandara ihu
Al'amarin da ya janyo hankulan sauran dakarun kenan, suka zubar da abincin suka
zare makamansu suka ruga izuwa inda yarinyar take.
koda ganin hakan sai yarinyar ta ɗauko wata doguwar igiya cikin wani irin zafin nama ta
yiwa igiyar wasu ƙulluna barkatai ta jefawa dakarun, sannan ta daka wawan tsalle ta faɗa izuwa
cikin tekun tana riƙe da sauran igiyar a hannun ta, take igiyar ta zarge kafafuwan dakarun ta ja
su izuwa cikin tekun. Koda ganin hakan sai Sharkar ya dakawa sauran dakarun tsawa da su sake ɗaure
fursunonin, kuma aka umarci masu tuƙin jirgin su tsayar da tafiya, sannan ya yiwa dakaru
hamsin inkiya da hannu da su biyo bayan shi suka ruga izuwa bakin jirgin.
Ai kuwa koda tsayuwar su sai suka yi arba da gawarwakin 'yan uwansu dakarun da suka
faɗa sun taso izuwa saman ruwa, gaba ɗayan su an yi masu yankan rago,
Al'amarin da ya yi matuƙar ba su mamaki kenan kuma ya harzuƙa su.
Abin da ya ba su mamaki shine ya za ayi a ce yarinya ƙarama ta samu ƙarfin damtsen da
za ta yiwa zaratan dakaru sha biyar yankan rago.
Cikin matuƙar fushi Sharkar ya umarci dakaru goma waɗanda suka ƙware wajen iya
ninƙaya a ruwa, suka faɗa izuwa cikin tekun domin laluben inda yarinyar ta shiga.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, domin da a ce waɗannan dabaru sun san abin
da zai biyo baya da ba su gangancin faɗawa tekun ba, domin abin da ba su sani ba shi ne
lokacin da suka faɗa tekun wani ƙaton kifi ya wangame bakinshi, yana hamma ai kuwa bisa sa'a
sai suka faɗa ciki, kawai sai ya lamushe su ya yi loma ɗaya da su sannan ya yi nutso izuwa
cikin tekun.
Nan fa ya zamana cewa Sharkar ya tura gaba ɗaya dakaru hamsin dake biye da shi
izuwa cikin tekun, amma ɗayan su bai taso a raye ba.
Kwatsam Sai aka ga gawarwakin dakarun birjik sun taso daga ƙarƙashin tekun.
Al'amarin da ya ƙara firgita shugaba Yasiran da Sharkar kenan.
Kawai sai shugaba Yasiran ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu, sannan daga bisani ya
murtuke fuska tamkar an aiko mashi da WASIƙAR MUTUWA, sannan ya buɗe bakinshi yana
mai karanta waɗansu dalasiman tsafi, gami da yin nuni da ɗan yatsanshi izuwa saitin inda
fursunar yarinyar ta faɗa.Take ruwan wajen ya daskare ya zama ƙanƙara, kawai sai ya zare
waɗansu zabga-zabgan takubba a godon bayanshi, sannan ya dako wawan tsalle ya faɗa tekun
yana mai yin nitso izuwa ƙarƙashin ta,
A dai-dai wannan lokaci ne rana ta take kuma ta yi zafi ainun, nan fa gaba ɗaya fursunonin
suka shiga cikin mawuyacin hali, musamman ƙananan yara, suka fara faɗuwa ƙasa sumammu,
wasu ma na sheƙawa barzahu, nanfa iyaye matan da 'ya'yansu suka mutu suka shiga rusa
kukan baƙin ciki.

Inda a ce mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da wannan al'amari ke faruwa, dole
ne tausayi ya kama shi ya zubar da hawaye.
Al'amarin shugaba Yasiran kuwa lokacin da ya yi nutso izuwa ƙarƙashin tekun
Baharul-sawara, domin ya lalubo yarinyar fursunar da ta faɗa cikin tekun, sai ya shafe tsawon
rabin sa'a yana dube-dube da kalle-kalle, amma bai ga inda ta shiga ba.
Al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan kuma ya fusata shi, ya cigaba da yin
nutson.
Lokacin da ya zamana ya shafe sa'a biyu cur! Yana wannan bincike, kwatsam bazato babu
tsammani sai ya ji an kirɓa mashi wawan naushi a wuya.
Saboda ƙarfin naushin sai da ya yi katantanwa sau uku, ya saki takubban dake
hannunshi yana mai kurma wawan ihu.
Cikin baƙin zafin nama ya juya domin ya ga wanda ya naushe shi ɗin. Ai kuwa sai ya yi
turus bakomai ya gani ba face yarinyar 'yar shekaru sha biyar, hannayen ta ɗauke zaratan
takubban da suka suɓuce daga hannun shi.
Abu na farko da ya bashi mamaki shine ya aka yi wannan yarinya ta samu ƙarfin
damtsen da ta hallaka dakarun tamkar takasance basadaukiya mace mai kamar maza.
Koda ya zo nan a tunanin shi sai jikinshi ya kama tsuma yana ƙyarma, idanunshi suka
kaɗa suka yi jajur, gashin jikinshi ya mimmiƙe.
Kawai sai ya zare waɗansu takubban na daban a damtsen shi, yana mai yin iyo ya durfafi
inda take yana shaƙar numfashi ta hanyar amfani ƙarfin sihiri.
Koda ganin hakan sai yarinyar ta gyara riƙon wani mazirari a bakinta da take amfani da
shi wajen shaƙar iska. Lokacin da suka haɗu sai suka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar
muni daban al'ajabi.
Shugaba Yasiran da fursunar suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar
zafin nama JUTIYA DA BAJINTA ta ban mamaki.
Babu abin da zai burge mutum ga jaruman biyu irin yadda suka kaiwa juna hare-hare cikin zafin
nama tamkar na'ura ce ke sarrafa su.
A wasu lokutan sai kaga sun taso izuwa saman tekun.
A cikin jirgin ruwa kuwa
koda sadauki Sharkar ya ga an shafe tsawon sa'a biyu bai ji ɗuriyar shugaba Yasiran, kuma ya
ga yadda fursunonin na sheƙawa barzahu sai hankalinshi ya dugunzuma ainun, ya rasa abin
da yake yi mashi daɗi, domin hakan za su iya rasa rayuwar su baki ɗaya idan har su ka isa ga
sarki. Nan take ya faɗa izuwa kogin tunani domin samun mafita, abu na farko da ya faɗo
masshi shine, shin yanzu zai sake ƙwance fursunonin ne ya ba su abinci da ruwan sha domin
su rayu? Ko zai ƙyale su, sannan ma yanzu za su cigaba da tafiya ne ko kuwa za su jira fitowar
shugaba Yasiran daga cikin tekun. Sa'adda Sharkar ya zo nan a tunanin shi, sai kwakwalwarshi ta saƙe dagulewa, da ƙyar
da siɗin goshi ya samu mafita.
Koda samun mafitar sa kawai ya juya ya nufi wani ɓangaren a jirgin, ya umarci waɗansu dakaru
mutum ashirin ya ce su buɗe wani katon murfi, take dakarun su ka cika aikin su suka murfin, sai
ga wata matattakala guda goma ta bayyana wacce ta zata shigar da mutum zuwa ƙasan jirgin,
sannan Sharkar ya yiwa dakarun wata inkiya ta wutsiyar idanu.

Kawai sai suka kwance fursunonin suka shigar da su izuwa ƙarƙashin cjirgin, sannan ya yi
umarni da a basu abinci da abin sha.
Sannan ya juya yana hangen inda shugaba Yasiran ya yi nutso izuwa cikin tekun
Baharul-sawara.
A ɓangaren shugaba Yasiran da wannan fursuna kuwa, sun wanzu suna bawa hamata
iska suna kaiwa juna hare-hare, gaskiyar masu iya magana da suka ce, duk wanda ya riga ka
kwana dole ne ya riga ka tashi.
Nan fa yazamana idan shugaba Yasiran ya kaiwa yarinyar hari idan ta kare harin da takubbanta
sai ka ga ta durkushe ta nutson izuwa ƙasa, amma ta sake taso sama, nan fa ya zamana ta fara
galabaita ainun, ya zamana bata iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kanta, domin daƙyar
take iya shaƙar iska. Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne Yasiran ya shamma ce ta ya yanke ta da takobinshi a
gadon bayanta. Nan take inda ya yanke ta ya haddasa wani lafcecen rauni, jini ya kwaranya,
saboda tsananin zafi da zugi sai da ta tsandara ihu.
Sannan ta saki takubban dake hannunta, jikinta ya sandare tamkar babu rai tare da ita.
Al'amarin waɗannan dakaru kuwa suna cikin rabawa fursunonin abincin ne sai waɗansu
zaratan yan mata guda ashirin waɗanda suka ƙware ainun a fagen sarrafa takobi da sanin
dubarun yaƙi, su ka shammaci dakarun suka afka masu da yaƙi, cikin ƙanƙanin lokaci suka
hallaka dakarun ta hanyar murɗe masu wuya. Koda samun wannan nasara sai wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa mai annurin fuska
da kwarjini daga cikin 'yan matan, ta dubi wasu 'yan matan daban a cikin fursunonin ta ce da su
"ina so ku cigaba da baiwa jama'ar mu wannan sauran abinci, kuma ko me zai faru dar ku
kuskura ku fito daga cikin wannan ɗaki, ko ku kira sunayenmu, kawai ku kira sunayen ababan
bautarmu.
Ina so ku yi sani cewa ɗayan mu ba zai dawo nan ba face mun tserar da sauran rayukan
jama'ar birnin mu kuma mun ɗauki fansa akan sarki Husnalu".
Koda kyakkyawar budurwar ta zo nan azancenta sai jama'ar suka cika da matuƙar farin ciki
mara musaltuwa.
Sannan budurwar ta zira hannunta a aljihun riga ta ɗauko hodar banju ta miƙa wa sauran 'yan
matan ta ce da su "wannan hodar zamu yi amfani da ita ne kafin mu kai ga ɗaukar makaman
yaƙi ina fatan kun fahimce ni, tana gama faɗin hanak sai ta juya ta shige ba sauran suka mara
mata baya. Su na fita sai suka shiga yin sanɗa da laɓe-laɓe, suka nufi madafa.
Lokacin da kyakkyawar budurwa da ake kira Nabihat suka iso izuwa bakin madafar, sai Nabihat
ta ɗauko hodar banju a cikin aljihun rigarta ta busa ta izuwa ciki, jim! Kaɗan sai suka kunna kai
ciki suna shiga suka tarar dakaru masu dafa abinci sun kama barci mai nauyi.
kawai sai suka cire tufafin su suka maye da na dakarun, sannan suka rufe fusakunsu da
hulunan ƙarfe.
Kawai sai suka matsa izuwa inda dakarun suka ɗora sanwa akan wuta suka buɗe
murafun tukunyoyin suka zazzaga wannan hodar banju a cikin, sannan suka mayar suka rufe
ruf.
Bayan shuɗewar daƙiƙa goma sai suka zuzzuba abincin a cikin waɗansu ƙananan
akushi, suka ɗora akan farantai na azurfa, sannan juya suka fice daga tantunan suka shiga

rarrabawa dakarun dake cikin jirgin ruwan abincin mai dauke da hodar banjun har suka iso
izuwa inda wani sadauki yake.
Nabihat ta ɗauki akushi ɗaya ta miƙa mashi ya karɓa ya bude ya sanya hannunshi ya yi
loma ɗaya, kawai sai ya dubi Nabihat ya ce "ya kai Himairu ya aka yi abincin nan ya yi ɗan
karen daɗi haka?
Koda jin wannan tambaya sai Nabihat ta yi murmushi gami da gyaɗa kai, kawai sai ta huce
gaba ba tare da bawa sadaukin amsar tambayar shi ba.
Haka dai suka cigaba da rabawa dakarun abincin, har suka iso inda suka bar saduki Hushaibu.
Nabihat ta ɗauki akushin ta miƙa mashi ya karɓa.
Har Hushaibu ya buɗe da nufin cin abincin kwai ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi, kawai sai ya yi
jifa da akushin ya durfafi madafa cikin hanzari.
A dai-dai lokacinne su jaruma Nabihat suka kammala raba abincin suka samu wata
maɓuya a cikin jirgin suka laɓe.
A fusace Hushaibu ya kunna kai izuwa cikin tantin, ai kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login