Showing 12001 words to 15000 words out of 16862 words

Chapter 5 - Tsutsar Nama Book 3 Complete end by By Billyn Abdull.pdf

a hankali ta ce, “Ke dai Jannifer
sheɗaniya ce wlhy. Lallai da ace bakiyi ridda daga musulimci zuwa kiristanci ba da ba ƙaramar
sheɗaniyar matar hausawa musulma akayi ba. Amma yanzu mun bar musu, dan inba ma
wanda ya sani ba taya zai taɓa yarda kin haɗa iri da fulani. Humm ALLAH dai ya jiƙan General.
Ya tafi yabar baya da ƙura. Maybe da za'a shawarcesa a dawo da shi duniya yaga Munirra
ɗinsa yanda ta koma kamar bata taɓa haɗa jini da yan arewa da musulunci ba da dakansa zai
kashe kansa ma wlhy”.
        “Hummm Hajjaju kenan masu Lagos da jama'ar cikinsa. Ai duk nawa wasan yara ne. Idan
kuna guri mu kuma wake ta tamu ƙananun ƙwari. Mufa a riddar kawai muka tsaya sai ɗan
cinikin goron nan da muke kafawa a faifai da ɗan hutawar nan muna more ƙuruciya. Ku kuwa
fa, idan akace ai tone-tone ai kema musulman sai sun gwammace riddar kikayi wlhy”.       “Uhhm to ya isa. Dan ke baki gajiya da zakuɗe-zakuɗe. Yanzu dai sai anjima idan na tashi
zan zo gida na sameki mu ƙarasa. Dan zan ɗan shiga theater”.
     “Hummm” kawai Jannifer tace daga can tare da yanke wayar tana dariya. Itama sai Hajiya
ƙaramar tai dariyar kawai tana ƙoƙarin ajiye wayar, a dai-dai nan wani kiran ya sake shigo mata.
Ido ta zubama number na tsawon lokaci, YALLAƁAI ɓaro-ɓaro ya fito. Mamaki ya sake kamata
dan rabon da mai number yay kiranta ta jima sosai, dukan tara-tara ƙirjinta ya shiga hi har sai
da wayar ta kusa yankewa ta dawo a hayyacinta. Da sauri ta ɗauka tana miƙewa ta nufi ƙofar
office ɗin ta murza key cike da rashin gaskiya....

      _Hummm wai ina matan nan suka dosa ne?  Sannan waye yay kiran Hajiya Ƙarama
kuma? Idan na fahimta dai Hajiya Ƙarama na waya da Madam ne a farko, matar data ɗakko
Samraah daga Abuja zuwa Lagos. Tab ɗin babbar magana. Ashe ita ɗin musulma ce shine tai
ridda. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Anya wannan duniya kuwa. ALLAH mun tuba badan
halinmu ba._

      __________________

   *_THREE DAYS LATER_*

          Kwanaki uku kenan da faruwar komai. Sam Maash yaƙi yarda ya zauna da family ɗin
nasa akan batun Samraah. Dan haka ran kowa a matuƙar ɓace yake. Amma shi ko'a jikinsa sai

manna musu hauka kawai yake. Dan gaba ɗaya ma ya maida hankalinsa ne akan binciken
yanda akai containers ɗin companyn sa suka ɗiba yara da wiwi saɓanin lodin kayan abinci. Dan
suna shirin tunkarar Mr Paul ne da ƙarfinsu a court saboda sun shigar da ƙara ne kafin shi bisa
shawarar lawyers ɗinsu.        Ta gefe kuma ga jikin Ummie da ya rikice. Ga kuma Samraah dake asibiti har yanzu ba'a
sallamota ba itama, sai dai wata irin kulawa take samu ta musamman da tattali a wajen Hajiya
ƙarama har Mama Balki ta fara shan jinin jikinta. Sai dai abinda Mama Balki bata sani ba ita
kanta Samraah nazartar Hajiya ƙarama take sannu a hankali. Gefe kuma tana kaima ALLAH
kukanta. Koda labari Mama Balki bata sanar mata da ciwon Ummie ba sai yau da Falak tai kiran
wayar Mama Balkin, a lokacin ita kuma ta ɗan fita dan haka Samraah ta ɗaga. Har yanzu basu
taɓa haɗuwa da Falak ba sai dai tana cin abincin gidanta kullum. Bata da lafiya ne tana fama da
tsohon ciki shiyyasa bata zo tama dubata ba, sai dai sun gaisa ta waya har kusan sau uku.
Yanzun ma sun gaisa cike da kulawa ma juna tamkar dama can sun san junan nasu, kafin
Samraah ta sanar mata Mama ta ɗan fita ne, amma idan ta dawo zata faɗa mata sai ta ƙara
kira.
     Daga can Falak tai murmushi da faɗin, “Okay ba damuwa ALLAH ya ƙara lafiya, dama zanji
ko yaya jikin Ummie ne dan na kira Yaya Hayat ashe garin sauri yama bar phone ɗin a gida,
gashi yanda ya fita a hargitse duk na kasa nutsuwa”.
         Ɗan jimmm nayi zuciyata na bugawa da sauri-sauri jin ta ambaci Ummie, da ƙyar na iya
tambayarta “Ummien Maash Mansion? Wani abu ne ya sameta?”.
     Batare data fahimci kan tambayar ba cikin damuwa muryarta na rawa ta ce, “Eh ita, kin san
kwana biyun nan jikin nata duk babu daɗi, to yau dai da alama ya tsananta ne dan shima Yaya
Hayat a rikice ya fita TJ ya kirashi. Wlhy ina tausayawa Ummie, da ace inada wata babbar
dama akan baiwar ALLAHr nan abinda zan farayi shine tsayawa akan samun lafiyarta, amma
muna gani an hanamu taimakonta. Wanda keda ƙarfin yin hakan kuma an kulle masa tunani
gaba ɗaya, dan wlhy da ace Yaya Awwab basu shiga tsakaninsa da lafiyar baiwar ALLAHr nan
ba da kowama yaci ubansa, ai sun san shi ɗin ba kanwar lasa bane har Baba prof ɗin da Paah
ba iya tankwarashi suke ba. Amma ba komai ALLAH yana nan, watarana sai labari”.
       Tuni ma ni ba fahimtar zantukanta nake da ƙyau ba, rawa sosai jikina ke mun, ga hawaye
suna bala'in gudu a saman fuskata. Ashe shiyyasa duk jiya bai zo asibitin ba, yau ma haka. Ko
Hayatu mai ƙoƙarin zuwa sama da sau uku yana kawo musu abubuwa jiya sai dare ya shigo ya
duba ta. Abinci ma TJ ne ke kawowa. Amma Maash tun daren shekaran jiya da zai tafi take
cemasa ya dinga duba mata Ummie da bata abinci bai sake zuwa ba, harta ƙullacesa ma ita da,
da tunanin ya gama cin moriyat ganga zai yada kwautrnta, ashe abinda ke faruwa kenan...
      “Ya subahanallah Samraah! Wani abu ke miki ciwo ne? Ko tashi kikayi da ƙarfi kika fama
ciwon?”.
    Mama Balki ce mai maganar nan a rikice. Ɗagowa nayi ina kuka mai tsanani dan
shashshekar da nake tasa har fisga numfashina keyi. Lallashina Mama Balki ta shiga yi tare da
bani ruwa tace nasha. Da ƙyar na amsa nai maƙwarwa uku, jikinta ta jawoni ta rungume, hakan
sai ya taimaka min wajen samun nutsuwa na fara sassauta kukan. Kaina na a saman cinyarta
tana shafa gashina ta ce, “Samraah”.
       Cikin dasashjiyar muryata na amsa mata da, “Na'am Mama”.
   “Mike faruwa?”.

  Da ƙyar na iya danne kukan dake taho min na ce, “Mama Ummie. Ashe bata da lafiya amma
shine babu wanda ya sanar min”.
     Iska ta ɗan furzar cikin damuwa. Kafin ta ce, “Waye ta faɗa miki?”.
    “Falak”.
Na bata amsa ina sharce hawaye.......✍️


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _**_Typing_*

*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_




_����� ������ ��_



_���� �����_
_��� �����_


*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku
bari ayi babu ku._

*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram_*

I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG


https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

___________

......Kanta ta girgiza da faɗin, “Ni ban san sai yaushe bakin Falak zai iya dinga koyon shiru ba.
Kiyi haƙuri an ɓoye miki ne saboda kema ga yanayin da kike ciki. Shekaran jiya ne Alhaji ƙarami
ya shiga yana ƙoƙarin bata abinci shine fa kawai jikin ya rikice. Ta jimasa ciwo sosai a hannu da

ƙyar aka iya fiddoshi a ɗakin, daga nan duk wanda ya shiga da duka take korosa, to yau kuma
sai ta yanke jiki ta faɗi saboda kwana biyun nan bata ci bata sha rashin abinci jikinta yayi week.
Amma ki kwantar da hankalinki zuwa yanzu sun ce Alhamdullah komai ya dai-daita. Dan
Hayatu ma ya tabbatar min tana barci saboda drip ɗin da aketa ƙara mata.”       Duk da na ɗan ji nutsuwa sai da na sake sharce hawaye, ɗan shiru mukayi kafin a hankali
nace, “Mama”.
    Da kulawa ta amsa min da, “Na'am Samraah”.
        “Mama a yanzu sai nake ganin kamar shi yafi dacewa ma abinda ke tare da shi ya rabu da
shi kafin a samu nutsuwar yima Ummie magani. Duk da dai wani abu ya jima yana damuna.
Yanzu duk kuɗinsa ace gidan nan babu cctv camaras tako ina?”.
       “Tabbas gaskiya kika faɗa Samraah. Sai dai mun kwatanta hakan muma bai yiwu ba, a
dalilin tsanar magani da Alhaji ƙarami yayi tun yana ƙaraminsa. Ko yaya ruwa ya surka wlhy
bazai sha miki shi ba koda da kala ne. Shiyyasa yin maganinsa keda matuƙar wahala. Gashi
kuma shi ba'a zaune yake ba waje ɗaya, duk yanda muka so fara bashi koda ruwan addu'a ne
sai kiga abin ya zama shiririta. Ina da tabbacin kuma wanda ke wannan aikin kullum cikin
sabuntashi suke bawai sun koma sun kwanta bane suma. Maganar camara kuwa ai Alhaji
ƙarami yasha sakawa amma sai a wayi gari duk an ciresu. Har ɓoyayyar camara an saka a
gidan nan amma kamar abin maita wlhy sai da aka cireta. Hakan na nufin koma su waye a biye
suke, shiyyasa ma kikaga ina sake jin tsoron al'amarin gidan nan da mutanensa. Dan idan bana
jikinka ba banga wanda zai dinga maka wannan bita da ƙullin ba a nesa da kai”.
     Baki na buɗe zanyi magana sai naji kamar amalar motsin tsayawar mutum a ƙofa. Shiru nayi
bance komai ba, sai kuma kamar ance na ɗaga ido na hango inuwa ta jikin window. Magana
Mama zatayi na wayance ina mai zame kaina da ga cinyarta na ce, “Mama barci nake ji. Dan
ALLAH idan Nurse ɗin nan tazo kice bana son allurar nan ni nama warke karki bari tamun”.         Kallon mamaki da naga Mama namun yasa nai mata nuni da window da ido. Tuni ta ɗauki
haske kasancewar dama a ankare take. Itama sai ta wayance ta shiga ƴar dariya da faɗin,
“Ja'ira ai allurar nan sai an kaita har ƙarshe, bari ma Hajiya tazo zance ta sake ƙara miki kwana
biyu kiyi digir dake yanda zamu koma gida da ƙarfinki”.        Shagwaɓa na shiga mata da faɗin ni bana so. Itako tana dariya. Daga haka mukayi shiru.
Kwanciya nayi zuciyata na faman kai-kawo. Tabbas lokaci yayi fa dazan dawo hankalina. Dan
na fahimci in har shi bai fita a halin da suke sanyashi ba baiwar ALLAHr nan bazata taɓa samun
ingantaccen lafiya ba. Domin sauƙi yana samuwa a gareta, sai dai yanayin kwan-gaba
kwan-baya da ake fuskanta yasa al'amarin ke taɓarɓarewa. Idan kuwa har za'a iya hana cctv
camaras zama lafiya to lallai waɗan nan mutanen ba ƙaramin shiri sukai ba. Suma kuma suna
buƙatar a shirya musu yanda ya kamata. Dan dole wayo al'amarin yake buƙata da hikima kamar
yanda suma suke komai ta cikin basira”. Wannan tunane-tunanen da hawayen da suka kasa
barin idanuna ne suka haifar min da zazzaɓi mai zafi, gashi naƙi gayama Mama har bayan
sallar isha'i. Dan da ƙyar ma nayi alwala saboda sanyin da nake ji. Ina idarwa na haye gado na
kwanta tare da duƙunƙunewa cikin bargo. Sosai na gaji da zaman asibitin nan, fatana kawai
ALLAH yasa yazo dan shine kawai zaisa a sallameni. Yan gidansu dai dama babu wanda ya
sake zuwa sai Hajiya ƙarama da nake gani, ita kam kullum ne sai ma tazo sama da sau uku, sai
daga baya na fahimci ai dan asibitinta ne shiyyasa itama muke yawan ganintan.....

        

   Sosai damuwar halin da Ummie ke ciki a kwana biyun nan yasa bai sake waiwayen asibitin
ba. Duk da kuwa wani sashe na hankalinsa na'a can ɗin. Sai dai rashin isashen lafiya shima
dana lokaci ta sashi baiyi wani yinƙuri ba. Yau kuma zafi da ƙuncin da gidan ya masa matuƙa ya
sashi ɗan kimtsawa bayan ya dawo sallar isha'i. Tun la'asar ya kora Hayatu gida dan haka shi
kaɗaine a sashen sai Laalah da TJ dake leƙowa akai-akai duba shi shi da Shu'aibu amintaccen
guard ɗinsa. Tsaff ya fito yana zuba mayataccen ƙamshin nan nasa tamkar ba dare ba. Tj da
Shu'aibu na ganinsa suka miƙe da sauri, hakama sauran ma'aikatan gidan sai gaisuwa suke
miƙawa. Hannu kawai yake ɗaga musu dan kwana biyun nan miskilawan ne a kusa. Da ga shi
sai TJ da Shu'aibu sukai fitar dan hana sauran guards ɗin binsu yayi. Tj ke driving Shu'aibu a
gefensa. Shi kuma yana baya zaune idanunsa akan wayarsa yana daƙila. Kicin-kicin fuskar nan
take babu alamar ya taɓa sanin minene ma dariya.
     Cike da girmamawa TJ ya ce, “Boss ina muka nufa?”.
    Shiru bashi da niyyar amsawa. Sai da ya mula dan kansa ya furta, “Hospital”.
     Cike da girmamawa TJ ɗin ya amsa masa tare da ɗaukar hanya. Har sun gota wani bakery
yace TJ ɗin ya dakata. Tuna duk lokacin da zasu je asibitin tare da Hayatu sai ya sa an tsaya ya
sayi wasu abubuwan ya sashi cewa a dakatan. Shima TJ ɗin tun bai furta ba ya fahimci abinda
yake nufi tunda dai koda yaushe da shi ake zuwa asibitin shima. Fita yayi zuwa cikin bakery ɗin
batare daya amshi wani kuɗi ba, dan boss ya wuce fiye da haka a wajensu ai. Bai wani jima ba
ya fito ɗauke da ledoji masu ƙyau har guda uku. Booth ya buɗe ya sakasu sannan ya dawo cikin
motar. Zuwa yanzu ba wayar yake daƙila ba kansa ya kwantar a jikin kujerar ya lumshe
idanunsa. Koda suka iso ma sai da ya ja kusan mintuna biyu tamkar mai nazarin ta yanda zai
shiga cikin asibitin sannan ya fito. Yana gaba cikin takun nan nashi na ƙasaita da isa su TJ na
biye da shi. Babu yawaitar mutane har ma ma'aikatan jefi-jefi ne. Ko kallon wanda suke a
reseption ɗin kuwa baiyi ba yayi wucewarsa. Sai su TJ ne suka gaishesu. Suko suka bishi da
kallo tamkar wasu tsoffin mayu. Sai faman washe bakuna suke yau gasu ga Maash, mutumin
da yafi kuɗi wahalar gani a Nigeria. Dama wasu a abokan aikinsu sun sanar musu da zuwansa
a kwana biyun nan, sai dai su basu taɓa cin karo da shi ba sai yau ɗin...

Har yanzu duƙunƙune nake a cikin bargo ina rawar sanyi dan zazzaɓi nake ji sosai. Ga
hawayen damuwa da halin da Ummie ke ciki sun kasa tsayawa a idanuna. Ita mama Balki ta
ɗauka nayi barci ne, dan haka ta maida hankalinta a kallon tv tana sauraren wa'azin malam Ali
isa fantami da aka saka a African tv3. Knocking ƙofa da akayi a hankali kamar abin dole ya sata
rage ƙarar tvn, shiru kamar baza'a sake ba sai kuma aka ƙara. Miƙewa tayi zuwa jikin ƙofar tana
tambayar waye? Jin ba'a amsa ba ta buɗe. Ni dai duk ina jinsu amma da yake har kaina na'a
cikin bargo ba ganin komai nake ba.
     Murnar da naji tana yi da ambaton sunan Alhaji Ƙarami ya sanya gabana faɗuwa. Sai ko ga
mayataccen ƙamshinsa ya gama isowa har cikin hancina. Wasu muryoyi biyu naji suna gaisheta
da tambayarta mai jiki. Na gane muryar driver ɗinsa. Ɗayan ne dai ban gane waye ba amma
nasan ba hayatu bane ba. Sai da naji alamun fitarsu da rufe ƙofa sannan shima naji muryarsa a
daƙilen nan can ƙasa-ƙasa kamar abin dole yana gaida Mama. Ita ko da kulawa take amsa
masa da tambayarsa jikinsa da kuma na Ummie. Nan ɗin ma da ƙyar ya amsa itama yana

tambayarta ya mai jiki. Itako da fara'a ta ce masa, “A jiki da sauƙi sosai. Yau ne ma ta so
birkicewa saboda samun labarin jikin Ummie daya motsa da tayi. Dan har bayan sallar magriba
ɗin nan tana shartar hawaye sai da na ɗan mata nasiha sannan tai shiru, inaga shine ma dalilin
kwanciyar da wuri sai kuma barci ya ɗauke ta. Banji yace komai ba, sai dai haka kawai na dinga
jin kaifin idanunsa a jikina. Shiru ɗakin na kusan minti ɗaya sai kuma naji ƙarar buɗe ƙofa da
rufewa. A zatonta shine ya fita, dan haka cike da shagwaɓa na janye bargon daga saman
fuskata zanyi magana da Mama. Zuuuu naji jinina na falfala uban gudu ta cikin jijiyoyina tsabar
shock ɗin cin karo da abinda nai zaton shi ya fita. Da sauri na kauda kaina na sake maida
fuskata cikin bargon.
        A bazata naji alamar an zauna a kusa da ni, Ji nai na sake daburcewa kamar zan fasa ihu,
amma sai na dake tare da yin luff a cikin bargon ina addu'ar ALLAH yasa kada yace sai na buɗe
kaina........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login