Showing 3001 words to 6000 words out of 16862 words
Chapter 2 - Tsutsar Nama Book 3 Complete end by By Billyn Abdull.pdf
mata kallon mamaki. Itako sai ta kallesu
sai ta fashe da dariya, da tayi kamar zata tsagaita sai ta kallesu ta sake fashewa da dariyar.
Wani irin tuƙuƙi zuciyar Mom ta shiga yi, tana yunƙurowa a fusace zata sake shaƙo Halimen sai
kawai ta kauce mata tare da ɗaukar kayanta data tara a kwandon kife kaya tai ficewarta. Sai dai
taje bakin ƙofa sannan ta ɗan dakata. Juyowa tai ta kalla Mom har lokacin fuskarta da sauran
dariyar ta ce, “Ƴar baƙin ciki, so kike na biye miki muyi dambe dalin Imamu ya talauce saboda
ke kin gama shan daɗin romin zabbi. To wallahi bashi yiwuwa nima sai na dandali arziƙin nan.
Ɗan romon kifin nan dana kaji da ban samu naci a gidanmu ba sai na sha farina ya sake fitowa
nayi ɓul yanda zanje ƴan tumaki ana ku matsa ga matar Alhaji Imamu nan ta iso haaaah”. Ta
ƙare maganar da gatsine mata baki tana yin gaba abinta.
Kasa ko motsi Mom tayi, sai zuciyarta dake wani bala'in yunƙurowa. Wai itako yaya zatayi
da mahaukaciyar yarinyar nan a gidan nan. Tayi bala'in, tayi fitinar, tayi boren, tana kan asirin
amma duk a banza. Babu irin maganin da batai amfani da shi ba a kofar shiga ɗakinta da cikin
abincin da Abba da Halime zasu ci amma ko gezau. Jiya har layun da teacher ya bata ta shiga
har ɗakinta ta sanya a ƙarƙashin gado amma ko gezau, bayan kuma Umma ta tabbatar mata
idan har ta saka layun yarinyar nan ta kwanta a gadon bazata kwana a gidan ba sai dai gidan
Ubanta. Kuma komai dare sai ta koma garinsu a ƙafa. Haka ta kwana zaman saurare amma har
gari ya waye babu ko dogon motsi daya faru a gidan. Sai ma da farar safiya Halimen ta tashi ta
damesu da aiki da waƙe-waƙenta na iskanci kai kace ita ɗin jikar barmani choge ce ko shata.
A fusace itama ta bar kitchen ɗin tana dakama mai aikinta tsawa....
Suna akan hanya nufar gida Hayatu ke bashi labarin rikicin da Ummie tayi yau a gida na
neman Samraah. Har falon ƙasa ta sakko yau tana riƙe duk wanda ta gani ta bisa da kallo, sai
kuma ta girgiza kai ta saki wanda ta kama ɗin ta tafi na gaba. Bayan ta gama bin kowa bata ga
wadda take neman ba sai kuma ta zauna ta sanya kuka. Abin yayi matuƙar bama kowa
mamaki. Nima na koma amso kayan da zasuyi amfani da shi ne na tadda wannan drama. Da
ƙyar na lallaɓata bayan na ambata mata sunan Aunt sai ta shiga gyaɗa kanta alamar dai
tabbacin ita ɗin take nema. Lallashinta nayi tare da tabbatar mata zanje na kirawo mata ita
sannan ta yarda ta koma saman. Shine dana kai musu kayan na samu abinci na kai mata taci
na bata magungunanta. Tana kammala ci sai barci. Koda na koma bayan magrib ɗin nan na
samu har lokacin tana barcin. Yaya abin nan yamun daɗi, da'alama Ummie ta fara samun lafiya,
tunda har take iya banbance mai ƙyautata mata. Lallai Aunty Samraah alkairi ce a rayuwarmu.
Lallai akwai hikima a cikin sanadin shigowarta rayuwarmu”.
Kamar yanda Hayatu yayi tsammani baice komai ba. Sai dai a bazata badan kar ace yayi
ƙarya ba sai yaga kamar yayi murmushi. Amma dai baya ce ba, tunda ba gani yay ƙuru-ƙuru ba
kasancewar fuskarsa na gefe.
Shiru ya samu gidan da alama kowa ya kwanta, maimakon wucewa nasa sashen duk da
yunwa da gajiyar dake addabarsa sai ya nufi sashen Ummie. Daki-daki yake bin ko'ina da kallon
tsaff, gaba ɗaya sashen ya canja yanzu akoda yaushe cikin ƙamshi da tsafta yake. Duk da a
yanzu falon farko ne kawai mai kujeru, amma sauran duk an kwashe komai tunda Samraah tayi
magana. Duk da a ɗari-ɗari yake bai dakata ba sai da ya dangane da bedroom ɗin da a yanzu
yafi samunta. Sassanyar ajiyar zuciya ga sauke yana mai jingina da bango da lunshe idanunsa
sannan ya buɗe a kanta. Barci take har yanzu, sai kuloli masu ƙyau ata gefenta alamar abincine
a ciki, yasan wanda Hayatun ne ya kawo, dan haka ya ƙarasa a hankali cikin takun sanyin jiki
ya bubbuɗe kulolin. Lafiyayyen abincine da ko ba'a faɗa ba yasan Falak ce ta yisa duk da tana
fama da kanta itama. Ajiyar zuciya ya sauke tare da furzar da iska mai nauyi daga bakinsa. Sai
kuma ya maida komai ya rufe ya koma bakin katifar ya zauna. Blanket ɗin data ɗan zazzame ya
gyara mata, a hankali ya kai hannu ya gyara mata hularta da ita ta zame. Sosai ya zuba mata
idanunsa da suka kaɗa sosai. Daka gani kasan kukan zuci yake yi. Ya jima zaune a ɗakin duk
da uban barcin da yake ji har kusan gabannin asuba ciwon kai ya takura masa sosai sannan ya
miƙe........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NE_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _**_Typing_**_Typing_*
*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_
_ _
_ _
_ _
_______
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku
bari ayi babu ku._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
_______
.......Tsaff sashen nasa yake an gyara komai tamkar koman bai faru ba. Yasan aikin Mama Balki
ne wannan. Dan hatta bedsheet ɗin saman gadonsa da blanket an canja su da wani fari tass
mai ƙyau da masifar laushi. Bathroom ya shiga, can ma ɗin dai an tsaftacesa. Sai kawai yayi
wanka tare da ɗauro alwala ya fito. Sai da ya fara gabatar da shafa'i da wutri sannan ya kwanta
dan barci sosai ke cin idanunsa ga ciwon kai da baya raba ɗayan biyu a dalilin zaman sashen
Ummie da yayi ne. Dan lafiya lau suka shigo gidan sai gajiya dake damunsa. Yana kwanciya
kuwa barci mai nauyi yayi awon gaba da shi...
Da asuba makarar da yayi ce ya sashi yin salla a ɗakinsa ya sake kwanciya. Barci ne mai
nauyi ya ɗaukesa har ya manta ma safiya ce ba dare ba. Duk da kuwa shi da wahala kaga yana
barcin safe ko rana. To inama yaga wannan lokacin kullum abubuwa sun ma kansa yawa. Idan
har kagansa yini guda a gida yana hutawa lallai ba lafiya ba. Ko kuma akwai wani
ƙwaƙwƙwaran dalili. Dan ko nan ta samu ya gudo dan ya huta baka rabashi da laptop ko tab a
hannu yana harkokinsa.
Cikin barci sautin knocking ɗin ƙofa ya addabesa. Dole ya buɗe idanunsa yana mai karanto
addu'a. Sai da yaja kusan mintuna uku kafin ya miƙe zaune cike da takaicin wanda ke damun
nasa. Agogo ya kalla goma da wasu mintuna na safe. Yaɗan furzar da iska kaɗan tare da zuro
clean ƙafafunsa ƙasa. Nan ɗin ma sai da yaja wasu sakanni sannan ya ɗauki remote ya danna
ƙofar ta buɗe kanta. Paah ne ya shigo, dan haka ya zuba masa ido kawai yana kallonsa. Sai
kuma ya motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Good morning”.
Amsa masa Paah ɗin yay da, “Morning dear, ka tashi lafiya?”.
“Alhamdullah”.
“To masha ALLAH. Dama Baba ne yazo tun ɗazun, da yace kar a tashe ka harka tashi da
kanka, sai kuma ga baƙi munyi da ga human right, wai sunzo ne akan case ɗin yarinyar nan.
Bamu san wanene yaje ya sanar musu ba a gidan nan. Muhammad wai miya kaika aikata
al'amarin nan? Bayan nasan wannan ba halinka bane ba. Baka aikata a waje ba sai a cikin
gida, haba Muhammad da mahaifiyarka na cikin lafiyarta mi kake zato”.
Komai Maash bai ce ba har Paah ya gama maganarsa. Cikin ɓacin rai ya juya ya fita
yana mai bashi umarnin fitowa yanzun nan ana jiransa kada ya ɓata musu lokaci. Da kallo
kawai ya bishi na tsawon mintuna har biyu, kafin ya furzar da nannauyar iska ya miƙe.
Bathroom ya nufa, bai wuce mintuna biyar ba ya fito. Ba tare daya canja pyjamas ɗin jikinsa ba
ya zura bedroom slippers ɗinsa masu taushi farare tas kamar pyjamas ɗin nasa ya fito. Baiyi
zaton a falonsa suke ba. Dan haka yay ɗan turus yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Gaba
ɗaya manyan gidan ne sai baƙi fuska mata biyu da maza biyu. Ɗauke idanunsa yay cike da
basarwa, a dakile ya furta, “Good morning”. Yana kaiwa cikin kujera da ke gefen Baba prof
alamar shi aka barma wajen zaman dama. Duk da dai kowa ya samu nasa gurin kasancewar
falon bawai kujeru bakwai bane ba kawai. Yanda ya tsuke bakinsa da ga gaisuwar farko kowa
ya fahimci jam'i yayi. Kuma bazai sake wata ba. Harara Hajiya Mammah ta watsa masa.
Hakama Hajiya ƙarama sai da ta ɗan cija lips. Maman Malika ce kawai tayi ɗan murmushi da
faɗin, “Awwab babu dai wata matsala ko?”.
Kansa ya jinjina mata. Sai kuma a hankali ya ɗan motsa lips ɗinsa ya ce, “Alhamdullah
Mamy”.
Da fara'a itama ta ce, “Alhamdullahi mun gode ALLAH. ALLAH kuma ya kiyaye gaba”.
Baba prof, Paah, Uncle Abdullahi suka amsa da amin. Duk da dai fuskokinsu babu walwala
suma. Kallonsa Baba prof yayi kamar mai nazari, kafin ya masa nuni da baƙin fuskar yana
faɗin, “Baƙine daga human right. Wai sun zo ne akan case ɗin yarinya da akai raping anan
gidan. Sunyi-sunyi da ita tun jiya wai ta faɗa musu amma taƙi. Shiyyasa suka zo domin ganawa
da kai, suna son a basu izinin yin bincike akan case ɗin”.
Shiru babu alamar Maash zai amsa kamar ba da shi Baba prof ɗin ke magana. Dan tun
kallo ɗaya da yayma mutanen bai sake ba. A yanzu ɗin ma da yaji bayanin komai daga baba
prof ɗin bai kallesun ba bai kuma tanka ba sai da ya mula dan kansa. Zamansa ya gyara cike
da ƙasaita a wulaƙance ya kallesu a karo na biyu. Cike da gizagonsa ya furta, “Ko zan iya sanin
mai kai report ɗin?”.
Kallon juna sukayi, sai kuma cikin ƙarfin hali namijin dake facing Maash ɗin ya furta,
“Ranka ya daɗe wannan ai sirri ne bama buɗesa. Duk wanda ya kawo mana report akan wani
case yana da cikakkiyar kariya a garemu tako wace fuska. Amma idan munyi kuskuren shigowa
bada izini ba ayi mana afuwa. Muna akan aikinmu ne”. Kamar bazai tanka ba dan har sai da kowa ya zuba masa ido a falon, sai kuma ya yunƙura
ya miƙe yana faɗin, “Okay tunda har kuka fahimci hakan da kanku ina fatan zaku gane hanyar
da kuka shigo. Dan bana buƙatar fitowa na sameku koda a gate ɗin gidan nan ne”. Daga haka
yay wucewarsa cike da takunsa na izza. Duk binsa sukai da kallo, sai da Baba prof ya katse yanayin cikin wayancewa ya saki
murmushi da faɗin, “Kufa yi haƙuri, shima tun jiya ransa a ɓace yake da faruwar al'amarin. Wani
dalili ne ma daya ɗan gitta yasa bai ɗauki mataki ba. Amma na tabbatar tunda har kuka zo nan
da kansa zai nemeku idan ya huce. Maybe shigowar karan tsaye da kukayi mana ne ya
tunzurashi. Amma in har komai ya dai-daita ni da kaina zan nemo ku in sha ALLAH”.
Badan sun gamsu da bayanin Baba prof ɗin ba suka miƙe. Sai dai sun tabbatar da yanda
suka karanci tsagwaron rashin mutunci a fuskar Maash ɗin to lallai idan har ya dawo ya same
sun komai zai iya faruwa. Har gate Baba prof yay musu rakkiya yana ƙara basu haƙuri. Sai da
ya ga fitar motarsu sannan ya dawo. Zama suka sake yi jugum-jugum amma babu alamar
Maash zai sake fitowa. Hajiya Mammah ce ta katse zaman shirun nasu da faɗin bara ta sake
kiran Maash ɗin. Amma sai Baba prof ya dakatar fa ita akan ta barsa yana son yanzu shi yaje
asibiti yaga yarinyar kafin su san ta hanyar da zasu ɓullo ma al'amarin. Sam bata so haka ba,
sai dai ganin sauran duk sun bada goyon baya yasa ta yin shiru....
Maash kam daga falon hanyar da zata sadashi da sashen Ummie ya nufa. Ya samu sashen
na sabon ƙamshi alamar an masa gyara. Sosai yayi mamakin waye kuma? Tunda yasan ita
tana asibiti. Yana shiga yaci karo da mama Balki na shirin fitowa. Cikin kasa ɓoye mamakinsa
ya ce, “Mama kece?”. Murmushi tayi cike da kulawa ta ce, “Eh Alhaji ƙarami. Ai mutuniyar taka ce tun asuba data
farka take ta roƙona nazo na duba mata Ummie, tasan maybe bata ci abinci ba. Harda kukanta.
Dan haka ina yin sallar asuba gari yay haske nai shirin tahowa sai kuma ga Hayatu ma yaje kai
abinci shine na biyosa ya kawoni. Gata nan har ma taci abinci tasha magani barci ya ɗauke ta.
Sauri nake kuma na koma can asibitin yanzu dan zata iya ƙin shiga ruwan zafin dana bar mata
itama”.
Idanunsa ya ɗan lumshe tare da buɗewa a lokaci ɗaya. Sai kuma a hankali da silent
voice ɗin nan nasa ya furta, “ALLAH ya saka da alkairi Mama”.
“Amin Alhaji ƙarami ai yiwa kaine. Bismillah ka shiga, Bara naje Hayatu na jirana zai maida
ni”.
Shiga yay ita kuma ta fice. Ya jima a ɗakin yana kallon Ummie har sai da kansa ya fara juya
masa sannan ya fito. Da gaske sauƙi ya fara samuwa. Dan inda dane a yanda ya shigo ɗin nan
komai barcin da take yi saita tashi kansa. Amma kalla jiya yafi zaman awa biyu amma harya fita
bata ko motsa ba sai shine da ciwon kai ya addaba. Sashensa ya koma batare daya bi takan su
Paah dake a falo ba. Yay wankansa ya shirya tsaff da shi. Bayan ya gama fesa turarurtukansa
masu ƙamshi da tsada kala kusan biyar, shiyyasa ba'a gane ainahin turaren da yake amfani da
shi yay zaman saka takalmi. Wayarsa da akai kira ɗazun bai ɗauka ba ya duba. MD ɗin
companyn sa ne na Kano. Kiransa yay back, dan yasan akan maganar Musaddiq ne. Cike da
girmamawa baturen mutumin ya gaishesa da ga can. Kafin ya ɗora masa bayani akan komai na
Musaddiq ɗin ya kammala. Zuwa next week zai biyo jirgi zuwa nan Lagos daga nan sai ya
wuce. Kamar yanda ya saba amsa wayarsa bata wuce ɗaya biyu koda zakuyi maganar awa ne
ya amsa masa da “Okay” kawai ya yanke wayar. Daga haka ya ƙarasa shirinsa ya fito.
Hayatu da Tj kawai ya samu a falon suna jiransa. Bai zauna ba da ga tsayen ya amsa
gaisuwarsu yana mai ɗan kallon agogon hannunsa mai shegen tsada da ƙyau. Sai kuma a
hankali ya furta, “Let's go”. Duk miƙewa sukayi, yana gaba suna binsa a baya, sai ma Hayatu ne
dake ɗan masa bayani daya shafesu dan akan kasuwanci ne har suka iso gaban motocin da
aka gama shiryawa domin fitar tasa. A tare guards ɗinsa da sauran ma'aikatan gidan suka
dinga kawo gaisuwa da jajanta abinda ya faru, tare da masa addu'ar kariya daga sharrin duk
wani abun sharri. A karo na farko ya ɗan saki gajeren murmushi tare da haɗe hannuwansa a
waje guda alamar ya gode. Kamar ko yaushe yana baya TJ na mazaunin driver Hayatu a
gefensa. Sai motar guards ɗinsa guda biyu ata gaba da baya su suna tsakkiya.
Sam yawo da guards ɗin nan ba sonshi yake ba. Sai dai baida wani zaɓin daya wuce hakan
saboda yanayin ƙasar tamu balle shi mai yawan maƙiya da masoya. Yasha tsallake tarko da
aka shirya halaka rayuwarsa. Ana kusan ƙarshe ne da har ya samu harbi gab da shirin buɗe
Companynsa na kano har aka harbesa, ALLAH dai ya taƙaita wahala harbin ya samesa a gefen
kafaɗarsa ta hagu, daga nan ne Hayatu ya dage akan fitarsu da Guards ɗin.
Tsaiwar motocin ya sashi kauda tunanin ya ɗago, ganin asibiti ya sashi ɗan kallon Hayatu
daya buɗe masa ƙofa. Murmushi Hayatun yayi yana duƙar da kai da sosa ƙeya. Komai baice
masa ba face ɗan girgiza kansa kawai ya zuro ƙafafunsa ya fito. Ciki suka nufa batare da ya
lura da motocin su Paah ba, amma shi Hayatu sarai ya gansu dan tsakanin isowar tasu da tasu
ma ƴan mintuna ne.........✍️
To Masha ALLAH. Barkan mu da dawowa, ku tayani addu'ar dagewa na gama book ɗin nan
kafin salla
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_