Showing 9001 words to 12000 words out of 16862 words
Chapter 4 - Tsutsar Nama Book 3 Complete end by By Billyn Abdull.pdf
í ¾íº´í ¾íº´í ¾íº´í ¾íº´í ¾íº´
    Â
   *_KARAMCI HOSPITAL_* asibiti ne da zamu iya kiransa tsaka tsaki a girma. Dan bai
kasance ƙaton gaske ba, bai kuma kasance ƙarami ba. A ɓangaren kayan aiki komai an
wadatashi da shi. Duk da sunansa asibitin kuɗi ana aiki a cikinsa tamkar ƙyauta ne saboda
sauƙi da sauƙaƙama al'umma. Hakan yasa mafi yawan talakawa suke saurin garzayowa jiyya
da karɓar magani a cikinsa. Sai dai da yake komai nasu a tsare yake bazaka taɓa samunsa
barkatai ba komansu a tsare yake.
   Kamar dai yanzu daya kasance rana ta fara ɗagawa, tako ina tsaftace yake sai ma'aikata
dake É—an kai kawo. Sannan shiru yake babu wata hayaniya ko yawan kai-kawon mutane bayan
ma'aikatan saboda dokarsu ce irin yanzu ba'a zuwa duba mara lafiya sai yamma daga huÉ—u
zuwa shida. Koda motocin su Maash suka iso ma da farko securitys ɗin ƙin tashi sukayi su buɗe
saboda dokarsu ce ba'a ganin mara lafiya da dare ko safiya zuwa kafin cikar huÉ—u ko kai
wanene, sai da Hayatu yay kiran number Hajiya ƙarama sannan securitys ɗin suka tashi cikin
rawar jiki suka wangale gate É—in. Suna gama parking Tsaki Hajiya Mammah tayi tana mita harda
zagin Hajiya Ƙarama lokacin da take fitowa. Babu dai wanda yace da ita komai.
    Hajiya ƙarama da kanta ta fito tana musu barka da zuwa dan ita tunda safe tana anan
asibiti batama san sunje duba Samraah É—in ba, ana gama case É—in human right ta baro gidan.
Cikin girmamawa ta gaida Baba prof.. ya amsa mata tare da mata bayanin maido Samraah da
sukai nan dan a cigaba da kulawa da ita duk da dai shi ba sunanta ya ambata ba ya dai ce
yarinyar dake jiyya. Amma kuma yanata tunanin a ina yasan fuskar yarinyar ne tun É—azun. Cike
da girmamawa Hajiya ƙarama ta amsa musu. Tare da musu jagora har cikin manyan ɗakunan
jiyyarsu na vip na ƙarshe a daraja. Kowa baiyi mamakin rashin biyosu da Maash yayi ba, dan
sai da Baba prof ya koma da kansa ya masa umarnin bari a shiga da ita kasancewar tare ya tafi
da nurses dake É—auke da gadon É—aukar mara lafiya. Amma mi, ammakinsu ma ko kallon inda
Nurses É—in suke baiyi ba yanzun ma ya sake É—aukarta camak yay cikin asibitin. Da kallo kawai
Baba prof ya bisa abubuwa da yawan gaske na masa kai-kawo. Dan a wannan gaɓar ya gama
sarewa da al'amarin jikan nasa. Sai ma yake wasiwasi anya kuwa shine ya aikata fyaÉ—en nan
kamar yanda Nafisa ta faɗa. Dan al'amarin akwai matuƙar ban al'ajabi a cikinsa da ma ban
tsoro.
   Acan daga ciki suma kansu kallonsa kawai suke kowa da abinda yake tattaunawa da
zuciyarsa musamman ma Hajiya ƙarama da bata ga abubuwan daya faru a farko ba sai wannan
ɗin. Dan baki ta hangame har sai da taji iska na kai mata har maƙoshi sannan ta iya haɗiyewa
da Æ™yar.........âœï¸
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARí ½í²–í ½í²¯í ½í²–ALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NEí ½í²ƒ_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu í ½í¸í ½í¹_**_Typingí ½í³²_*
*_í ½í°›TSUTSAR NAMA....!!í ½í°›_*
_(Itama nama ce)_
_ í ¾í´™í ¼í¿»_
_ _
_í µí±· _
......Baba prof da bai koma ciki ba Nurse É—in nan ya aika yace a sanarma su Paah su fito yana
jiransu. Babu jimawa kuwa sai gasu É—aya bayan É—aya. Hajiya Mammah da Mama Balki da
Hayatu sai shi uban gayyar kawai aka bari. Dan haka Baba prof ya sake aika Uncle Abdullahi
yace yay kiran Hajiya Mammah saboda sanin halinta shi kuma baya buƙatar jan wannan
maganar a waje shiyyasa ma da Maash É—in yace a bama yarinyar sallama bai tanka ba. Ya
kumace a kawota nan É—in ne tai jiyya dan yasan asirinsu zai kasance a rufe tunda dai Hajiya
Ƙarama ta gida ce. Rai a ɓace Hajiya Mammah ta fito. Dan itafa gaba ɗaya an ɓata mata
shirinta. Dan har magana ta gama da waccan likitar akan ta riƙe Samraah har sai nan da wasu
Æ´an kwanaki da za'a iya fahimtar da ciki ko babu. Idan akwai ta fallasa a gaban kowa, idan
kuma babu zata biya ko nawa ne aima Samraah dashensa sai kowa ya gama sani sannan ta
tafi plan na gaba da za'a zubar da cikin wajen zubarwar a kashe Samraah. Sai kuma gashi cikin
abinda bai wuce awa guda ba shegen yaron nan daya zame mata masifa da bala'i ya hanama
rayuwarta rawar gaban hantsi tun yana mitsitsinsa ya rushe komai. Suma waÉ—an nan Æ´an
human right É—in sai taci abu takazansu dan sun mata aiki ba'a yanda tace musu ba. Idan kuma
basuyi himmar ƙarasawa ba ALLAH sai sun biyata maƙudan kuɗinta...
   A ɓangaren Maash kuwa bai bar asibitin ba sai da aka gama yima Samraah dukan abinda ya
dace. Duba magungunanta da sake bincikata in and out. Sai dai kuma anan É—in ma dai doctor
ɗin data duba Samraah ɗin dan ba Hajiya ƙarama bace saboda ba faninta bane. Abinda ta fara
bincike da tambaya shine reping É—inta akayi ne?. Shiru Maash bai tanka ba, bai kuma da
alamar tankawar. Dan haka Mama Balki ta girgiza mata kai alamar a'a. Rasa abin cewa tayi,
dan dukkan alamu na jikin Samraah ya tabbatar da anje mata babu tausayi. Amma tunda ita
Mama Balki tace ba haka bane sai ta tambayi mijinta, acewarta tana son ganinsa taji dalilinsa
na nuna irin wannan rashin tausayi akan yarinya ƙarama. Kasa sake cewa komai Mama Balki
tayi, sai É—an satar kallon Maash É—in da take ta gefen ido. Shi kuma yay masifar haÉ—e girar sama
data ƙasa dan haka doctor ta haɗiye maganganunta a cikin rai dole.
    Ruwa tasa aka sakama Samraah dan tana buƙatarsa. Kasancewar akwai cannula ɗin
wancan asibitin da ba'a cire ba sai hakan ya sauƙaƙa musu. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa barcin
ya fara ɗaukarta dan shi dama suke buƙata tayin. Kiran wayar da Paah ya addabesa da shi ya
sashi miƙewa cikin ɗan ɓacin rai sai dai bai ce komai ba bai kuma ɗaga wayar ba. Ƙofa ya nufa
abinsa batare da yayima ko Mama Balki sallama ba.
   Dishi-dishi nake ɗan hangosa, cikin mayen barcin dake ɗaukata a hankali batare da tunanin
zai ma jini ba na furta, “Dan ALLAH ka dinga duba min Ummie akai-akai da bata abinci da
maganinta. Kace kuma ina gaishet....â€
  Cak ya tsaya daga yunƙurin fitar da yake yi, hannayensa duka a cikin aljihun wandon suit ɗin
nasa. Tamkar mai ciwon wuya ya juyo da kansa a hankali ya zuba su a kanta. Idanunta masu
cikar gashi dake a É—an kumbure har yanzu a lumshe suke. Kallon kusan minti É—aya yay mata ciff
kafin ya motsa a hankali cikin tafiyar nan tasa tamkar baya so ya fice. Da kallo Mama Balki ta
bisa, sai kuma ta saki murmushin da har haƙoranta suka bayyana. A hankali ta furta, “Humm
Alhaji Ƙaramiâ€. Sai kuma ta juya ta zubama Samraah da har ta fara sauke munshari idanun
nata. Shigowar Hayatu ne ya katseta. Sallama yay mata dan yasan ba lallai yau ya samu damar
sake shigowa asibitin ba tunda suna tare da boss. Gashi ma acan office jiransu ake sakamakon
meeting da yasa Juliet ta tara na gaba É—aya exco É—in companynsa na cikin Lagos dama wajen
Lagos masu alaƙa da abinda ya faru. Ya kuma tabbatar dole meeting ɗin zai jasu lokaci mai
tsayi....
 Â
Â Â Â Â í ¼í¼ºí ¼í¼ºí ¼í¼ºí ¼í¼ºí ¼í¼º
    “Magana ta gaskiya sai kun kula Attahir. Kun fa san Hajiya nada hawan jini. Yanzu badan
ALLAH ya taƙaita ba a wannan faɗuwar da tayi fa komai zai iya faruwa. Dan ɗayan biyu ne.
Paralysis ko heart attack. Saboda a kwanakin nan bincikenmu ya nuna zuciyarta na samun
matsi sosai da yawan damuwa. Dan haka dan ALLAH ku kula. Zamu riƙeta anan zuwa 2days,
ga wannan sai kaje konan pharmacy na asibiti ka samo dan data farka za'a buÆ™acesuâ€.
   Numfashi mai nauyi Attahir ya sauke tare da jinjina kansa. Kafin a hankali ya ɗaura da yima
doctor ɗin godiya sannan ya miƙe. Tafiya kawai yake amma shi baima san a inda yake jefa ƙafa
ba. Dan shi a karan kansa yana buƙatar gadon ne a wannan gaɓar. Da ƙyar ya iya kai kansa
pharmacy ɗin cikin asibitin ya miƙa musu takardar da doctor ɗin ya bashi kawai. Koda
pharmacist É—in ya duba ya sanar masa kuÉ—in baima bi takansa ba ya zaro ATM É—in sa a wallet
kawai ya miƙa masa. Hakama da aka saka adadin kuɗin bai wani dubaba ya amsa ya saka pin
É—insa. Ledar ya amsa ya koma É—akin da aka kwantar da Mamy.
  Har dare yay nisa babu Dad babu Mansoor. Babu kuma wanda ya kirashi koda sau ɗaya yaji
yaya Mamyn take. Haka ya kwana cikin asibitin shi kaÉ—ai, sai a washe gari bayan sallar asuba
yana fitowa a massalaci fita yay a asibitin dan likita ya tabbatar masa Mamy zata iya kai sha
ɗaya ma bata farka ba. Kai tsaye gidan ƙaninsa na ɓangaren Ummie ya nufa. Kakarsu mace ta
rasu, sai tsoho mai ran ƙarfe da ya ragema Ummie kawai. Bai tsaya kwana-kwana ba ya
zayyane masa komai dake faruwa. Sosai hankalin kakan nasa ya tashi, Attahiru na gabansa ya
shiga bugama sauran ƴaƴansa waya duk yace suzo yana buƙatar ganinsu. Cikin ƙanƙanin
lokaci kuwa duk sai gasu, ALLAH ya taimaka ma abin ya haÉ—a da weekend. Sake saka Attahir
yay ya maimaita duk abinda ya faɗa masa. Suma ransu yay matuƙar ɓaci da wannan hali na ƴar
uwarsu. Tun tana budurwa sunyi matuƙar yaƙi na ganin ta ajiye waɗan nan banzan halayen
amma a banza. Kullum shari'arta da miji bata wuce akan wannan halin na son kuɗi da ƙarya.
Gashi nan dai sai da takai ta watsa farin cikin gidanta da kai wa matsayar da suka dinga guje
mata sannan hankalinta ya kwanta. Itama autar tasu Sakeena zama da gurɓataccen miji ashe
ya canja musu ita ta koma irinta. ÆŠunguma sukai su duka harda tsoho zuwa asibiti suka dubata.
Sunko samu ta farka, haka duk suka jajanta mata sama-sama. Gaba É—aya kunya ta hanata iya
kallon kowa a cikinsu musamman ma Attahiru. Nauyin yaron take ji, dan yanada matuƙar haƙuri
da kawaici. Duk irin banbancin da take nunawa tsakaninsa da ɗan uwansa bai taɓa ɗauka ya
sakama ransa balle har taga ɓacin ran hakan akan koda fuskarsa ce. Yau ga wanda take
matuƙar nunama soyayyar ya tsallaketa ya wuce akan mace. Duk da dai tasan ita duk ta jawo
komai, sosai take jin dana sani da nadamar ƙwaɗayayyar rayuwarta a yau.
   Kwananta biyu a asibiti babu ko ƙyallin Dad. Tana son ta tambayi Attahir tana jin tsoron jin
abinda bashi zuciyarta take son ji ɗin ba. Dan tana matuƙar so da ƙaunar mijinta. Hasalima
kamanninsa da Mansoor ya É—ebo yasa take fifita soyayyarsa akan sauran yaranta. A ranar aka
basu sallama. Tun da suka baro asibiti taga an É—auki hanyar gidan babanta gabanta ke faman
faÉ—uwa. Sai dai tsoro ya hanata tambaya har suka iso. Isowarsu babu jimawa suma su Amal
suka iso. Dama suna Abuja gidan kawunsu ne. Sanda zasu wuce India su aka turasu can sai
yau suke dawowa.
   Anan ɗin ma babu wanda yace mata komai har tsawon kwan biyu, abu ya dameta amma
itama tsoron jin abinda bashi take son ji ba ya hanata iya tambaya. Zuwan Sakina biyu gidan
babu mai tankama wani ita da ita. Su duka sun É—auki zafi da juna tamkar ba Æ´an uwa ba jini
ɗaya. Hasalima a baya sun fi shiri da juna matuƙa, dan rayuwar ƴammatanci gaba ɗaya
Sakeenar a gidanta tayita ma..
   Attahir dai yakan zo da safe kullum kafin ya wuce aiki ya gaisheta. Hakama idan ya tashi sai
yazo nan ya gaisheta sannan yake wuce gida. Kamar wasa a haka kwanaki suka dinga tafiya
tana a gidansu. Ga baba ma sama-sama yake amsa mata gaisuwa. Baya shiga sabgarta baya
kuma bata damar shiga tashi har gata da watanni biyu cif a gida. Su Amal ma tuni suka tattara
kayansu suka gudu gida. Dan sunce bazasu iya zama gidan Baba ba saboda gidansu komai
najin daÉ—in rayuwa suna da shi. Nan ko duk da Æ´aÆ´an baban maza sun tsaya akan al'amuransa
shima kasancewar matarsa ba itace kakarsu ba abubuwa da yawa sai a hankali kawai. Ta
kankane komai daga ita sai nata jikokin Mamy ma sai tayi da gaske wataran take samun abinci
a gidan. Dan ma Attahir baya gajiya da kawo mata kayan shayi da ƴan kayan maƙulashe.
Amma itama da tuni yunwa ta kai rayuwarta Æ™asa kam.........âœï¸
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARí ½í²–í ½í²¯í ½í²–ALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NEí ½í²ƒ_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu í ½í¸í ½í¹_**_Typingí ½í³²_*
*_í ½í°›TSUTSAR NAMA....!!í ½í°›_*
_(Itama nama ce)_
_ í ¾í´™í ¼í¿»_
_ _
_í µí±· _
........Tun fitarsu a É—akin jiyyar yarinyar har barinsu asibitin akan idanunta ne. Numfashi ta sauke
mai nauyi tare da ture ɗan kwalin kanta baya. Dauriya kawai take da danne abinda ke matuƙar
cimata zuciya. Wayarta ta É—auka a É—an zafafe, tai Æ´an danne-danne tare da kaiwa kunnenta.
Ana É—agawa daga can ta É—an sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin É—an farin ciki mai gauraye da
sauran damuwa ta furta, “Sabon labariâ€.
   Cike da zumuÉ—i daga can akace mata “Name fa Hajjaju masu Lagos da kayan cikinta.â€
     “Hummm Jannifer bar batun wasa Please. Yarinyar nan ce fa suka maido asibitin nan
yanzuâ€.
   “What! Kina nufin Samraah?â€.
 “Yess. Yanzu haka tana nan tare damu. Ban san miya faru ba suka maidota nan ɗin. Naga dai
mutuniyarki a zafafe cikin matuƙar damuwa kuma. Yanzu kam na fara zargin akwai abinda take
Æ™ullawa. Na kuma yi alkawarin sai na bincikosa a koma ina taje ta bizne shiâ€.
    “Karki wani damu Hajjaju wannan duk mai sauƙi ne. Ko ni nan na isheta. Har mi akai akayi
Alaja Nafee kuma. Matar da bata iya komai ba sai da shawaran banzan Madan Rubayya É—in
nan. Ni dai kawai yanzu shawaran da zan baki kawai kiyi ƙoƙarin ki kula da yarinyar nan da
ƙyau, tunda dama tun farko kayanki ce. Kin zauna sakaci ne Alaja Nafee ta nema ƙwacewa.
Banzama irinta da ta ƙare a ƙarƙashin guzumomi irin su Rubayya. Dan bana raba ɗayan biyu
shakkar Rubayya É—inne ya hanata taya yarinyar kafin ke, tunda itama ai mayyar ce. Saboda
haka kiyi amfani da wannan damar akan ita yarinyar kiyita banka mata maganin da zai fidda
mata sha'awar namiji gaba É—aya a ranta, ina tabbatar miki da kanta zata kawo miki kanta tana
kukan ki mora albarkacin jikinta. Haba Alaja Lawusa kamar baku bane Lagos É—in. Ni fatana ma
idan zakije honeymoon da ita aje dani koda a Æ´ar riÆ™on handbag ceâ€.
   Dariya mai ƙayatarwa Hajiya ƙarama ta saki, tare da sake lume kanta a cikin kujera idanunta
a lumshe tana siffanta cikakkiyar surar Samraah data jima tana birkita mata lissafinta. Dan tun
randa Jannifer tayi kiranta ta sanar mata da zuwan yarinyar gidan matsayin gift da Mashi'a tai
shirin kawoma Hajiya Babba dan ta kula da ita ta gama jin ƙaguwa da son ganin yarinyar.
Saboda haka ta azalzali Paah suka dawo Nigeria washe gari badan ma sun kammala abinda ya
kaisu ba. Koda suka iso tai ido biyu da Samraah sai da numfashina ya nema shiÉ—ewa. Dan
yarinyar irinsu ne ake kira da full option. Komai yaji yanda ya kamata. Sai dai kash abubuwa da
dama sukai mata katanga da hakan, tayi ƙoƙarin riƙe kanta har zuwa sanda ta gama shiryawa
sai kuma ga wannan abin ya faru da yay matuƙar ƙona mata rai, dan a yanzu haka ita kaɗai
tasan irin kalar zafin yaron nan Awwab da take ji a rayuwarta. Wani irin kishi take ji tamkar ta
kashe banza a wuce wajen dan son Samraah take na gaske. Har ma ta gama yankema kanta
shawarar auran yarinyar zatayi ta ɗauketa daga Nigeria zuwa duk ƙasar da take so sai ta dinga
kai mata ziyara....
    “Alaja!â€.
  Jannifer ta katse mata tunani. Firgigit ta dawo hayyacinta tana mai sauke nannauyan
numfashi. Cike da basarwa taja ɗan sirrin tsaki da faɗin, “Sorry Jannifer na tafi wata sabgar ne
kuma.â€
   Dariya Jannifer ta ƙyalƙyale da shi daga can, cike da shaƙiyanci ta ce ko dai kin tafi tunanin
kayan alatu baâ€.
  Murmushi Hajiya Ƙarama tayi tana mai cije lips ɗinta. Kafin