Showing 6001 words to 9000 words out of 16862 words
Chapter 3 - Tsutsar Nama Book 3 Complete end by By Billyn Abdull.pdf
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARí ½í²–í ½í²¯í ½í²–ALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NEí ½í²ƒ_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu í ½í¸í ½í¹_**_Typingí ½í³²_*
*_í ½í°›TSUTSAR NAMA....!!í ½í°›_*
_(Itama nama ce)_
_ í ¾í´™í ¼í¿»_
_ _
_í µí±· _
_______
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaÉ—a ado da kwalliyar birgewa. Kar ku
bari ayi babu kuí ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_WhatsApp_*
https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG
https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5
____________
......A ɓangaren su Paah kuwa isowarsu kenan asibitin suma. Ba kuma su san da su Maash a
bayansu ba. Kai tsaye suka nufi cikin É—akin bisa rakkiyar Mama Balki da sukai kira a waya. A
tsorace cikin damuwa ta musu jagora dan bata san dami suka zo ba. Sai dai babu yanda zatayi
dole tabi umarninsu. Sauƙin ma taga akwai Baba prof a tare da su. Sun shigo Samraah na
zaune a kan gadon jingine da filo tana shan tea É—in da Mama Balki ta haÉ—a mata a hankali. Fes
take dan har tayi wanka saboda gashin ruwan zafi da Mama Balki tai mata bisa umarnin likitan.
A hankali ta É—ago ta kallesu.
    Sai da zucuyata ta motsa da ganin waɗanda banyi zato ba. Idanuna na maida na rissinar
ina ƙoƙarin haɗiye mamakina da ƴar tsorata. Sai da suka gama zama a inda Mama Balki ta
nuna musu sannan na gaishesu cikin muryata da sam bata fita saboda kukan da naci na kwana
da yinin jiya. Wasu sun amsa wasu basu amsa ba. Ni kuma sai banji damuwar komai ba tunda
nasan dama ba lallai duk su amsa É—in ba. Kasa cigaba da shan tea É—in nayi ban kuma É—ago na
kalla kowa ba a cikinsu, suma kuma babu wanda ya sake yin magana. Dai-dai nan aka É—an
sake knocking ƙofar. Mama Balki ta zabura domin buɗewa. Jin yanda take jaddada kalmar
sannunku da zuwa cikin jin daɗi ya sani ɗan ɗago idanuna na kalla ƙofar. Tamkar abin shiri sai
karaf suka faÉ—a a cikin nasa. Wani irin É—an jan nasan yayi yuuuu zai lumshe nai saurin fara
ɗauke nawa da maida kaina na duƙar. Sai kuma naji duk zaman yama gundireni, ga wani
bugawa da zuciyata keyi dan harga ALLAH ko ganinsa tsoronsa yake ƙara min, ni kaɗai nasan
kalar masifar dana gani a daren shekaran jiya hannun mutumin nan, dan haka ko matsoraciya
kika kirani a wannan gaɓar Bily ni bazan damu ba. Kofin tea ɗin na ajiye a side drawer ɗin
gadon na zame a hankali na kwanta tare da lumshe idanuna. Ƙasa-ƙasa na tsinkayi wata
muryar dattijo da kamar na taɓa jinta na masa magana. Banji amsar daya bashi ba kasancewar
shi dama idan zai yi magana sai in yaso kowa ya jisa ne. Ya ringa yinta acan ƙasan maƙoshi
kamar mai jin haushin mutane. Kaɗan nai ƙoƙarin buɗe idanuna dan ina son ganin mai muryar
nan sai naga ya nufo inda nake gadan-gadan. Sai da zuciyata ta sake harbawa. Babu shiri na
maida idanun nawa na lumshe. A bazata, matuƙar bazata naji alamun rankwafowar mutum da
mayataccen ƙamshin turarensa da saukar numfashinsa akan fuskata. Ai babu shiri na ware
idanuna. Shi É—in ne kuwa, gaba É—ayansa yamun rumfa hannayensa duka biyu ajiye a saman
gadon ta gefe da gefena. (Kambu! Anya mutumin nan nada kunya?) Na faÉ—a a zuciyata ina
waro gaba É—aya idanuna waje. Amma shi sai ya wani kaÉ—a min cat É—in nasa da É—age gira
hankali kwance. Tuni ƙwalla sun cika min ido, cikin marairaicewa na shiga motsa lips ɗina zanyi
magana. Sai kawai naji saukar yatsarsa a saman bakin nawa, idanunsa cikin nawa, cikin salon
lumshe idanu da maida muryarsa low sosai ya ce, “Shiii!! Bana son surutuâ€.
   Kunya takaici suka lulluɓeni a lokaci ɗaya. Gefe na kauda kaina tare da ture yatsansa daga
saman lips É—ina, dan kalmar baya son surutun faifan taswirar daren shekaran jiya ta dawo min
da shi fes. Hannun ya saka ya taro fuskar tawa ya maidota inda take. Baki na tura masa, ina
son na hararesa amma shakkarsa da kwarjininsa sunyi masifar min É—aurin goro, ga mayataccen
ƙamshinsa dake tsarga min zuciya.
    “Bakin nan yana buƙatar wani abu ne halan?†ya faɗa cikin soft voice yana ƙoƙarin maida
yatsarsa a saman lips É—in nawa. Hannu na na kai da sauri na rufe bakin ina zaro idanu, amma
shi ko gezau zama ka iya rantsewa ba shine ke maganar ba. Hankalina sake tashi yayi na saci
kallon inda Æ´an gidansu suke. Duk suna nan a É—akin har Mama Balki ma. Tamkar zan fasa ihu
idanuna cike da Æ™walla na ce, “Duk suna kallonmu faâ€.
    Ƙoƙarin juyawa yay zai kallesu, ai bamma san na kai hannuna ba da sauri kan fuskar tasa
na dawo da shi.
  “What? kuma. Bakin ce na faÉ—a musu ne su fita kina son mijinki ya É—anyi kissing É—inki baâ€. Ya
faɗa cikin salon kashe ido da ɗan ɗage gira sama murya can ƙasa kamar mai raɗa yana ɗora
hannunsa kan nawa da nake ƙoƙarin janyewa daga fuskar sa.
      Harararsa na ɗan yi hawaye na cika min ido na ce, “ALLAH ya kiyaye ni yaushe na ce
hakan? Kuma ni ba Æ´ar iska baceâ€.
   “Oh reallyâ€. Ya faÉ—a cikin É—age gira sama yana É—an taÉ“e baki kaÉ—an da sake matso da
fuskarsa daf da tawan. Wani irin bugawa zuciyata ta shiga yi da sauri-sauri tamkar zata faso
ƙirjina ta fito. A hankali na fara jin saukar iska da ƙamshin mouth freshener mai ƙamshin
strawbarry. Luff nayi zuciyata na sauka a hankali daga bugawar da take da motse-motse a cikin
ƙirjina, harda tura baki batare dana sani ba.
    Ɗal ya É—alle lips É—in da yatsunsa murya can Æ™asa ya furta “I'm not interested maida bakinâ€.
  Cikin sauri na buɗe idanuna wani irin tuƙuƙi na turnuƙe min zuciya da takaicinsa. Dai-dai nan
yake ɗagawa da ga duƙowan yana wani yin fuuuu da idanun nasa. Jinai kawai hawayen da
nake riƙewa sun wani irin silalowa a hankali...
    Maash kam da ya ɗago kallo ɗaya yayma kowa na ɗakin ya ɗauke kansa tamkar baiga irin
kallon da duk suke masa ba na tsantsar mamaki da tu'ajjibi. A zafafe Hajiya Mammah ta
yunƙura zatayi magana Baba prof ya girgiza mata kai alamar kar tace komai ba. Badan taso ba
tai shiru, sai dai kallo É—aya zaka mata ka fahimci yanda ta gama cika tai famm. Duk abinda ke
faruwa hankalinsa na kansu ta wutsiyar ido, amma yay tamkar hankalin nasa akan file É—inta
daya É—auka yake dubawa. Dai-dai nan likitar da ke dubata ta shigo É—akin Nurse biye da ita. Ita
ta fara gaishesu, dan duk inda akaga Family É—insu ana gurmamasu saboda Maash É—in.
    Sai da suka gama gaisawar sannan shi da bai ko kalleta ba ya ɗago shanyayun cat
idanunsa ya É—an kalleta, sai kuma ya kauda kansa cikin dakewar nan tasa ya mika mata
takardar daya zare jiya a cikin file ɗin ya miƙa mata. Amsa tayi cikin mamaki, sai kuma ta kalla
takardar. Ɗagowa tai cikin rashin damuwa, sai ma gani da take ai tayi abin arziƙi dan haka baki
a washe ta ce, “Sir komai da ya kamata mun rubuta kamar yanda binciken mu ya bamu akan
fyaɗen, dan a yanzu haka ma muna muku albishir ɗin samar da ƙwararriyar lawyer da zata
tsaya mata akan case É—in. Yau kuma zan kai report É—in ma police dama izininku kawai nake jira
kasancewar ita Hajiya tace ba huruminta bane sai kai yayanta kazo. Amma gaskiya sir ina ƙara
bada shawaran kowa ya aikata irin wannan zalincin ga baiwar ALLAHr nan shima ya É—anÉ—ana
kuɗarsa. Dan ALLAH ne kawai ya taƙaita al'amarin da zata ma iya kamuwa da matsalar yoyon
fitsari. A yanzu haka ma dole tana buƙatar kulawa sosai saboda ɗinkin dake jikinta abin sam
babu daɗi, dan ban taɓa ganin case ɗin fyaɗe na tsagwaron zalunci irin wannan ba. Banama jin
mutum É—aya ne ya aikata abi.....â€
     “Ina buÆ™atar sallama by nowâ€.
  Ya faɗa cikin katseta da yanayin da kowa ya kasa fassarawa daga garesa. Sororo likitar tayi
tana kallonsa. Sai kuma ta ɗan marairaice fuska cikin nuna damuwa ta ce, “Sir ko akwai wani
kuskure da mukayi ne anan ɗin? Wlhy duk kulawar da kake buƙata muna kan bata ita yanda ta
kamata. Yanzu fa nake maka bayanin har lawyer Æ™wararriya mun samar akan case É—inâ€.     Komai baice ba, sai ma É—auke kansa da yay cikin nuna Æ™osawa da maganar tata. Da yaga
bata da alamar fahimtar shirun yake buƙata sai kawai ya nufi gadon da Samraah take cikin
takun ƙasaita da bajinta hannayensa duka zube a aljihu. Duk abinda ke faruwa ina jinsu, dan
haka zuciyata ke wani irin gudu raina fal mamakinsa. Guy É—in nan he is stubborn mutum wlhy.
Rayuwarsa har mamaki take matuƙar bani, mutum kamar wani dutsi baka taɓa iya gane
gabansa da bayansa. Cak É—in da aka É—agani ya dawo dani hayyacina, sosai na zazzaro
idanuna waje cikin matuƙar mamaki da ruɗani, rawa lips ɗina suka kamayi. Da ƙyar na iya haɗa
kalmar, “Mi...miye haka kake yi?â€.
   Ko kallona bai yi ba, sai ma takawa daya fara a hankali babu wani alamar jin shi yayi ba
dai-dai ba ya bi ta tsakkiyarsu ya fice. Nikam ai sai naji bazan iya jurewa ba kawai na cusa
kaina cikin ƙirjinsa tare da saƙalo duka hannayena ta wuyansa na saki kukan da ban san dalilin
yinsa ba........âœï¸
_Ehem ehem Yayanmu ikon ALLAH, na Samraah bada kanka a sare kace ma su baba prof
ya faÉ—ií ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£_
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan
wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYARí ½í²–í ½í²¯í ½í²–ALLAH YA KARA ARZIKI...
ZAFAFA BIYAR NAKU NEí ½í²ƒ_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu í ½í¸í ½í¹_*
*_í ½í°›TSUTSAR NAMA....!!í ½í°›_*
_(Itama nama ce)_
_ í ¾í´™í ¼í¿»_
_ _
_í µí±· _
.......Da sauri Hayatu dake tsaye daga bakin ƙofa yaja da baya kansa a ƙasa yana ƙoƙarin
ƙumshe dariyar dake neman kufce masa. Isowarsa dai-dai saitinsa ya sashi haɗiye dariyar da
ƙyar ya buɗe masa ƙofar da sauri yana ƙoƙarin matsawa.
   “Kuzo da kayanâ€.
Ya faÉ—a a hankali dai-dai yana ficewa gaba É—aya daga É—akin.
     “A lallai Mu'azz ka haifoma kanka jaraba wlhy.â€
  Hajiya Mammah ta faɗa cikin tafa hannaye da riƙe haɓa. Babu wanda ya iya cewa da ita
komai dan duk abin faÉ—ar ya gudu musu a bakuna. Sai ma Baba prof ne daya motsa a hankali
kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki yabi bayansa. Dole duk suma sauran duk suka motsa
suka take masa baya. Sai da suka gama fita Hayatu ya ƙarasa gaban doctor ɗin. Kallon Mama
Balki yay yayi murmushi. Itama sai ta murmusa tare da nufar kayayyakin su kawai ta shiga
haɗawa. Doctor data gama shiga cikin ɓacin rai kallon Hayatu tayi zatai magana. Da sauri ya
katseta da faɗin, “Doctor kiyi haƙuri kawai ki bada takardar sallamar nan. Dan wlhy boss da kike
gani baya magana biyu. Tunda ya yanke hukunci ya yanku, ya kuma fiki sanin muhimmancin
wannan patient É—in takiâ€.
   Cikin ɗan ɓacin rai ta ce, “Wane muhimmancin ta ya sani anan?. Ana gaya masa haɗarin da
yarinya ke a ciki saboda zaluncin da akai mata yana nuna kamar ma baya fahimta. Ni ban taɓa
sanin guy É—in nan stubborn bane sai yau. Idan ma É—akin ne bai masa ba way not yay magana
sai a canja mata da waniâ€.   Murmushi kawai Hayatu yayi dan ya fahimci bafa zata fahimta ba. Itama sai ta fita rai a É“ace
tana mita dan gani gake shima Hayatun neman raina mata hankali yake yi. Binta kuwa yayi
bayan ya amshi kayan da Mama Balki ta haÉ—a suka fito tare. Yana zuwa office É—in doctor ta
miƙo masa takardar sallamar a harzuƙe. Komai baice mata ba ya ɗauka ya juya abinsa ya fito.
     Samunsu yay suna shiga mota, dan shi gogan nasa ma har ya shige abinsa. Gaba ya
buɗe ma mama Balki ta gefen sa ta zauna, shima yana ƙoƙarin shiga Baba prof ya ƙaraso
wajen, umarni ya bama Mama Bilki kan ta fito ta koma motarsa, shi kuma ya shiga gaban ya
zauna yana bama Hayatu umarnin suje *_KARAMCI HOSPITAL_* asibitin Hajiya ƙarama
kenan. Amsawa Hayatu yay yana satar kallon Maash dake a baya tare da Samraah ta cikin
mirror. Jingine kansa yake da kujera idanunsa a lumshe tamkar bai san mike faruwa ba. Shi
kuma ya tabbatar duk yana jinsu. Kallo É—aya yay ma Samraah dake kwance kanta a saman
cinyar Maash ɗin itama idanunta a rufe ya ɗauke kansa yana ɗan sauke ɓoyayyar ajiyar
zuciya......
Â Â Â Â í ¼í¼¿â¤ï¸â€í ½í´¥í ¼í¼¿â¤ï¸â€í ½í´¥í ¼í¼¿
   Hajiya Sakeena na kai ƙarshen bayaninta Mansoor ya fasa wata gigitacciyar ƙara da ɗaga
Centre table ɗin gabansu ya wancakalar. Babu wanda bai firgita ba. Ƙafa yasa ya bugi table ɗin
da masifar ƙarfi, badan takalmin dake a ƙafarsa ba babu abinda zai hanashi jin ciwo. Da sauri
Attahir ya miƙe yana ƙoƙarin riƙo hannunsa da kiran sunansa. Amma sai shima yay wani irin
wancakalar da shi gefe har sai da Attahir ɗin ya zube a kujera. Cikin zafin zuciya da basu taɓa
sanin yana da ita ba ya nuna Hajiya Sakeena da Mamynsa da take wani irin kuka tamkar ranta
zai fita. Cikin kaushin murya da rufewar idon da fushi ya haifar masa ya ce, “Na tsane ku. Ku
biyun nan ba bana son sake ganinku a rayuwata har abada. Kuma yanda kuka zama sanadin
rabani da ita kuma na barku har abada!!!!!!â€.
   Daga haka ya figi bag ɗinsa fuuuu zai fice. Ƙoƙarin miƙewa Attahir yay cikin ƙarfin hali yana
kiran sunansa. Yayinda Mamy tai wani irin fashewa da kuka ta bisa da gudu ta riƙo rigarsa. Ko
juyowa ma baiyi ba yasa hannu ya kaɓe natan tare da hankiɗata yay ficewarsa. Kafin ta miƙe
tabi bayansa tuni yama fice a gidan ko mai kama da shi babu a compaund. Nan É—in ma fita
Attahir yay a guje, sai dai yana fitowa napep ɗin data ɗauki Mansoor na barin ƙofar gidan.
Komawa yay cikin gida da gudu bawan ALLAH duk ya ruÉ—e. Dan key É—in mota yake lalube
amma ya gagara ganin ko guda É—aya. Haka ya sake fitowa da gudu ya fita shima ya tare napep
ya shiga suka bi bayan Mansoor. Amma ko mai kama da shi basu gani ba. Har airport yasa
suka bishi a tunaninsa can zaiyi. Sai dai nan É—in ma babu alamar Mansoor É—in. Abinda bai sani
ba kuma Mansoor bai je airport ba, dan ya fahimci abu na farko da zasu farayi kenan dan haka
yaje ya kama hotel anan anguwarsu da yasan bazasu taɓa tunanin zai tsaya anan ba. Na
kwana ɗaya ya kama, dan daga yau zuwa gobe yake son sake barin ƙasar nan. Sam bazai iya
zama ba. Gara yayi nesa nesa can inda bazai sake ganin kowa ba a cikinsu har ƙarshen
rayuwarsa...
   Duk wannan budiri da ake Dad bai ko motsa ba. Yana zaune ne kawai kamar saƙago a
falon. Ba haka Hajiya Sakeena taso ba. Taso ace tana gama bada labarin nan yanda Mansoor
ya fusata shima Dad ya fusata ya dinga É—irkar Mamy da jera mata kalmomin saki uku sannan
yace ta bar masa gida. Amma ba komai, ko yanzu ma ai tasan ƙurar bawai ta ƙare bane ba.
Dan ita shaidace akan zuciyar Dad tamkar akku kuturu yake. Kusan zuciyar tasa ce ma yau
Mansoor ya kwatanta. Shi kansa shirun da yayi ta tabbatar zuciyar ce ta kume Æ´an maza
wayaga kutu-ban-ban. Haka ta fito babu tausayi babu imani ta tsallake Mom da nunfashi ke
neman ƙwacewa tai ficewarta. Acewarta ai itama haka Mansoor ya tsallake tata ɗiyar ɗaya
kwallin kwal a duniya ya tafi babu tausayi balle imani bayan ya gama zana mata kalaman saki
uku da gasa mata magana iya son ransa...
   Duk neman daya dace Attahir yayi ma Mansoor amma bai gansa ba. Dole ya haƙura cikin
maÉ—aukakin tashin hankali ya koma gida ransa duk a dagule. Yana zuwa kuma ya iske Mamy a
sume a farkon shiga falo. Tashi hankalinsa ya sake yi, dan ga Dad zaune tamkar saƙagon gunki
zuciya ya kumesa tamkar shima É—in ya suma. Baima san ya sunkuci Mamy yay waje ba cikin
tashin hankali yana kwala kiran sunan drivernsu.....