Showing 15001 words to 18000 words out of 18444 words

Chapter 6 - RAINA KAMA KAGA GAYYA True Hausa Book Na Marubuciya billyn Abdul .pdf

da dai 'yan gidanmu suna mana d'agawar sun
fimu komai, saboda danginsu masu kud'ine, suna ganin kayansu sunfi namu tsada. hakan
baita6a damunmu ba, dan aganina duk sutura sunanta sutura, yawan kud'in nawani bai d'ad'ani
da k'asaba, to barema Munubiya da babu ruwanta.
Ana cikin haka muka shiga goman k'arshe Na azumi (goma ta d'okin sallah�😂).
Ranar wata weekend yayyanmu maza suka kwashemu domin za6o takalma da sauran
tarkace Na kwalliya, dama duk ankai yaran suma kowa ya za6o, mu matasan 'yan matan muka
rage dakuma yayyenmu su Aunty khaleesa.
Plaza ce babba mai k'yau da burgewa, kayansu Na manyane, amma yayyenmu dayake
sunaso mufito suka kaimu can, sa6anin da da ake kaimu kasuwa kamar sauran yaran, su aunty
khaleesa ne kawai ake kawowa nan saboda sune manyan 'yan mata, to yanzu muma mun
shigo layi💃🏻. Sosai muka rikice da tsarin wajen, takalmane 'yan waje wad'anda duk inda kayi taku sai an
kalleka ansan kagama Isa. Harda bags, kayan makeup, turarurruka da dogayen ruguna irinsu
Arabia's gowns, gyalilla da kayan 'yan kunne, kananun Maya Na garari Na mata da maza, kai
inaga babu abinda zakazo Baja sameshi awannan PLAZA d'inba kamâ€. Lallai an narka dukiya a wannan waje, ko plazan wanene? oho. munga dai sunan plaza d'in
*BIRNIN GAYU!!*
“Lallai kuwa taci sunanta birnin gayuâ€. ‘ cewar Anty Ramlah’.
Haleematu tace, “wlhy wannan ace plaza d'in mijinace to bazan maimaita kaya sau uku ba,
hakama waya duk wata za a dinga canjaminâ€.
Dariya tabamu, dan haka muka shiga darawa kuwa. kowa yad'auki abunda yakeso
gwargwadon iko, yayyanmu suka biya da kud'in dasu Abba suka basu, sannan suka cika mana

danasu kud'in, kowa yafito cikin farin ciki muna jera musu godiya, mun d'auki picture's sosai
awajen kuwa. muna tafiya a mota nake cewa yaa Anas dan ALLAH wai Plaza d'in waye
wannan?â€.
“ai plaza d'in ta babban kwaroce k'anwata, plaza d'in *GALADIMA* ceâ€.
shiru nai kamar banjishiba, danjin sunan wanda ya ambata, inada tabbacin kuma wannan
mai girman kan tsiyar yake nufi kenan, yayinda 'yan uwana suka rud'e da firar galadiman.
d'an tsaki naja nace, “ashema Na mai shegen girman kai d'innan neâ€.
Kusan atare sukace ke a ina kika sanshi? dahar kikasan yanada girman kaiâ€.
Shiru namusu, sai Munubiya ce tashiga basu labarinsa da had'uwar damukayi a asibiti da
shi, aikam duk sai sukabi suka rikice, harda masu fatan yazame musu mijin aure.
bansan miyasa duk hirar tasu ta k'untataniba, tabani haushi, saina maida hankalina ga
kallace-kallacen jama'ar daketa kai kawo akan titi.
Har mukaje gida suna hirar Galadima sudasu yaa hameed dake basu labarin halayen kirki Na
Galadima d'in, wai kuma bashida girman kai kamar yanda Na fad'a, kawai dai dan ban
fahimcesa bane nima.
Nidai jinsu kawai nakeyi, amma badan Na yarda baida girman kai ba, tunda da idona
Nagani ba labari aka baniba.�ehe


Innarmu tayi mamakin wad'annan kanya, dan haka takasa hak'uri, har 6angaren samarin
gidanmu taje tamusu godiya da fad'an d'awainiyar tayi yawa ai, ga hidimar biki Na tunkarosu.
Sunji dad'i sosai akan hakan da innarmu tayi, koba dad'i kowa yayi aikairi yanaso anuna
jindad'i kuma amasa godiya.
Sukace tayi hak'uri, ai k'annensu ne, idan basu mana ba wazai mana, da samari suzo suna
mana hidima su lalata mana rayuwa ai garasu sumana su kare mutuncinmu.
Sosai innarmu ma taji dad'in furicinsu, dan hakan ya nuna cewa su basu d'auki halayen
iyayensu mataba Na raba d'aya biyu.

Salla nata gabatomu, yayinda aka fara 'yan kimtse-kimtse Na shirin bikin sallar, masallatai
nata rufe tafseer, hakama gidajen redio dana talabijin..............âœí ¼í¿¼

*Kusaka yayan mahaifiyata a addu'arku, ALLAH yamasa rasuwa ranar alhamisí ½í¸­í ½í±í ¼í¿», ALLAH ya
gafarta masa, ya raya abinda yabari.*


_Bansan makaranta Raina kama.... kunada yawa hakaba wlhy, nazata ki rabin group bazaku
kaiba🙆🏻, gashi yacika wasu basu sami wajeba kuma._



Na gaisheku k'yauta, ina fatan duk kuna cikin k'oshin lafiya kuda iyalankuí ¾í´í ¼í¿»�?.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*.í ½í±í ¼í¿»í ½í¸­
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing📲_*



*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_

*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_

👉🏻7⃣

.......Yau ake saka ran ganin wata, dan haka kowane gida zaka iya jiyo kamshin miya dana
nama, harma da kayan snacks.
Muma agidanmu kusan hakanne ta kasance, dan kowanne 6angare sunata hidimarsu, yau
ko bud'a baki bakowa yasamu zaman yinsa ba.
Muma muna namu 6angare muna taya innarmu ayyukanta, dayake kowa yana miyarsane,
da safe ahad'u ayi tuwo da masa da shinkafa, haka muke had'a kalolin abinci iri-iri saboda
yawan jama'a da gidanmu kan tara a ranar salla, abokan yayunmu maza, abokan su abbanmu
dawasu dangin iyayenmu mata. Har wajen 10 munata aiki, sai kuma a lokacinne mukaji ana sanar da ganin wata.
Nannafa yara suka shiga murna gobe salla, Muma kanmu manyan murnar mukeyi. badan
mun kammala aikiba muka kwanta.

Washe gari tun kiran sallar farko aka tadamu muka fara aiki, sai wajen 7am muka samu
kanmu, a gurguje muka fara wanka da shirin tafiya idi, duk shekara dama 'yan gidanmu a
masallacin da sarki yake salla muma mukeyi.
A gurguje duk mukaita fitowa saboda horn da yayyenmu suketa mana, yara an d'urasu a
school bos d'insu Na makaranta, yayinda mukuma muka rarrabu a motar yayinmu datasu Abba
dasuka bayar, tunda bakowa keda motarna acikin yayyen namu.
Dagani har Munubiya cikin shigarmu muke iri d'aya tamkar yanda muka saba a koda yaushe,
dai-dai da kwalliyama iri d'ayace a fuskarmu, komai namu mukayishi iri d'ayane, wannan yasaka
ake gaza banbancemu akoda yaushe.

Mun Isa filin idi, inda muka taddashi dank'am da jama'a maza da mata, wasu harda iyalansu,
kamar yanda muma muka taho baki d'aya harsu innarmu, mu mata muna 6angaren mata,
yayinda mazan sukayi nasu 6angare.
Khud'ubar da aka gabatar tazamo mana mai ratsa jiki da 6argo, Malam yayita cikin
tsantsar larabci, yayinda wani malamin ya fassara acikin harshen Hausa, saboda marasa jin
larabcin irinsu o e🙊.
Daga nan aka gudanar da sallar idi kamar yanda addini ya koyar.

Had'a kan yaran muka shigayi gudin karsuyi wani waje, sai dai hakan bata samuba, dan
annemi Kamal da Haneep an rasa, nannafa muka shiga bulayin nemansu, duk mun rikice, gashi
baba k'arami da Abbah sai fad'a suke wai sakacinmu ne.
Tamkar zan kifa haka nake tafiya da sassarfa ina kalle-kalle. ban ankaraba naji naci karo da
Abu, tunkan inkai idona kansa k'amshin turarensa yabigi hancina. da sauri na ware manyan
idanuna bisa kamilalliyar fuskarsa dake d'aure babu alamar yasan miyema dariya, janye idona
nayi cikin fargaba da fad'awa kogin tunani, inban mantaba irin wannan k'amshin naji a asibiti
wajen Wanda aka kira galadima a wacan ranar da feena batada lafiya.
Cikin yanayin tantama Na maida idona nad'an saci kallonsa...
Tsaye yake kyam tamkar dutshin da aka dasa waje d'aya, idonsa akan wayarsa dake k'asa a
tarwatse, Wanda inada tabbacin karon damukacine yasaka wayar fad'uwa.
A rikice nace “ya Salam†tareda duk'usawa nafara harhad'a wayar.
A hankali ya durk'usa kamar yanda nima nayi, ya d'ora hannunsa akan wayar dana ke
k'ok'arin sakama battery ya zareta daga cikin hannuna. bugun zuciyata yak'aru saboda tsoro
gashi yak'i cewa uffan, nasan nice da laifi, kafin Na ankara ya sake d'oramin wayar bisa
hannuna yamik'e yabar wajen. Sororo nabisa da kallon mamaki da al'ajabi, sanye yake cikin farar shadda k'al, wando da
riga harda malun-malun, ya murza hularnan da ake kira Minister bak'a a kansa, takalminsa da
agogonsa duk bak'ak'e, duk da bawani k'are masa kallo nayiba fuska da fuska nasan tabbas
yayi k'yau, kayan sun maidashi wani babban mutum. Ajiyar zuciya Na sauke saboda ya 6acema
ganina, nabi wayar daya barni da ita a hannu da kallo, tomi yake nufi da hakan?.
Banida mai bani amsa, dan haka nacigaba da had'a wayar, sai alokacin Na lura da sim card
d'insa dake kan wayar yacire d'azun lokacin daya kar6a kenan.Jujjuya wayar nashigayi cikin
tafin hannuna, wayace mai azabar k'yau ga k'amshin turarensa ya manne jikin wayar tamkar
itama ana fesa matane. 'Yar tsagewane tayi kad'an daga gefe, amma daga hakan ni banga
wata matsalaba, kenan yana nufin koyaya waya ta tsage a hannunsa tatashi aiki a garesa?.
Nanma babu mai bani amsata. Cikin mak'oshi Na furta to wanene wannan d'in shikuma?â€.

“Galadima!â€. ‘naji wata murya tafad'a abayana’.

Cikin hanzari najuyon dan inga mai bani amsar tawa. wayam naga babu kowa, sai alamar
gittawar mutum mai jajayen kaya.
Goshina Na dafe inamai runtse idanuna, cikeda mamaki nace, “kenan shine wanda yabama
feena jini? Galadima!â€.
Nafad'a cikin bud'e idanuna inabin inda yabi da kallo tamkar zan sake ganinsa, a hankali
nakuma furta _“Galadima!â€_.

“galadima kuma?â€.
Najiyo muryar Safara'u a bayana, da sauri a cusa wayar cikin hijjabina Na mik'e, kallonta
nayi cikin basarwa nace, “ya angansu neâ€.
Tace “eh mana an gansu tun d'azun, saikuma aka koma nemanki, miya faru naji kina kiran
sunan galadima?â€.
d'an guntun tsaki naja “naji wasu 'yan matane suna fad'in wai INA zasuga Galadima, tunda
ance yazo sallar idi. shine nikuma nake maimaita sunan Galadiman saboda takaicinsuâ€.

Dariya Safara'u tayi, ke 'Yar uwa karkiga laifinsu wlhy, koni zan sameshi saina bar Sadeeq
wlhy, yanzu fa Nima ake nunaminshi, dama haka yahad'u? Wayyo ALLAH yau naga tsantsar
gwanzartakar sarauta ajikin bawan ALLAH nan, tafiyarsama kawai abin kalloce, inaga kuma
yayi magana?, kai ALLAH yakai damo ga harawa...... kedai kawai........ Baki kawai Na ta6e, batareda nagamajin k'arshen zancen nataba nayi gaba abuna da
mamakinta a raina, wai zata iya Barin sadeeq?, saikace ba'akan sadeeq d'in bane akaso cin
zarafina da innarmu, amma yanzu saboda taga Wanda ya fishi bakinta yake furta haka.
Da gudu Safara'u tabiyoni. Kusan a tare muka k'arasa Inda motarmu ta tsaya, yaa hameed
yafara zagina akan INA kuma naje Na tsaya?, hak'uri nabashi muka Shiga mota kawai, dan
nasan shima d'in masifafene kamar su abbanmu.
Amotar ana fira amma ni tunanina yanakan had'uwarmu da Galadima ta yau, ga mamakin
wayarsa daya bari yatafi a hannuna batareda yace min uffanba, kai wannan Bawa yanaji da
k'asaita da mulki.
Har muka Isa gida bakina bai iya furta komaiba acikin hirar tasu. Mun tatar su innarmu ma
harsun huta su, yara kan summa fara cin abinci.
Ban zauna faloba kamar yanda munubiya tayi, saina zarce bedroom d'inmu Na 6oye wayar
sannan nacire hijjab d'ina nashiga bathroom Na wanke hannuna gudun kar wani yaji k'amshin
turaren saina dawo falon.
Tuni gidanmu ya kacame da hayaniya, munubiya tazubo mana masa da fankasu zamu
faraci Ayusher da Feena suka shigo da gudu, juna muka rungume muna murnar ganinsu, Yaa
Fadeel & yaa Marwan suma suka shigo, sai mama Rabi'a dake take musu baya tana rik'e da
hannun Ahmad. Nan muma muka kacame da farin cikin ganin 'yan uwanmu wad'anda bamuda kamarsu,
innarmu ta baje mana abinci da kayayyaki da dama dansu duk ta tanadesu, sai makwafta
dasuke gaisawar arzik'i suma duk tabada ankakkai musu.
Bamusan hidimar da kowa keyi anasa 6angarenba, mudai namu muka sani.
Ayusher takawo bakinta saitin kunnena, ahankali ta rad'amin sweet sis.... Wlhy k'amshin
turaren Galadima kikeyi, kinsan har abada bazan mance k'amshi nan baâ€.
Cikin dakiya Na d'ago kai Na kalleta tareda balla mata harara, “Ayusher wlhy ki kiyayeni,
a'a k'amshin turaren sarki kikaji bana Galadima ba k'arewaâ€.
dariya ta sanya harda rik'e ciki, nikuma Na tashi Na canja waje ina mamakin Ayusher mai
gani har hanji, duk dawanke hannuna danayi sosai amma ace wai har yanzun anajin k'amshin
turaren?, kai shikam wannan dawane mayen turare yake aiki haka?â€.
Wajen 12 muka fito domin zuwa kallon sarki dazai wice yima governor barka da salla.A
wannan karan tafiyarmu daban data 'yan gidanmu, dan mafi yawancinsu duk sun fice gidajen
kakanninsu, tacan masu ra'ayin zuwan suma zasuje.
Mukuwa mudasu yaa marwan muka tafi.
Acikin gari duk inda ka kalla jama'a ne keta kai kawo, musamman yara da 'yanmata da
samari, kowa yaci kwalliya ta kece raini da garari (yo dama ai ance ba'a za6ar budurwa ran
salla, saboda duk k'azantar mutum ranar saika sameshi cikin tsafta da gayu😂).
Dukda akwai rana hakan bai hanamu jeruwaba domin kallon wucewar mai martaba
sarkinmu da jama'arsa.
Masu busa algaita da kid'an taushine suka fara wucewa, sai kuma ga tawagar sarki Na
biye.

tawagar saiki Na wucewa sai ta Galadima, kamar yanda mukaji wasu gungun samari Na
fad'ar cewa ga Galadima nan.
Kowa yasan dama tsarin haka yake, daga sarki sai shi.
'Daga idanuna nayin donson sake ganinsa a karo na biyu. yanzu kam ya canja shigarsa
zuwa milk coulor d'in janfa da wando Na lallausan yadi, Wanda aka k'awatashi da d'inkin surfani
Na ainahin gidan masu sarauta, ya d'ora Brown Na alk'yabba mai kwalliyar Milk Color, hakama
rawaninsa daya zagaye fuskarsa ya kasance milk ne, takalmansa heir cover masu lankwasa
daga gaba irinna sarauta, sukuma Brown. yanzun kam fuskarsa d'auke take da k'asaitaccen
murmushi mai kama da anmasa dole, hannunsa d'aya dayake d'agama mutane yana d'aureda
farin agogon azurfa, sai zabba biyu a yatsunsa Na tsakkiya Wanda nake k'yautata zaton
azurfane suma.
Nanfa su Ayusher suka fara d'aukarsa hotonsa a wayoyinsu.
Tsaki naja ina hararsu, “mtsoww wahalallu kawai, dama kanku kuka d'auka yafi Ku k'are
wajen d'ura hotunan Wanda baisanma da zamankuba a wayarkuâ€.
Kafin cikin su Ayusher wata tabani amsa, wasu 'yan mata dake kusadamu d'aya ta kar6e da
fad'in “k 'yan mata kama kanki, kodai kema son nasa ne yakaiki ga kishinsa?â€.
Wata wawuyar harara Na buga mata, “kekuma shasha waya sako bakinki?, kajimin
ballagaza kawai, uwarmiye abin so a jikinsa dahar ya isa ayi kishinsa? Ke dai dabakisan inda ke
miki k'aik'ayiba ita dakon wahala, dan nakula ke amatanma suffar mata maza ALLAH yayiki....â€
Gaba d'aya suka taso min da masifa tamkar zasu cinyeni d'anya itada k'awayenta..
Yaa marwan dake zaune saman mota a bayanmu duk yana saurarenmu yad'ago kai ya
kalleni, yasan tabas Munaya ce, baya buk'atar k'arin bayani kuma ko tambayar wacece ita,
tunda Na nuna halin nawa, yace, “K munaya zoki shige motaâ€.
Nasan halinsa sarai baya wasa damu, cikin tunzura baki gaba nazo nashige motar Na
zauna, amma saina bar k'ofar abud'e k'afafuna awaje, banida buk'atar cigaba da kallon kuma,
dan haka nabud'e data nashiga chart kawai ina cika ina batsewa masifa nacin raina, gashi
kuma an hanani amayar da'ita,. sai antayama yaa Marwan harara nakeyi ta gefen ido baima
San inayiba, gaba d'ayama sainaji dama banzo kallon hawanba.

Koda muka bar nan ba gida muka komaba, yawo yaa Marwan yaytayi damu gidajen dangin
babansu, bamune muka dawo gidaba sai magriba, kowa yayi ti6is da gajiya.
Mun tarar innarmu da mama Rabi'a sunata shan hirarsu ta zuminci.
Sai kusan 10 suka bar gidan.


★★★★


Washe gari muma agidansu mama Rabu'a muka yini har innarmu, koda yakema fitarmu
mukayi nida Munubiya, Feena, Ayusher, mukabar su mama agida dasu Aryaan.
Yauma mun zaga gari sosai, dan Ayusher takira mana wani saurayinta yazo ya kwashemu,
yauma munje munga hawan sarki da la'asar, saidai yau babu Galadima a tawagar, hakan bai
dameniba, dan nama manta da lamarinsa ni.

Kwanaki kusan biyar zuwa 7 munashan shagalin salla, munsha yawo tamkar bamuda
mafad'i mudasu Ayusher, sai Fauziyya dakan bimu wani lokacin idan basu fitaba da mamarsu
suma.
'Yan matan gidanmu kowa sabgar gabansa yayi, rana d'ayane muka fita gaba d'aya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login