Showing 9001 words to 12000 words out of 18444 words

Chapter 4 - RAINA KAMA KAGA GAYYA True Hausa Book Na Marubuciya billyn Abdul .pdf

tashiga ta falo.
Yanda sukaita zumud'in kallonmu wancan karon a yau ba haka bane, gaba d'aya
hankalinsu Na kan Siyama da zahra, abin ya bamu mamaki har sauran 'yan uwanmu.
Tunda mukaga haka duksai muka fice muka koma gida, su Haleematu harda kukansu,
mukanmu zukatanmu sun sosu, dan harga ALLAH Sa'eed ya kwantamin arai.
Wanan lamari saida yajawo gagarumin fad'a agidanmu irinma wanda ba'a ta6a yiba, dan
saida takai matan gidanmu da 'Yar tone-tone asirinsu yanda suke kulle-k'ulle wani lokaci akan
innarmu da junansu.
Sosai ranar saida ran kowa ya 6aci, amma mamansu yaa Hameed da momy Hadiza su wasai
sukejin kansu, koba komai sune a sama suke gani, 'ya'yansu zasuje gidan Hutu.

Abbanmu yasamu innarmu yayta bata hak'uri, dan tabbas yanada tabbacin akwai lauje
cikin nad'i akan lamarin, tunda su Sa'eed da kansune suka Samar masa za6insu, amma gashi a
wannan karon since su siyama ne ba 'yan biyu ba.
ALLAH sarki innarmu sarkin hak'uri, cewa tayi babu komai, dama can su Siyamar ne
matansu, Dan haka tunran gini tun ran Zane, suma sauran ALLAH yabasu Na kwarai.
Sosai Abba yak'ara jin jinama hak'uri da tawakkali irin Na matar tasa, abin sonsa, wadda
yakejin har duniya ta tashi k'aunarta dabance a ransa, yana sonta harma baisan yanda zai
fassaraba, kullum cikin mata k'yak'yk'yawar addu'a yake akan ribar hak'urin datakeyi da kowa
agidan har mahaifiyarsa. yana ganin Kimar Aisha sosai da girmanta, tunda suke babu rana
d'aya dazaice gawani abun aibu data aikata masa, sai dai abinda ba'a rasaba saboda zomu
zauna zomu sa6a, balle shekara kusan 40 ba wasabace.



★★★★★★★
An tsaida bikin Siyama da Zarah dai-dai danasu aunty Hauwa'u, komai kuma ankawo, saura
lefe da sadaki kawai.

Ahaka muka koma makaranta inata yak'in fidda Sa'eed daga raina, ALLAH ma ya taimakeni
dama bawai yashiga irin cancikin nan baneba.

**

Yau lectures d'in safe garemu, dan haka mukayi shiri da wuri nida Munubiya, a tsaitsaye
mukasha kunun da innarmu ta dama mana, Dan yau girkin mamansu ya Hameed ne, idan bata
gadama ba sai takai 8 bata kammala ba, har yara saisun makara,
Aiyaan yashigo d'auke da lunch boxs nasu yana tura baki gaba. “kai kuma lafiya kake cuno
baki uwa na agwagwa?”.
6ata fuska yakuma yi tamkar zai fasa kuka, ya zube lunch boxs d'in saman kujera “Aunty ba
mama bace tace wai yau batayi abincin dazamuje dashi makaranta ba, hakama fa jiya abincin
dare ta d'umama ta zuba mana, amma damukaje school saigashi a kulan Haneep Indomi ne da
kwai”. Aryaan ya kar6e da cewar “ALLAH kuma aunty namu tsami yayi kafinma muci, haka
mukadawo da yunwa”.
tausayi yaran suka bani, Munubiya tace, “kuyi hak'uri kunji 2 d'in inna, watarana sai labari ai”.
Kansu suka jinjina mata sukace “to aunty”.
innarmu tana jinmu amma uffan bataceba.
Fita nayi batareda nacema kowa komaiba, wani shago dake can k'asan layinmu naje, nasiyo
musu yoghurt da cake k'ananu, nahad'o musu da biscuits.
A harabar gidan Na iskesu harsun fito, sauran yaran sunata shiga school bos d'insu da ake
kaisu makaranta. School bag d'insu nabud'e Na saka ma kowa nasa, sannan nace ayi karatu da
k'yau kunji babys d'inmu”.
Cikeda jin dad'i suka amsa min da fad'in “to auntynmu”.
Kumatunsu Na sumbata sannan na taimaka musu suka shiga motar suma.
Ina shigowa munubiya tamik'e tana fad'in “wai ina kikaje? kinsanfa jarababben lecturer
d'inanne zai shigar mana yau”.
“sorry sweetheart tashi muje”.
Dubu 1 innarmu tamik'o mana, kar6a mukai muna mata godiya, muka fito tana binmu da
addu'oin fatan alkairi.
Mun lek'ama su Siyama, kowacce sai tace batada lectures d'in safe, fauziyya da Feedausi ce
kawai muka tafi, dansu duk department d'inmu d'ayane..........✍







One luv


*_ALLAH ka gafartama iyayrnmu_*
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing_*

*_HASKE WRITERS ASSO..._*
_(Home of expert and perfect writer's)_

*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_




*_Bilyn Abdull ce_*



5⃣

...........Wajen 4pm muka fito daga cikin makaranta, mu 6 ne yanzu, sa6anin d'azu damukazo
mu hud'u, bayan tahowarmu Safara'u da Haleematu suka taho suma, duk da mun rigasu gama
lectures sai muka jirasu suka fito muka rankayo tare domin tafiya gida, bamu samu school bos
ba, dan haka muka da6o sayyadarmu har zuwa babban gate, muna tsaitsaye abakin titi, tareda
wasu daga cikin tsirarun d'alibai irinmu, tundaga nesa muka hango tahowar motocin da uban
gudu, saika d'auka sukad'aine akan titin saboda gudun dasuke tsulawa tamkar zasu tashi sama.
duk baya muka matsa, dan tabbas wad'annan suka sameka babu abinda zai hanasu takeka su
wuce batareda sun damuba.
Tamkar wucewar iska haka suka dinga gittamu, jikake shuuuu!! shuuu!! shuuu!!.
Furicin wani mayshin saurayi dake jingine jikin motarsa yazo d'aukar wasu 'yan mata biyu
dake gefenmu 'yan matan sunada jin kan masifa, ko'a makarantar bakowa sukema maganaba,
department d'inmu d'aya dasu amma ko kallo basu isheniba, dan ko sallama bata ta6a had'ani
dasuba.. Saurayin yabi motocin da kallo yana fad'in “tab ashe *_GALADIMA!_* yashigo gari kenan?”.
“Da gaske yaa Usman?”. ‘d'aya acikin 'yan Matan tafad'a cikin matuk'ar zumud'i’.
Yace, “da gaske mana baby, baga motocinsa kuna ganin sun wuceba”.
Dan danan suka shiga murna, kai kace an musu albishir da aljanna ne.
Baki na ta6e inajan k'aramin tsaki. Fiddausi tace, “to waye shi galadima d'in?”.
“oho musu”, ‘cewar Munubiya’.
Budurwar dake tsaye d'ayan gefenmu itada saurayinta suna jiran abin hawa suma tace,
“Galadima d'an Sarki kenan, *Yarima Sameer!”*.

“humm lallai kuce manyane, shiyyasa suke gudun da kosunbi takan talaka babu abinda
za'ayi”. ‘cikeda 6acin rai nake maganar’.
Dariya su siyama sukayi suna fad'in “toke ina ruwanki?, k'asarfa tasuce, sai yanda sukayi
da ita, tsakaninmu dasu saidai mu hangesu cikin mota ko ranar hawan salla”.
Dogon tsaki nakuma ja tareda kauda kaina daga garesu na maida hankalina wajen tare
wata taxi dake gabatomu.

A motama firar dasu Haleematu sukaitayi kenan, ta Galadima ne ko uwarmi ne ma Na
manta. nidai uffan ban kuma tofawaba, hasalima haushi hirar tasu takoma bani, dan mai taxi
d'in yasaki baki sai wani basu labarin Galadima d'in yakeyi dakuma kwarzan tashi, earphone na
jayo a cikin lady's bag d'ina na manna a kunne danma nabar jinsu gaba d'aya. Saida muka iso gida sannan Fauziyya dake kusa dani ta zungureni, d'agowa nayi Na
kalleta sainaga duk sun fice, bance komaiba nafito nima.

Mun iske innarmu bata nan, saisu Aiyaan kawai zaune a falo suna kallo, shigowarmu
yasasu tasowa da gudu suna mana oyoyo, muma mun taryesu da murnarmu, Munubiya tace,
“Aryaan miyasa baku cire Uniform ba kukayi wanka?”.
“yo aunty mun dawo munga Innarmu bata nanane”.
Nace “innarmu bata nan? to ina taje?”.
“muma bamu saniba aunty, munje kuma kitchen bamuga abinci ba, kuma yunwa mukeji”.
Munubiya tace, “ya salam, kujira ina zuwa”.
Fita tayi, babu dad'ewa sai gata tadawo cikin damuwa, ina cirema su Aryaan Uniform, Na
kalleta ina fad'in “mike faruwa Munu...? Ina abincinne?”.
Kwallar idonta ta share, ta zauna bisa kujera sannan tace, “naje mama tace wai innarmu ta
d'auka abinci tatafi dashi hospital, dan haka shine rabonmu”.
Raina a 6ace na mik'e zan fita, da sauri munubiya ta ruk'oni, “please Munaya, kibarta kawai,
yakamata mu kira innarmu muji waye a hospital? Inaga wannan yafi komai muhimmanci nake
gani akan abinda mamar tamana”.
“Haba Munubiya, wannan wane irin rashin mutunci ne, wai mi Matan gidannan suke
tak'ama dashine? Idan suna tak'ama da Ubanninsu muma ai nan gidan Ubanmune ko, yanzu
ace yarannan kamar su Aryaan su dawo school tun 3 amma ahanasu abinci, wannan wane irin
zaluncine? Kisakeni kawai naje naci kutumar uban matarnan munubiya, wlhy sai dai yau Abba
yace nabar masa gidansa”.“A'a munaya, duk hakama bata tasoba, idan hankali ya6ata hankali
ke nemosa, bai kamata mutaru muzama d'ayaba mu da su. bara kawai naje kicin d'in Na dafa
mana wani abun mai sauk'i, kiyi hak'uri dan ALLAH, kinga innarmu bazataji dad'iba idan tatarar
da faruwar hakan”.
Badan raina yaso ba Na hak'ura, saman kujera nakoma Na zauna ina huci, nikad'ai nasan
minakeji a zuciyata.
Munubiya tafita dan nema mana abinda zamuci, nikuma Na d'auki waya domin Kiran
innarmu naji abinda tajeyi asibiti.
Harta katse bata d'agaba, nakuma kira akaro Na biyu sannan ta d'auka, gaisheta nayi da
tambayar mitajeyi asibiti?.
Daga can tace min Nafisar mama Rabi'a Ce jikinta ya motsa yanzu hakama jini ake buk'ata
amma an Gaza samu, gashi yaa marwan dayakan bata jinin baya nan yayi tafiya shida
Abbansu.
Hankalina a tashe nace “innarmu ganinan zuwa yanzunnan insha ALLAH, kuna general
hospital ne?”.
“eh muna nan”.
“ok insha ALLAHU ganina zuwa”.

'Dakinmu nashiga da Sauri nad'an watsa ruwa a tsaitsaye saboda naji dad'in jikina, komai
ban tsaya shafawaba Na zira doguwar Riga jallabiya Na fice da hanzari. A k'ofar fita falo naci
karo da munubiya d'auke da babban faranti tazubo spaghetti tanata turiri.
namatsa baya da Sauri INA fad'in sorry, munubiya bara naje asibitin wajensu innarmu, wai
jikin feena ne ya motsa kuma ana buk'atar jini, gashi yaa marwan sunyi tafiya da abba”.
Munubiya tace, “toko Na juye mana abincin a kula mu tafi gaba d'aya?”.
Nace, “a'a munu... Ki zauna dasu Aiyaan bara naje ni kad'ai, baikamata mubar wajen ba
kowaba”.
“to shikenan, yanda akayi ki ta6oni awaya, amma in kunkai dare zakuganmu muma,
abincinfa?”.
“humm munu bar abincinnan, banida wata nutsuwar cinsa, saina dawo”.
Ban jira amsarta ba nafice. ALLAH ya taimakeni INA fita nasamu napep. Mintuna kad'an
muka isa hospital d'in, kud'insa na biyashi nashige da hanzari ina k'ok'arin kiran innarmu.
Babu dad'ewa kuwa ta d'aga, nace mata gani acikin asibitin. Kwatance tamin na inda aka
kwantar dasu 6angaren masu sikila.
A rikice na iske innarmu da mama Rabi'a, saboda jikin feena ya motsa mata sosai a wannan
karon.
Nace, “mama yanzu mi ake cikine?”.
“Rashin jininne matsala yanzu Munaya, sunce kuma anemoshi da gaggawa, to dama can
jinin Fadeel baya yimata shiyyasama ko gwadasa ba ayiba, Marwan dake bata kuma sunyi
tafiya da abbansu”.
“mama ina zuwa, bani takardar da suka baku”.
Mik'omin tayi nafita da saurina. dukna rikice inata kai kawo dan ganin ansami jinin, amma har
magriba ta rufa ba a samuba, saboda jinin feena yanada wuyar samu, ana cikin kiraye-kirayen
sallar isha'i saiga Ayusher ta iso itama, dama an barta a gidane saboda babu kowa, to takasa
hak'uri tabiyo sahu, da ita muka cigaba da shiga da fita, saida aka fito sallar isha'i ALLAH yasa
aka dace da samun leda 1, saura 1, dama biyu suke buk'ata. ana cikin d'aura mata saiga
Munubiya ita dasu Aryaan da kulolin abinci.
Koda aka gama sakawa sai muka koma Neman d'ayar ledar data rage, yanzu harda
munubiya muke tare.
Muna a lab d'inne muna shawarar ko a d'iba namu jinin idan zaiyi babu damuwa. Takun
takalman damuka jiyo yasamu juyawa harda likitan da maganarsa takatse bisa k'ok'arin bamu
amsa dayakeyi. wani ni'imtaccen k'amshine ya iso hancinanmu tunkan mamallakin turarenma
yakai ga isowa inda muke. d'auke kaina nayi na maida ga mai d'ibar jinin. Likitan naga yafara gyara kujera yana fad'in “dama yalla6ai ya shigo gari yau? Ni nama
manta yaune ranar dayake bada jini”.
Bai samu mai bashi amsaba a cikinmu har tawagar Wanda yakira yalla6ai suka iso wajen.
Munubiya da Ayusher suka matsa gefe saboda wata uwar tsawa da masu take masa baya
suka daka mana, nikam koma motsawa banyiba bare nasan ALLAH yayi ruwansu awajen,
saima baki dana ta6e na d'auke kaina daga saitin dasuke.Bulala d'aya daga masu jajayen
rigunan ya d'aga da nufin zubamun. “Wanda suke kira Yalla6ai dake zaune a kujerar da doctor ya ajiye masa ya d'agamasa
hannu da Sauri, alamar karya dakeni”.
Cikeda girmamawa yace, “angama zaki s.........”.

Hannu Yakuma d'aga masa alamar baya buk'atar kirarin.
Baki nakuma ta6ewa sannan na ra6a ta gefensu nafice, banga fuskar Yalla6ai d'in nasuba,
saboda ya juyamin bayane ni, sananan shima tunda yashigo bai kalli kowaba a lab d'in, yanata
aikin danna wayarsa, kuma baiyi magana ba, ko doctor da Norse's d'in da suka gaidashi hannu
kawai ya d'aga musu, kuma ko d'agowa baiyiba yanata aikin danna waya kai kace zai danno
hanyar zuwa aljannane aciki.

Waje na dawo nayi zamana ina cigaba da game a waya, su Munubuya dai suna cikin,
bansan uwarmi suka tsaya yiba awajen.
Kusan mintuna 40 saigasu sunfito, takun takalmansu kawai naji, amma ban d'agoba, sai
k'amshin turarensa daya cika illahirin wajen, saikuma gaisuwar da mutane keta faman zubewa
sunayi masa, ko sau d'aya banji ya amsaba.
Tsaki naja inamaijin haushin wannan mutumin, to wayema shine? dayakema mutane
wannan jinkan., motsooww aikin banza kawai.

Tabbas yaji tsakin da akayi, hakanne yasakashi d'ago k'yawawan idanunsa yakai duba saitin
Inda yajiyo tsakin, akan *munaya* dake zaune bisa kujerun dake Jere awajen ya sauke su, sai
dai baya ganin fuskanta sosai, saboda ta duk'ar da kai tana danna waya, kuma gyalen
jallabiyarta yarufe mata Rabin fuska, ita kad'aice zatayi wani motsi awajen suji, dan tafi kusanci
da Inda suke tsaye.
Janye idanunsa yayi kawai daga gareta, yay saurin d'agama bayin dake k'ok'arin tafowa
gareni hannu. Cikin Wata tattausar murya mai aji dake cike da k'asaitar masu isa najiyo yana
fad'in “Bayta kawai”.
Cikeda girmamawa bawan yace, “ya shugaba tsaki tayi fa”.
Shiru yay kamar bazai tankaba, saikuma najiyo yace, “kasan dawa take?”.
Bawan girgiza kai yayi alamar a'a.
Bai sake cewa komaiba yay gaba suka bishi a baya.
'Dago ido nai nabi bayansu da kallo, sainaga sun nufi 6angaren mata masu haihuwa.
janye idona nayi ina fad'in “kadaiji dashi Malam, kana fama da Girman kai kamar wani Sarki?
Abinma dariya ko (R) bai iyaba, wai bayta”.
Dai dai nan su Ayusher suka iso cikeda farinci, hannunsu d'auke da ledar jinin

Cikeda jin haushi nace, “wai uwarmi kuka tsaya yi acikin lab d'inne?”.
“Uwarmu ta gode”. ‘ cewar Ayusher’.
Munubiya kuma tace, “zaman namu aiko yayi amfani, tunda gashi mun samo sauran jinin
ko”.
Na kallesu da mamaki, “ina kuka samo jinin kuma to?”.
“Galadima ya bayar”.
Cikin ta6e baki nace, “miye kuma Galadima? A inama kukaga wani Galadima kome ma
kukace?”.
“wanda yashigo muna cikifa, ai Galadima ne (Yareema Sameer d'an sarki)”.
Ido na waro waje, “wai kuna nufin wannan mai shegen girman kai d'in dama shine
Galadiman? kenan munu.... shine yawucemu d'azu munfito makaranta?”.

“kwarai kuwa sweetheart shine, kuma wlhy bashida Girman kai kamar yanda kike zato ko
Sis.. Ayusher? ”.
“Wlhy kuwa hakane Munu..., ashe duk k'arshen ko wane wata saiyazo asibitinan yabada
jininsa gamasu buk'ata, gashi jinin nasa mai irin wahalar samu d'inanne irinna feena, kai
mutuminnan yayi wlhy, Sarauta ba karya baceba, danyau naga tsantsar sarauta da mulki da
k'asaita ajikin Galadima, yanzu haka zai zagayane yaduba marasa lafiya”.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login