Showing 12001 words to 15000 words out of 18444 words

Chapter 5 - RAINA KAMA KAGA GAYYA True Hausa Book Na Marubuciya billyn Abdul .pdf

Harara na ballama Ayusher daketa zabga surutu uwa aku, na warce jinin daga hannun
munubiya ina fad'in “idan kun gama shirmen kwa taho”.
Kallo suka bini dashi, Ayusher tace, “Anya yarinyarnan batada aljanu?, ke kowama bai
mikiba?, yanzu nan duk had'uwar Galadima Munaya tana nufin bai burgeta ba kenan?”.
Dariya Munubiya tayi, sis... Ayusher har yanzu baki gama fahimtar Munaya ba na lura,
kyagama abinda yafi haka indai daga wajentane. Yanzu hakama tunda kikaji tace haka ko sau
d'aya bata kalleshiba wlhy bare tasanma kalarsa. kinga muje kinji.“humm aiko wlhy inabata
kalleshiba anyi babu ita kuwa, ruwa ta shata kuma, yo kobabu komai aina bada koda labarine
nace nata6a ganinsa ido da ido ko”. ‘cewar Ayusher’.
Dariya kawai Munubiya tayi, taja hannunta suka tafi.

Sanda suka iso harma an fara k'ok'arin sakama feena jinin, dama wancan yak'are.
Duk muna zaune a k'ofar d'akin bisa kujerun wajen, Aryaan da Aiyaan duk suna jikin mama
Rabi'a barci ya d'aukesu, fadeel na kusada innarmu yanacin abincin dasu Munubiya suka kawo,
zama nayi kusada fadeel d'in na saka hannu nad'au cokalin dayake cin abincin ina fad'in bro...
nimafa yunwarnan nakeji, rabona da abinci tun kusan 1 danaci a kafteriya na makaranta”. Kallona yayi yana cewa “sannu da k'ok'ari sis...., shiyyasa gakinan tsula guda bak'ya gaba
bakya baya keda munu....”.
Cokalin nakai zan kwala masa a kai ya kauce yana dariya, nima dariyar nayi na d'auki kular
abincin na k'ara mana.
Muna cikin ci Ayusher ma tamatso tace zataci, munci mun k'oshi sannan muka gyara
wajen, mama da innarmu ma sukaci, dan zuwa yanzu duk mun sami 'Yar nutsuwa.
Kusan 10pm saiga Abbanmu shida baba k'arami, duk muka gaidasu suka tambayi mai jiki,
innarmu da mama Rabi'a suka amasa musu da sauk'i.
Har d'akin suka shiga, suka duba feena daketa barcinta, sannan sukace muzo mu tafi gida,
za'a bar innarmu da mama Rabi'a su kwana.
Saida safe mukai musu muka fito, Fadeel ya d'akko Aryaan, baba k'arami ya d'akko Aiyaan.
Saida muka fara sauke Ayusher da Fadeel gida sannan mukuma muka wuce.
Mun tarar gidan tsitt alamun duk anyi barci, saidai masu wayar dare da samari irinsu aunty
Ramla, saikuma masu charts.
Abbanmu da baba k'arami suka d'auki su Aiyaan, har d'akinsu suka kaisu sannan suka fita.
Muma shirin barci mukayi muka kwanta cikeda kewar Innarmu, muna kwanciya muka kirasu
da k'arajin mai jikin sannan muka tafi duniyar barci muma, dagani har Munubiya babu mai wani
saurayin da zamu 6ata lokaci wajen yin hirar dare...............✍

Kumuje zuwa my guys�



Gobe idan ALLAH ya kaimu baza kujiniba, inada wani d'an uziri, sai Monday idan ALLAH ya
kaimu kuma.


https://chat.whatsapp.com/K1qwmMusX7ILDLATGSvfHJ


*_RAINA KAMA........ FANS CLUB_*


_Duk Wanda yasan yana karanta wannan buk d'in ya garzaya yanemi link Na RAINA KAMA
FANS CLUB, a wannan gidan kawai zan dinga posting a halin yanzun, awannan karon bazan
turama kowa buk ta PC ba, narigada nayi rantsuwa. Amma annan zaka iya samu da faro,
sannan inhar ba'a tattaunawa akan novel d'in zanyi waje da mutum babu ruwana, kuma kar a
turomin kowanne novels acikinsa Dan ALLAH, inba hakaba zan fidda mutum ko Yaya nake
dashi, nabud'e gidanne saboda anan kawai zan dinga posting yanzu, sai wasu groups
dabasu wuce 3 ba._

Ina fata zaku bani had'in kai please, inba hakaba ALLAH zai koma Na kud'ine saboda tsaro
ba tsoroba�



One luv




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing_*



*_HASKE WRITERS ASSO..._*
_(Home of expert and perfect writer's)_

*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_

*_Bilyn Abdull ce_*

_________

*_ASSALAMU ALAIKUM_*

_Jiya da daddare akaita kirana mutane Na tanbayata Yaya jiki, tun ban fahimci maganarba
hardai nafara tsarguwa nayi tambaya. Dan sai kira kan kira ake jeramin, wata take sanar dani
taga wani posting ne yana yawo wai za'amin CS. babu shiri nabud'e data naga mike faruwa,
group d'in farko dana bud'e sainaci karo da wannan posting d'in mutane nata comments,
nabud'e nabiyu ma hakan dai._

*_Assalamualaikum Alaikum,Dan Allah kuyiwa billyn Abdul(ma rubuciyan RAINA KAMA.
Adua'baby ya mutu a cikin ta zaa cire Mata Shi yanzu_*

_sai daga baya nakejin Bily galadanci ce batada lfyar, amma wata ta maida zancen haka
saboda sunan namu yazo d'aya, to ALLAH yabata lfy itama._
_sannan ina shawartar jama'a Dan ALLAH kuringa nutsuwa wajen tantance Abu kafin Ku
yad'ashi, domin wadda tayi wancan write up d'in ta zaunane ta tsara nata son zuciyar, wadda
tayi posting d'in farko akan ciwon Bily galadanci sunan Bily tasaka ba nawaba, itakuma ta canja
nata tsarin tashiga ya d'awa, ALLAH ya shiryar damu, yakuma bama marasa lfyarmu lafiya._
*banyi niyar posting ba yau, amma ganin wancan write up d'in yana cigaba da yad'uwa
yasani dole yi Dan na warware muku zancen.*


__________________________




6⃣

.......Bamusan abinda yafaruba, mukaji 'yan gidanmu suna k'ananun magana da safe, wai
girkin jiya na dare da mamansu yaa hameed tayi sai asararsa akayi, girkin yay d'anye yak'i
dahuwa, kuma a gas tayi girkin bare ace iccen yabata matsala, gashi kuma normal gas d'in
yake aiki. Muna cikin yima su Aiyaan shirin school muka fara jiyo hayaniya, sai da muka gama musu
shirin sannan muka fito, cirko-cirko muka iske 'yan gidanmu, yayinda mamansu yaa hameed
keta zabga masifa. tana fad'ama abbanmu wai mune muka mata kwari shiyyasa jiya abinci yay
mata d'anye danta hanamu abinci, kuma gashi yanzuma tasaka doya amai tak'i soyuwa.

Ni dariyama taso bani wlhy, wai mune muka mata kwari, to miye kwarinne ma datake
magana a kai? danni bamma sanshiba.....
Maganar Abbanmu ta katsemin tunanina.
“ 'Yan biyuna kuzo nan naji kunji”.
K'arasowa mukayi kusada abbanmu harsu Aiyaan, ya kallemu cikeda kulawa, “haba 'yan
albarka mike faruwa haka?”.
Cikeda rashin fahimta nace, “Abba a ina?”.
“haba twins d'in Abba, bakuji mi mamanku take fad'aba? abinci yamata d'anye jiya da yau”.
“amma Abba Dan abinci yayi d'anye kuma sai ace mune? Kagafa jiya munama asibiti
bamuci abincin dareba agida, darana ma mama hanamu tayi tace innarmu tatafi da kasonmu
asibiti, haka muka dawo muka iske su Aryaan sunajin yunwa, sai Munubiya Ce tamana girki,
kuma tayi takai mana wani asibitin, ni wlhy Abba bammasan wani kwari dasuke maganaba akai,
wannan ai canfine, tunkuma zamanin da aka barsa”.
“canfin uwarki, kujimin munafukar yarinya, inbakune kukayi muguntarba uwarwaye yayi, to
wlhy ahir d'inku, ba 'yan biyu ba ko 'yan gomane ni ubanku zanci a gidannan.......”
Afusace Abba yace, “to ai gani, saikizo kici ko, ai gaskiyama yarinyarnan tafad'a, wannan
canfine kawai, dan abinci yayi d'anye saikuma a fassarashi dawani Abu daban, haba Dan
ALLAH, saikace wata mara ilimin addini? Karna sake jin wannan maganar, inba hakaba
rankowa zai 6acine a gidannan”. Yana gama fad'a yabar wajen. muma ganin haka muka tasa su Aiyaan gaba muka koma
6angarenmu. duk da nakasa fassara mi mama ke fad'i hakan yamun dad'i, koba komai dai ai
ALLAH yamana sakayya da hanamu abinci datayi muda wad'anan k'ananun yaran da basu da
alhakin kowa. Yanzuma munubiya Ce ta dafo mana indomi mukaci, sanan ta zubama su Aiyaan a
kulolinsu Na makaranta, suna tafiya muma mukayi shirin tafiya School.
Bamu tsaya jiran sauranba mukayi gaba saboda zamu biya ta asibiti, kuma munsan acikinsu
babu mai binmu, harmun fita saiga Fauziyya tabiyomu, itama zataje taduba feena d'in.Alhmdllh
munma tarar an sallamesu sunata shirin tafiya gida, mukaima feena sannu, ta amsa tana fara'a
da tambayarmu ya makaranta?. mukace gatanan zamu tafi. Bamufi mintuna 30 ba muka fito, Fadeel ya d'aukesu, mukuma muka wuce school.

A mota Munubiya take bama Fauziyya labarin ganin Galadima damukayi jiya a asibiti, ko
sau d'aya ban saka musu bakiba har muka sauka.



★★★★★

A wannan karon har mamansu yaa hameed tagama girkinta Na kwana biyu asarar abinci
akaitayi, Dan kullum d'anye yake mata. hakan yasa taita sakin habaici agidan itada
muk'arrabanta irinsu momy hadiza,.
Maman Fauziyya ta sanar ma innarmu komai tun randa taje duba feena agidan mama
Rabi'a, Dan haka Innarmu tayi kunnen uwar shegu dasu, tamkarma batasan da ita sukeba balle
ta nuna tama fahimci zancen nasu.

Innaro ma tazo tayi tata tsiyar San rai, tabi duk ta zagemu dacin mutuncin innarmu, koma
fitowa innarmu hanamu yi tayi, har Innaro tagama tafice. Matan gida najin dad'i.


★★★★★★

Haka rayuwar tacigaba da tafiya, yau da gobe kayan ALLAH har gashi azumi ya rage saura
kwanaki uku kacal a fara, Dan haka musulmai NATA shirin tarbar wannan wata mai tarin albarka
da falala.
Kasuwanni sun cushe saboda yawan hada-hada, duk da 'yan kasuwa sunyi taiyar tasu ta
k'arama abinci kud'i, maimakon su sassauto bayin ALLAH su sami sauk'i (ALLAH ka shirya 'yan
kasuwarmu subar wannan hali dai).

A 6angaren gidanmu ma iyayenmu maza duk sunyi shirin, Dan dukkan wani abun buk'ata an
tanadeshi, sai abinda ba'a rasaba dazai iya lalacewa idan an ajiye, wannan anbarsa yayunmu
maza su ringayo cefanensa kullum kamar yanda aka saba.
Itama Innaro an ajiye mata dukkan abinda zata buk'ata, dukda kullum daga gidanmu ake
kaimata abinci, safe yamma da dare, kuma dolene kowane 6angare sai sunkai nasu.
Muma a 6angarnmu munyi dukkan namu shirin, dukda abin zai had'e mana da zuwa
makaranta, hakan yasa nake tausaya mana, gashi ana tsula rana mai zafi kuma.
Alhmdllh yau ta kasance Alhamis, kuma yaune ake saka ran ganin wata atashi da azumi
washe garin juma'a.
Har zuwa 9pm kunnen kowa naga redio da talabijin, jira kawai Muke muji sanarwa daga
sarkin musulmai. sai wajen 9:30pm sanan aka Sanar da ganin wata, duk wani Muslim yana
cikeda d'okin fara azumin watan Ramadan da zamu Shiga goma ta marmari (inji hausawa).
Tun alokacin duk muka d'auki niyya, kasancewar girkin innarmu ne tayi shirin tafiya d'akin
Abbanmu, muma tace mu kashe TV muje mu kwanta kar atadamu da asuba kuma muzo muna
k'unk'uni.
Badan mun soba muka kashe mukaje mukai shirin barci muka kwanta da addu'ar
abakunanmu.

Aiko da asuba dak'yar innarmu ta iya tashinmu mukai sahur, tea kawai muka shama, dama
mu bama sahur da abinci nida munubiya, garama ita wani lokacin takan had'a da kunu ko fura.
Bamu kwantaba saida akayi sallar asubahi, still kwanciya muka kumayi, sai 8 innarmu ta
tadamu, kasancewar yau saima 10 mukeda lecture, kuma zamu fito 12 ne.

Tunkan aje da nisa azumin yafara garani, dak'yar Na daure aka kammala lecture muka fito,
amma badan Na fahimci komaiba nidai yau.
Su Munubiya sai dariya suke mini wai Raguwa, nidai ban kulasuba, Burina kawai naga mun
Isa gida Na kwanta.
Tunda muka dawo school nazube a falo k'asan carpet, ban sake Sanin duniyar danake
cikiba saida munubiya ta tadani nayi salla, Ashe harsu Aryaan sun sako masallacima inata
barci, sallarma dak'yar nayita atsaye, INA kammalawa nakuma kwanciya.

“oh ni Aisha, wai Munaya mikikeson maida kankine? yanzu azumin kikema langa6e haka?
saikace yau kika fara azumi a rayuwarki?”.
“ALLAH innarmu bazaki ganeba, nidai ALLAH yasa akira salla da wuri”.
Munubiya dasu Aiyaan suka sakamin dariya. “Aunty yanzufa k'arfe 2 ma, sauran kusan awa
5 dawani Abu asha ruwa”. ‘Aryaan yafad'a yana dariya’.Harara Na Dalla masa INA fad'in
“ALLAH inbaka rife wannan bakin naka mai gajerarrun hak'oraba zaka dakune, Dan k'aniyarka
kaiba yanzu kagama lodama cikinka abinciba?”. Aunty nimafa Dan innarmu bata tadamu baneba kawai, amma insha ALLAHU gobe zamuyi
ko Aiyaan?”.
cikin zumud'i Aiyaan yace, “eh mana, muma zamuyi bro”.
“kuma wlhy yaro bai Isa karyashiba, garama karku d'auka”.
Munubiya tamik'e tana dariya, “imm innarmu bara kiga naje nafara rage aikin, miza'ayi?”.
“ki fere doya kafin Na fito, Munaya tashi maza kuje, kekuma ki gyara kayan miya”.
“wayyo innarmu ki tausaya min mana”.
“mukuma mu kashe kanmu tunda bama azumin ko?”. ‘cikeda gatse tayi maganar’.
“a'a innarmu, bara naje kodaga zaune sainayi”.
“kimayi daga kwance, raguwar banza kawai, ai mijinki yashiga uku, wataran sai yadawo aiki
baki gama abinciba”.
Baki Na tura gaba sannan nafita.

Mun rage aiki sosai kafin la'asar, sai bayan sallar la'asar d'in 'yan Matan gidanmu suka
shishshigo kitchen d'in kamar yanda aka saba, dama duk shekara gaba d'aya muke had'uwa a
kitchen d'in 6angarenmu ayi abincin bud'a Baki, saidai saboda munada yawa akanyi time table
saboda a rarrabu kowa da ranar da Zai taya mai aikin ranar.
Da yake aikin yawane dandanan muka kammala kafin 6, a can tsakar gida aka shinfid'a manyan
tabarmi bayan an tsaftace wajen, duk azumi gaba d'aya muke had'uwa asha ruwa dama anan,
kafin matar ya hameed ta rasu har itama anan suke zuwa suyi bud'a Baki.
Bayan mun had'u mun gama shirya komai kowa yanufi 6angarensu ya watsa ruwa kafin
akira salla, dolene kaga jama'ar gidanmu aranar mu burgeka, babu fad'a babu hantarar juna,
(yo kowa azumi yagama cin k'aniyarsa�).
Kasan cewar babu wuta ya kamal yazuba fetur a Gen... Ya tada, kowa yayi wanka saiyayi
shirinsa da alwala yadawo tsakar gida ana jiran kiran salla, yara dabasuyi azumi baneba suketa
shargallensu a tsakar gidan.
Yanda na zube a tabarman tamkar mara kashi yasaka yaa Shafi'u fad'in “kai kekam anyi
raguwar yarinya wlhy, nasan dai Munaya Ce, Dan Munubiya tafiki jarumta”.
Dariya wad'anda ke wajen sukayi, yaa Naseer yace, “gaskiya mijinki yaga banu, yo idan
yayi wasa dai bazai dinga cin abincin bud'a bakiba a gidansa”.
Cikin dariya Aunty Hauwa'u ke fad'in “sai ya d'auka mata 'Yar aiki ai”.
Caraf maman Safara'u ta amshe zance... “yo basai idan mai halin d'aukar 'Yar aikin bane,
ana fama da masarar tuwo da shinkafa a jajibo mai aiki?”.
Gurin tsit yayi kamar ruwa ya cinyemu, da alama kowa baiji dad'in furucin Na maman
safara'u ba, sai mamansu yaa hameed ce tayi dariya itada momy Hadiza.

Ganin abin zai koma cin zarafin juna sai maman fauziyya ta d'ako wani zance, daga nan aka
koma hirar d'inkin salla. babu dad'ewa ma aka kira sallar magriba, cikeda d'oki kowa yafara
k'ok'arin cin dabino. tab aini kam bandani, tuni Na d'ebi ruwa mai sanyi nafara sha, Dan shine
babban burina. a gida mukayi jam'i, baba k'arami yajamana limanci. da ganan kuma kowa ya
maida hankalinsa wajen bud'a baki, harda su hajiya innaro, tayi kane-kane ita masu gidan
'ya'ya�, koda wasa dagamu har innarmu babu Wanda yashiga sabgarta gudun gwalasa, har
aka gama lafiya muka gabatar da sallar isha'i da asham. daga nan aka d'an ta6a hira kowa
yahad'a kan 'ya'yansa zuwa 6angarensa.

haka muka cigaba da gudanar da ibadar azumin watan ramadan, tun ina ragwan taka harna
fara daurewa, an gama goman farko aka shiga ta biyu (goma ta wuya ).
Gaskiya nad'an wahaltu a tsakanin, ga makaranta ga aikin gidanmu dabaya k'arewa, ko
wanke-wankema ya isheka, dukda had'uwa akeyi anayi kuwa.
Azumi yana 13 aka kawo kayan sallarmu, an bajesu tsakar gida kowa ya za6a, kala uku-uku
ne dama duk shekara, atanfa, shadda, les, saikuma iyayenmu mata su k'ara mana gwargwadon
abinda ALLAH ya hore musu.
Munada telolinnmu masu mana d'inki iya 'yan gidanmu kawai, shiyyasa bamuda matsala.
Washe gari kuwa sukazo suka gwadamu, kowa aka saka sunansa ajikin kayansa da style d'in
data za6a.
Innarmu ma sun saya mana itada mama Rabi'a, dan tunma kan azumi an kammala mana
d'unkunanmu mudasu feena, (innarmu tana business itada mama Rabi'a) shiyyasa duk wani
abun kwalliya Na 'yan mata bama rasashi, duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login