Showing 18001 words to 18444 words out of 18444 words

Chapter 7 - RAINA KAMA KAGA GAYYA True Hausa Book Na Marubuciya billyn Abdul .pdf

domin
gaida danginsu Abbanmu da Innaro takafa ta tsare akan sai munje wai su Anty Ramla sunyo
musu sallamar aure.Kwanaki 10 cif dagama bikin salla muka koma makaranta.
Haka rayuwa tacigaba da shud'ayawa, yayinda 'yan gidanmu keta shirin bikin 'ya'yansu, shiri
akeyi babu kama hannun yaro, kowa burinsa ace 'ya'yan d'akinsa sune Star's, kuma sunfi kowa
komai.
Sati uku kacal bikin yarage, an kawo lefe daga gidan senator halliru, akwatina 24, siyama 12
Zarah 12.
Humm ai ranar munsha kallo Na al'ajabi wajen mamansu yaa Hameed da momy Hadiza,
habaici da gugar zana da burga, kowa yashashi, har dai abin yak'ure mamansu haleematu da
maman Safara'u suka tanka musu, kafin kice mi gida yagama kacamewa da hayaniya, kowa
yana ya6ama kowa magana, saida suka gama cin zarafin junansu sannan sukayi shiru bisa
tsawatarwar baba k'arami, dayake yana gida a lokacin.
An bar maganarne kawai amma badan ta k'areba, mudai a 6angarenmu ma innarmu hana
kowa fitowa tayi, dayake weekend ne.
Suma sauran duk an kawo nasu lefan, Aunty Rahaima, Ramlah, Hauwa'u sai aunty
khaleesa, suma dai Alhmdllh, komai sai dai mak'iyi, duk da basukai nasu siyama ba gaskiya. a
wannan karonma dai saida akayi 'yan gulmace-gulmace a gidanmu, amma basu bari tafito
sarariba. Suma su yaa Hameed aka kai nasu lefan gidajen matan dazasu aura shida Ya shafi'u da yaa
Nasser. suma iyayenmu sunyi k'ok'ari wajen had'a musu lefen girma, ankai kuma kowa Na
sambarka.
Tun bayan gama kai lefe gidanmu yakuma d'inkewa da k'us-k'us na gutsiri tsomar gidan
yawa, kowa yana gulmar kowa akan aga wace rawa zaka taka, su 5 masu aurar da 'ya'yan.
Mamansu yaa hameed zata aurar da 3, yaa hameed, aunty khaleesa da Zarah.
Sai maman Haleematu zata aurar da aunty Hauwa'u.
Sai Momy Hadiza zata aurar da Siyama da aunty Raihan.
Mama Ruk'ayya kuma zata aurar da yaa Shafi'u da yaa Naseer.
Maman Safara'u kuma Aunty Ramlah.
Innarmu da maman Fauziyya ne kawai bazasu aurar da kowa ba, dan haka suka zama 'yan
kallo, sai idan mazajensu sun saka su acikin shawarane.............✍









*_Ya Rabbi ka gafarta iyayenmu_*

[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing_*



*_HASKE WRITERS ASSO..._*
_(Home of expert and perfect writer's)_

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login