Showing 24001 words to 27000 words out of 37792 words
Chapter 9 - Rainon Soja Part 3 Complete Book By Maman Teddy .pdf
68-69
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500
Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko
katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number
09061466409....✍#Mamanteddy#mrsusm.* Book 3
“......Meye na rufe ƙofa da key...?
Ammmm motsa baki yayi zai mata magana Daddy da ya Khalil suka shigo Bedroom din
Wannan yasa shi yin shiru , duka nufar gadon da Ma'eesha take suka yi ba tare da sun bi ta kan
Aliyu ba . Wanda da ganin Khalil ya Gimtse fuska yana aikin cika maƙoshi . My Queen ya jikin
naki,Ashe baki ji daɗi ba jiya .....? Daddy ya furta yana shafa kan ma'eesha cike da kulawa.
Gyaɗa masa kai tayi tana cewa “ Daddy Ina ƙwana! Ya Khalil an tashi lafiya?” . Lpyl alhmdlh
Khalil ya amsa kana yace “ Ya jikin baki? Ina ne ke yi Miki ciwo ?....kai da ba likita ba meye
amfani sanin inda yake mata ciwo zai maka...” Muryar Aliyu ya katse su , inda cikin Sauri Daddy
ya furta “ Ai Doctor Isma'il yana hanya yanzu zai taho sai ya duba ta ”. Ɗan lumshe ido mami
tayi tana Girgiza kai a zuciyar ta tana mamakin kishi irin na Aliyu da masifa babu haƙuri
ƙwata-ƙwata ”.
**
Gidan Alhaji Adamu ( Yes da No) .
A yanzu ne ake yin ta , duka matan nasa sun banzama wurin bokaye kowa burin ta ta zama ta
gaban gaba a cikin wannan gida. Inda Hajiya Falmata ta lashi takobin duk wanda ya nemi shan
gaban ta , to sai ta aika shi lahira kamar yanda ta aika Rabi . A yanzu Halin da ake ciki Hajiya
Atika da kan ta ta fara Yabaawa aya zaƙi , don kullum a ciwo take , ta kaima ko wajen falo bata
iya fitowa sai dai kullum a wuri ɗaya a tattare kaman tsumma. Wanda wannan ba Aikin kowa
bane face Na Hajiya Falmata da ta saka a sakar mata da ciwo wanda zai ta cinta har Ajali.
Hasbunallahu wani'imal wakeel... .
Alhaji Adamu ne ya kalli Aminin nasa Malam barau wanda yake cigaba da cewa “ Gaskiya
Alhaji lamarin rayuwar ka da iyalinka babu gaskiya a cikin ta. Wannan wani irin mata ne Allah ya
baka , tabbas rashin Ahali ba dadi , Gashi duk cikar su babu wacce ta taɓa ko ɓatan wata ....sai
dai kowa fa da rashin halinta. Girgiza kai Alhaji Adamu yayi yana furta “ Allah kenan! Shike juya
ma ko wani bawa Al'amarin sa . Kowa da kallon nasa ƙaddarar a rayuwa , Ni kuma wannan
shine ƙaddara ta. Yanzu ba abun da na kama na samu sauƙi da matan nan da ya wuce karatun
Alkur'ani. Wallahi ƙur'ani kariya ce babba barau, A da baya kai ka isa ka faɗa mun Aibun mata
na musamman ka haɗa da Hajiya Falmata , don ji nake gaba ɗaya ƙwaƙwalwata tamkar ba
nawa ba. Amma a yanzu Alhamdulillah wallahi Ni ban ƙi duka na rabu dasu ba na zauna Ni
kaɗai har mutuwa don na cire ma raina ganin wani daga cikin a halina ”..... subhanallah! Kayya
Alhaji....Don Allah ka bar wannan maganan , Addu'ar mu ba zata taɓa faɗi ƙasa banza ba.
Shiru Alhaji Adamu yayi yana ɗan tunani kana yace “ Wallahi ji nake kamar na taɓa rayuwa da
Iyali na , Tom idan haka ne a yanzu ko suna Wani hali? Shin ina da Yara ko kuwa ma babu su ,
kamar yanda nake a yanzu? . Cike da ƙwantar masa da hankali Malam barau ya furta “ Kayi
haƙuri Alhaji komai bai gagari Allah ba , mu cigaba da fauwala masa al'amaran mu ”.
Saurin kallon malam barau Alhaji Adamu yayi sakamakon jin hayaniyar da ya karaɗe farfajiyar
gidan .
Subhanallah meke faruwa kuma ? Allah dai yasa lafiya! Mu fita daga Waje....Alhaji Adamu ya
furta yana ƙoƙarin miƙewa daga ƙayataccen kujeran da yake zaune . A'a Alhaji ka zauna ,kai da
kake fama da jiki ,Bara Ni na leƙa na gani . Barau ya katse shi yana miƙewa. Girgiza kai Alhaji
Adamu yayi yana cewa “ A'a ko ɗaya mu tafi dai tare zai fi ” .
A farfajiyar gidan Alhaji Adamu kuwa yan aikin gidan ne cike da su Hajiya Falmata da Turai
matar Alhaji Adamu ta uku . Kowa na sallami tare da faɗin Albarkacin bakin sa bisa ga Ganin
Basiru da suka yi ya zauna a ƙasa yana zunduma ihu tare da tsine ma Rabi , yana tona ashirin
duk abun da suke yi , Tare da fashewa da kuka yana cewa “ Ashe tana da cutar karya garkuwar
jiki HIV . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un......Kalmar da kake ji mata nayi kenan suna tafe hannu .
Ihu yake yana karawa yana me yasa Rabi zaki mun haka ? Rabi kin cuce Ni.
Ran Malam barau ne ya ɓaci da tun da suka iso wurin basu yi magana ba suna sauraren duk
abun da ke faruwa. Muryar Hajiya Falmata ce ya katse su tana cewa “ To ai sai a kira Uwar
ɗakin ta Atika , tazo taji Ashe Ƴar ɗakin nata Cutar ƙanjamau take dashi. Tafe hannu Bibbiyu
Turai tayi tana cewa “ To ko dai itama ƙanjamau ɗin ne da ita , Wannan jinya ta fara
yawa......Ahirr! Ya ishe Ni haka!! Muryar Alhaji Adamu ya katse su cikin fushi da tsaye . Wannan
wani irin shashanci ne kuke yi haka . Kowa ta wuce ta bani wuri. Nan take kowa ta juya , da
makarƙabanta . Shi kam Barau cike da fushi ya faɗa Basiru da faɗa da zagin ƙwal kana yace “
Idan ba kai cikakken Mara kunya ba , ku gama lalata kazo kana faɗa mana anan uban me
zamuyi maka. Wallahi duk ranan da ka sake dawowa cikin gidan nan sai na Saka An yi maka
raga raga dukan da tun da uwarka ta kawo duniya babu wani mahaluƙi da ya taɓa yi maka tashi
ka fice mawa mutane tantirin banza.
**
11:am (Lagos)
Jirgin su ya sauka .
Don dama da Wuri yake son su isa. Bin airport ɗin take da kallo . Kana ta kalli Aliyu dake sauka
stairs ɗin idanun sa cikin baƙar gilashin nan nasa na Rashin kirki . Murmushi yayi mata yana kai
hannun sa tare da riƙo nata, a hankali ya ɗan rage Tsawon sa zuwa saitin kunnen ta yana furta “
Ina sonki Ma'eesha....Allah ya taimaka mami ta Bani ke da ƙyaaar...” Huwwwmmm Numfashi ta
sauke ba tare da tace masa komai ba , don a yanzu duk wannan surutun nata ta ne meshi ta
rasa. Ko me yasa? .
Wani irin kallo tayi masa cikin sauri tana bin Motocin da ta gani na sojoji da kallo , kaman Wani
Shugaban ƙasa. Motoci ne kusan 12 , guda 7 duka sojoji ne a ciki ....Wayyo Uncle mu gudu
sojojin nan fa basu da imani baka fuskokin su ba? . Ta furta maganan ita sam ta manta Uncle
ɗin nata fa Soja ne babba. Don a gida take ganin sa bata san shi ba a waje. Hannu tasa tana
shigewa jikin sa tare da ƙanƙane shi tana furta “ Uncle tsoro nake ji bindigogi ne fa a hannun
su”. Murmushi yayi yana yin ƙasa da Muryar sa kana yace “ Babu abun da zasu yi Miki kin
manta Uncle Aliyu shima soja ne ? Mu tafi kinji ki saki jiki. Cike da Yarinta ta sakin masa
murmushi don ita sam ta manta ta burkice gaba ɗaya . Oho yanzu na tuna, to mu tafi. Ta furta
tana kokarin sauya hanya ba inda Sojojin suke jiran su ba .....Hannun sa yasa yana riƙota tare
da nufar motocin nasu, Ma'eesha kuwa duk...............!
[1/28, 5:24 AM] Real~Mamanteddy: *RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
70-71
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500
Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko
katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number
09061466409....✍#Mamanteddy#mrsusm.* Book 3
Duk ta rikice sosai ta manne da jikin sa , gani tayi sojojin na ƙame masa wasu na buɗe masu
moton , ita ta fara shiga , kana ya shima ya shigo daga baya yana zama tayi saurin ƙwantar da
kan ta bisa ƙirjinsa. Murmushi yayi yana kai hannun sa tare da Shafa bayan ta a hankali ya
furta “ Ashe dama kina da Tsoro, ai na ɗauka masu surutu irin naki basa da Tsoro haka”. shiru
tayi tana ƙara maƙale masa kana tace “ Uncle ba dai Laifi mukayi ba ko?”. Duk da shi ba mutum
bane ma'abocin dariya amma a wannan karon sai da ya dara . Kawai sai ya girgiza kai yana
ɗaura laɓɓansa a saman Goshin ta yana sumbatar ta . Abun da Ma'eesha ba ta sani ba shine ,
wannan tafiyar da sukayo na masa ƙarin matsayi ne zuwa Major a soja. Mami da Daddy sun
san da hakan , amma ita Bata sani ba sam , kuma ganin yana da mata yasa Mami a wannan
karon cewa su taho taren da Ma'eesha zai fi . To pah yanzu Ma'eesha ta ga rundunar sojoji to
ya zata yi kuma kenan? Gashi a Bisa abin da bata sani ba ma sam.
A wani irin babban wuri taga motocin sun tsaya. Inda Aliyu ya ɗago yana kallon ta tare da shafa
fuskar ta yana ɗan sakar mata murmushi. Ki dakata anan yanzu zan je na dawo ”. Ya furta yana
miƙa ƙafarsa tare da ficewa daga cikin moton yana barin Ma'eesha da take ta bin wurin da kallo
.....Mutane ne sun fi yawan da ba zasu ƙirgu ba . Duk da sojoji sun fi yawa kowa da kakin sa .
Wannan ya tabbatar mata da taron sojoji ake yi. Dan komawa tayi ta ƙwantar da kan ta jikin
seat ɗin tana furta “ ai Uncle ka zaɓa ma makanka zaman lafiya , ina zan fito a wannan
rundunar jibi yanda kowa ya riƙe bindiga yazo a harboni a kashe banxa, ko a rashin sani ne ko
da gangar Soja ya kashe ka fa an ce ya kashe banxa a wofi , ai gwara na zauna anan Allah ya
taimaka kaima ALLAH dai ya dawo da kai.........tunanin ta ne ya katse sakamakon ganin Aliyu
Haidar da tayi ya buɗe moton yana cikin kakin sa na soja ,bayan sa sojoji ne ke bin sa. Taho
muje daga can mu zauna”. Taso ta ce a'a ,amma ganin sojojin dake bayan sa yasa ta
saukowa a hankali tana gyara mayafin kannta da tayi rolling don dama ita Tafiye saka Abaya for
all the time kayan sun fi burgeta ko a yanzu wani Black abaya ne jikin ta Wanda akayi masa
Adon flower da red. Zama tayi a tare dashi a wani side da ban da aka ware masu , inda take
bin komai na Wurin da kallon tsanaki. Zaman su kenan taji an fara kiran sunan Uncle ɗin nata
kamar haka “ MAJOR ALIYU SALEH YELWA...” kallon sa tayi a maimakon taji an yi tafi sai gani
tayi Sojojin suna masa fareti na girma tare da Sarawa suna ƙamewa . A hankali yayi mata
magana a kunne yana mikewa cikin zumma irin nashi tare da nufar can high table. Ita dai har
yanzu ta kasa fahimtar inda wannan al'amuran suka dosa. Major naji fa yace ? Ba Canonel
bane ? Yaushe ne Uncle ya koma Major kuma? .hummm Numfasawa tayi tana kallon direction
ɗin can da yake . Kana ta kalli inda ya miƙe yanzu. Saurin kai hannun ta tayi tana Ɗaukar
littafin da ta gani da alama ya manta dashi ne . Diary book.! Ta furta a sarari kana ta riƙe tana
cigaba da jin jawabinsa da Manyan General a sojojin ke yi tana saurara . Kusan mintuna sha
biyar kana ta buɗe Lemu tana fara sha don ta fara gajiya da zama .
“.....Humwwwmm Sauke numfashi tayi tana kai hannun ta haka kawai tare da buɗe diary ɗin a
cewan ta zama ya isheta sai tana ganin sa tamkar story book ne. A lokaci daya fuskar ta ya
sauya idanun ta da take lumshe su tana ƙara ware su. Farko kuma mafari~ ta ga ya rubuta da
shekara ta 2008 . Wannan shine fara rubutun diary book Dina na farko a duniya a wannan
shekara . A ranar wata Talata na........Labarin Ta ne ciki tun daga Farkon yanda ya tsinceta da
yanda yayi Rainon ta . Kai har murmushi idan tayi ko taci Abu sai ya rubuta yau Ma'eesha na
taci Abu kaza kuma taji dadi ,nan gaba Irin shi za'a rinƙa yi mata . Yau Ma'eesha ta fara zuwa
skull da dabara na irin na kaza da kaza. Kar ka takaf labarin duk abun da ya faru take
karantawa , Wanda kamin tayi Rabi tuni ta jiƙe da hawaye har da su sharɓan majinu tana
sharewa da Hanckie . Wani irin kuka ta fashe dashi tana furta “ Why dad! Me yasa zaka nemi
kashe shi , Ni baku kashe Ni ba? Kuka dinga azabtar dashi ....Wayyo Ni Ma'eesha ta furta tana
sakin kuka a hankali mai taɓa zuciya da karya ta. Saurin juyawa tayi tana juya baya yanda Ali
ba zai iya hangota ba tana cigaba da karanta diary ɗin .....”
**
Bin Nasreen da kallo Mami ke yi inda take karkaɗa a tsakiyar falon ta . Mamaki ne ya kama
Hajiya Hajara wacce bata daɗe da isowa gidan ba . Keeee wacece ke? Kalmar da Jidder tayi
kenan cike da Tsiwa da masifa irin nata . Wani irin kallo Nasreen ta watsa mata , kana ta saki
Murmushi na yan bariki tana cewa “ Ayyya ƙanwata Yayan naki Haidar bai taɓa baki labarina ba
, ikon Allah! To sunana Nasreen , kuma nice matar da zai Aura nan kusa!
Topa! Jidder ta furta a wulaƙance tana bin Nasreen da wani matsiyacin kallo . Kana tace “
ammm To munji zaki iya tafiya ko sai na saka an fitar dake babu mutunci ?” . Jidder! Mami ta
furta tana ƙoƙarin magana Hajiya Hajara ta katse ta da cewa “ A'a ai barta tun da itama tazo
mana da rashin kunya ai sai ayi maganin ta . To ko Ali ya rasa mata ba zai Aure ki ba , ai gwara
mara Asalin da ya Aura akan ki , don ko ba komai mun san halinta mai kyau da ko mara kyau .
Amma ke ji bita da Allah , Mom Hajara ta furta tana bin Attachment ɗin kan Nasreen da kallo .
Ke dattijiwa shiga taitayin ki , idan ba haka ba zan nuna Miki ƙarshen rashin kunya ta! Kamin ta
rufe baki ne jidder ta ɗaga hannu tana tsinke fuskar Nasreen da mari ji kake tassssss dai dai
Khalil wanda ke shigowa yana furta “ Da ƙyau.....! masifa!
Ni kika mara ? Kin san Wacce Ni Nasreen? Ko ke Wacce an mare ki , aka ce miki ina ɗaukar
wargi ne ke Wacce da zaki shigo har cikin gida ki nemi cin ma iyaye na mutumcu and kina
expecting ki fita kisha lafiya . To ko iyayen ki ne basu isa ba bare ke!
Jidder ta furta cike da Masifar ta .
Murmushi Mom Hajara tayi tana cewa “ Khalil ku fice mun da Wannan mara kunyar yarinyar ,
Sannan Ni da iyayen ta xanyi , a cikin a wa biyu nake so ku bin ciko mun komai nata , Dama
ance ɗan kuka mai ja ma uwa da uba . Zaki san wacece Hajiya Hajara , zaki ga yanda iyayenki
zasu taho su dafa ƙafana su na bada haƙuri fice mun da gani tabbatacciya”. Mom Hajara ta
furta cikin Tsawa , inda Nasreen dake dafe da kunci ta furta “ Zan fita , amma wallahi rayuwar
ku sai na jefa ta cikin masifa, sannan kuma ba zaku taɓa gane kan gadon ɗan ku ba har abada ,
sai dai idan ya Aure Ni zaku ma ku gani”.
[1/28, 8:12 AM] Real~Mamanteddy: *RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
72-73
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500
Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko
katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number
09061466409....✍#Mamanteddy#mrsusm.* Book 3
Tana furta hakan da sauri ta juya cike da ƙafa tana ficewa daga falon . Bin ta da kallo mami tayi
kamin ta furta “ Ikon ALLAH! Wannan yarinyar daga ina take haka? Kar ki damu Mami kiyi
Haƙuri, zan sa a binciko mun naga yar gidan uban waye? . Khalil ya furta yana janye idanun sa
daga hanyar da Nasreen ta wuce . Mom Hajara ce ta furta “ a yau nake so ba sai gobe ba!
Murmushi Khalil yayi yana furta “ Kiyi Haƙuri Momy yau inshallah ”. Juyawa yayi yana bin bayan
Nasreen don shima ran sa sosai ya ɓaci da ita .....Bin bayan sa Suka yi da kallo Mami na sauke
wani irin gwauron Numfashi kana tace “ Ya tabbata Ali yana kula watsatstsun mata irin wannan
yarinyar kenan? . Ta furta zancen tana kallon su tare da