Showing 33001 words to 36000 words out of 37792 words

Chapter 12 - Rainon Soja Part 3 Complete Book By Maman Teddy .pdf

04 Nov 2025

488

shigowar da kallo . Nurse Narret ta furta cikin wani irin murya ”. Kallon Ma'eesha
Aliyu yayi kana ya kalli inda Narret ke shigowa da Akwati a hannu tana jaaaaaaa!



*Mmnteddy 08081202932.*
[1/31, 6:15 AM] Real~Mamanteddy: *️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

84-85
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500
Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko
katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number
09061466409....✍#Mamanteddy#mrsusm.*

Book 3
Haɗe giran nan nasa yayi yana murtiƙe fuska tamkar wanda bai taɓa dariya ba . Don tuni yasan
labarin Narret duka kallon ta yake yi , don ƙawarta ta sanar dashi komai har ta ƙaryar ciwon
ma'eeshan . Miƙewa Aliyu yayi yana raba jikin sa da Ma'eesha kana ya kalli Narret dake bin su
duka da Kallo na cikakkun yan duniya tana kallon Ma'eesha ƙasa ƙasa . Me ya kawo ki gidana?
. Ya furta cikin dakakkiyar Muryar sa.

Murmushi Narret tayi kana tace “ Fatan kaga tayin soyayya ta ”.

Na gani sai aka yi yaya? Fice mun daga gida bana son sake ganin ki a rayuwata dana iyalina .
Wani irin Abu Narret ta haɗiye kana ta Girgiza kai tana kallon Ma'eesha wacce itama ita take
kallo jiki a sanyaye,don ta tuno da Alƙawarin da tayi ma Narret.

Murmushi Narret tayi tana ƙare mawa ma'eesha kallo kana cikin Wani irin murya ta fara magana
da cewa “ Allah Sarki Yarinya! Gaki kyaƙyƙyawa tabbas ke matace ta nuna ma Sa'a . Amma ki
sani ba zai yiwu Miki ki zauna ki sance tasa har abada ba. Saboda masu so da yawa dole ki
dan matsa wasu su shigo! Takawa tayi tana juyi a tsakiyar falon kana ta cigaba da cewa “ A
wancen lokacin da kin fada mun duka a layi ɗaya muke ai da ban azabtar da Zuciyar ki wurin
faɗa mata irin Soyayyar da nake mawa abun da kuke so da hari ba ...amma ko a yanzu ba abun
damuwa bane , a namiji mijin mace huɗu ne ....yanzu nazo ne a bani ɗaki, kamin na shigo a na
biyu ko uku ko huɗu ....ke idan ma babu Wuri to zai sake ki ya Aure Ni......Kamin ta rufe baki Ita
dai taji saukar marine mai tartsatsin wutaaaa “...tasssss”.

Wani irin tsorata Ma'eesha tayi ganin lokaci guda ya koma mata Aliyun da baya . Narret kuwa
dauke gani tayi na sakanni kana ta furta “ Mari na kayi ?”. Yessss! Na mareki komai ma zan iya
Miki Indai bakin ki ya cigaba da furta kalmar cewa “ na rabu da Ma'eesha, daga yau kar Na sake
ganin fuskar ki idan ba haka ba Wallahi sai na karairaya Miki ƙafa ”. Juyawa Ma'eesha tayi da
sauri tana ƙoƙarin Guduwa jikin ta na rawa , carafff taji ya riƙota yana Haɗata da jikin sa tare da
Rungume ta yana shafa bayan ta a gaban narret wacce ta kusa haɗiye ranta don baƙin ciki . Ita
Rayuwata ce! Fice ki bani wuri. Ya furta yana haɗe giran sama da ƙasa. Fuskar sa na huci .
Ganin a tsume yake ya saka Narret saurin juyawa tana furta “ Wallahi ba zan bar ku ba da kai
da ita duka zaku gani...”

Kallon Aliyu ma'eesha tayi hawaye na ciko ƙwarmin idanun ta. Uncle Zan koma gida ”.

Gida!
Ai ke kuma da su Mami sai dai ziyara, wani gidan bayan gaki a gidan mijinki . Ƙwanan nan
zamu wuce Ƙasar Oustralia ina tunanin zan kwana biyu acan, amma anan zaki zauna ba zaki
koma gidan Daddy ba . Ya furta yana kissing ɗin bayan ta. Shiru tayi tana kasa ce masa komai
, don ita gani tayi al'amarin narret ko a jikin sa . Mtswww!!! Wai to Ni sai aka yi yaya? Ya furta
yana ƙara wayar A kunnen sa tare da Sauraren Maganan da Khalil ke faɗa masa na Dawowan
Mijin Mom Hajara .

Alhamdulillah ”. Ali ya furta kana ya datse kiran ya na kallon Ma'eesha tare da cewa “ Kinji an ga
mijin Mom Hajara, alhmdlh kin ga yanzu inshallah zata sakar mana mara muyi fitsari, zata yi
laushi ,don naji labarin yanda take mugun Masifar son mijin nan nata . Kallon shi Ma'eesha tayi
kana tace “ Ɓata yayi ne dama ?. Gyaɗa mata kai Ali yayi kana yace mu zauna na baki labarin
Wacece Mom Hajara da Auren ta da Mai Mata wankin takalmi da yankar fulawa. Ni fa soyayyar
naga bugeni yayi ,wannan shine definition of true love kaman dai soyayyar mu kennn! Aliyu
ya furta yana murmushi Hushiryar sa na bayyana ”.
**

Shiru duka aka yi a falon Hajiya kaka , Dangin Alhaji Adamu, dangin Mom Hajara duka zaune
ana kaji yawa. To Alhamdulillah Allah kenan mai yanda yaso , yau gashi Wai Hajara ce Da
Adamu aka ƙara haɗuwa. Itama yarinyar Allah zai bayyana ta! Hajiya kaka ta furta tana Girgiza
kai na ganin Abin tamkar a mafarki.
Wasu irin hawaye ne suka zubo ma Mom Hajara, a hankali tasa hannun ta tana goge su , kana
tace “ Ina? Ai Hajiya na cire ma kaina ganin Zahra a duniya , sai dai kuma a lahira. Don nasan
ta daɗe da barin duniya....kayya! Muryar Alhaji Adamu ya katse ta , kana cikin girma da
Rarrashi ya furta “ Idan ma ta mutu Allah ya bamu wasu ya'yan masu albarka ”. Yanzu ki natsu
ki kwantar da hankalin ki kisa lokacin da zamu je wurin mata na kuga juna ”.


Ai ko yanzu a shirye Miki Alhaji , da zafi zafi ake bugun ƙarfe ”. Mami ta furta tana kallon su
duka. Ehhh to kuma haka ne . Daddy ya faɗa shima yana kallon dangin Alhaji Adamu ,wanda
suma nan take suka goyi bayan a tafi yanzu zuwa gidan Alhaji Adamu....ko awa wani irin hali
gidan ke ciki a yanzu.......? [1/31, 8:39 AM] Real~Mamanteddy: *️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

86-87
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500
Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko
katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number
09061466409....✍#Mamanteddy#mrsusm.* Book 3
Gidan Alhaji Adamu
Tun daga Wajen gidan ya zamana babu masaka tsinke sai Ɗan Adam da talakawar layi da ya
saba taimaka masu . Da yawa nayi ma ALLAH godiya don sunyi farin cikin Dawowan sa a
hayyacin sa , matan sa kaman ashirin su ya tonu ne don da yawa an sam amanar sa suke ciki
ƙwarai ”. Gawan Hajiya Falmata da aka shiga daga shi ne yasa Alhaji Adamu furta “ Innalillahi
wa'inna ilaihir raji'un.... Lahaula wala ƙuwata, Saurin kama shi Malam Barau yayi yana nufar
ɓarayi daban da shi da sauran su Daddy da suma basu da Labarin Mutuwar nata sai a yanzu .
A takaice Cikin sasan Hajiya Turai suka nufa inda itam a take zaune tsumi kama r wacce ruwa
yaci yacinye ta. Don gaba ɗaya suna Wani hali , ga Hajiya Atika can an sata a ɗaki an rufe tana

hauka tuburan tare da faɗin duk wani abu da ta aikata a rayuwar ta da Alhaji Adamu .

Sai bayan an kai Hajiya Falmata gidan ta na gaskiya ne ,sannan Su Daddy da Abokan Alhaji
Adamu dashi kan sa suka nufi Ɓangaren Hajjiya Turai daga nan suka wuce na Hajiya Atika
anan ne Alhaji Adamu sai da yayi ma kan sa Hawaye. Iraki Mom Hajara ji take kamar ta damƙo
wuyar mahaukaciyar a cewan ta tayi mata dukan Tsiya, Amma haka ta Daure tana kuka ta fice
don sosai mijin ta ya bata tausayi ƙwarai .


Mami taso su zauna amma firrr taƙi zama don dole suka tarkata da cewan zasu yi ta zuwa har a
gaba zaman makoki ayi uku . A kwana ukun nan asiri ne kawai ke tonuwa ta faru ta ƙare , don
dangin Alhaji Adamu suma da kan su sai da suka ce ai rabuwa da duka matan zaiyi , daga
ƙarshe Allah ya bashi mata ta Gari . A haka suka tashi babu tsuntsu bare tarko . Nasreen kuwa
ko dangin mahaifin ta sunƙi amsar ta bare mahaifiyar ta. Yanzu Tasan menene rayuwar
Duniyar?.
**
Tsaye take a bakin ɗakin Chawai inda yake ciki yana sheƙe ayar sa da Ƴammatan sa . Hannu
tasa tana bugun ƙofan wanda kaman mintuna biyar sai gashi ya fito fuska a murtiƙe babu harka
da walwala yana faɗin “ Meye kuma , haba Don Allah mutum yana jin daɗin sa da mata masu
daɗi kinzo kina Wani damun mutane ƙara gaba Malama!
Kallon sa Nasreen tayi jiki a sanyaye kana tace “ Haba Chawai nafi minti arba'in anan Wurin ,
yanzu kuma ka fito kana mun faɗa aka , Chawai ko ka manta wacece Nasreen? . Don kece
Nasreen sai aka yi yaya? Malama ɗan Allah karagaba, kar na sake ganin ki a rayuwata! Duka
munji abun da mahaifiyar ki tayi mawa mijin ta Alhaji Adamu, kai har uban ki ma ance itace ta
kashe shi . Don haka bana son ƙara ganin ki Idan kuma kinƙi ji ba zaki ƙi gani ba”. Ya furta yana
rufo ƙofarsa baaaaammmm tare da barin Nasreen anan Wurin tsaye .......Juyawa nayi ina kare
mata kallo , gaba ɗaya ta sauya kamanni fuska tayi baƙi tayi kanta na talauci da shiga Masifar
rayuwa . Ni kuwa nace dama komai yayi farko zai ƙarshe ,ka ƙulla Alheri sai bayan yayi ƙyau
.wannan kenan!
**
Wow Uncle kayi ƙyau sosai ina zamu je da sanyin Safiyar nan? . Ma'eesha ta furta tana kallon
Aliyu inda ya yayi shigar Sa ta cikakken bahaushe shadda milk an masa ɗinkin zamani ɗinkin
yabi jikin sa yayi ƙyauuuu ƙwarai.


Har wani ɗan ƙiba yayi ƙwana biyu ya aje Ɗan taɓa kaɗan na Hutu da ƙwanciyar hankali .
Murmushi yayi yana kashe mata ido ɗaya tare da cewa “ Yau gidan Mami zamu je ”. Wani irin
farin ciki ne ya kama ma'eesha da Sauri ta kai hannun ta tana Rungume shi tare da tsallen
murna , har yanzu yarintar bai sake ta ba . Murmushin shima yake yi kana yace “ Ai ba daɗewa
zamuyi ba . Kawai saboda ina so mu haɗu da mijin Mom Hajara ne , to zamuyi masu kwana
biyu , don naji Ance An maida Auren ma nasu yanzu haka tana gidan mijin ta. Kuma nan da
Sati Ɗaya za'a daura Auren Khalil da Maryam ”.

“....Hummmm”. Sauke Ajiyar zuciya Ma'eesha tayi kana ta ce “ Yayi ƙyau Uncle , Allah ya kaimu
lokacin ”. Amin ya furta yana riƙe mata hannu tare da nufar Farfajiyar gidan ......! Gidan Mom
Hajara zamu fara zuwa .....ya furta yana raɗa mata a kunne . Ita dai kawai taji gaban ta na ta
faɗi, musamman yawan sunan Mom Hajara da yake kira , kuma gashi tasan yanda ta tsane ta a
rayuwa . Wannan yasa ta yin shiru tana ta tunanin zuciya ita kaɗai don tsoro ne yake kamata.

Bayan sun shiga garin Abuja”.
Ɗaga Wayar sa yayi yana kiran Mom Hajara inda yasa Wayar a amsa kuwa. Hello Mom gamu
a hanya zamu zo Ni da Amaryamatata ”. A lokacin Mom Hajara tana zaune ne a daya
daga companin Alhaji Adamu na shinkafa tana gudanar da Wasu Ayyuka tare da bin
ƙwaƙƙwafin inda yake da maguɗi don ta yi gyara sosai . Gyara zaman Gilashin ta tayi tana
kallon Alhajin nata tare da murmushi, Sai tace “ Alright Kar kazo kuma kayi mun wannan rawar
ƙafar akan yarinyar nan , Wacce kake jin ta tamkar ran ka , da tana da iyaye to da tabbas nace
An shanye ka ne ba a hayyacin ka ka be .


Ƙaassa ma'eesha tayi da ido ƙwallah na turuwa a cikin su. Ɗan cije laɓɓan sa yayi kana yace ”
Mom stop please...ai gaskiya ne....kayya! Wai Da wane kike magana haka Hajara ? Muryar
Alhaji Adamu ya katse ta , inda ta furta “ Da yaro na ne Aliyu , ina masa faɗa ne akan matar sa
da ya Aura ko nace Yarinyar da ya Raina ....Ammmm kana jina Haidar?. Sauke numfashi Aliyu
yayi a ɗan ƙasa ƙasa yace “ Ina jin ki Mom ”. Hunmm na taɓa ƴar zinare ba , dole ka amsa Ni
ƙasa ƙasa . To yau akwai event da za'a fara na Maryam , mu haɗu a guest house ɗin Mamin ka
duka har dashi yanzu zamu nufa can . Duk da taron sai 4:00pm ne , Amma mu tun yanzu zamu
je don a fara komai a idanun mu . Ohk ya furta yana datse wayan tare da danne damuwar sa
kar hankalin Ma'eesha ya tashi...........!
[2/1, 3:35 PM] Real~Mamanteddy: *️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

88-89
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500
Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko
katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number
09061466409....✍#Mamanteddy#mrsusm.* Book 3
Kallon ta yayi yana sakin mata murmushi kana yace “ Guest house zamu wuce yanzu ”. Tom ta
basa amsa fuskar ta ba tare da ta nuna masa Wani damuwa ba.

**
Wani ƙayataccen gida ne mai ƙyaun gaske , Amma girman sa yayi yawa , Don kamar ba guest
house ba . Wannan yasa Idan zasu yi ɗan taro yasu yasu suke zuwa nan. Tun daga Wajen
falon take jin Muryar ta cike da izzan nan nata da mulki wanda sai da gaban Ma'eesha ya yanke
ya faɗi dammmm” . Saurin kai hannun ta tayi tana riƙo Hannun Aliyu wanda Cike da kulawa

yake kallon ta ....idanun ta ne yayi rau-rau , cikin narkakkiyar murya ta furta “ Uncle Bana son
shiga ”. Ma'eesha su Mami ne fa a ciki , kar ki damu ko Mom Hajara ba zata yi Miki komai ba ,
ai yanzu ta rage wasu abubuwan da yawa , taho muje! Ya furta yana kamata tare da riƙe
hannun ta suna shiga cikin tsakiyar falon bakin su ɗauke da Sallama .
Haɗa ido Ma'eesha tayi da Mami wacce daganin ta fara'anta ya ƙaru, Ma'eesha na! Ta kira
sunan ta tana kare mata kallo . Da sauri Ma'eesha ta nufi mami tana Rungume ta tare da furta “
I miss You mami ”. Rungume ta mami tayi tana shafa bayan ta tamkar jaririya a hannu .....Kana
tace “ Lallai Ali ya kula mun dake sosai , kin ga yanda kika yi ƙyau dake Baby na....ko da yake
yanzu babyn Haidar ne kar yayi mun iyaka dariya Aliyu yayi yana zama a ɗaya daga kujerun
dake zagaye kana ya gaishe dasu Daddy da Alhaji Adamu wanda shima ganin su yake ta sakin
Fara'a .

Muryar Jidder ne ya katse su tana cewa “ A'a Momy meke faruwa ne ?”.....duka juyawa suka yi
suna kallon inda Mom Hajara take gaba ɗaya bin Ma'eesha take da Wani irin kallo tamkar zata
cafke ta ....Hajara wannan kallon da kike mawa Aishatu na menene? Muryar Alhaji Adamu ya
katse su. Hummmmm Wani irin Ajiyar zuciya Mom Hajara ta sauke tana miƙewa tare da ƙara
ƙare mawa ma'eesha kallo , kawai sai ta juya ga Alhaji Adamu tana furta “ Ka kalle ta da ƙyau
ko dai idanuna ne? . Ali wannan itace wannan dai Ma'eeshan ko wata ce daban? .

Aaaahhha'aa! Mami ta furta itama tana miƙewa, yayin da Ma'eesha duk sai taji tasha jinin jikin
ta. Yanzu kuma mene zata ce akan ta ? Abun da take Tambayar Zuciyar ta kenan ?. Kaman
Wanda Alhaji Adamu ya san Ma'eesha cikin ƙarfin murya yace “ Ita ce dai gata nan menene
kuma?”.
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un....ta furta tana kallon su duka , Wasu irin marayun ƙasƙantattun
hawaye na zubo ma kuncinta sharrr³. Cikin sauri Jidder ta riƙo Mom Hajara itama tana fara
kukan tare da cewa “ Mom don Allah wai menene? Meke faruwa ne Mommy? . Kallon su tayi
kana ta kalli Ma'eesha wacce ta maƙale jikin Mami....Jan numfashi Mom hajara tayi tare da
cewa “ Wannan ba Ma'eesha Bace! Zahara ce!! Zahara tace!!!

Wani irin kallo su duka suke bin ta dashi , kana Aliyu yace “ Anya Mommy babu matsala kuwa a
tare dake ?.

Gaskiya kam! Mami ta furta tana bin ta da wani irin kallo , kana ta cigaba da cewa “ Ya kamata a
bincike ƙwaƙwalwar Hajara gaskiya da matsala.

Cikin matsanancin damuwa da rashin sanin hujjar ta , ta kalli mijin nata Alhaji Adamu kana tace
“ Ka faɗa musu Wannnan itace Zahra na , ko kai ma ka manta da ƴar da muka haifa ne? Idan
su basu san ta ba kai ai ka san ta! Ta furta cikin ɗaga murya wasu hawayen na daɗa ƙwaranya
mata ”.

Shiru Alhaji Adamu yayi kaman mai nazari ...Gaban Ma'eesha kuwa wani irin faɗuwa yake yi
yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi . Kallon al'amarin take yi kamar a mafarki , Wani irin magana
Mom Hajara ke yi wai itace ƴar ta ? Kai gaskiyar Mami ne da tace a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login