Showing 39001 words to 42000 words out of 137497 words
Chapter 14 - GARGADAN SO Book Complete by Maman AbdulShakur .pdf
hada ido yace “wace irin magana
haka kikeyi Ni’ima”? Mikewa tayi a fusace ta nunashi da hannu tace “don’t you dare lie to me, nasan son
Hawwa kawata kake why are you hiding it? Eh maisa kake boyewa bayan ka kamu da mugun sonta” hade
giran sama dana kasa yayi yadan dafe kanshi yace “kinsan mene? I don’t want your drama this afternoon
I had a long journey I just want to sleep peacefully, dan Allah ki kyaleni I don’t know wat you are talking
about” yajuya zai wuce yanda abu kecin zuciyan Ni’ima batasan sanda tai ihu ba tace “Namiji munafuki,
namiji mara amana, namiji butulu! Aliyu I know everything! I know about hotunan Hawwa dake wayana
da duk ka sace suna wayanka, I know kana stalking friend dina kana biye biyenta kana mata hotuna
without her knowledge, how dare you kana karyata cewa sonta kake don’t be a coward, kaji be a man for
once mayaudari kawai” “Ni’eematullah!” Baban Yaseer yakirata azafafe idanunshi sun kada sunyi ja, yace
“yes yes yes I love Hawwa! Yes inason kawarki! Yes I love your best friend Ni’ima and so what!?” Hannu
Ni’ima takai tadaura kan bakinta tana kallonshi completely heart broken hawaye masu jarababben zafi na
saukowa daga idanunta, yace “do you think I’m happy with the fact that I’ve fallen in love with your
friend? Kin dauka choice dina ne? Kokin dauka son Hawwa ya tambayi izinina? Why are you insulting me
calling me names mena miki? Tayaya na yaudareki? Kinga na sanar da ita ina sonta ne? Ko kinga nayi
wani abu ne? I love Hawwa yes and I also love you! Sabida I don’t wanna hurt you saisa all this years ban
auri Hawwa ba, I can’t bring kaina into to hurting u that much, nasan yanda zakiji, I know wat kishi is! Yes
I love Hawwa, and I also love Ni’ima, nima I don’t know mesa Allah zai dauramin soyayyan kawaye biyu
kuma best friends, I know this same reaction kikeyi maybe na gayama Hawwa ina sonta zatamin more
than yours, so just let me be, ban miki komiba ban yaudareki ba, and bance zan auri Hawwa ba cus nasan
bazata yardaba, but all I know is harna mutu bazan taba daina son Hawwa ba, son danake mata yawuce
tunani na, when it comes to Hawwa banmasan me nakeyi ba, I just want her to always be happy, I want
to protect her, and always be there for her and make her happy, that’s just it” yayi maganan yana
komawa wardrobe yadauki kayan dazaisa yafice daga dakin, Ni’ima tafashe da kuka bana wasaba gwanin
ban tausayi tana zubewa akasan dakin…….
TOH JAMA’A IMAGINE MIJINKI NA SON BEST FRIEND DINKI, YAYA ZAKIJI???
HOW WOULD YOU HANDLE THE SITUATION???
KAI YAYA ZAKIYI NE????
IDAN KECE NI’IMA MEZAKAYI KO YAYA ZAKIYI DA HAWWA???
THINK AND TELL ME
[9/18, 5:03 PM] M Shakur: GARGADAN SO
✍M SHAKUR
EPISODE 2️⃣5️⃣
FOLLOW MY WATTPAD ACCOUNT AKWAI FREE COMPLETE NOVELS DAYAWA AWAJEN KUSHA KARATU
https://www.wattpad.com/user/MSHAKURworld?utm_source=ios&utm_medium=link&utm_content=sh
are_profile&utm_campaign=invitefriends&wp_page=home&wp_uname=MSHAKURworld
Ni’ima kuka kawai take bana wasaba, tana ganin tunda aka haifeta bata taba feeling wannan kalan zafin
da zuciyanta kemata yauba, for years sunyi aure itada Baban Yaseer basu taba having issues ba like
babban issue haka, batada wani complain akanshi but yau yayi hurting nata kwarai, kalan soyayyan
datagani a idanun Aliyu ko ita baitaba mata shi ba, duk soyayyan dazaisa kafara stalking mace kana
bibiyan hotunanta harda na kusan tsiraici ma dan kayan bacci ne ba karaman soyayya bane, soyayya ce
ma dakana bukatan kaga therapist, he is sickly in love with Hawwa that’s idan akwai word din, ciwon son
Hawwa yake, yanzu Hawwan ta Baban Yaseer zaiso? They’ve been through so much together with
Hawwa, Hawwa is her biggest support bazata taba manta sanda Hawwa tasayo mata form na school of
Nursing takawo mata ba, sabida lokacin Babanta baida lpy basuda kudin daza’a saimata form agida haka
Hawwa tadinga dinki tahada kudin tasayo mata form 5k takawo mata that day was the happiest day of
her life, Hawwa tarakata taje tai entrance exam na shiga school of nursing din, dataci Hawwa was
happier than her ma datai jarabawan, bayan 2days aka kirata zuwa interview still Hawwa tabita sukaje
tajirata awajen tayi tafito suka tafi gida dagabaya aka saki admission taci an bata admission, babu kudin
registration Hawwa tadinga dinki day and night, tasaida babban wayanta alokacin tasa sim nata akaramin
waya takawo mata 30k itama Maman Ni’ima tasaida sarkanta da dankunne aka hada 20k daga wajenta
aka hada mata taje tai registration da 50k, the first ever book da pen datai rubutu dashi a school of
nursing Hawwa ta siyamata su, hawaye ta share tana tuna rayuwansu da Hawwa duk yanda mutum zaiyi
tunanin friendship, kawancenta dana Hawwa yawuce haka, sabida kawance ne mai asalin amana,
Hawwa harda Maman Ni’ima take fada akanta just like yanda take fada da Baba akan Hawwa tanajin
haushinsa kan Hawwa haka sukema junansu wajen iyayensu, they supported each other like better half,
kawance su babu ha’inci, babu kyashi ko rowa, babu bakinciki, they’re always happy for each other,
dudda tayi aure Hawwa bata taba mata bakincikin wani abuba, datana da ciki wlh wlh ko Baban Yaseer
mai cikin baikai Hawwa kula da ita ba, idan tana craving wani abu Hawwa zata iya barin aiki taje ta nemo
takawo mata, yanzu haka yaranta su Yaseer sun fison Hawwa kan mahaifiyarta grandmother su sabida
aminci da kaunan dake tsakaninsu, she’s just crying bitterly bamatasan ina zata saka kanta ba, kawai taji
ta bama kanta tausayi bamatasan inda zatasa kanta ba wannan wani irin intertwine situation ne haka?
Wani irin kaddara ne wannan? Ita da Hawwa started friendship ana maganan tun suna around 6yrs old
cus primary one suka hadu, yanzu suna 30yrs, 20yrs plus friendship kifa kanta tayi akafanta tana
shesheka tajiyoshi an budemai gate yafita tasan mosque zashi yau juma’a.
**
Har yamma na rannan Friday din nan shiru ba kiran Ni’ima which is so unlike her, dudda su Ramla dake
damunta da labarai but still binibini Hawwa na duba wayanta ko Ni’ima tamata watsapp message ko kira
ko wani abun amman shiru, tasake kira but still ba amsa dan damunta abin yafarayi sosai.
Bayan sallan magrib suna zaune sunacin abinci duka tare harda Hamza wayan Ammi yahau ringing wayan
ta kalla taga Baba ne hakan yasa tadauki wayan tafito daga dakin dan bataso yaran especially su Ramla
susan maisa Hawwa tazo tawuce ta shiga side nasu Hamza zama tayi kan katifarsu tayi dialing number
Baban ringing daya yadaga ya buga mata sallama yace “ya wajen naku Rukayya” Ammi tace
“Alhamdulillah” ijiyan zuciya Baba yasauke yace “Baban Yaseer ya sanar dani Hawwa na wajenki kice
mata ni ban koreta ba ta tattaro tadawo gidan nan” anatse Ammi tace “sabida kacigaba da tallatata a
masallaci kana neman kai da ita” dan shiru Baba yayi saikuma chan yace “kinga Rukayya ni ba kira nayi
fada dake nayi ba, tun fadanmu na farko bayan rasuwan mahaifiyan yarinyar nan kikaso tafiya da ita nace
a’a kika dinga bala’i dani nasan ba kaunata kikeba da akwai yanda zakiyi ma da rabani zakiyi da yarinyar,
ni duk wannan ba itace matsalata ba kawaidai kice mata tadawo gida kar fushina yabita” dan sauke ijiyan
zuciya Ammi tayi tace “yarinyar nan kawai sabida kaine mahaifinta saisa muka barmaka, wlh na sanar da
Baffan ta saidai duk abinda zai faru yafaru, aure na Allah ne ba nakaba, da iyaye ke aurar da yara da tuni
kowa yayi, Allah shine komi ke hannunsa, kaida yakamata ka godema Allah dayabaka irin wannan yarinya
a’a sai tsalle tsalle kake” katse wayan Baba yayi danshi dama da Ammi basa jituwa kona sakan daya.
Around 8 nadare Hawwa taga Ni’ima na online ta karanta duka messeges nata amman bata kulata ba,
watsapp call ta danna mata but harya katse bata dauka ba abin ya bala’in damunta voice note ta danna
tace “Ni’imyyyyy sorry please kidena fushi, wlh I know kema na sanar dake abinda yafaru ni da Baba you
will not be happy with abinda yayi, banson na tadamiki da hankali koki hanani zuwa wajen Ammi saisa
ban sanar dake ba sorry, ina Yass dina da Meen” ta aika mata voice note din tarike wayan tana kallo
ganin yaje but still ba asaurara ba kuma tana online abin yafara damun Hawwa sosai bahaka Ni’ima ke
fushi da ita ba saidai tai masifa dukansu basu iya gababa saidai suyi fada ayi zage zage da baki a shirya,
dukji tayi ba dadi haka ta tasa wayan agaba tana kallo kusan 20min kuma tana online chan saita sauka
ijiye wayan Hawwa tayi ta kwanta kan gadon Ammi tana sauke ijiyan zuciya.
Yau Saturday Baffa (mijin Ammi) na gidan tun goma dayazo baibarta tahuta ba da labarai da surutai dan
yana mutuwan son Hawwa, tana yawan turamai kudi akai akai kaman yanda takema Ammi ta, surutunsa
yasa tadan manta da damuwanta sai dare kuma tashiga kiran Ni’ima harsaida Ammi talura tace “banji
kinyi waya da Ni’ima tunda kikazo ba da tuni tace abani waya tai magana dani, Ni’ima dana sani da saita
kawo karinki kin shiga hanya da daddare” dan murmushi Hawwa tayi tace “tana hospital ne Ammi shift
take covering, chatting mukafiyi this days Ammi” dan murmushi kawai Ammi tayi bata sake magana ba
tace “bari nakaima Baffan ku shayi” tafice.
Washegari Sunday around 11 tafito su Hamza na samata komi a booth, Baffa yace “Hawwa ayi tuki
ahankali kinjini” murmushi tayi tace “toh Baffa na” Ammi tace “Allah kiyaye hanya, dan Allah banda
gudu” Gyadamata kai Hawwa tayi su Ramla suka rungumeta tamusu sallama tafito, text tama Ni’ima tace
“gani nashiga hanya zan dawo office gobe”.
Karfe biyu dawani abu anadai neman karfe uku Hawwa ta shigo Abuja hanyan hospital din su Ni’ima
tawuce direct ta shiga tai parking ta kashe motan, wayanta tadauka tafito abayane ajikinta baki tawuce
ciki office din Ni’ima tawuce tareda knocking tana budewa wata nurse ce aciki tana ganin Hawwa tai
murmushi tace “wajen Ni’ima kikezo? Bakuyi wayaba ai batanan yau is her off” amutunce Hawwa tace
“okay okay nagode” tajuyo tafito motanta tashiga tafita daga hospital din wlh she’s so worried rabon
datai magana da Ni’ima tun Friday wani irin fushi Ni’ima keyi da ita haka, hanyar gidansu Ni’ima tayi har
zuwa layinsu mai kyau, gaban gidansu ta tsaya tai horn maidaidaicin gidane mai kyau ga babban bakin
gate nasu, lekowa mai gadin yayi Hawwa tadanmai murmushi tana jiran taga yabude gate saitaga yabude
karamin gate da fara’a kan fuskanshi yace “Hajiya barka da yamma” gyadamai kai tayi tace “ya kuke” yace
“Alhamdulillah” saikuma ya tsaya sakaka yana kallonta Hawwa tace “budemin gate ko basanan ne”?
Bazai taba iya maimaita abinda Ni’ima tacemai ma hakan yasa dasauri yace “eh basanan tun safe suka
fita” danjimm Hawwa tayi kaman daga sama sukaji muryan Yasmeen ta tsandala ihu tana kuka wayyo
kafanta dasauri maigadin yakalli gate saikuma yajuyo yasauke kanshi kasa, Hawwa dake juyo muryan
yaran tace “kace basanan ba muryan Mims naji na kuka ba” dan sosa kai yayi da hannu kanshi na kasa
yakasa kallonta yace “ahhhmm Madam tacemini duk randa nakara barinki kika shiga gidan abakin aikina
kiyakuri Hajiya” dasauri da kunya yajuya ya shiga gidan tareda maida gate din yarufe Hawwa tai shiru
tana wajen she don’t even know wat to think, her mind just went blank wlh takai minti ashirin awajen
kafin tadan fuzar da iska taja motan tabar wajen.
[9/18, 5:03 PM] M Shakur: GARGADAN SO
✍M SHAKUR
EPISODE 2️⃣4️⃣
LUKUKU GENERAL ENTERPRISE gidan spices kenan da abubuwa daban daban, babu kalan spices din da
basuda shi, tundagakan su ginger, garlic, tea different kind da sauransu, this is tasted and trusted brand,
chat them up kisai spices now!!!!!
wa.me/+2348095660030
EPISODE 2️⃣4️⃣
Kawai tausayi taji tabama kanta saisa takasa rike hawayen dan tana cikin jarabawan rayuwa, she’s 30
batai aure ba babu miji, kowa is pressuring her, her biggest support, her biggest fan is her best friend
Ni’ima da tun suna yara suke tare, kawancen amana da iyayensu sun zama daya ma, she’s not a small girl
when she sees love she knows love, wani irin kaddarane wannan? Baban Yaseer can never be her amsa
nooo please Ya Allah not my best friend’s husband, ganin hawaye yakasa tsayawa daga idanunta
asanyaye Aliyu yace “I’m here for you, I will forever be right here! Ina taredake Hawwa in good times and
bad times, dare da rana, I’m right here” ahankali yadaura hanky kan fuskanta wani sanyi taji dayasa ta
lumshe idanunta da sauri takai hannunta i ta karbi handky tana goge fuskanta, tadanja majina dadan
ragowan karfin zuciya tace “maisa kabiyoni Baban Yaseer? Nace kabiyoni ne must u follow me
everywhere? Must you get involved in my issues? An gayamaka I can’t take care of myself ne ko I need
your protection”? Ataushashe yana kallonta ganin ranta abace, cikida zazzafan kauna yace “sabida bazan
taba iya bacci ba bayan nasan kina irin wannan hanyan, I care for you” ahankali Hawwa tace “wat if
something happens to you”? Asanyaye yace “I don’t care koma menene yasameni I just wanna keep u
safe” abu tahadiye a wuyanta sai kawai ta juyo ta yunkuro tace “I need to change my tire, spare tire na
booth” matsamata yayi tafito tai booth yabi bayanta tana bude booth din takai hannunta zata dauki
tayan yarigata dauka yace “let’s go muje motana ki zauna” tsayawa tayi tana kallonshi, “muje dan Allah
Hawwa dare ne mu kadai a titi” batai musu ba yayi wajen motanshi da ita yabude mata gaba ta shiga ta
zauna ya maida yarufe sannan yadawo booth nata yaciro supanu yaje gaban motan yana kwance tayan
dayay less, sosai Hawwa take kallonshi kaman yauta fara ganinshi abubuwa da dama suna yawo aranta,
tana zaune awajen saiga yan sanda sunzo wajen fitowa tayi ta nuna musu ID card dinta tayasu gyara
tayan sukayi, suna gamawa Baban Yaseer yabar musu motanshi yabasu kudi su tsaremai sannan yashiga
na Hawwa, hakan yasa ta zagayo ta zauna ya kunna motan yaja waje tajuyar da kanta tana kallo ahankali
yace “do you think is right kije kidan Anty ki middle of the night? Kodai idan mukaje zaria namiki booking
hotel, idan gari yawaye saikije”? Tana kallon waje batare data juyoba tace “zan iya zuwa wajen Ammi na
anytime anyday” gyadamata kai yayi bai sake magana kusan 30min sai chan yace “Hawwa it’s okay not to
be okay” lumshe idanu tayi tabude anatse yace “you got this! Karki bari kalaman Baba natabaki, karki
karaya, I hate seeing you like this” yadan kalleta yanda take kallon waje yace “kinji” gyadamai kai tayi
daganan basu sake magana ba harsukakai zaria, nunamai hanya tadingayi har zuwa wani gida a wani
anguwa mai dan kyau da mutunci, saukowa tayi ta zagayo tadan kalli Baban Yaseer dake kallonta tace
“dan bani car key” zare key motan yayi yabata yana kallonta, a gate tasaka wani key dake jikin motan
tabude kofan tashiga ciki tana sallama tsakar gida ne mai fadin gaske, tourchlight taga an haskewa taji
muryan yan dattijuwa na “waye awajen gate din nan” ana bude kofa da gudu Hawwa tai wajen kofa
matan na bude kofa dadan charbi a hannu Hawwa ta rungumeta da karfi tace “Ammiiii na” ririketa matan
tayi tace “Hasbunallahu wa ni’imal wakeelu Hawwa kece da daddaren nan, ke tashi kiga na ganki lafiya
Hawwa” tadago Hawwa daga jikinta murmushi Hawwa tayi tace “Ammi baban Naseer na waje bani key
gate na bude ya shigo da mota saiya dan zauna zuwa safiya yakoma Abuja” wani dan kallo Ammi tamata
tace “Baban Yaseer kuma? Aliyun Ni’ima”? Gyadamata kai Hawwa tayi Ammi tabata key fita tayi Ammi
itama tafito tana haskawa bude gate din Hawwa tayi yashigo da motan ta maida gate din tarufe Ammi
tace “maraba da Baban Yaseer, sannunku sauko sauko” Saukowa yayi kanshi akasa cikeda kunya yace
“Ammi mun sameku lpy” cikeda fara’a tace “Alhamdulillah ina jikokina? Da y’ata Ni’ima hope duk suna
lpy”? Akunyace ya gyadamata kai yace “Alhamdulillah” murmushi tayi tace “muje nakaika side din su
Baffa ka kwanta bazakabi hanya da tsakar daren nan ba sai idan Allah ya kaimu da safe akawo maka
abinci ne”? Dasauri yace “a’a Ammi dare nayi bana iya kara cin abinci” satan kallon Hawwa yayi dake
gefen Ammi tana wasa da hannunta yamika mata car key ta yace “take” dan dagokai tayi kafin tasa
hannu ta karba Ammi tace “muje” suka wuce suna hira itakuma tawuce wajen motar ta booth taciro
akwatinta ta gu huri ta shiga dashi ciki, bayin Ammi tafada tana cikin wanka Ammi tashigo tasami waje ta
zauna yanda ta ganta haka tasan dawani abu.
Towel din Ammi ta dauro tafito Ammi ta kalleta tace “zonan Jidda” kayan shafanta tadauka tazo kusada
Ammi ta zauna tana bata cream dinta a hannu Ammi ta karba tana sauke ijiyan zuciya tace “meya faru?”
Dan shiru tayi sabida kawai taji komi yadawo mata sabo, hannunta Ammi takama tana shafa mata mai
kafin takalleta strictly tace “ya akayi kike tare da mijin kawarki at this type of time and day Hauwa’u”?
Baki tabude zatai magana saikuma tadan sauke ijiyan zuciya Ammi tace “speak” anatse tace “Ammi wlh I
don’t know cus ni ko kiran Ni’ima ma banyi da abun yafaru ba, probably Baba ne yakirasu to check ko ina
gidansu, saita kirani daga gayamata ina hanya zanzo wajenki hala to shine ta turoshi” Ammi na kallonta ta
sauke ijiyan zuciya tace “Hawwa babu wani naki dabaisan relationship dinki da Ni’ima ba, yarinyar nan
kawar amana ce, yanda kika daukeni haka tadaukeni, don’t ruin friendship naku under no circumstances,
you know maganan danake” gyadamata kai Hawwa tayi tace “nasani Ammi” saikuma ya tashi daga gadon
ahankali zuwa akwatin nata tadauki dogon riga na bacci tasaka ta zare zanin wankan ta shanya ta dawo
gadon tahau ta daura kanta kan cinyan