Showing 3001 words to 6000 words out of 15545 words
nayi maza
nakai tawa inbiyo ki kitchen ɗin".
"toh sekin taho ɗin bara inje so nake yau mu hutar da iya Haire ta huta ta wanke kayan da muka
ɓata".
"toh sena tawo".
nanta shiga toilet itama ta fita.
Tana sauka tashiga store ta ɗebo doyar da zatayi amfani da ita ta fere ta wanke ta ɗora a gas ta
zuba gishiri sannan ta ɗakko eggs ɗinta ta faffashesu ta zuba spieces ɗinta ta yanka albasa
tashiga kaɗa kwan bayan ta kammala ta ɗakko frying fan ta zuba mai ta sauke doyar ta tace
tamaida frying fan ɗinta ta zuba mai yana yin zafi tashiga suya doyar bata wani daɗe ba ta
kammala ta buɗe loka ta ɗakko wasu tsadaddun warmers masu colour ɗin golden ta zuba doya
ta mayar ta rife ta ɗakko napkins ta gogesu tas ta ɗauka kenan ta juya Rahama tashigo saurin
ansar warmers ɗin hannunta tayi tare da cewa"sannu da aiki Aunty nabarki kinata jirana ina
zuwa toilet na hau kan peat kenan zanyi fitsari mezan gani priod ɗina yazo shine kawai na
zarce da wanka gabaki ɗaya sorry My Aunt".
taƙarasa zancenta tana fita dankai warmers ɗin hannunta dining murmushi Inteesar tayi tare da
cewa"bakomai Sis bara inmaida ruwan kunun gyaɗa to".
"la Aunty ashe babban abinda mijinki yakeso zakiyimana kenan".
"eh".
a zuciyarta ko cewa tayi "base in zeshaba ma kumama ai koya kushe aiba donshi nayi ba dan
Ammi nayi ina ruwana ko yasha kar yasha ruwanshi".
nan suka cigaba da aikinsu seda sukayi abincicika da yawa suka shirya su tsaf a dining sannan
suka tafi shiryawa.
10:300am
Fuskar nan kamar kullum a haɗe take tafiya yake cikin takun zaratan maza masu ji da class har
ya isa part ɗin Abbih yana isa yayi knocking Abbih dake zaune a dining ne yabashi izinin shiga
nanya buɗe yashiga bakinsa ɗauke da sallama ƙasa-ƙasa domin idan ba kasa kunne kayi ba
bazakasan ma yayi ba ƙarasawa yayi dining ɗin cikin ladabi ya duƙa tare da cewa"Abbih barka
da asuba antashi lafiya".
"lafiya ƙlau Son yajikin naka miƙe ka zauna muci abinci".
"naji sauƙi".
nan ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun dining ɗin yayi servung ɗin kansa yana kai loma
ɗaya ya lumshe ido saboda baƙaramun daɗi kunun gyaɗar yayimasa ba nana yashiga sha yana
tsikarar doya seda yaci sosai sannan ya ture plate ɗin ya zari tissue ya goge bakinsa yayi
gyaran murya haɗe da cewa"amm dama Abbih jibi idan Allah yakaimu zamu tafi Spain ɗinnan
ɗazu su Ahmad suke sanar dani shine nace bari insanar dakai muji yadda za'ai".
"masha Allah,Allah yabada sa'ah ka dawa zaka tafi".
"ni kaɗai ne sesu Ahmad da matansu".
haɗe rai Abbib yayi lokaci ɗaya tare da cewa"tokai wazaka barwa taka matar?".
murmushin gefan baki yayi ba tare da Abbih ya lura ba a zuciyarsa yace"anzo gurin hmm
yarinya bakiga komai ba yanzu zakisan wanda kika taɓo".
a fili kuma sosa ƙeya yayi kamar gaske alamun waishi me kunya yace"ai gani nayi kamar tafi
son zama da Ammih shiyasa nikuma banason na takurawa ƴar amanarka".
sauke numfashi Abbih yayi domin da yaɗauka Namijin duniya aibata Inteesar zeyi seyaji
saɓanin haka ƙara faɗaɗa murmushinsa yayi tare da cewa"banda abunka mesunan Manya
yaza'ai kabarta anan bayan kasan gasar nan dole se mutum yanada aure zeyi ka ɗauki matarka
ku tafi Allah ya dawomana daku lafiya ka kula da ita sosai dukda nasan banda haufi kanka
amma dan Allah inaso ka riƙe Aishatu amana idan ka wulaƙantata tamkar ni ka wulaƙanta
insha Allahu bazakayi danasanin aurennanba".
"godiya nake Abbih Allah yaƙara girma ameen insha Allahu zan riƙeta amana".
"yauwa sannan zuwa gobe ka shirya ka ɗauketa kuje tayiwa gidansu sallama".
"toh Allah yakaimu ni zan wuce".
"toh Allah yayimuku albarka Allah kuma yabaku zuri'ah ɗayyiba".
"ameen ya Allah".
nan ya wuce ya tafi yana mejin wani farin ciki ya lulluɓeshi yana fita ɓangarensa ya nufa direct
ya wuce toilet.
Zaune take a falo ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana danna waya bugu ɗaya aka ɗauka daga
ɗaya ɓangaren ne akace"salamu alaikum".
"wa'alaiki salam oyoyo Bestyna nayi missing ɗinki".
a zabure Hauwah ta tashi zaune daga kwancen da take cikin murna tace"Ammih wallahi
Bestyna miss you too Bestyna mu muna nan hankalinmu yakai ƙololuwar tashi kar muje Abbah
saidake yayi lafiyarki dai ƙlau ko".
murmushi Inteesar tayi tare da cewa"kice kina gidama kenan lafiya Alhamdulillah yasu Ammih
dasu Mummy dasu Ummah".
"duk lafiyarmu ƙlau amma waɗannan gayyar tsiyar kuma bansanmusu ba".
"kai Besty kice hali na nan kenan".
"eyi se abinda ma ya cigaba Besty wai wa kika aura ne ke ai zancewa halinki na nan na
mutuwar zuciyar nan taki ni wallahi har kin bani haushi wallahi Allah bakije kinayin wannan
sakarcin naki a gidan naki ba".
sauke numfashe me zafi Inteesar tayi cikin yanayin dake fallasa tana cikin tsananin damuwa
tace"Besty ai ƙara shiga uku nayi ni wallahi har gwarama masifar Umman su Jameelah akan
wannan dana faɗa narasa meke bibiyar rayuwata daga wannan ƙaddarar se wannan Besty ku
tayani da Addu'ah Allah yabani ikon cinye wannanma". taƙarasa zancenta tare da sakemata wani marayan kuka cikin tsananin tashin hankali Hauwah
tacewa babbar aminiyartata"Besty wai wayene".
murya na rawa tace"waye mana Besty banda Namijin duniya".
a zabure Hauwah ta miƙe tare da cewa"bangane ba wanne Namijin duniyar".
"wanda dai kika sani Abdallah Besty ina cikin tashin hankali".
murna tashiga yi tana cewa"Allah mungodemaka dama haka Allah yake ikonsa Bestyna ta haye
wayo bara inkwaso shoki".
tana magana tana rawa a harzuƙe Inteesar tace"wake Besty meke damunki ne ya infaɗimiki
damuwata inji kuma kina murna kamar baki damu da damuwata ba".
cikin murna Inteesar tace"Besty dole kijini ina murna Allah mungodemaka daka canzawa
ƙawata da mijin da kowacce ɗiya ke burin samu wayyo Allah daɗi kasheni ishara ce Allah ya
nunamusu Allah ne ya duba zuciyarki yabaki mafiyin wannan jakin".
"da Allah ni bani su Ammih tunda bazaki tayani baƙin ciki ba".
miƙawa Ammih wayar Hauwah tayi tanata tsalle tana kwaso shoki nan suka gaisa da Ammih
tabasu labarin duk abinda yafaru sosai sukaji daɗi nan sukayi sallama Khadija na shigowa ɗaki
ta dawo daga islamiyya Hauwah tabata labari suka haɗu sukaita murna nan Hauwah ta fito
tsakar gida.
Tana aje wayarta kashe wayarta Ammih na fitowa daga Bedroom ɗinta zama tayi kusa da
Inteesar tare da cewa!!!!!!!!
Votes and Comments
_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_zo.*_# Real eeshow
_*Paidbook,Amount Nml grp 300,Vip 800,pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar
Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai
kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_
Book 2
6️⃣7️⃣➡️6️⃣8️⃣
"Ki shirya inji Abbih ɗinku jibi idan Allah yakaimu da rai da lafiya zaku wuce ƙasar
Spain keda mijinki zasuyi wata gasa da har yace a kyaleki dan bayaso ya takuramiki yaga
kamar kinfi son zama kusa dani shine muka yanke hukuncin gwara ku tafi tunda dama gasar
dole se mutum yanada mata sannan kuma kema kyaga gari". tunda Ammih tafara magana Inteesar tayi shiru tafaɗa duniyar tinani domin tasan dagayya yace
bayason ya takuramata dan yasan dole za'ah ce ya tafi da ita taɓata Ammih tayi tare da
cewa"lafiya daughter kikayi shiru ko bakya son binsa ne naga kinshiga tinani inbakyason binsa
bazamu takuramiki ba kifaɗa domin babu me takuramiki kinada right karkiga idanmu kibisa
inkinsa bakyason binsa ki faɗamun kanki tsaye kinji ɗiyata?".
a sanyaye Inteesar ta girgizamata kai tare da cewa"zanbishi Ammih".
"masha Allah nagode ɗiyata Allah yayimuku albarka yabaku zaman lafiya da zuri'ah tagari".
cikin sanyin murya tace"Ameen ya Allah Ammi kidenamun godiya yazama wajibi a gareni
inyimiki biyayya kamar yadda zanyiwa Ummih saboda kema uwace a gareni ba abinda zaki
nema a gurina inkasa yimiki shi matsawar inada halin yi insha Allahu".
"hakane kam ɗiyata Allah yayimuku albarka".
"Ameen ya Allah meza'ah dafa da rana".
"oh ɗiyata bakya gajiya aida kinbari Haire tayi kin huta domin kinga tun asuba kike abu ɗaya
kamar wata inji".
"ai Ammih ba'ah gajiya da aikin lada bare ɗan wannan aikin duka nawa yake dazan gaji
kumama ai kozan gaji da komai bazan gaji da aikin uwata maganin kukana ba".
"haka ne ɗiyata Allah yayimiki albarka ki dafa duk abinda kikaga ya dace ni bara na wuce inɗan
kwanta domin wani bacci-bacci nakeji a idona au kuma yace gobe kishirya Mesunan Manya
zekaiki kiyiwa su Ummihnku sallama".
"toh Allah yakaimu".
"Ameen".
nan Ammih ta haye sama tabarta nan tana jimamin yadda za'ai su zauna da Namijin duniya
inuwa ɗaya furzar da numfashi tayi me zafi tare da cewa"gaskiya ƙila wata kitumurmurar yake
ƙoƙarin haɗamun domin nidai a iya sanina idan da za'ah ce Namijin duniya ya nuna babban
abinda yake ƙi da tsana baze wuce ni ba amma wai shine ke cewa Abbih wai bayason ya
takuramun kai gaskiya da sakal anbawa me kaza kai ƙila dai wata muguntar yake shirin
haɗamun koma dai menene Allah yafishi ni yanzu nadena biyemasa ko yankani zeyi insha
Allahu bazan kulashi ba idan ya gaji ya bari".
nan tayita tufka da warwara daga ƙashe ta tashi tashiga kitchen tafara haɗamusu lunch.
Ɓangaren Zaid da Jameelah ko abin ba'ah cewa komai domin da asubar fari Zaid ya sunkuci
Jameelah yakaita toilet yasakata a ruwan zafi dukda ko ƙarar nan da amare keyi ita be damuba
sema jikinsa daketa tsuma akanta kafin tace abu yayimata jikinsa na ɓari seda yagama gasata
tas sannan yabarta tayi wankan tsarki tana gamawa ya naɗeta cikin towel kamar wata ƴa baby
be direta ko ina ba sekan chair ɗin dressing mirrior yazauna tare da ɗorata akan cinyarsa yasa
yaɗauki ƙaramin towel yashiga gwaggogemata jikinta sannan ya shafeta da tsadaddun lotions
ɗinsa yashamata powder tafito ras da ita ya tashi da ita a jikinsa ya ɗorata kan bed ya buɗe
wardrobe ya ɗakkomata wata doguwar riga mara nauyi da bra da pant yabata tare da
cewa"Baby bara nima inje inyo nawa wankan kisaka kafin indawo".
"toh".
nanya wuce toilet itakuma ta shirya cikin wannan tsadaddiyar doguwar rigar ta wani harɗe akan
domin baƙaramin haushin Zaid takeji ba nayimata ɗanɗani haukacin da yayimata bewani jimaba
yafito shima ya goge jikinsa da towel yashafa mayukansa yasaka wata haɗaɗɗiyar jallabiya fara
sol da ita cikin kulawa yaƙarasa inda take yakama hannunta yana murzawa yace"Baby bara
intafi masallaci ki tashi kiyi sallah sorry ko nagaji dake ko".
girgizamasa kai tayi tare ƙara narkemasa tace"a'ah bakomai Sweetheart aiba a gajiya da aikin
lada seka dawo nima bara natashi nayi".
"yauwa Baby ki kulamun da kanki ".
"kaima haka bye".
nan ya tafi ta rakashi da harara tare da buga uban tsaki tace"gajiyar ubanka kasa nayi bayan ko
gama shigata bakayi ba saboda kai rago ne yafita zakawani kagaji dani aiko dole na nemowa
kaina mafita domin bazan zauna da hotiho ba mara amfani ba Haliru kawai zan riƙa nemowa
yariƙa biyamun buƙatata ina biyansa kuɗi shege mekyan ɗan maciji bawata sallah dazanyi a
wannan halin da nake ciki sede kuma ta anjuma".
nan tayi kwanciyarta tana yamutsa jikinta domin baƙaramar sha'awa Zaid ya tasarmata ba.
Ɓangaren Zaid ko suna fitowa daga masallaci ya tafi cikin gidansu dan gaida mahaifansa a
falon ƙasa yasamu Abbanshi da Mummynshi suna hira suna ganinshi suka haɗe rai domin
tunda yayimusu wannan abun suka fita sabgarshi ƙarasawa yayi bedamu da yadda suka
haɗemasa rai ba yazauna akan carpet tare da cewa"Ina kwananku". a ciki-ciki suka ce"lafiya ƙlau".
miƙewa Abbih yayi tare da cewa"ni bara in hau sama".
"toh nima yanzu zan hawo".
cewar Mummyn shi nan Abbah ya haye sama gurin ya rage daga shi se Mummyn shi itama
kuma danna wayarta takeyi tayi banza dashi dube-dube yashiga yi tare da cewa"Mummy ina
Sis take".
ba tare data ɗago daga chart ɗin da takeyi ba tace"tana ɗakinta lafiya".
"lafiya ƙlau Mummy dama gani nayi banganta ba shiyasa na tambayeta".
"ok".
nanya miƙe ya haye sama be zame ko inaba se bedroom ɗin Maryam yana murɗa handle ɗin
ƙofar yaji ta buɗe yashiga yamaida ƙofar ya rife akan gado yasameta kwance tana chart idonta
biyu wata uwar harara ya watsamata haɗe da cewa"kee wato saboda kin rainani shine zaki
zazzagi mata ta ko to tashi dan kutumar ubanki kije ki bata haƙuri inba haka ba in tattakaki". sosai Maryam tayi mamakin yadda ya haƙiƙance kan Jameelah yake cemata ze karairayata
harda zaginta abinda tunda take da yayenta ko zaginta da wasa be taɓayi ba yau gashi kan
wata banza yana zaginta dole tayi maganinta tana tsaka da wannan tinanin taji yaƙara
cewa"wallahi na buɗe idona naganki baki tafi kinbata haƙuri ba wallahi se jikinki yafaɗamiki
saura kuma ki faɗawa Mummy kiga yadda zanyi dake kuma ki ɗauki abinci kikaimata".
saurin sauka tayi daka kan gadon tawuce domin taga ba alamun wasa a tattare dashi nan yabi
bayanta a inda yabar Mummy nan suka sameta ƙarasawa yayi inda take tare da cewa"Mummy
abawa Maryam abincinmu takaimana".
sheƙeƙe Mummy take kallonsa domin ita lamarin Zaid har yafara bata tsoro yadda yake rawar
ƙafa kan Jameela ganin Mummy batayi magana ba yasashi jiki na rawa yaje kitchen ya ɗakko
wani basket dayaga anhaɗa ya miƙawa Maryam ta tafi shima yabi bayanta har yakusa fita
Mummy ta dakatar dashi ta hanyar cewa"Zaid zonan". bakan ranshi yaso ba haka ya juya yakoma falon yazauna yayinda rabin hankalinshi gabaki
ɗaya yana ɓangarensa gurin Jameelah cikin tsananin ɓacin rai Mummy tace"kaga Zaid idan
baka bimu a hankali ba wallahi ina gabda saka ka rabu da wannan tambaɗaɗɗiyar yarinyar
mara tarbiyya nasan da Inteesar ce da yanzu tazo tagaidamu amma itako ko arziƙin wannan
bamu samu ba daga gurinta amma saboda kai bakasan ciwonmu ba jikinka har tsuma yakeyi
akaimata abinci ko".
"Mummy kiyi haƙuri Allah ya huci zuciyarki idan muka ci abinci mukayi wanka zamuzo tagaidake
da harta biyoni wai zata zo tagaidake nace tabari indawo semu zo tare amma dan Allah Mummy
kidena cewa zaki rabani da Jameelah zuciyata nakejin kamar zata fashe tanamun zafi idan na
rabu da Jameelah ba makawa mutuwa zanyi Mummy". sosai ran Mummy yaƙara kaiwa ƙololuwar ɓaci tace"dan ubanka wallahi sede ka mutu domin
wallahi seka saketa".
nan Mummy tayita yayyafa ruwan masifa .
Ɓangaren Maryam ko tana shiga ɓangaren Zaid taga Jameelah da ƴar wata guntuwar tsintsiya
ɗayan hannun kuma riƙe da wata roba fara me ɗauke da rubutu baƙiƙirin a ciki tana yayyarfawa
a falo karaf sukayi ido huɗu da Maryam data shigo ko sallama babu saboda tsananin ɓacin ran
Jameelah, Jameelah ko garin gigicewar datayi ne yasa robar rubutun dake hannunta ta kife kif
lokaci ɗaya jikinta yashiga karkarwa domin batayi tsammanin shigowar wani ba a wannan
lokacin saurin aje basket ɗin dake hannunta tayi tare da shaƙo wuyan Jameelah tare da
maƙureta tace"dan ubanki sekin faɗamun ubanme kike yayyarfa mana a gida tsinanniya inma
wani tuggun kika haɗo albarkar Annabi sede yakoma kanki tsinanniya mu da Allah muka dogara
bada wani gardin ba ta Allah ba taki ba yayana yafi ƙarfinki kuma wallahi sena tonamiki asirinki
kowa yasan abinda kikayiwa ɗan uwana aidama munsan sede idan wani abun kikayimasa
amma banda haka me Yah Zaid dake tsinanniya me kama da aljanu".
itako Jameelah ba abinda takeyi se aikun tutturo ƙananun idanunta waje wurgi Maryam tayi da
ita ta nufi cikin gida dan sanar dasu Mummy abinda ke faruwa.
Ɓangaren Zaid ko yamiƙe kenan ze tafi ɓangarensa ya yanke jiki yafaɗi jikake timm da gudu su
Mummy da Maryam dake shugowa sukayi kansa cikin firgici!!!!!
Question?
1-Meyasami Zaid?
MAN OF THE WORLD BOOK 3
Book 3
6⃣9⃣➡7⃣0⃣
Suka haɗa baki gurin cewa"Innalillahi wa'innah ilaihi raji'un Zaid,Yah Zaid ?".
amma ina shiru kakeji domin babu ko alamar numfashi a tattare da Zaid jijjigashi Mummy tashi
ga yi tana kuka tana cewa"Zaid! Zaid!! Zaid!!!".
tanayi tana jijjigashi jin kukansu ne yasa Abbah dake sama saurin sakkowa har yana tuntuɓe
garin sauri ya isa gurin su ganin halin da Zaid ɗin ke ciki ne yasa Abbah saurin juyawa ya nufi
gurin pridge ya buɗe ya ɗauki faro yakoma ya buɗe marfin robar ya shiga yayyafamishi a
hankali ya buɗe idanunsa yashiga bin kowa na gurin da ido kamar wanda yafara ganinsu a
ranar sauke a jiyar zuciya Mummy tayi me ƙarfi tare da cewa"sannu Zaid".
yunƙurawa Zaid yayi ya tashi zaune tare da yin wani ƙasaitaccen murmushi yace"yauwa
Mummy meyafaru ne naga duk hankalinku a tashe lafiya ko wani abun ne yasamu Nisful-hayat
Inteesar ne dan Allah ku faɗamun Mummy kardai kucemun wani abunne yasamu Inteesar
inason Inteesar son da ban taɓa yiwa wani mahaluki ba a duniyar nan banason na rasata
Mummy dan Allah ku faɗamun bakuji yadda zuciyata kemun zafi ba ".
yaƙarasa zancensa yana mai dafe ƙirjinsa .
Kallon juna Mummy da Abbah sukayi suna mamakin sabon rainin hankalin dayazo musu dashi
sosai ran Abbah ya ɓaci ya wurgamasa wata uwar harara ya buɗe baki kenan zeyi magana
sukaji sallamar Muhseen shiru Abbah yayi da maganar dayaso yi tare da cewa "wa'alaika
salam Son ne a gidan namu". cikin girmamawa Muhseen yaƙarasa inda suke tsaye cirko-cirko ya duƙa har ƙasa cikin ladabi
yace"eh nine Abbah ina kwananku".
"lafiya ƙlau yasu Ummahnku ".
"duk lafiya ƙlau suke suna ma gaidaku".
"masha Allah muna amsawa Maryam kawowa Yayanku abun motsa baki".
"toh ".
"a'ah wallahi Mummy a ƙoshe nake ban daɗe da cin abinci ba nace bara inzo ingaidaku inwuce
gurin aiki saboda na kwana biyu banzo ba".
"hakane kam angode Allah yashi albarka ".
"Ameen Mummynmu".
"masha Allah kazauna man bakata tsugunno ba".
"hmmm bakomai Mummy ai sauri nakeyi ma dan banaso 8:30am tayimun bankai gurin aiki