Showing 15001 words to 18000 words out of 31845 words

Chapter 6 - Masarautarmu Book 2 Hausa Book By Takori Kabara .pdf

ta. Daga taimako Sa'ade zata baro musu tashin hankali da yake ita butulu
ce, ina ruwan ta da abinda ke faruwa tsakanin Yarima da matar sa? Bayan ta gargadeta? Sai ta
tuna Sa'aden bata san tana turakar Askirama ba, kuma ita ta bata damar duk halin da take ciki
ko karfe nawa ne ta kira ta ta gaya mata.
"Ba shirme bace Bilkisu..... he has this taboo since childhoood". Ya fada muryar sa abin
tausayi. Har yaran bayi yake raping...na dauka ya bari, na dauka girma ya sa ya nutsu, na
dauka aure ya canza shi...ashe i'm mistaken. To aikin zai bari ya dawo gida kusa da ni kawai ya
karbi sarautar gidan su, in cika masa gida da mata da kwarkwara tunda hakan yake so.....da
raina da lafiya ta bazan bar shi ya karasa rayuwar sa a haka ba........".
The way Mai Askira ke magana ya taba zuciyar Bilkisu, bata taba ganin sa cikin wannan sad
mood din ba. A muryarsa da fuskarsa bakin ciki ne zallah. Ya kare zancen sa da cewa "zan
raba Sa'adatu da gidan sa, tsoro na Allah yanzu tsoro na kada itama ya taba ta......"
"Haba-haba Askirama! Kada bacin rai ya kai ku ga yi masa mugun fata, ni na tabbata ko Yarima
na neman mata bazai nemi na cikin gida ba balle Sa'adatu kanwar sa, don Allah a kyautata
masa zato, kada a raba shi da aikin sa he is very young da karbar sarauta yanzu, sannan kaima
in ka zauna a gida me zaka yi? Da cikar lafiyar ka da shekarun da basu kai 70 ba. A yi masa
hakuri ayi masa addu'a, ita ce kawai mafita. Kuma daga Sa'ade ta fadi abu ai bai kamata mu

yarda ba tunda bamu gani da idon mu ba". Mai Askira yayi murmushi mai ciwo "baki san
Yarima ba!"
Da kyar, da lallashi da ban baki Fulani ta ciwo fushin maimartaba ya fasa cewa Yarima
Sageer ya dawo gida, amma ya ce dole zai dauki mataki. Shi ya gama amincewa Sa'ade ba
karya take ba, ta fadi abinda ta gani ne da abinda ta ji tabbas. Koda ya tura Sa'ade gidan
Yarima yana da dalilin sa, gashi tun ba'a je koina ba zuwan ta ya sa yanzu ya san halin da
Yarima yake ciki.
****
Da asubah Fulani ta koma daki ta kira Sa'ade, wadda ta kwana zungurgur a bakin kofa, ta
dade bata ji ma'auratan sun gama fadan nasu ba, ta ji abubuwa da yawa da suka razanata,
Sultana ta dage in ya takura mata akan shan giya to zata koma addinin ta na Jew (ridda).
Shikuma ya ce ta koma din, amma ta sani muddin ta bar muslunci a bakin auren ta. Zina kuma
yanzu ya fara in ita uwarsa ce ta hana shi. Sa'ade bata taba fadawa tashin hankali irin na yau
ba, ta ji ta tsani Yarima da matar sa bata ko marmarin sake ganin munanan fuskokin su. Kuma
sai gwada wayar Fulani take ta tubure mata azo a dauketa ta kasa samun ta, sai goshin
asubahi sannan ta samu kiranta.
Jiki na rawa ta amsa wayar, cikin kuka tace "Don Allah Fulani....don Annabi ki aiko a dauke
ni, bazan kuma kwana a gidan nan ba, ko na minti daya ban yi barci ba, they are fighting....."
Fulani tace "Ki nutsu Sa'adatu ki saurareni, babu inda zaki, ba ruwanki da fadan su tunda basu
sanya ki a ciki ba, kiyi kamar baki ji komai ba ki cigaba da harkokin karatun ki. You are not there
for Yarima or matar sa, you are here to study. Kada ki kara sauraron maganganun su kin ji na
gaya miki. Yanzu baki san abinda wayar ki ta jawo ba. Askirama ya ji duk abinda kika fada kuma
ya ce sai ya dau mataki akan dan sa, duk akan surutun ki, ina ruwan ki?"
Cikin kuka Sa'ade tace "wallahi ba sauraron su nake ba, ba labe nake musu ba, da karfi suke
magana, ni ina daki na ma" Fulani tace "na fahimta, amma ki kwantar da hankalin ki kin ji? Kiyi
pretending as if baki ji komai ba, fadan mata da miji sai Allah, kwana biyu zaki ga sun shirya.
Tunda dai ba takura miki suke ba to ba ruwan ki dasu" da haka Fulani ta samu ta lallasheta ta
daina kukan, tace tayi alwallah tayi sallah tayi azkar tayi shirin tafiya makaranta.
Yadda Fulani tace ta yi haka ta yi, da misalin karfe 8:30 ta fito rataye da jakarta, tayi shirinta
tsaf. Hannun ta rungume da manyan littafan ta na chemistry. Da Yarima ta fara tozali yana
sipping shayi akan dining, gabadaya ya birkice kamar bashi ba smart guy mai tafiya da imanin
mai kallon sa, gashin kansa ya cukurkude kuma ga dukkan alamu ko wanka bai yi ba. Ta gefen idon ta ta saci kallon sa, a ranta tana fadin how comes this perfect and handsome
gentleman is adulterer? Ga goshin sa har da tabon sujjadah. Watakila matar sa ta dai fada ne
don ta bata masa rai tunda shima ya ce tana shan giya.
Ta dan russuna daga bakin kofar dakin ta ta ce ciki-ciki "barka da asubah". Ya dago
lumsassun idanun shi ya dube ta wadanda suka canza kala zuwa brownish sabida rashin barci.
Ta ki yarda su hada ido ta sunkuyar da kanta wanda hakan ya bashi damar ganin yadda idanun
ta suka tasa, kada dai kuka tayi? Kada dai ta ji fadan su shi da Sultana? Tabbas da ya shiga
uku ya lalace. Murya a cunkushe ya ce "come take your tea" cikin rawar murya ta ce "i'm ok"
tasa kai zata wuce ya daka mata tsawar data firgitata "kina nufin haka za ki fita baki ci komai
ba? Me ya samu idanun ki haka? Have you slept yesterday night?"
Jikin Sa'ade ya soma rawa sabida bai taba yi mata magana cikin tsawa ba. Ta tuna Fulani ta

gargadeta akan ta nuna bata ji komai ba. Sai tayi narai-narai da ido gab take da sakin kuka ta
ce "na tashi da ciwon ciki ne" Yarima ya ji wani irin relief ya sauko masa, ya nuna mata kujerar
dake gefen sa "zauna ki sha tea ko kadan ne, bai kamata ki fita haka ba, sai in baki magani" ta
bi umarnin sa kan ba yadda zata yi, amma kwarai take so ta bar gidan ko ta samu sa'ida. Da kansa ya hada mata tea din, wanda shi ya dafa shi da kansa. Uche ya masa waya cewa
ya tafi garin su Ogun mahaifiyar shi ta rasu a safiyar yau.
Ta karbi tea din da yake mika mata ba don ranta ya so ba, amma kaifin idanun sa da ya tsare
ta dasu ya sa ta kasa kurbar shayin. Yarima ya mike ya bar dining din zuwa dakin sa don ya
bata dama ta sha shayin, ya lura yau wani tsoro-tsoron shi take ji, jiya kuwa har labarin
karatunsu ta bashi. Yana tashi tayi maza ta kurbe shayin, saura kadan ta kware, ya fito a daidai lokacin da ta
mike tana daukar handbag dinta, hannunsa rike da kwalbar gestid. Ya jijjiga ya zuba a murfin ya
mika mata. Hannu na rawa ta karba daidai lokacin da Sultana ta fito daga daki cikin nata shirin
na tafiya ofis. Wani kallon banza tayi musu sannan ta dauke kai ta wuce su fuuuu! Sa'ade na fadin "good
morning aunty" ko kula ta bata yi ba. Salis ya soma horn don ta gane ya iso yana jiranta. Kallon
Yarima tayi ta kasa-kasan ido tana jiran ya bata umarnin tafiya sai ta samu idanun sa a kanta
suke. Da sauri ta kara sadda kanta. Ya ce "in kin dawo kin yi abinci ki sa da ni, Uche ya tafi
garin su Maman sa ta rasu" kai kawai ta gyada tana mamaki a cikin ranta. Ita wacece da zata yi
abincin da Uncle Yarima zai iya ci?
Har suka isa makaranta tana kakabin abin cikin ranta, in matarsa ta ce ta yi mata shishshigi
fa? In Uche baya nan meye amfanin matar sa? Koda yake wannan mai jan kunnen bata taba
ganin ta tana dafa ko da ruwan zafi ba. Gara dai ta fara tambayar Fulani, kada ta yi abinda ba
dai-dai ba. Data gama lectures din yau zata fito ne ta tadda Salis a parking lot ta kira Fulani tana cigaba
da tafiya a gefen hanya, bayan sun gaisa tace "Fulani wai uncle Yarima ne yace yau in zan yi
abinci na in sa da shi, sabida Uche yayi tafiya, ina tsoron kada in yi abinda ba shikenan ba"
Fulani ta yi dan jimm! Kafin ta ce "meye gamin ki da Yariman da har kuke hira?" "Ba hira muke
ba, dazu ne da safe da zan fito ya gaya mini" Fulani ta yi ajiyar zuciya ta ce "Sa'adatu! Ki kula
da kan ki kin ji? Ba zan hana ki bashi abinci ba tunda Yayanki ne, amma bana son wata
mu'amala mai zurfi a tsakanin ku bayan kasancewar shi guardian din ki. Maza duka ba abin
yarda bane you have to be careful!" "To Fulani in ce bazan bayar ba mana? Wani abu ne?"
"A'ah kar ki ce hakan, just cook and keep it on dining ki shige dakin ki, ban yarda da hira mai
tsayi tsakanin ku ba" da haka suka yi sallama. Tana shiga gida ta ajiye littafanta tasa apron ta
shiga kicin.
Girki na nutsuwa ta yi, wanda ta inganta da kayan kamshi na gargajiya, lallausan tuwon
semovita miyar danyar kubewa data ji ganda da busashshen kifi. Sannan ta markada abarba ta
hada da zobo da pinapple flavour. Sai tayi farfesun kayan ciki mai rai da motsi. Sugar kadan ta
sanya. Tana gamawa ta shirya masa a dining ta shige dakin ta ta kulle ta hau yin assignment
din da aka bata yau daga laptop dinta.
Yarima ya riga Sultana dawowa domin data tashi aiki Bar ta wuce ko don ta sauke bacin ran
data kwana ta kuma wuni da shi, domin hakika tana shakkar sake shan giyar a gaban sa don
yadda ta ga ya rikide mata jiya ta san komai zai iya faruwa da auren ta, one thing shine tana

son Yarima bazata iya rabuwa da shi ba.
Yana shigowa falon, falmaran din black Italian suit din jikin sa ya fara cirewa, yayi loosen tie
din wuyan sa, kai tsaye dining ya nufa, a yunwace yake sosai, rabonsa da abinci tun tea din
safe. Yana budewa ya ja kujera ya zauna ya soma ci cikin nutsuwa irin tasa, kunnen sa har wani
irin motsi yake yi. "She's blessed in cooking!"
Ya fada a hankali.
Yana so ya kira ta, bai san in ta zo mai zai ce mata ba, he just want to check she is well, don
haka yasa murya a tausashe ya kira ta.
"Sa'adah!"
Ta ji kiran nasa amma sai ta kasa yarda kiran nata yake yi, it sound so weird, don bai taba
kiranta da wannan sunan ba, sannan amon muryar ya taimaka wajen sawa taji kiran kamar ba
nata bane, don haka ta cigaba da aikin ta, hankalin ta ya rabu biyu, ya kan kirata Sa'adatu ne in
full. Da ya ji shiru kai tsaye ya mike zuwa dakin nata, bayan ya wanke hannun sa a sink din
dake manne a gefen dining din, ya tsane da karamin tawul.
Kanta a sunkuye tana sarrafa na'ura mai kwakwalwar ta, riga da wando ne na pakistan a jikin
ta ruwan goro turarre, ta yane mayafin su a kanta. Bata ji karar bude kofar sa ba sabida yadda
hankalin ta yayi nisa kan abinda take yi. Sai sassanyan kamshin INVICTUS (By Paco
Rabbanne) ya ziyarci hancin ta, ya kuma sauya atmosphere na dakin bakidaya wanda ke
cakude da rabar iya kwandishan. Har gabanta Yarima ya zo ya tsaya hannayen sa biyu zube
cikin aljihu, a hankali Sa'ade ta dago ido sai idon ta cikin na Yarima.....wani abu mai karfi tamkar
magnet ya manne idanun su wuri guda. Yarima Sageer ya tuna wannan kanwar sa ce a gaban
sa (step-sister) kuma amanar mahaifin sa.... amma akwai wasu abubuwa cikin idanun yarinyar
da ke da matukar tasiri akan sa, wadanda yake kasa controlling din su, wadanda bai san yadda
zai fassara su ba. Watakila kyawun idanun ta ne ko hasken da ke cikin su? Juyawa ya yi ya
bata baya don kaucewa kaifin idanun ta. Murya cunkushe ya ce "I just want to check on you.
Have you eaten?" Kai ta gyada duk da ba kallon ta yake ba "zan ci in na gama" ta fada da
sassanyan sauti. Taku daya, biyu yayi kamar zai fita, sai kuma ya juyo gabadayan sa.
"Sa'adatu will you help me with your food har Uche ya dawo?" Ba tare da ta dago ba tana
cigaba da typing din ta ta motsa dan bakin ta a hankali "sai na tambayi Fulani" yadda tayi
maganar innocently ya burgeshi, ta nuna bata da wani ra'ayi kai tsaye sai na uwar ta.
"Fulani bazata hana ki sammin abinci ba, nima uwata ce har fiye da ke" murmushi tayi wanda
ya kara fiddo kyawun karan hancin ta. "Har fiye da ni? Ai daga ni sai Zarah ta haifa. Ka ga kuwa
bata da kamar mu" ya dubeta straight cikin idon ta duk da ba shi take kallo ba "ni ta fara haifa
kafin ta haife ku" murmushin ta ya zarce zuwa dariya "ai watakila ma ka girmeta Uncle Yarima"
"sabida kin ganni da furfura?" "Ni ban gani ba, amma ko baka girme ta ba zakuyi age mates" ya
juya ya fita yana murmushi cikin fadin "i look forward to my dinner Sa'adah. Na bar ki lafiya".
Bin sa ta yi da kallo har ya fice, amma dakin ta bai bar INVICTUS perfume ba. Abinda ta ji
jiya ya fado mata a rai. A fili ta ce "ba kama....". Sannan tayi ajiyar zuciya ta cigaba da aikin ta.
Wannan baturiyar ta yi sa'ar zankadeden miji wanke hannu ka taba, amma don asara ko abinci
bata bashi... tadin Sa'ade kenan ita da zuciyar ta. Ta kira Fulani ta gaya mata yadda sukai da Yarima, Fulani ta shiga dan rudani, ta ce
"Sa'adatu ya ce da ke wani abu bayn wannan?" "Wallahi iya abinda ya fada kawai kenan, sai

cewa kema uwar sa ce har fiye da ni" Fulani ta yi murmushi ta ce "bakomai ki dinga dafa masan
in har kina gida, kinsan turawa basu daukarwa kansu irin wannan wahalar, shikuma watakila
yana marmarin abincin mace ne".
Da wannan Sa'ade ta cigaba da dafawa Yarima Sageer abinci har tsayin kwana uku, wanda
ya haifar da wata 'yar kwarya-kwaryar shakuwa a tsakanin su, duk da Yarima ba sakar mata
fuska yake ba itama kuma hakan, amma yana nuna concern akan al'amarin karatun ta. Da
tabbatar da ta ci abinci akan lokaci don in tasa kwamfuta a gaba mantawa take da cikin ta. Aisha Sultana bata san me suke ciki ba, ta dai lura yanzu tana bashi abincin ta tun tafiyar
Uche, hakan kuma bai dadata da kasa ba don ta san ita bazata iya ba. Ga yarinyar da shegen
zafin nama cikin 'yan mintuna ta sarrafa abinci mai wahala. Ko suna shiri a tsakanin su ko basa
yi ita dai Sa'ade bata sani ba. Yau da Sultana ta dawo hatta firjin kicin sai da ta cika shi taf da kwalaben giya bana dakin ta
kadai ba. Sabida za'a shiga weekend bazata samu zuwa bar ba ta san Yarima bai barin ta fita
koina a karshen mako. Yarima ya fito falo misalin karfe na goma na safe yayi wanka yayi fresh
da shi cikin kananan kaya DKNY ash colour, tsammani zakayi saurayi ne dan shekaru ashirin
da biyar ba magidancin dake neman talatin da biyar ba. Maganar da maimartaba yayi masa a
daren jiya a waya da ita ya wayi gari tana cin zuciyar sa, ya kuma yanke tunkarar Sultana da
maganar.
"Kai da matar ka sai yaushe zaku kawo min jika? Ko sai na mutu ban ga kwan ka a duniya
ba? Aure shekara biyar ana neman ta shidda babu ko labarin bari a gidan ka Yarima? A
matsayin ka na mai jiran gado?"
Wannan magana ce da maimartaba bai taba yi masa ba sai wannan lokacin, don haka sai
yaji tamkar an yi masa tuni ne akan abinda ya manta. Sultana ta fito sanye cikin wando 3 quater
da yar karamar rigar shan iska armless ta nemi waje ta zauna a nesa da shi duk don ta nuna
masa har yanzu fushi take. Ya hadiye wani abu da ya tsaya masa a makogaro sakamakon
kallon zara-zaran kafafun ta da suka sha adon jan farce purple abinda ya hanata sawa sabida
ya gaya mata baya sallah amma ta ki daina shafawa. "Ki shirya mu tafi asibiti yanzu, a bincika a
ga shin ni da ke waye baya haihuwa?"
Ba karamin duka maganarsa ta yiwa Aisha -Sultana ba, amma bata bari fuskarta ta nuna ba.
Mikewa yayi tareda daukar mukullin mota yayi waje yace yana jiran ta a mota.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login