Showing 12001 words to 15000 words out of 31845 words
Chapter 5 - Masarautarmu Book 2 Hausa Book By Takori Kabara .pdf
luf a gefen fuskarsa. A duniya bata taba katari da mutum mai cikar kamala da kyawun suffa kamar sa ba, ga wani
irin kwarjini da ya banbanta shi da sauran maza. Sarauta ta gama bayyana kanta a komai nasa.
His lips are so luscious kamar ana basu extra kulawa, fatar jikin sa fresh kamar haifafen kasar
Morocco. Sai ta ga kamar ta taba ganin sa, somewhere else da bazata iya tunawa ba.
Yadda ta saki ido, hanci da baki tana kallonsa shi ya fi komai bashi haushi, amma da yayi
kokarin yin magana sai ya samu halshen sa da kasa motsawa. Suka dubi juna directly cikin ido
yayin da wani gravity mai karfi ya fizgi ido da zuciyar kowannen su. Alal hakikah a rayuwar Dr.
Sageer Yusuf Askira, bai taba ganin macen da ta tabo wani sashe na kololuwar zuciyar sa irin
wannan da ke gaban sa ba. As professional as he is akan sha'anin mata, ya fada a zuciyar sa
cikin 'yan dakikan da suke tsaye..... "ta mallaki komai da yake mafarki a diya mace". Amma
kuma nan da nan mulkin sa da izzarsa ta Yariman Askira ta zo ta shafe komai, daga ganin
yarinya baka san komai akan ta ba, sannan wadda ta fito daga gidan ku?
Tuni ya mallaki kansa, fuska a daure ya ce da ita "come for breakfast".
Ya juya ya fita, ba tareda ya kara wata kalma ba.
Komawa ta yi ta dauko mayafin ta ta yane kanta akan doguwar abayar dake jikinta ruwan
hanta, da sallama ta shigo falon, can bisa dining ta hange su shida matar sa. Gaskiyar Fulani
ashe...baturiya tsantsa. Ai kuwa sun dace duk da shi baki ne kamar Askirama. Sa'ade ta fada a
zuciyar ta. Sultana ta daga ido tana kallon Sa'ade, kallo daya Yarima yayi mata ya maida kai ga
cin abincin sa. A take ta ji wani irin kishi ya soke ta, wannan kyakkyawar yarinyar za'a dauko a
ajiye mata a gida? Ai da sake wai an bawa mai kaza kai.
Ta dauke kai daga kallon Sa'ade ta mayar kan abincin ta. Har kasa ta tsugunnan tana gaishe
su, daga matar har mijin babu wanda ya amsa mata. Wannan abu ya sosa mata rai. Daga
bisani Yarima ya mike yana goge bakinsa da tissue. "If you finish meet me outside" ya ce da
Sa'ade. Matar ta tambayeshi inda zai kai ta? Yace tare zasu dinga shiga makaranta. Har zata yi
magana, sai kuma ta ja bakin ta tayi shiru, itama ta mike ta bi bayan sa.
Haka jiki ba kwari ta ja jiki zuwa tebir din cin abincin, ta zuba abinda zata iya ci, duk yunwar
data ke ji sai taji ta rasa appetite din ta, sabida irin tarbar da masu gidan suka yi mata.
A can kofar gida rigima ake tsakanin Sultana da Yarima, ta ce ita sam bata yarda su dinga
tafiya tare ba, ko dai ya daukar mata direba ko ta dinga tafiya da kanta tunda babu nisa zuwa
cikin makaranta. Ya san halin nacin Sultana in bai yi mata abinda take so ba bazata barshi ya
fita ba, don haka yace zai daukar mata direba amma for the mean time zasu dinga tafiya tare
kafin a samu direban kuma ta gama registration dinta. Daga bisani ya sassauta murya "you
want to me into trouble with my father? Do you know how much he loves this girl?" Sultana tayi
narai - narai da ido, sai ya sunkuya ya sumbaci bakin ta cikin lallashi. "Ki kwantar da hankalin ki
ni babu wata bakar mace a gabana, look at you me zan nema a wurin sauran mata? I just want
to live in peace with my father shiyasa na karbi yarinyar kuma da an yi hutu zan maida ita Askira
sai an koma makaranta".
Dai-dai lokacin da Sa'ade ta fito ta gansu a haka kamar zasu manne cikin jikin juna, sai ta
samu kanta da jin kunya tayi maza ta juya don bata taba ganin namiji da mace so close hakan
ba. Sultana ta harareta sannan ta ja da baya ta budewa Yarima kofa shikuma ya budewa
Sa'ade kofar gefensa ya ce ta shigo. Don haushi bata iya ta tsaya ta ga fitar su ba ta juya ta
dauki tata motar don tafiya nata wajen aikin. Tana tafe tana tunanin irin takurawar da zaman
Sa'ade zai yi mata don tun shekaranjiya Yarima ya kwashe duk wata kwalbar giya dake cikin
gidan ya zubar. Jiya sai Bar ta je ta sha abinda ta dade rabon ta da yi.
Suna shiga cikin makaranta Sa'ade ta bude ido tana shan kallon NTNU (Nigerian Turkish Nile
University). Its various faculties and administrative offices...the equisite lecture halls and
different departments. Wani shauki na diban ta idan ta tuna ta zama cikakkiyar dalibar NTNU
yanzu. Haduwar ofis din YARIMA Sageer Yusuf Askira ya tafi da ita, ko'ina sai raba da sanyi da
kamshi mai sanyi. Sai da ta jira ya gama abinda zaiyi sannan ya hadata da assistant dinsa ya
taimaka mata ta fara registration. Cikin kwana na uku ta gama, ta zama cikakkiyar dalibar
tsangayar (Pure and Appplied Chemistry). Ranar litinin zata fara daukar lacca. ****
Yau asabar, daga matar har mijin duk suna gida, Sa'ade in ta gansu a falo bata fitowa tayi ta
zama a dakin ta kenan, ko abinci bata yarda ta zauna ci tare dasu sai ta jira sun gama sun
tashi, sannan zata zo ta zuba ta ci ta kwashe kayan ta kai kicin, Uche ya karba ya wanke ya
dora wani. Saidai ita sam ba jin dadin abincin gidan take ba sabida abincin turawa ne ake yi
kullum, wani ma bata san da me aka sarrafashi ba ko sunan sa, ga kaguwa (shrimps) da ake
zubawa a kowanne girki, don haka yau da bazasu je cikin makaranta ba kasancewar hutun
karshen mako ne sai tace da Uche kada ya sanya abincin su da ita, she want to cook for herself
(tana so ta dafa da kanta).
Uche ya bata duk abinda zata bukata don ta ce tuwon acca zata yi miyar egusi. Nan da nan
ta hau girkin ta cikin kula da takatsan-tsan da kuma kwarewa.
A can falo Sultana ke tambayar Yarima yaya zacen direvan da ya ce zai daukarwa Sa'adatu?
"Ana nan ana bincikawa", yace da ita, a lokaci guda yana cigaba da marking takardun
dalibansa ba tareda ya bata hankalin sa ba. Ya rasa me yarinyar ta tare mata, bata da zance sai
na Sa'adatu a tsayin satinnan bakidaya. Shikuma a yadda ya lura sam yarinyar bata da
matsala, sannan bata takura musu, bata sa musu ido kamar yadda suka yi tsammani, tana da
tsananin kamun kai da gudun zuciya. Sannan rayuwar ta is very simple.
Wani unique kamshin girki da bai saba ji ba ya bakunci hancin sa, dama kuma yunwa yake ji,
ya kwalawa Uche kira. Ya fito da sauri har yana tuntube. Daidai lokacin da Sa'ade ta zo ta wuce
su da food flask biyu a hannun ta na tuwo da miya da plate da cokali tayi dakin ta. Ya dan kalle
ta ta gefen ido yadda bazaka taba zaton ya kalletan ba yace "Uche, me kake girkawa haka?"
"Ba ni bane Oga, Sa'adu ne" yayi murmushi jin sunan da ya kira Sa'ade dashi yace "me ta
girka?" "Tuwo ne Oga, with egusi soup" "ok idan da saura debo ka kawo min" "ya kwashe duka
ya tafi daki" "saboda rowa ko saboda me?" Uche yayi dariya, "Oga akwai wanda ta diba min,
lemme bring it" "thank you Uche".
Uche yaje ya kawo abincin a kyakkyawan flasks a rufe ya aza bisa dining. Sultana na daga
kwance tana kallon Yarima yana cin tuwon nan zuciyarta na tafasa, bata isa kuma tayi magana
ba yace zai bar gidan, don yace duk renakun weekends baya son korafi, in ta yi masa complain
ko guda daya ne zai bar mata gidan ya tafi gun Dr. Ziyad. Ita kuma sam bata son alaqarsa da
Ziyad don bashi da aure kuma kullum tana ganin shi yana kwashe-kwashen mata a motar sa
zuwa gidan sa. Shiyasa take making sure bata yi abinda baya so ba a kowanne weekend don
dai su zauna tare.
Bai san yayi missing cimar gida ba sai yau, sosai ya ji dadin tuwon, da izzar shi zata barshi ai
da yace da daddare ma ta kara yi masa, musamman mai miyar ganyen Ugu, yana son ganyen
sosai.
Shikuma Uche tunda ya lura Ogan sa na son tuwo sai yake kokarin yi masa, amma sam baya
kyau da dandano kamar na Sa'ade don bai kware ba, a wurin Sa'ade ya koya don ya ce mata
ta koya masa ya dinga yiwa Ogansa. To amma kullum yayi haka yake dauko shi Oga ya yi loma
daya ya ajiye, ko yace ya dafa masa wani abun. Don haka Uche yake mata wayo, kullum zata
dora girki sai ya ce ta dora da dan yawa, shima yana so, tana bada baya zai shirya abincin ya
kaiwa Yarima, ya gaya masa Sa'adu ne ya girka, ya rasa ya aka yi Uche ya dago shi kan yana
son cin girkin Sa'adatu. Duk ranar da bata yi girkin ba ta wuni a makaranta ne yake cin na Uche.
Sultana ta shigo gida yau da sabon bed-side fridge wanda babu a dakin ta. Washegari kuma
data dawo aiki ta dawo da manya-manyan kwalaye. Tana kokarin fito dasu daga mota direban
da Yarima ya dauka ya sauke Sa'ade. Ganin tana kiciniyar ciccibar kwalayen Sa'ade ta karasa
da sauri ta ce. "Can i help you aunty?"
"No, thank you"
In ji Sultana.
Ta ciccibi manyan kwalayen ta daya kan daya tayi cikin gida.
****
Tun daga ranar Sultana ta daina zuwa Bar ta koma shaye-shayen ta a dakin ta, a zuciyar ta
tana tsinewa Sa'adatu, ita da gidanta an zo an takura ta. Bata sha a weekend sabida Yarima
yana gida, da yamma kuma sanda ta dawo shima ya dawo, don haka sai ta tsiri kulle kanta da
zarar ta dawo aiki bata kara fitowa sai lokacin barcin su. Dr. Sageer yana lura da sabon sauyin nata, ya rasa me take kulle kanta tayi a daki, bugun
duniya in zai yi bazata bude ba sai ta ga damar fitowa wajen sha biyun dare. Tuni ya harbo jirgin
ta. Rannan ya faki idon ta ya dauke safayan mukullin. Tana tsaka da shan whisky ya bude kofar
dakin ya shigo ya mayar ya rufe.
Kayan barci ne na RALPH LAUREN farare sol a jikin sa. He never looked so handsome in
her eyes like today. Ya tsaya a kanta ya harde hannayensa a kirji yana kallon ta with furious
eyes... "Sultana why? Ba na hana ki shan giya ba? Ko syrup ban hana ki sha ba? Ban gaya miki
haramun ne a muslunci ba? Idan da kin yi na kyale ki yanzu kin sani ba mu kadai bane a
gidannan, a slight mistake will probably go to my father, har yanzu jiki na na bani spy ce ya
sanya mun. Ki yi a hankali idan ba kina son janyo min bala'i ba".
Ta daga rinannun idanun ta ta dube shi, cikin maye tace "I....i cannot live without beer, a haka
ka ganni ka aure ni, kai ma ka sani bazan taba iya barin giya ba". "Sai ki zaba ko aure na ko
giya, tunda na sanar dake addinina ya haramta kika ce kin amince zaki daina, tunda kika fara
aiki na san kin koma shan beer, sallah kin dade da daina ta, na sa miki ido ne don in ga iya
gudun ruwan ki, and now na lura duk musluncin ki ba na gaskiya bane kin dade da daina sallah.
Ni kuma bazan zauna da kafira ba".
Ya fadi yana watso kwalaben dake jere cikin firji, ya hada su da bango ji kake taratsatsa!
"Kika sake shigo min da wannan kazantar gida, zaki ga yadda zamu kwashe, i'm not that fool
and i respect my religion......". Wani wulakantaccen kallo Sultana tayi masa....tace "addini! Kai
nan har kana da bakin cewa ka san addini? Addinin naka ne ya baka damar yin adultery?
Tunda na san ka na san you are an adultrer wanda baya iya rayuwa sai da mata. Na dauka in
mun yi aure shikenan zaka bari, gara ni giya da kayan maye kawai nake sha amma bana zina,
balle da aure na".
Tamkar ta watsa masa garwashin wuta haka fuskarsa ta koma, bai taba sanin ta san wannan
side din nashi ba, abinda bai sani ba shine tana bibiyar wayar sa. Sultana ta lura da efffect din
kalamanta akan sa, sai ta yi wani miskilin murmushi "tunda na barka kana zina, ban taba takura
maka ba, sai ka bar ni in sha giya, ko wannan yarinyar ta bar min gida......" ta mike tana layi tayi
toilet ta bar shi a wajen.
****
Kwana biyu basa magana da juna, abinda basu taba yi ba a rayuwar auren su, wani abu da
Sultana ta tsiro da shi don ta baiwa Yarima haushi shine ta daina boye shan giyar da kayan
mayen ta, nan falo take zama ta baje tana abin ta. A ranta ta kudure duk ranar da ya gayawa
iyayensa tana shan giya itama tace musu yana neman mata. Gara ma yayi hakuri su ci gaba da
zaman su yadda suke yin sa, wata figigiyar yarinya bakauyiya bata isa ta canza mata rayuwa
ba.
Sa'ade ta shigo falon da sallama, misalin karfe shidda na yamma, direbanta Salis ya riko
mata manyan littafan chemistry har zuwa kofar shiga falo, ya mika mata tayi masa godiya. Tana
kokarin shiga Yarima na parking. Ta juya suka hada ido ta cikin gilashin motar sa, sai ya yafito
ta, yace "Sa'adatu help me with these files" ta karasa cikin nutsuwa ta karba, shi kuma ya dauko
daurin answer sheets na daliban sa ya bi bayan ta suka shiga falon tare. Nan idanun sa suka yi
kyakkyawan gani.
Kamewa yayi a inda yake tsaye, a lokacin ta kai bottle na whisky bakin ta, ta gefen idon sa ya
saci kallon Sa'ade don ganin reaction din ta, sai ya ga babu wani sauyi a tare da ita, ga dukkan
alamu bata san menene a hannun Sultana ba, ta dauka just lemo ne.
Sannu da gida kawai ta yiwa Sultana ta ajiye masa takardunsa bisa centre table, daga nan
bata kara kallon su ba tayi shigewar ta daki. Yayi catching breadth din sa da karfi tana bada
baya ya wankawa Sultana mari, ya sake wanka mata, sai da ta nemi jin ta da ganin ta na wucin
gadi ta rasa. Tana farfadowa ta kai hannu zata rama ya kama hannun ya murde shi. Ta saki
karar data kai kunnen Sa'ade. Har zata fito da gudu ta tuna hudubar Fulani (ba ruwan ki da
shiga shirgin da ba'a sanya ki ba) tunda dai ta san su biyu ta bar su.
Kwanan tashin hankali aka yi tsakanin ma'auratan, irin wanda bai taba faruwa tsakanin su ba,
zagi ta uwa ta uba babu irin wanda Sultana bata yi wa Dr. Sageer ba, har tace duk da
kasancewarta kafira kamar yadda yake kiranta bata taba zina ba shi ya koya mata, shi yayi
disvirgining din ta, musluncin sa bai kare shi da komai ba, fasiqi mara tsoron Allah. Gara ita giya
kawai take sha.
Duka wannan a kunnen Sa'ade, wadda hayaniyar su ta hanata barci, ta tsaya jikin kofar dakin
ta sai shivering take (karkarwa). Bata taba jin abinda ya kada ta ya gigitata irin wannan ba,
gidan masu zina da shan giya aka kawo ta! Uncle Yarima da take gani da matukar girma da
kima shine mai yin zinar? Ko dai Sultana karya take yi? Abinda ta gani tana sha dazu shine
giyar kenan kuma shi ya hada fadan?
Tana jiyo kukan Sultana da alama marin ta ya kara yi, jikin ta na rawa ta dauki waya ta kira
Fulani, hawayena zuba mata tace "Fulani! Ni dai gobe a zo a dauke ni bazan iya zama a
gidannan ba, zan koma hostel" cikin muryar kwantar da hankali Fulani tace "take it easy....gaya
min me ya faru? Ana miki wani abu da ba kya so ne?" Cikin kuka tace "no, Uncle Yarima is very
nice to me....amma yana dukan matar sa....gata can sai ihu take.....kuma ta ce shi mazinaci
ne...." ba shiri Fulani ta dauke wayar daga kunnen ta ta juya, sai idon ta cikin na Askirama da ke
gefen ta da alama shima sauraron wayar yake yi don ta manta a (hands-free) take. Yanayin da
ta ga fuskar sa a ciki yasa ta jin kamar ta shiga cikin wayar ta shaqe Sa'ade har sai ta daina
numfashi.
"Wallahi maganar Sa'ade shirme ce ni na tabbata....". Fulani ta fada muryar ta na rawa,
kwalla cike da idon