Showing 9001 words to 12000 words out of 31845 words
Chapter 4 - Masarautarmu Book 2 Hausa Book By Takori Kabara .pdf
amfani da turarukan Borno a jiki da
tufafin ta.
Duk da ta bawa Sa'ade damar shiga koina cikin masarauta Sa'ade bata yawon, kullum tana
sassan su ko dakin Fulani, ko kuma suna kicin suna girkin Askirama idan ita ce da girki. Hatta
gashin kan Sa'ade Fulani da kanta ke zama ta gyara mata yanzu, gyara na masu kwarewa akan
kula da gashi, wata irin shaquwa suke yi cikin 'yan watannin nan wadda basu taba yin ta a
shekara shidda da suka yi tare ba, ta yadda har Fulani ta soma zullumin zuwan ranar tafiyar
Sa'ade makaranta Abuja.
Maimartaba ya fi kowa jin dadin wannan sauyi da ya ke gani a tattare da Bilkisu da 'yar ta
Sa'adatu, 'yar da yake jin kamar shi ya haifeta saboda son da yake wa mahaifiyar ta. Jin dadin
hakan yasa ya hada musu tafiya umrah karshen wannan watan don dai su kara shaquwa da
juna ba idon kowa tare dasu, amma dole tareda Fanna zasu tafi sabida kula da hidimar Fulani. A saudiyyah ba abinda Fulani Bilkisu ke roko a wurin Ubangiji sai miji nagari ga Sa'adatun ta,
wanda zai rike mata ita amana ya rike maraicin ta, wanda ba zai taba duban asalin ta ya
wulakantata a kan sa ba. Wanda zai zame mata miji kuma uba sannan Yayan da bata da shi a
kafatanin rayuwarta. Ta kuma sakankance cewa an amshi rokon ta, don wannan shine ladabin addu'a. Ba son
tafiyar Sa'ade jamia'ar Turkawa take ba, amma ta yarda da hujjojin Maimartaba, na cewa gara
Sa'ade tayi karatu kafin Allah ya zaba mata mijin aure. Karatun zai zamo gata kuma majingina a
agareta ranar da babu su. Suna dawowa suka tarar da sakamakon su Sa'ade ya fito, Mai Askira da kansa ya kira
Yarima ya gaya masa kowacece Sa'ade, gaskiyar ya gaya masa cewa 'yar Bilkisu ce. Ya damka
masa komai na alhakin nemo mata makaranta da daura masa dukkan nauyin hidimar karatun
ta. Ya kuma gaya masa a gidansa zata zauna ba a hostel ba. Wata irin zufa ce ta soma ketowa
Yarima ko mu ce Chiroman Askira. A tsarin rayuwar su shi da matar sa, ko kuda basa so ya
gifta a tsakanin su balle dan mutum ya zauna a cikin su.
An tarbiyyance su da rashin yin musu ga magabatan su, an raine su a bisa bin umarnin na
gaba, balle Mai Askira gabadaya. Don haka amsar sa ita ce kawai "toh" amma a ransa ya ce
kora da hali kawai zai sa yarinyar ta bar masa gidan sa. To amma kuma Maimartaba ya ce 'yar
Fulani Bilkisu ce ta cikin ta, matar da duk fadin gidan su in ka dauke mahaifiyarsa ba wadda
yake gani da mutunci kamar ta, ba wadda ke kula da al'amarin sa dana matar sa kamar ta.
Anya zai iya wulakanta jinin ta? Babbar damuwarsa Sultana bazata taba amincewa ba
musamman sabida yadda take shaye-shayen ta babu takura, ta dauka bai sani ba, amma kallon
ta kawai yake, duk abinda take ciki ya sani, baya magana ne don ya san shima da nasa guntun
kashin a katara.
Aka ce wai in ka ji ma'aurata masu ha'intar juna suna zaman lafiya to tabbata daya na
ha'intar daya, babu yadda dayan zai yi ya hana, kada nashi asirin ya tonu. Wannan shine
tsakanin Yarima Sageer da matar sa Aisha-Sultana.
****
Babu yadda zai yi, haka yasa neman admission din Sa'ade a gaba a washegari a matsayin
first thing da ya shiga ofis ya zauna, takardun ta duk sun yi kyau. Ya tsurawa sunan ido....
SA'ADATU HASHIM ASKIRA. Hatta course din ma nasa ta dauka......Pure and Applied
Chemistry. "Does she know me?" Ya tambayi kansa cikin mamaki. Salon karatun ma mai Askira
ya ce ni zan koya mata???
Tsaki yayi ya ture takardun gefe ya janyo na wasu, a lokacin da Dr. Ziyad ya turo kofar ya
shigo dauke da sallama a bakin sa. "Wata hot baby na samo yanzunnan daga zuwa na
Millenium Park, akwai abubuwa, kayi maza ka gama mu bar ofis dinnan". Tsaki yayi ya ce "kai
baka san halin da nake ciki ba, wata yarinya za'a kawomin riko daga gida, Allah ya sa ba spy
mai martaba zai kawo min ba, ko wani ya kai gulmata ban sani ba, ka san a ko'ina yana da
jama'a musamman nan Abuja" ya fada kyakkyawar fuskarsa dauke da damuwa tsantsa.
Dr. Ziyad yace "i don't think so. How old is she?" "JAMBITE ce fa" "whao!" Inji Dr. Ziyad.
Kace sweet 16 za'a kawo mana kawai, yo meye abin damuwa banda mu dinga kwasar rabon
mu kawai muna saya mata pizza muna cika mata aljihu? Gida na is very quite and secret ko
Sultana bazata san muna kwasar gara ba". Wata muguwar harara Yarima Sageer ya zabga masa, ya tsartar da miyau da sauri. "Allah ya
sawwake Allah ya tsare ni, ni ba dan akuya bane, ina dai neman matan bisa titi amma ban da
na mutunci balle wadda ta fito daga gidan mu, daga gidan mun ma daga hannun mahaifi na,
'yar matar mahaifi na mai yawan karamci a gareni. Allah ya kiyaye! Iskancin nawa mai limit ne,
and i'm hoping watarana in bari gabadaya". Dr. Ziyad ya kyabe baki tareda mikewa tsaye yana
dariya yace "kai din? Na yarda bazaka iya neman ta gidan ku ba, ko don kada asirin ka ya tonu,
amma bazaka iya barin mata ba i swear ...." Yarima ya dauki mukullan dake bisa teburin sa ya
jefe shi dasu, Dr. Ziyad ya dafe keya ya fice da gudu yana masa dariyar data kara masa takaici
kan wanda yake ciki, na yarinyar da za'a turo masa babu gaira babu dalili.
Cikin sati daya ya gamawa Sa'ade duk shirye-shiryen ta, an dauke ta a NTNU a tsangayar da
yake koyarwa (B. Sc Pure and Applied Chemistry). Ya aikawa Askirama admission letter din ta
ta email. Abinda ke gabansa yanzu shine ta yadda zai tunkari Sulatana da maganar.
Amma abin mamaki da ya koma gida da yamma, ya tarar ta riga shi dawowa, ta shawo ta yi
mankas tana kwance dai-dai a tsakiyar falo. Haka ya tsallake ta yana tsaki ya wuce dakin sa ya
sunce ya shiga wanka. Yana fitowa ya shiga kitchen don neman abinda zai ci, ya bude firji, abin
takaici babu komai sai Giya nau'i nau'i, yanzu Sultana ta daina shakkar ya san shaye-shayen ta,
kai tsaye take komai don ta ga baya daga ido balle ya nuna ya san tana yi.
Wani mugun tsaki ya saki ya rufe firinjin da karfi, yanzu in yarinyar nan ta zo ta gani fa? Mai
Askira yace rana ita yau za'a kawo ta tare da kayan ta su gyara mata daki.
Ji yayi yunwar da yake ji ta kama gaban ta, da sauri ya fito ya sa kafa ya shuri Sultana da
karfi. Ta bude idanu jazur dasu, ta sauke su a kan shi, dama gasu tun asali kamar na mage
(brown eyes). A fusace yace "ki tashi ki kwashe abubuwan da kika cika min firji dasu, we're
having a guest from Askira, and she's going to stay with us for years, so mind yourself
else.....duk abinda ya biyo baya ba ruwa na".
Sultana tayi mici-mici da ido "bakuwa? A gidannan? Daga Askira? To ban yarda ba" ya galla
mata harara yana hango wani irin muni a tare da ita da bai taba gani ba wanda yake bayyana in
ta sha giya "sai ki kira maimartaba ki gaya masa" ya jefa mata wayar hannun sa.
Har dare suna fafatawa, ta dage sai ya kira Babansa ya ce bata yarda ba, shi kuma yace ba
tarbiyyar da aka yi musu kenan ba but she's free to call him herself.
"To ko dai aure suka yi maka shine za'a fake da karatu don nasan mamanka bata so na!"
Sultana ta fada cikin kuka. Shi don mamakin kalamanta ma dariya yayi, wai aure! Wa ya isa
yayi masa aure ba da yardarsa ba? Besides, su gidan su ba'a auren dole. Sannan ya gama
aure a rayuwar sa ba zai taba yin mata biyu ba duk da kasancewarsa basarake.
Tashi yayi ya dau motar sa ya bar gidan zuwa inda ya tabbatar za'a faranta masa rai, yau
ranar kwata-kwata a birkice ta zo masa. He's upset, sannan wannan mahaukaciyar Sultanar ta
kara masa bacin rai.
Ai kuwa ya samu Dr. Ziyad ya dauko musu baby din da ya gaya masa sun hadu a millenium
park, nan ya manta da zancen Sa'ade da Maimartaba ya shantake acan har karfe daya na dare.
Sanda ya shigo gida ya tadda Sultana ta baje kwalabe sun fi biyar duk tayi emptying din su.
Ta koma zukar marijiuana cikin tsumma, gashin kanta a birkice, gabadaya sai ta zame masa
kamar motsatsiyar tsohuwa, ya dinga tambayar kansa tun farko me ya gani a tare da ita ya
yarda ya daukota har kasar sa ya aureta??? Tsaki yayi ya tsallake ta ya wuce dakin sa. Wanka ya fara yi ya tsaftace kansa, yana jin wani
abu na tsirga masa a zuci da gangar jiki, wanda yafi kama da jin kunyar Ubangiji. Wankan
janabar da bata aure ba alhalin ga matar sunnar ya tsallake tana nata sabon Allahn. Wannan
wace irin rayuwa ce??? Idanun sa a rufe ya hau gadon sa ya kwanta. Addu'a yake cikin ransa in yana da rabon
dainawa kafin ya mutu, Allah yasa ya daina......!!!
****
Tunda Askirama da kansa ya shigo ya ce da Fulani gobe ne tafiyar Sa'ade gidan Yarima jikin
ta yake a sanyaye, don bata san wane irin riko da karba Sultana zata yi mata ba, tunda ita ba
jinin gidan bace, duk da su Humaira suna fadin bata da matsala.
Amma ga Sa'aden sai murna take, very enthusiastic ga tafiya makaranta, bata tunanin komai
da ya danganci abinda zata ta tarar banda kasancewa dalibar Turkish University.
Don a daren Fulani ta zaunar da ita a gabanta. Don ta ga murnar tata har ta so ta yi yawa,
tun azahar ta kammala daure kayanta tsaf. Kadan ta bari wadanda bata cika amfani dasu ba.
Allah-Allah take garin Allah ya waye ta kama hanyar birnin tarayyah.
"Sa'adatu bani hankalin ki nan" inji Fulani.
Ta dago fararen idanun ta ta dubeta, wadanda a lokuta da dama suke wani irin sheki da
walainiya (sparkling eyes) wanda shine babban sirrin kyawun Sa'adatun. Fulani tace.
"Na ga sai rawar kai kike, ki kama kan ki, gidan Yarima zaki je, sannan matarsa asali ba
musulma bace, sannan ba bahaushiya bace, don haka dole ki kula da tarbiyyar kan ki da kan ki,
ki maida hankali akan abinda ya kai ki kawai, ba ruwan ki da rayuwar su, ban da sa-ido, banda
daukar zance, banda shiga shirgin da ba'a sanya ki ba. Tsakanin ki da su yi na yi bari na bari. Ki dinga taimaka mata da girki da ayyukan gida tunda
ita ma'aikaciya ce. Na hore ki da kama mutuncin kanki, ko ya kike da namiji kada ki yarda ki
kebe da shi, Ko hannun ki namiji ya taba cikin shege zaki yi, kin ji na gaya miki?"
Sa'ade ta gyada kai cikin fahimta, sannan ta dan zaro ido ta ce "to ai gidan ba maza ko?"
Fulani ta hana kan ta yin dariya sabida yadda muryar Sa'ade ta koma razana zallah. Tace "shi
mai gidan ma ai namiji ne, kuma ba muharramin ki bane ba, don haka matsayin uba yake a
gare ki, ki kama kan ki, ki rike mutuncin ki. Allah yayi miki albarka ya saka albarka a neman
ilmin ki. Ga waya karama na saya miki duk halin da kike ciki ni zaki kira ki gaya min, ban yarda
ki bawa kowa lambar ki ba".
Sa'ade ta gyada kai cikin murna a lokaci guda tana mika hannu don karbar karamar wayar
siemens da Fulani ke mika mata. Kawai sai ta ji Fulani ta hada da hannun ta ta janyota jikin ta
ta rungumeta...
"Ki yafe min Sa'adatu don Allah ki yafe mini..." "ni baki yi min komai ba Fulani, na yafe miki
abinda na sani da wanda ban sani ba. Nima ki yafe mini!"
Sallamar tasu is very emotional da ta fiddo hawaye daga idanun kowaccen su.
Washegari daya daga cikin direbobin gidan karkashin rakiyar kuyangin Fulani Bilkisu mata
guda biyu maimartaba yasa suka dauki Sa'ade zuwa Abuja a daya daga cikin motocin 'Askira
Emirate'. Tun asussuba suka kama hanya basu isa Abuja ba sai karfe takwas na dare. Inda
Allah ya taimake su shine sun yo guzurin abinci da abin sha wadatacce wanda har suka iso
Abuja sallah ce kawai take tsayar dasu a gidajen mai na gefen hanya.
Suna fitowa daga mota Sa'ade tayi mika....ta ware ido tana kallon kyawawan gidajen estate
din malamai na NTNU kamar kana kasar Istanbul. Ashe ba ginin masarauta kadai ne gini mai
kyau ba, ginin Turkawa ma abu ne mai matukar kyau da daukar hankali.
Ita dai tunda take bata taba ganin kananan gidaje masu tsari da kyawun zubin wadannan ba,
ko ya mutanen cikin gidan suke? Koda yake Fulani ta ce turawa ne, ai sai turawan.... "wannan
gida wanke hannu ka taba". Sa'ade ta ce cikin ranta. Daidai lokacin da daya daga cikin
kuyangin da suka zo tare ta yi mata magana ganin ta shagala a kallon gidan "ranki ya dade mu
karasa daga ciki ko?"
Suka isa ga entrance na gidan suka hau danna kararrawa, suka yi har suka gaji ba'a bude
ba, a lokacin Sultana na kwance a falo ta sha ta kai mata karo, tun misalin karfe 6 na yamma
take kwance har a lokacin bata san inda kanta yake ba.
Allah ya kawo Uche (kukun gidan) zai shiga da cefane, kasancewar yana da mukullin gidan
ta kofar kicin ta baya. "Hey! What do you want here?" Ya tambaye su. Aka rasa mai amsawa
don 'yan rakiyar Sa'aden basa jin turanci, sai itace ta gayamasa daga Askira suke, sun zo wajen
masu gidan ne. Ya tambayeta ko Dr. Sageer ya san da zuwan su? Ta ce "ya sani" a takaice,
domin bata da tabbacin hakan, Allah-Allah take ta sanya hakarkarinta akan shimfida sabida
gajiyar zaman mota data kwaso.
Wayar sa ya dauko ya kira wata lamba yayi magana cikin harshen turanci, ya kalle su,
sannan ya maida wayar aljihun sa ya ce su biyo shi. Ta baya suka shiga ta kofar kitchen suka
kurda zuwa falon gidan. Nan Sa'ade taga mace jajawur kwance magashiyyan a dandaryar
tayals, gashin kanta ya baje ya rufe fuskarta, Uche bai ko dubi inda take ba ya bude wani daki
yace su shiga nan ne dakin bakuwar. Sannan ya ce su bashi minti 15 zai kawo musu abinci.
Kafinnan ga ruwa da lemo su sha.
Tsaruwar dakin ya burge Sa'ade, duk da bai kai dakin ta na Askira ba amma daki ne mai tsari
irin na turawa babu tarkace sam a cikin sa. Gado ta fada tana ce da Fariha daya daga cikin 'yan
rakiyar ta in an kawo abincin ta tashe ta tunda ita tana fashin sallah, in taci abinci sannan tayi
wanka. Uche ya kawo musu abinci mai rai da motsi suka ci suka koshi, sannan Sa'ade ta fara yin
wanka, ta shirya cikin kayan barci tabi lafiyar gado bayan ta kure iyakwandishan, sukuma
kuyangin suka kwanta daga kasa. Ba wanda ya nemesu har washegari. Da asubah suka kama
hanyar Maiduguri lokacin Sa'ade tayi sallah ta koma barci.
****
Sai karfe takwas na safe Sa'ade ta tashi, ta duba babu 'yan rakiyarta, sai ta tuna sun ce da
asubah zasu kama hanya, tsaki tayi tana mitar shine ko su tashe ta su yi sallama.
Wanka ta fara yi, kafin ta ji cikin ta yana kiran chiroma, a gurguje ta shirya tana fadin bari in bi
su kitchen din tunda sun manta da mutum a gidan.
Tana kokarin fita bayan ta murda kofar dakin taji ta yi karo da mutum....Wani irin sassanyar
kamshi mai huda zuciya, coupled with his gait and geniusness, beautiful elegant face wadda
babu far'a sam a cikin ta.
A kiyasce yadda ta kimanta shekarunsa zasu kai talatin da biyar zuwa da shidda. Alamu sun
gama nuna ya gama samun duk wasu achievements na rayuwar dan adam. Kama daga ilmi na
addini dana zamani, sannan ya zauna da kafafun sa ya gama kama kasa.
Da farko ta dauka Askirama ne a gabanta (mai martaba) sabida tsabar kamannin su, saidai
data lura sosai sai ta fahimci wannan akwai tarin kuruciya da hasken boko a tare da shi, bi
ma'ana yaro ne mai jini a jika, babu ko tsillin furfura a kwantaccen sajensa zuwa gashin kansa,
wanda ya kwanta