Showing 30001 words to 31845 words out of 31845 words

Chapter 11 - Masarautarmu Book 2 Hausa Book By Takori Kabara .pdf

na Sageer da wuya ka iya karantar abin da ke zuciyarshi.
Maimartaba ya ce, in zo mu taho ni da kai yanzun nan.
Cikin mamaki Yarima ya ce, Lafiya?
Sai dumbin alkhairi. In ji Awaisu, Amma a yammacin nan mu kama hanyar Askira is too late,
ka yi hakuri ka kwana zuwa gobe, sai in tattara hankalina waje daya in kammala aikina a daren
nan da safe mu kama hanya.
Awaisu ya ce, Zan bi shawararka ne only in ka amince za ka jinkirta kiran Saadatu har sai ka
fara ganawa da Maimartaba ko in ce ka yi hakuri da kunna wayar zuwa goben after encounter
dinku da Maimartaba
Kokari yake ya fahimci me Awaisu ke son boye masa ta hanyar kura masa ido, kuma sai
kawai ya ji gabansa ya fadi.
Wani abu ne ya faru da ita? Ya tambaya in subdued (cikin karayar murya).
Awaisu ya gyara kwalar rigarshi yana murmushi, ya ce, Ita wa ke nan?
Ita Saadatun da ka ce kada in kira. Ya fada cikin daure fuska don ya kasa gane inda Awaisu
ya dosa. Awaisu ya sake sakin murmushi, in dai wannan damuwar da ya gani kwance a kan
fuskar Yarima a kan Saadatu ne, to insha Allahu komai zai zo wa Maimartaba da sauki, Yarima
ba ya taba damuwa da lamarin wanda ba ya so, ko da kuwa ba so ne na soyayya ba, to akwai
alamun shakuwa da aminci.
Babu abin da ya faru da ita, tana dakin uwarta. You better call your wife not Saadatu, bana
tunanin tunda ka zo ka kira ta. A hakan ake mana ikirarin duk duniya ba wadda ake so sai ita.
Ita ma ko za ka kira ta, to fa sai gobe, in ka fito daga turakar Maimartaba Ya fada yana dariya,
tare da kwashe wayoyin Yarima guda uku da ke bisa center table din gabansa, ya zuba a aljihun
jamfarsa. Ya zabi daki daya cikin 3 bedrooms din da ke falon ya shige yana ce da Yarima,
Lemme take a shower, ko na samu saukin gajiya ta.
Yarima ya bi shi da kallo, ya kasa cewa komai, lamarin Awaisu sai shi. Sai ya dauki kan
telephone ya yi dialling lambobin da yake bada umarnin a kawo masa abinci, ya yi wa Awaisu
odar abin da zai ci. Daga haka ya maida hankalinsa kan macbook dinsa yana ci gaba da abin
da ke gabansa. Sai dai kuma duk hankalinsa ya rabu biyu, jikinsa ya ba shi akwai muhimmin
abin da ke faruwa a cikin gida da Awaisu ba ya son gaya masa, ya fi so ya ji kai tsaye daga
bakin Maimartaba. Kuma da kyar in alamarin bai shafi Saadah ba, in ba haka ba don me
Awaisu zai ce kada ya kira ta?
Yana aiki yana ta tunane-tunane, duk a kan Saadatu da alamarinta da ya yi wa zuciyarsa
karan tsaye, ya hana shi sukuni ya kuma hana shi enjoying komai da yake yi sabida rashin
ganinta cikin kwanakin nan, sai dai ya kudire a ransa suna isa Askira da ya ga Maimartaba zai

je har unguwar Fulani Bilkisu don kawai ya ga Saadatu.

******

Suna kwance a bayan mota 4-matic mai dauke da rubutun ASKIRA EMIRATE, direba na ta
sharara gudu don su isa Askira cikin lokaci, ta garin Damaturu suka bi, duk da ta fi nisa amma
ta fi lafiya sabida insurgency da ya fara kafuwa a daidai lokacin a jihar Borno. Zuwa Askira ta
Chibok bai yiwuwa dole sai an bi ta Damaturu. Duk hirarrakin da Awaisu yake masa don ya dauke masa tunani ya ki kulawa, jikinsa ke ba
shi kawai, theres something fishy going on akan Saadatu da har ya sa Maimartaba ya yi masa
kiran gaggawa.
Ana kiran sallar magriba suka shiga Askira. Inda Awaisu ya ji dadi shi ne kafatanin fadawa da
dogarai da duk wanda ke wajen ya shiga masallaci sallah lokacin da suka iso, ba don haka ba
da tun fitowarsu mota za a fara tarar Yarima da Allah ya sanya alkhairi. Yan tsirarun da suka
hadu da su a hanya mata ne bayi suke wucewa. Gaishe su kawai suka yi suka wuce. Suna shiga sassan Yarima da ke cikin gidan alwallah suka yi suka tada sallah, kafin su idar
hadiman Yarima sun gama jera musu abinci. Awaisu ne kawai ya zauna yana ci, Yarima sai
magiya yake masa ya ba shi wayoyinsa yana cewa, sai ya fito daga ganawa da Maimartaba.
Kawai sai jin sallamar Ya Gumsu suka yi a kansu, karkashin rakiyar kuyanginta. Daga bakin
kofa suka tsaya ita kadai ta shigo sai huci ta ke kamar mesa. Yarima da Awaisu suka mike
tsaye a tare har suna hada baki a tare wajen cewa, Ya Gumsu lafiya??
Kawai sai ta zauna a kujera ta sa fuska cikin tafuka ta fashe da kuka.
Yarima da Awaisu suka tsugunna a gabanta suka kasa magana, suna nan durkushe gaban
Ya Gumsu tana kuka suka jiyo takun tafiyar Askirama. Daga kirarin da ake masa daga waje
suka gane shi ne yake tahowa.
Ya karaso har dakin Yarima bakinsa dauke da sallama. Idonsa ya sauka a kan Ya Gumsu,
ransa ya yi mummunan baci, da kyar in ba ta lalata komai ba.
Biyo ni Yarima.
Abin da ya ce kawai kenan ya juya ya fita. Yarima ya kasa tashi daga gurin ya bar Ya Gumsu
da ke kuka har sai da ta dago idanunta jage-jage da hawaye, ta ce,
In ka karbi auren nan da ya yi maka sai na dauke maka albarka.
A razane Yarima ya cira kai ya dubi mahaifiyarsa, kafin ya samu zarafin ce mata komai ta
tashi ta fice kamar kububuwa.
Yarima ya shiga cikin halin rudu mara misaltuwa. Kawai sai ya bi bayan maimartaba ya bar
Awaisu a wajen.
Awaisu ya jinjina kai cike da taraddadin wannan alamari, bai yi zaton ya Gumsu ba za ta so
auren nan ba in ya yi laakari da yadda ta ke adawa da auren Yarima na farko. Da ya tuna kishin
da ke tsakanin matan gidan sai mamakinsa ya ragu, don Saadatu ta fito daga dakin Bilkisu ne
wadda suke kishi da ita fiye da kowacce matar sarki. Yarima bai zauna ba sai da Askirama ya fara zama a kujerar mulkinsa. Ransa a tsananin
bace don a zatonsa Ya Gumsu ta riga ta yi masa riga-malam-masallaci. Ya yi kokarin boye
bacin ransa sabida ba ya taba bari a gane fushinsa, ya dubi Yareema Sageer da ya samu wuri
ya zauna daga kasan kafafunsa.

Kafin in ce komai Yareema idan na yi maka umarni, uwarka ma ta yi maka, na wa za ka bi a
cikinmu?
Yarima ya kara rudewa, gabadaya sun rikita shi, ya kasa gane komai. Kawai sai ya yi shiru ya
sunkuyar da kai. Mai Askira ya yi murmushi ya ce, Aure na yi maka shi ne ta ke adawa, aure na
mutunci da rufin asiri, auren da na tabbatar zai dauke dukkan kwadayi da shaawarka daga kan
sauran mata kamar yadda ya dauke nawa daga kan Bilkisu ko kwarkwarorina na hakura da su
daga ranar da na mallaki Bilkisu, domin matan BAGGARA daban ne. Don haka ne nake da
kyakkyawan zaton cewa abin da ta haifa ma zai zamo irinta ga Sarki mai jiran gadon Askira. Na
aura maka diyar Bilkisu, wato SAADATU don in raba ka da kusantar zina da matan haramun. Ya
rage naka ka bi umarnina ko na mahaifiyarka. Ka tashi na sallame ka, ka je ka yi tunani kan
abin da ya fi dacewa da kai. Rana ita yau za a fara biki, biki irin wanda ba a yi a aurenka na fari
ba, bikin aladar gargajiya na masarautar Askira. Na kai shi zuwa rana ita yau ne don kawunta
da ke kasar Italiya ya samu halarta shi da iyalinsa.
A nan Maimartaba ya gaya wa Yarima labarin asalin Saade, tun daga auren mahaifiyarta da
Malam Hashimu zuwa rabuwarsu. Rayuwar Saade a kauye da ranar da abokin Babanta Malam
Saleh ya kawo ta Askira ya karbe ta, wahalar da ta sha a hannun fulani kafin ta amshe ta
matsayin ya, da nagartattun halayen Saade da ya dade yana fahimta. A karshe ya gaya masa
tun farko ya yi niyyar aura masa Saade a matsayin matarsa ta farko sai ya kawo zancen
Aisha-Sultana, shi kuma ya ba shi dama don ya fita hakkinsa. Yanzu ne yake so ya yi masa
biyayya da auren Saade, duk abin da suke ciki shi da matarsa ya sani, kuma wannan shi ne
matakin da zai iya dauka.
Ga mamakin Mai Askira tunda Yareema ya dukar da kai bai dago ba sai da ya kai aya, da ya
dago idanunsa sun kada sun yi jazur kamar an gumbuda musu borkono, labarin Saade da ya ji
daga bakin mahaifinsa ya gama kashe zuciyarsa, ya luguiguitata. Tun asali kuma ya dade da
wani irin feelings a kan Saadatu wanda daga shi sai Ubangijinsa suka sani. Feelings din da shi
kansa bai san ma'anar sa ba, bai san a muhallin da ya sanya shi ba. Yau da ya samu wannan
labarin na zamowar Saadatu halalinsa, matar auren sa ta sunnah daga bakin da ba zai taba yi
masa karya ba, zuciyarsa ta ki tsugunnuwa a waje daya, sai dawurwura ta ke a cikin kirjinsa
kamar za ta fito ta bakinsa tsabar contentment din da ya cika zuciyar sa da wani sabon yanayi
da ya samu kansa a ciki irin wanda biro ko yawun baki ba zai iya bayyanawa ba.

Lokacin da Yarima ya dago ido don ya baiwa mahaifinsa Askirama amsa, Askirama couldn't
believe cewa hawaye ya gani a idon Yarima......
Hawayen da bai san na menene ba, tsakanin.... bakin cikin abin da ya yi masa, tausayin
labarin Sa'ade, ko ko na farin - ciki ne kai tsaye? Ba zai iya cewa ba!!!

Mu karasa a littafi na 3.
Na yi muku alkawarin cigaban ba zai jima ba, insha Allahu.
Taku har abada;
Sumayyah Abdulkadir Takori.
27th August, 2021

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login