Showing 9001 words to 12000 words out of 53173 words
Chapter 4 - NAMIJI BAYA KADAN One To End True Hausa Novels By Aisha Garkuwa.pdf
time na zuwa zaki bari"
A bakin shiga cikin gidan suka had'u dasu Abba da malam Abubakar Na fitowa
tare suka dan kauce suka basu hanya tare da gaishesu mlm Abubakar ya fara amsawa cikin
girma yace
"Allah ya muku albarka yasa haske a rayuwarku".
Tare suka amsa shi oga yasan wacce Addu,ar akayi musu itako ta dauka a matsayin su na
yaransune suka musu Addu,arga,
Suna wucewa Abba yace "kai Mahmoud zonan"
Ita kuwa cikin gida ta shige abita.
Tana shiga parlon Anty ta shiga inda ta samu su Anty da Su Goggo Zahra gasu Aysha dasu
Rayhana da Fatima dama duk sunzo Anty Rayhana tana yar fawa Amarya Amira kitso suna ta
hira da nishad'i tana shiga suka bige da hira suna ta raha, har dare yayi sanyi sannan suka
farashirin bacci Fatima ce ta kalli Khadija cikin kula tace.
"Ni kam Khadija ina dinkin namu kin dawo shiru kinsan harda nasu Mami da Anty sannan harda
na Amarya"
Tsaki ta dan ja tare da kwanciya tana dan k'ulle igiyar rigar baccin ta
tace
"Kayan suna cikin motar Mahmoud sai goben zai kawosu "
Ajiyar zuciya Anty tayi tare da cewa "har naji tsoro kar bai d'inka ba"
Dariya sukayi tare da kwanciya.
*Kashe gari*
da safe misalin karfe 11 k'ofar gidan Alhj Ibrahim cike yake mak'il da Al,ummar Annabi manyan
mutanen masu fad'a aji da malamai manya da matasa da yara tako ina a cike ake.
Haka kuwa cikin gida
ma makil yake yan uwa da abokan arziki.
Su Khadija an tasa Amira a gaba dasu Fatima suna ta mata tsiya ita ko tuni ta nemi idannunta.
Cikin juyawar iska sautin d'aura Auren _Mahmoud Ibrahim Mahmoud_ da *Khadija Sani
Mahmoud* ya ratsa kunnuwan illahirin mutanen dake cikin gidan cikin mmk da Al,ajabi aka
rink'a kallo kallon juna.
Cikin sanyi Goggo Zahra dake gefe tace.
"Alhamdulillah Allah ya sanya Alkhairi Mahmoudu Allah ya tayaka rik'o"
Rayhana ce cikin kad'uwa tace.
"Goggo Wai wanne Mahmoud d'inne yayi Aure kuma da wacce Khadijan"?
Lkci d'aya kuma Aysha ma tace .
"Nima an d'aure min kai Wai da gske Mahmoud ne yayi Auren"?.
Mami ce ta fito cikin bak'in ciki da had'e fuska da takaici taje gaban Goggo Zahra cikin fushi
kamar zatayi kuma tace.
" fisabilillahi Zahra yayanki yayi mana adalci ace ina Mahmoud ina Aure kuma ko Aure zaiyi ai
sai a nema mai dai-dai dashi ina Khadija ina Mahmoud"?.
Khadija dake gefe cikin mmk da kad'uwa ta zazzaro ido woje tare da dafe k'irjinta
Murya na rawa tace.
"Wai me kuke fad'a ne ban gane kan mgnar ba Wai wacce Khadija kuma wanne Mahmoud
d'in"?.
Cikin fushi Mami tace
"waye kuma in banda ke akwai wata Khadijan ne bayan ke kin juya k'ok'olwan yaro"
Anty ma dake gefe cikin mmk tace
"Mami Khadija nanne aka aurawa Mahmoud"?.
Goggo Zahra ne cikin had'e fuska tace
" toh haramun ne ko yayuna basu kai suyi ikonsu kan yaran su bane"?
Kamo hannu Khadija tayi cikin kula tace
"ki nitsu ki rik'e mijinki Allah yasa shine mijinki na har abada rabbi yasa sai mutuwa ce zata
rabaku".
Lkci d'aya Hawaye ya ballo mata kamar da bak'in kwarya cikin zubda k'ollah tace.
" Na shiga uku Goggo Zahra me kuke nufi. Mahmoud k'anina shine kike kirada sunan mijina"
Sai kuma kuka mai k'arfi ya kofce mata fad'a wa jikin Goggo Zahra tayi cikin kuka mai tsuma rai
da kaji kasan zuciyar mai yinshi cike yake da takaici.
Cikin kukan ta rik'e hannun Goggo Zahra ta kalleta fuska duk hawaye tace.
"Goggo Zahra ase yanzu Dan Allah ya jarabceni da mutuwar Aure sai a maidani tamkar y'ar
kaza Goggo Zahra a rasa Wanda za,a cusamin sai Mahmoud yaro k'arami Goggo yanzu su
Abba ne suka min haka me Na aikata musu da zasu hukuntani da haka".
Cikin bacin rai Anty da ke gefenta ta yarfa mata mari baki na rawa tace.
" iyayen naki kike gayawa haka ase basu isa dakeba kenan Khadija ase bazaki iya musu
biyeyya ba"?.
Ita kam Khadija zuwa yanzu duhu ya rufe mata ido lkci d'aya ta fara jin jiri.
Kalaman, Mami yasata ta k'ara rud'ewa
Cewa take
"Ji muna furci ai da saninki bake kikace kar a gayawa kowa ba Dan gulma yanzu kice baki
saniba"?.
Cikin kuka tace.
" Wlh Mami ban saniba wlh bada yardana akayi ba ".
Sai Kuma ta zame tayi k'asa cikin.......
By Garkuwan Fulani
Maman Jabeer da ikram da Ibrahimν ½νΈ
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*NAMIJI BAYA KAD'AN* pg 7β£ Na Aysha Ali Garkuwa
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
Pure moment of life writer's
P.m.l.w
www.aishaaligarkuwa.blogspot.com
*Bani da lkcin ku bare nace naji zafin zantu kanku a kaina zaginku kanku zai koma abinda na
sani baku da damar dakatar dani akan harkar nan na rubuce-rubuce baku isaba dan baku kuka
saniba kuma bansa ko wacce karantawa a doleba kuma bazan FASA abin danayi niya ba fans
Na muje zuwa ga Mahmoud on top*
Zamewa kan gado tayi tare da kife kanta cikin pillows ta saki kuka mai tsuma rai tana kukanne
har numfashinta na fizga,
Goggo Zahra yace ta matso kanta cikin sanyi tace.
"Haba Khadija Aure fa akayi muku ba zaman banza ba Mahmoud fa d'an uwanki ne shin akwai
abinda baki sani bane a yanzu ba abinda ya rage face kiyi biyeyya ga Allah da manzonsa sai
kuma kiyiwa iyayenkin d'a,a kiyiwa mijinki biyeyyah".
Mgnar Goggo Zahra k'ara sata kuka tayi dan ji take kamar wuta take watsa mata in tace Wai
Mahmoud mijinta ne tuni fuskarta ta jeme tayi jazir idanta duk sun kumb'ura lkci d'aya muryarta
ta disashe har sautin kukan bai fita sosai,
Ayyah Aysha ma sai k'ollah tai ta sharewa dan tasan ba,ayiwa yar uwarta adalciba
Anty Rayhana dama mai sanyi ce da tausayin yan uwanta zama gefenta tayi tana.
" Ayyah Khadija kibar kukan nan haka zai cutar da ke,
Aurene an rigada a d'aura bamu da wani abin yi a kai ni Na fahim ceki,
Kiyi hak'uri da Abinda Mami tace miki insha Allah itama zata fahimta".
Kanta ta dago cikin muryar kukan tace.
"Ni na tsani Mahmoud bana k'aunar ganin shi sabida ya cuceni ya min k'arya sannan ya had'a
min sherri".
Fatima dake tsaye gefe cikin jin zafin furu cin da tayi Na cewa ta tsani Mahmoud ta dan ja tsaki
tare da cewa.
" Toh sai me ki tsaneshin mana ai Uwarsa da mukam muna sonshi".
Tana kaiwa nan ta fice abinta.
Anty ce ta bita da ido cikin mmk sannan ta kalli Goggo Zahra tace.
"Ni tsoro naji kar Auren nan ya haddasa mana fitina a family".
Mikewa Goggo Zahran tayi cikin cewa.
" insha Allah sai Alkhairi ".
Shi kuwa Mahmoud
A k'ofar gida hatta ya Auwal mmk ya rink'yi yana bin k'anin nashi da ido shi da zugar abokanshi,
shi dai yabar batun Auren Khadija tun randa iyayen Nazir sukazo Abba yace musu,
ya mata miji sannan ya basu hak'uri,
ase dama Mahmoud ne mijin"?.
Shiko Mahmoud Yau itace ranar farin cikinsa gaba d'aya bakinshi ya kasa rufuwa gashi yayi fita
ta alfarma ya fito a Mahmoud on top manyan kaya ya saka harda gare shaddace y'ar asali kalan
sararin samaniya sannan yasa hula fara sai takalmi shima fari
Sai agogon Daimon dake mak'ale a hannu shi farar fatarsa ta taimaka wurin fiddashi gashin
kanshi nan duk ya konto ta k'eyarsa sai k'amshi yake zubawa yana taku cikin k'asaita sai fatan
Alkhairi ake mai hatta manyan mutane sai sumik'a mai hannu suna mai Addu,ar Allah tayashi
rik'o.
A d'aya gefen zuciyar Sa kuwa cike take da farga ban ya Khadija zata tsinkayi zancen sannan
taya zata fahimce shi ko me zatace dashi,
a hankali kuma sai yaji sanyi inya tuna yadda suka shak'u a ganin shi ba zatayi wuyar fahimtar
saba.
Da k'yar ya samu ya zullewa abokanshi sannan ya nufi cikin gida amsa kirani Abba,
A parlon shi ya samesu kusan gaba d'ayansu ya suna parlon gaban Abbanshi ya zauna cikin
kula Abba yayi gyaran murya tare dacewa.
"Alhamdulillah yau Allah yasa An d'aura Auren Amira da Amir sannan kuma an d'aura Auren
Mahmoud da Khadija wanda nasan kad'anne daga cikinku suka san dashi.
Abin da nake so ku fahinmta shi Aure nufi ne na Allah haka Allah ya tsara Aure tsakanin
Mahmoud da Khadija ba yinmu bane, yin Allah ne,
Gaba d'aya shiru sukayi sai Auwal ne ya dan kalli mahaifin nashi tare da cewa.
" Tohhh Allah dai ya kyauta".
Amin suka amsa baki d'aya,
Mami ce ta kalli Mahmoud d'in cikin had'e fuska tace.
" Mahmoud matsayin na kenan ina mahaifi yarka Amman har kayi neman Aure cikin muna furci
duk ban saniba wato kana da wata uwar da tafini ko"?.
Cikin sanyi ya dan ja jikinshi ya matsota kanshi ya dan d'aura kan cinyarta tareda cirehular
kanshi.
Murya a sanyaye yace.
"Kimin afuwa Mami na Auren ne ya kama ni dole wlh bazan iya rayuwa ba mata ba ina da
buk'atar mace a rayuwa ta shiyasa Mami Na ba boye miki nayi ba Abba ne yace a bari sai Abu
ya tabbata sannan kuma kin sani,
Annabinmu da kanshi yace
A suturta nema a bayyana samu".
Duk parlon shiru sukayi duk kunya ta rufe su shiko ko a jikinshi,
Haka Abba yai ta musu nasiha har duk suka fahimci illar dake cikin hana shi yin Auren,
Shi kuwa Mahmoud cikin rad'a ya matsota gun Anty Rayhana a hankali yace,
" Anty Ray ina Matata ban ganta ba hankali na ya bar jikina".
Cikin sanyi itama ta bashi lbrin halin da Khadijan ke ciki.
Lkci d'aya fuskarsa ta sauya shi da kanshi yasan yayiwa Khadynshi laifi gashi bai son bacin
ranta'
Suna fita parlon kai tsaye cikin gida yayi aiko yan uwa da abokan wasa sukayi caa a kanshi
suna,
Masha Allah kaga yaro mai k'amshin angwaye Mahmoud on top kenan Allah ya sanya Alkhairi
ya bada zaman lfy.
Shi kuwa murmushi kawai yake d'an yi tare da cewa Amin.
Ita kuwa tana jinshi ya shigo parlon Anty ta tashi cikin jin jirin ta rufe k'ofar sannan ta zame a
wurin cikin jin tsanarsa a ranta.
Anty Rayhana tai ta kiranta ta bud'e tak'i, fir.
Cikin sanyi yace "Anty Ray barta"
Sai ya juya ya shiga d'akin Mami ananma k'anneta sunyi ta mai fatan Alkhairi yayinda wasu ke
mai kallon ya d'ebo dala ba gammo.
Ya fita d'akinshi ya shige cikin k'arfin hali ya ja woyarsa number ta ya tsurawa ido sannan a
hankali ya dannan Calling.
Ita kuwa tana d'akin tayi kukan har ta gaji ta koma ta konta cikin tsiyayar da k'ollah,
A hankali taji woyarta Na suwa bata dagaba har ta tsinke a haka har kusan 5 miss call
Sannan ta rink'a jin sautin shigar text message a nanne ta jawo woyar tana dubawa tabt'a shine
sai kawai ta saki kuka tare da cillah woyar gefe.
Haka yai ta tura mata text da kiranta Amman tak'i kulawa,
ta kuma k'iba bud'e d'akin,
har saida la,asar tai sannan Anty tazo tai ta fad'a tana bud'ewa
Anty ta shiga rik'e da phone d'inta cikin fad'a tace.
"Wai ke meyasa kike da taurin kai ne ya za,ayi mijinki yai ta kira bazaki d'aga ba har sai yaita
kirana".
Mik'a mata woyar tayi tare da cewa "gashi ki karb'a"
Dole ta karb'a
Tana goge k'ollah,
A hankali tasa a kunne cikin dashewar murya da rawan muryar tace,
"SLM "
Shi kuwa jin muryarta ya bashi tsoro cikin sanyi ya koma kan 3 str ya zauna cikin sanyi
da yanayin lallashi yace,
"kiyi hak'ura Matata ki dena wahal min da zuciyarki da jikinki ki jik'aina ki daina min asarar
hawayenki kiyiwa mijinki uzuri matata".
Kuka mai cin rai ta kuma saki jin Wai Mahmoud ke kiranta Matata Wai shi kuma mijin ta.
Shi kuwa kukan ya k'ara tunzuroshi baik'i ace tana kusa dashiba da ya tabbata zai tsaida kukan.
Cikin lallashi yace.
"Hayatina kimin mgn kibar kukan nan".
Cikin kukan ganin Anty ta shiga toilet tace.
" Allah ya isana kuma sai Allah ya saka min ka cuceni".
Sai kuma ta katse kiran.
Anty Na fita tace
"Maza kema shiga kiyi wonka ki fito ki bar kukan nan dan ya isheni haba da mai zanji da
habaicin Mami da k'anneta ko da kukanki haba Khadija ki tausaya min mana kinsan dai banson
kukanki kalli Nabila yarinya k'arama itama kin sata kuka har zazzabi ya rufeta".
A haka dai ta sata dole yaje tayi wonka tana fita ta samu su Anty Ray da Fatima har Amarya ita
suke jira tazo ta basu kayansu da ta karb'o musu jiya.
Mami ce ta lek'o cikin fad'a tace "wai ko baza,a bada kayan bane"?
cikin dishewar murya tace.
" Ayyah Mami kayan suna gun shine fa" Fatima ta karb'o mana".
Baki fatiman ta tab'e cikin takaici tace.
"Wlh bazan kuma zuwa ba naje kusan sau 3 yace bazai bayarba in mun damu kije".
Cikin cika da takaici tace.
" Toh wlh sai dai mu hak'ura Dan bazan jeba".
Anty ne tace .
"Ke harda wlh hinki to wlh maza mik'e ki karbo kinaga tun d'azu Amira ta shirya ke ake jira duk
wuri ya cika".
Mami ce ta kalleta cikin fad'a tace "maza fito ki karbo mana"
cikin zubda k'ollah tace.
" Ayyah Anty kirashi kice Anty Ray zatazo ta karb'a".
Jin tausa yinta yasa ta kirashi yana d'agawa sai cewa yayi Anty,
"Khadija taxo ta karb'ar muku abinku mana"
Haka tasa dole suka sata ta fito ta nufi part dinsu a parlon ta tsaya cikin jin tsanarsa tace
"ka fito ka bani kayan"
Shi kuwa dama tunda ya ga tana zuwa ta window yayi sauri ya fitar da Nata cikin din kunan
sannan ya fitar da saura ya kira Fatima tazo ta karb'a.so tana tsakiyar parlon shi kuma ya shigo
parlon ta bayan ta.
Jin motsin mutune a bayanta yasa ta juyo da sauri ganin shi ya sata sai hawaye shar a ranta
take cewa yanzu d'an yaron nanne za,ace mijin ta.
Kanta ya nufa itako ganin haka yasa ta rink'a Jan baya-baya har ta fad'a kan 3 str.
A hankali ya zauna gefenta cikin tsura mata ido yasa hannu zai jawota tai maza ta buge hannu
ganin haka yasa cikin isa ya fizgota jikinshi ya matsota a k'irjinshi cikin sauk'e numfashi ya
tallabo kanta murya da jikinshi na rawa yasa hannushi ya....
By Garkuwan Fulani
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*NAMIJI BAYA KAD'AN* pg 8β£ Na Aysha Ali Garkuwa
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
Pure moment of life writer's
P.m.l.w
www.aishaaligarkuwa.blogspot.com
_har kullum ina tare daku masoya na Allah ya barmu tare rabbi ya k'addara saduwarmu a
jannatul Firdausi_
Kanta ya tallab'e cikin sanyi da tsura mata ido,
ya rink'a jujjuya mata kai alamar tayi shiru,
ita kuwa tureshi take da iya k'arfinta cikin zubda k'ollah tare da kauda kanta don bata son ganin
fuskarsa bare su had'a ido,
Shi kuma k'ara tallabe kan nata yayi cikin sanyi tare da sa idonshi cikin nata ganin yadda ya
tsareta da mayun idanunshi yasa ta lumshe nata,
A hankali ya sunkuyo da kanshi kan fuskarta harshensa ya dire kan kuncinta hawayen dake
kwaranyan ya rink'a lasa tare da lumshe nashi idan.
Ita kuwa cikin tsoro da cikikar takaici ga mmk ta bud'e idanta jin wani sabon salon rainin wayon
da Mahmoud din ke mata hannu ta sa kan k'irjinshi da nufin tureshi shi kuwa jin hannu ta a
k'irjinshi yasa ya fizgota ta fad'a jikinshi matsota yayi da hannu d'aya d'aya hannun kuma ya
tallabo kanta ya manne bakinshi kan nata,
Cikin jin tsoron ta kuma zaro ido woje tare da rumtse bakinta gam tana tureshi amman ina koya
k'arfin na miji ya zarce na mace.
Shiko jin ta rufe bakinta bai karayar da shiba sai lalubo lips d'inta yayi cikin wani salo ya cabke
dan tsukekken bakinta ya rink'a mai wani irin tsotsa,
tuni ya fara fita hayya cinsa jikinshi ya k'ara d'aukan b'ari duk sai tsuma yake numfashi sa sai
korar juna suke idansa kuwa kamar suyi aman wuta tuni ya fara wani irin nishi.
Abin ya wuce saninta dole tsoronta ya k'aru dan Mahmoud ya koma tamkar mayunwacin zaki
duk sai rawa jikinshi keyi.
K'arfinta ta tattaro baki d'aya ta yunk'ura ta zame bakinta cikin nashi tasa hannu ta ture kanshi
cikin tsoro da tsanarsa tace.
"Wlh Allah ya isana aikin ba banza yaro k'ara mi da kai sai rashin kunya da fitsara yanzu kai in
kana da kunya da hankali zaka min haka sai kuma ta saki kuka tuna wai Mahmoud ne ke shirin
lalubeta harda tsotse mata baki.
Shi kuwa hannu ta ya kuma fizga ta fad'o kanshi yasa hannu duk 2 ya ruk'k'ume ta.
Da k'yer cikin wahala da rawan jiki da murya na carkewa yace,
" Haahumm hummm shihhhhihhh wayyyyyyy"
sai kuma ya k'ara narkewa jikin ta.
Cikin sab'b'atu da rud'u
Yace
"Ohhh Habitti kar kar karki gujeni plxx karki hukuntani da guduna nasan na miki laifi,
Amman wlh sonki ne sanadi,