Showing 42001 words to 45000 words out of 53173 words

Chapter 15 - NAMIJI BAYA KADAN One To End True Hausa Novels By Aisha Garkuwa.pdf

29 Aug 2025

1052

kallon Abidan tsaye akanta tana murmushi
"Anty Khadeeja ina kwana ? ga breakfast d'inki nan yakamata ki tashi kici kinga bake ka d'ai
bace"

kallon mmk Khadeeja tai mata ya akayi Abida ta xama haka ? yarinyar da ko kallan arxik'i bata

mata
d'aga mata kai khadeeaj tayi Abidan ta fice mik'ewa tayi akasalance ta shiga toilet tayi wanka ta
fito ta xauna ta fara breakfast d'in har ta gama kwanciya ta k'arayi a hnkl taji kwanciyar ta isheta
d'an k'aramin tsaki taja ta mik'e ta koma falonta k'amshin data ke so taji a hnkl ta lumshe ido
tana bin wajen da take jin k'amshin na fitowa har babban falon gidan muryar Mahmoud taji da
Abida suna kyalkyala dariya gabanta taji yayi mummunan fad'uwa labulen falon ya d'aga
hangosu tayi cikin wani yanayi na jin dad'i
wani irin xugi taji xuciyar ta nayi ta juya tana k'ok'arin barin wajen sbd bak'on yanayin data tsinci
kanta ciki wanda tarasa na menene ga uban jiri data ji lokaci d'aya ta juya kenan taja k'afarta da
tai mata nauyi gum ta bige gefan goshinta
k'aran buguwar sukaji suka fito dukansu shida Abida.


plc plc kuyi hakuri da wannan kad'an ne dai gobe inshaa Allah xan cigaba da gashi nagode
sosai fans da soyayyar ku


By
Garkuwan fulani
*NAMIJI BAYA KAD'AN* pg 4⃣8⃣to5⃣1⃣ Na Aysha Ali Garkuwa


pure moment of life writters
p.m.l.w

*K'aunar ki a raina bata da adadi har kullum ina alfahari dake Ummee Garkuwa ke tawace ni
takice rabbi ya sadamu a jannatul Firdausi*

```Bazan manta da k'iba kun zamo ni Na zamo Ku ina alfahari daku Khaleesat haydar
Anty Fauzo Ummu Khamal Dr Ruk'ayyat Aysha A Muhammad Rufaida Yusuf Jannart lamido```

sannu kawai suke jera mata shida Abida runtse idonta tayi sbd kayan dake jikin Abida na nuna
ilahirin siffarta kanta kawai ta d'aga musu ta ja k'afarta ta bar wajen xuciyar na mata wani irin
tuk'ik'i data rasa na menene
tana xuwa kan gadon ta tafad'a a wahale tana mmkin sauyawarta
wani uban tsaki taja had'e da runtse idanuwanta hangosu tayi a yanayin data gansu da sauri ta
bud'e ido tan jijjiga kanta sam tarasa wanne kalan tunani xatayi ta samu sauk'in wannan
yanayin data fad'a wanda tarasa gane kansa ga uban xogi da gefen goshinta ke mata.



washegari jikinta asanyaye ta tashi tarasa gane yanayin data ke ciki rabonta da Mahmoud tun

jiya data bige sukai mata sannu kanta ta dafe tana kallon breakfast d'in da Abida ta kawo mata
tun d'axu da safe.
jikinta ba kwari ta tashi daga xaunen da take ta shiga toilet tai wanka ranta ajagule.


tunda Khadeeja ta tare Mamy ranta ke suya abin na matuk'ar damunta tarasa gane inda
wannan k'addararren aure xaije uwa uba cikin da akace khadeejan nadashi sam ko kad'an bata
k'aunar wannan cikin hnklinta tashe take kai komo tarasa hanyar da xatabi ta warware wannan
d'aurin gwammon na auren Khadeeja da d'anta Mahmoud anty Ray ce tai sallama da kyar
Mamy ta amsa tana kallom fuskar ta hannunta tasa ta d'auki hijab ta kalli anty Ray tai mata
alama da ido na sutafi ba musu anty Ray tabi bayanta har suk fito haraban gidan inda motocin
su suke kai tsaye mota mamy ta shiga anty Ray ta shiga driver yaja su suka tafi gidan
Mahmoud d'in dan xuciyar mamy takasa nutsuwa sai taje daga kalan xaman da sukeyi babban
burinta taciwa baxawarar yarinyar nan mutunci ta hkr ta bar mata d'anta dan tasha alwashin yau
yau d'in nan sai Mahmoud yasaketa tagaji da tafasan da xuciyar ta ke mata

akan hanya Anty Ray taiwa Mahmoud test akan lallai ya fice ya bar gidan kafin mamy tak'araso.

yana ganin test d'in ya maxa ya bar gidan hankalin sa atashe yarasa gane kan mahaifiyar sa
tak'i hak'ura da wannan lamarin na aurensa da Khadeeja.

driver na tsayawa afusace ta bud'e k'ofar motar ta fito tun kan tashiga gidan ta fara kiran sunan
Mahmoud a k'ufule Anty Ray cikin sanyi da mmkin sauyawar mamy lokaci d'aya akan auren
Khadeeja da Mahmoud da tayi
kai tsaye b'angaren khadeeja ta nufa tana kwalawa Mahmoud kira dan tasan mayen ta ne
xuciyarta na bata yana cen d'akinta yana maitar tashi

kamar daga sama Khadeeja taji kiran tana barci dan har cikin d'akin mamy ta shigo tana surfa
masifa tana kwalawa Mahmoud kira
a hankali Khadeeja ta bud'e idonta dayayi ja alamun bacci ne sosai acikinsa
wani wawan mari mamy ta d'auketa dashi wanda yasa Khadeejan wartsakewa daga nannauyan
baccinta a gigice ta mik'e had'e da sakin wani bahagon kuka me ban tausayi Anty ray ma da
Abida mmkin marin sukai fuskokin su alamun tsoro suka k'ura musu ido cike da tausayin
Khadeeja nuna mami tayi da d'an yatsanta cikin k'araji da masifa tace
"uwarki xatai sallama ki kasa amsa mata ?? tabbacin baki da tarbiyya ko ? tun yaushe nake
kwalawa d'ana kira kina ji kinyi biris dani, to ni ce uwar Mahmoud ayau kuma sai ya rabu dake
tambad'ad'd'iya tarasa wa xata aura sai k'aninta har da d'aukan ciki dan tsabar tambad'ewa,
na tsani wannan k'addararren auren naku kuma ayau xaa warwaresa dan bazan iya cigaba da
xama dake a matsayin matar d'ana ba wllh !"

tak'ara tana fidda huci naban takaici babu abinda ke tashi sai sautin kukan khadeeja mai ban
tausayi.

waiwayowa mami tayi tana kallonsu Abida da suka tsura mata ido
"ina yake shima shanyayyen?"
girgixa mata kai Abida tayi tana jin ba dad'i aranta dan tasan muddin aka tab'a Khadeeja tofa
bata tab'a gane kan mijinta shiyasa ko kad'an batasan wannan hayaniyar yanxu
"mami ya fita cen gida wajen Abba kuma bana jin xai dawo da wuri"
wata wawar ajiyan xuciya mami tayi "sai ya dawo yau yasame ni shima dan ubansa yau sai ya
rabu da tsohuwar guxumar nan !" tana cikin masifar Khadeeja na fidda kukan takaici kuka na
fidda sauti na ban tausayi ga duk mai sauraronta

wayar mami ce tayi k'ara number Abba tagani a k'ufule ta d'aga itafa ayanxu batak'i aurenta ya
mutu akan raba auren Khadeeja da Mahmoud abinda taji abban na fad'ane yass jikinta ya
sanyaya ta kashe wayan tana fidda huci da kuma mmkin abinda Abban yace mik'ewa tayi ta
watsawa Khadeeja mugun kallo "kisani tsohuwar bazawara kik'a tunanin wani xawarcin nan
gaba zanje na dawo duk dare yau sai dai ki kwana gidan ubanki yarinya sai kace mayya !?"

fuuu ta wuce anty ray da Abida suka bi bayanta mota ta fad'a tana takaicin rashin samun
Mahmoud d'in a gida girgixa kai Anty ray tayi tace "mami yakamata ki fuskanci yarannan ki duba
damuwarsu, auren nan daga Allah ne kina kallon rabo har ya ratsa..."
katseta mami tayi
"rabon banza me ake da rabo irin wannan idan ina raye baxata haife wannan rabon ba"
shiru anty Ray tayi dan abin yafi k'arfin ta suna komawa gida lbrn da Mamy taji ya gigita sosai
Abba ne ya sa ta ta xauna ya fara mata jawabi
"kinga abinda akaiwa Amira ko ? baxan yarda ba sai na d'au mataki UWAR MIJINTA tai mata
dukan tsiya har cikin jikinta ya xube sannan ga gociyar k'ashi a hannunta duka na fitan hankali
kamar ba mutun ba kalleta fa !"

wani irin masifaffen yanayi mami ta shiga lokaci d'aya tana kallon amira da fuskarka tasha
bandage tana fidda kwalla ilahirin kamanninta sun sauya baxakace Amira y'ar gayu ce akai
mata wannan mummunan dukan kuma ma wai uwar mijinta wani kuka mai k'una ya kufcewa
mami kasa jure kallonta tayi gaba d'aya jikinta amace yake xuciyarta na harbawa da mugun
sauri takaici da bak'in cikin dataji yanxu bata tab'a tunanin akwai irinshi ba,

jikin Abba a mace ya mik'e ya fice daga falon yana ayyana shi kad'ai yasan irin matakin da xai
d'auka kan mutanen nan

wani bahagon kallo anty ray takewa mami tana girgixa kai kwalla na fitar mata
" mamy kin gani ko ? ishara ce wannan kome ? kin daki y'ar mutane anyiwa taki dukan tsiya
kina k'ok'arin xubar da cikin y'ar wani an xubar dana taki y'ar,
duniya kenan yanxu sakayya nan danan take xuwan wa mutun kanayi xa ai maka ninkin ba
ninki wanda Allah keso yake nunawa ishara"
ta mik'e kwalla na xubar mata tana kallon Amira da itama kwallan takeyi jikin mami asanyaye
take sauraron Anty ray xuciyar ta asanyaye.

yana kallon sun fice daga gidan ya shigo hnklinsa atashe kai komo ya fara yi yana son sanin
halin da Khadeejan sa ke ciki ya na matuk'ar k'aunarta da kyar ya iya jurewa rashin ta na kwana
biyu kasa jurewa yayi jikinsa na rawa yai b'angaren ta sautin kukanta ya hautsina masa xuciya
wani irin yanayi na b'acin rai ya xiyarceshi kai tsaye wajenta yayi yana jin takaicin fitar kukan
nata dayake tab'a masa xuciya.


by
Garkuwan fulani[5/14, 5:15 PM] Miwasmiti Author:
*NAMIJI BAYA KAD'AN* pg
5⃣2⃣to5⃣5⃣ Na Aysha Ali Garkuwa


pure moment of life writters
p.m.l.w

*Wannan shafi nakine ke kadai Aminiyar kirki Fiddausi Sodangi Allah ya bar zumunci*

cikin wani irin taku na k'asaita ya shigo cikin d'akin ganinta a takure cen k'arshen gado ta cusa
kanta cikin cinyoyinta kukan ta na fita cikin wani sauti me hautsina masa xuciya
kai tsaye kusa da ita ya k'arasa ya xauna gefenta had'e da janyo ta jikinsa k'amshin turarenaa
data ke so ta shak'a shiya hana ta hankad'esa dan mugun haushin sa
take shi akanshi akai mata marin data hango taurari
duk da haka sai da tayi yunk'urin kwace kanta ta kasa
dan ba k'aramin ruk'o yai mata a k'urjinsa va hannunsa ya sa ya xuge xif d'inta
ya cusa hannunsa cikin jikinta yana shafa gadon bayanta
had'e da shafar fatan jikinta mai laushi da tsantsi kasa mata magana yayi sbd
kukan ta na sa jin xafi
musamman yasan dalilin faruwan kukan
yasan mami ce cikin jarumta da dauriya had'e da jin dad'in shafar da yakewa fatarta data fara
sashi cikin wani yanayi ya fara magana cikin muryar lallashi
" kiyi hkr babyna ki dink'a kallon komai kamar bai faru ba, laifi nane ni na janyo miki amma kiyi
hkr komai xai wuce inshaa Allah,
ki d'auki komai amatsayin k'addara wacce xata xame miki alheri nan gaba ko ma ince ta xama
musammaan dan babyn dake jikinki da kuma aurenmu shi kad'ai ya isa yasa ki gane ko mai
muk'addari ne daga Allah,
khadeeja babu wani bawa da ya isa ya kaucewa k'addarar sa
tabbasa ikon Allah yafi k'arfin komai Allah ya k'addara ke tawa ce babu wanda ya isa ya rayu
dake saini babu wanda ya isa ya dasa miki d'a sai ni babu wanda ya isa ya san budurcinki
yasanki a y'a mace sai ni duk da irin aure auren da kikayi sai da Allah ya tsare min ke wannan
bai isheki yadda da k'addara ba ?"
abad'ini maganarsa taso yin tasiri axahiri kuwa wani d'ank'aramin duka ta kaiwa k'irjinsa had'e

da fashewa da kuka ta turesa ya rik'o ta sosai had'e da sake mannata k'irjinsa kamar xaa kwace
ta har sai da tayi k'ara dan ya had'a jikinsu sosai kamar xasu manne su xama abu d'aya.

cikin kuka ta fara magana ranta a b'ace yaron nan iskancin sa na k'ona mata rai
" ka kyaleni nace ! da gaskiyan mami data ce min k'atuwar banxa da k'anin cikinta wannan
wacce iriyar wahalalliyar rayuwa ne ace ina auren k'ani na harda ciki ? wannnan cikin sunasa
gawa dan baxan haife takaici ba !"
ta k'arasa da kuka sosai tana duka jikinsa
still hannunsa na cikin jikinta yana shafawa da k'arfe har xuwa saitin cikinta murmushi yayi yana
mamakin maganganunta
khadeeja akwai son girma yasani tun asali haka take amma meyasa tunaninta bai xuwa kan
way'anda suka fita daraja ?
hankalinsa kwance kamar bata fad'a masa wata magana ba
"khadeeja kina karanta tarihin me sunanki kuwa ? kina bincikan manyan mata da sukaiwa
addini hidima masu daraja da k'ima"
lumshe idonsa yayi
dai dai inda yakai hannunshi ruwan cikinta yana jin dad'in akwai d'ansa manne a ciki
"kin san tana da shekara nawa ta auri masoyinmu annabi MUHAMMAD (s.a.w)?
itace mace ta farko data fara karb'an addini meyasa tilastawa kanki abinda bai kai ya kawo ba ?
ni dake Khadeeja har abada ba rabuwa haka xaki cigaba da haifamin y'ay'a kyawawa kamarki !"
ya xamota daga jikinsa yana kallan k'aramin bakinta fuskarta tabb hawaye harshensa yasa ya
lashesu tana fusge fusge yasa hannu ya rik'e fuskan ya manna bakinshi cikin nata ya cafko
harshenta yai mata wani cool kiss yadad'e yana shansu cikin sanyi da kwarewa idon shi a
lunshe sannan ya saketa idonshi sun kad'a sun canza kala ajiyar xuciya yayi sannan ya mik'e
ya rungume da hannuwansa ya xuba mata manyan idanuwansa da suka sauya kala
ki kular min da kanki da kuma babyna idan baxaki daina kukan nan ba ayau sai na maimaita
abinda ya faru har na baki baby ya k'arashe maganar had'e sakin murmushin mugunta
wani wawan kallo tai masa na jin haushi ya juya gaf da xai fita ta d'aga muryan ta me kuka tace
"ciki dole na xubar Mahmoud ko baka so sai dai ko mai xai faru ya faru"

kai ya girgixa ya fice ransa ab'ace dan bai k'aunar yaji wani abun wanda xai tab'a masa lafiyan
babynsa balle khadeeja na shan alwashin rabasa da gudan jininsa yasanta da kafiya tsab xata
aikata abinda tashe girgixa kai yayi direct da yafito gidansu Khadeejan ya xarce sam baiyi
niyyan had'ata da iyayenta ba bashi da mafita tunda cikin ajikinta
yake tsoronshi d'aya
xata iya aikata duk
abinda taso kansa ya
dafe yana jin
takaicin halin data
jefa kanta tak'i
hak'ura

gidansu ya shiga cikin murna mama ta tarbe shi bayan sun gaisa kansa a k'asa yana tunanin
hanyar da xaibi ya fad'awa maman
ajiyar xuciya yayi
kokad'an bai son
had'ata da iyayenta bashi da wata mafita ne sai wannan
cikin hikima ya fad'awa mama kafin ya kai k'arshe ta fara fad'a ranta matuk'ar b'ace
harshi ta had'a kan meyasa tuntuni bai fad'a ba jikinsa asanyaye yabar gidan .


yana barin gidan mama ta kira baban Khadeejan ta fad'a masa kan xataje tai mata fad'a bai
hana ba dan shima ranaa ya b'aci abinda yaji khadeejan nasonyi,

tana kwance idonta a rufe maganganun da Mahmoud yai mata d'axu sun ratsata tabbas
wannan al'mari daga Allah ne amma yaxatayi da k'iyayyar mami ?
juyi ta k'arayi had'e da dafa cikinta wani takaici ya taso mata ta saki k'aramin tsaki muryar
mama taji tana sallama zunb'ur ta mik'e da sauri tai falo ganin maman yasa ta k'arasa wa da
sauri.
kallon data ga maman na mata ne yasa jikinta yai sanyi ta kalli mama da idonta da ya cicciko da
kwalla a hnkl tace

" mama sannu da xuwa"
shiru tayi bata amsa haushin maman d'aya ace wai khadeejan ta ke k'ok'arin aikata d'anye aiki
akan d'an cikinta tsaki mama tayi ta xauna tana karewa khadeejan kallo
cikin hasala da fad'a ranta ab'ace tace
"any'a khadeeja kina son ki cika da imani ? kin wa tsar da kyakkyawar tarbiyyan ki ? ina iliminki
hankalinki da tunanin ki ? wllh muddin naji wani lbr akan cikin nan xan yi mummunan sab'a miki
Abban kuma yace sai dai ki nemi wani uban!"
zaro ido khadeeja had'e da xuban hawaye na mmkin inda mama taji xancen wato Mahmoud ya
fad'a musu takaicinta ya k'aru
tsawar da mama tayi ne yasa ta d'agowa da sauri
" muddin baxaki bi mijinki ba toh ki nemi wasu iyayen tunda kike rashin hankalinki naji lbrn
komai xuba miki ido ne naga abin xai xama bana k'are ba to wllh ki kuka da kanki taurin kan
tsiya kamar kanki farau shi sunna yayi kuma Allah yai mishi albarka dan ina alfahari da wannan
auren wllh muddin kikace xaki dink'a b'ata masa rai sai dai ki nemi wasu iyayen, k'aramar
yarinya ce ke da xaayita lallashinki shashasha kawai !"
mama ta mik'e cike da fushi ta bar falon da sauri Khadeeja tabi bayanta tana bata hkr cikin
zubda hawaye tsayawa mama tayi
"muddin kina son zaman lfy ki kuma kiyaye b'acin ranmu kibi mijinki"
ta tafi tabarta a nan tsaye tana kukan takaici .

da daddare bayan ta idar da sallar isha'i xuciyarta ba dad'i sam bataji dad'in fad'an mamansu ba
Abida ce ta shigo d'akin tana k'amshi jikinta sanye cikin k'ananan kaya masu fidda surarta a fili
cikin yauk'i da iyayi tayi farr da ido

"anty Khadeeja barka da dare kixo babban falo xamuyi dinner megidan nason xanyi magana
damu"
ta juya ta fita kallon mmk Khadeeja tai mata sannan ta mik'e jikinta asanyaye ta tafi babban
falon yanayin data gansu ne yasa ta fad'uwan gaba abida na jikinsa tana xuba masa kissa yana
biye mata ganinta bai sa Abidan sauka daga jikinsa ba sai da ya janyeta had'e da xubawa
Khadeejan kallo haushi sosai yakamata dan jikinta har rawa rawa ya fara wanda tarasa na
menene.

da kyar taci abincin sbd tarin takaicin da Abidan keyi na shigewa Mahmoud shi kuma yana biye
mata duk idanuwansa na kan Khadeeja bayan sun gama yayi hamdala had'e da yi musu nasiha
na su xauna lfy sannan yace yau xasu raba kwana xai fara daga d'akin khadeeja itakam yana
gama jawabin tabar wajen dan gaba d'aya abunda sukai yasa ta nadamar xuwa falon tun farko
gashi ma wai har sun raba kwana kuma wai a d'akinta yake.


by
Garkuwan fulani
[5/14, 10:51 PM] Miwasmiti Author:

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login