Showing 15001 words to 18000 words out of 21631 words
mai keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin jaruma Husnaila da saurayi Hizmal a cikin gidan tsira domin tseratar da rayuwar yaro Humair makaho,
****
Lokacin da boka Dargas da sauran tawagar matsafa biyar suka bayyana a ɗakin sirri domin gudanar bincike bisa bayyanar bakuwar jarumar da ta ceci rayuwar al'ummar kasar daga GOBARAR DAJI wato gimbiya Hushriba bintu ishwar,
Bayan binciken da bokayen suka yi suka gabatar da jawabin binciken su
Sai sarkin bokaye Dargas ya dube su yayi gyaran murya yace
"Bisa ga dogon nazari da kuma abinda bincike ya tabbatar shine jaruma Hushriba ba tazo domin ya cutar da mu ba kawai dai taso ne mu haɗa karfi da karfe domin kowanne mu ya kai ga biyan buƙatar sa,
Amma sai dai ba zamu saki jiki da ita ba domin kunsan cewa ba'a bawa mata yarda a cikin al'amura
Matukar baku mallake su ba shin ina cewa kun taɓa karanta Littafin KUNDIN MATSUBBATA Hikayar jarumi Hilairu da Baiwa luzra
Kun ji irin cin amana da yaudarar da tayi masa daga karshe m
Bayan ya siyar da rayuwar sa ya ceto ta da ma mahaifan ta,
Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin bokaye Dargas sai sauran maysafan su kayi na.am
Boka Dargas ya ɗora dacewa "wani abun takaici da na gani a cikin halarar tsafi ma shine tuni su saurayi Hizmal sun samu nasarar fice daga cikin gidan tsira sun bazama izuwa duniya bisa taimakon wani hatsabibin aljani mai Marhutul-Azab da halin yanzu babu saurayin aljani mai tashen balaga kamar sa a fagen karfin damtse da jarumtaka,
Yanzu batare da bata lokaci ba zan umarci hadimin aljani na domin ya dawo dasu mai girma sarki Shazwan domin a halin yanzu jiran gawa babu rai suke yi a can gidan tsira,
Sa'adda Sarkin bokaye Dargas yazo nan a jawabin sa shafi wani gurun tsafi a damtsen hannun sa
Take wani aljani mai kama da tsuntsun batoyi ya Bayyana gare sa, ya kwashi gaisuwa
Boka Dargas ya dubesa ya kai Haulatul- infal kayi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka tafi izuwa gidan tsira ka ɗauko mai martaba sarki Shazwan da tawagar sa acan inda ka dauko mu a ɗazu ni da jama'a ta,
Koda jin wannan umarni sai Aljani Haulatul-infal ya risina sannan ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba.
Daga wannan jawabi ne kowa ya kama gaban sa ɗakin taron ya watse,
Wannan shi ne abinda ya wakana acan birnin zawatul-ifdal.
Lokacin da aljani Marhutul-Azab ya tsala da matsanancin gudu a sararin samaniya ɗauke da Jaruma Husnaila,saurayi Hizmal da yaro Humair makaho,
Sai ya wanzu yana mai keta gajimare tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Nan fa Saurayi Hizmal ya kama kalle-kalle yana mamakin yadda sararin samaniya yakasance domin wannan ne karon sa na farko a rayuwarsa da ya taɓa tashi sararin samaniya bisa kan aljani,
Tsawon daƙiƙa hamsin ana wannan tafiya babu wanda yace ƙala,
Sai daga bisani ne jaruma Husnaila ta katse shirun da ya wanzu ta hanyar buɗar baki tayi gyaran murya sannan dubi saurayi Hizmal tace"Yakai Hizmal shin kana ganin cewa yanzu kai tsaye zamu huce ne izuwa hanyar da zata sada mu da dajin Baitul-shamshan?,
ko kuwa zamu jira ne har izuwa lokacin da SARKIN SADAUKAI zai kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI?
Koda jin waɗannan tambayoyi Daga bakin Husnaila sai Hizmal yayi gyaran murya yace
"Ya sunaila haƙiƙa kin kawo maganganu masu muhimmanci daya kamata muyi dogon nazari akan su,
Amma dai bisa shawara ta ina ganin zai fi kyau ace mun tunkari dajin Baitul-shamshan domin a halin yanzu,
Dalili na na faɗin hakan kuwa shi ne a Kowa ne hali bokaye,sarakai cikin farautar yaro Humair suke
Idan muka ce zamu tsaya sai ranar da jarumi Hibairu zai kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI zai kasance waɗansu sun riga mu isa dajin Baitul-shamshan,
Haƙiƙa dai masu iya magana na cewa a bari ya huce shine ke kawo rabon Wani,
Koda jin amsar tambayoyin da ga bakin Hizmal sai sunaila tayi shiru tamkar tana nazari
Daga bisani ta dubi aljani Marhutul-Azab tace"yakai Marhutul-Azab mene ne ra'ayinka akan wannan magana,
Marhutul-Azab yace cikin kakkausar murya"Tabbas maganar da Hizmal ya faɗa shawara ce mai kyau,
Domin abinda baku sani ba shine,
Daga nan izuwa dajin Baitul-shamshan tafiya ce ta tsawon shekaru ɗaya bisa saurayin aljani mai tashen balaga,
Amma ni zan iya gajarce mana tafiyar cikin kwanaki sittin da huɗu,
Domin ahalin yanzu a kaf jinsin aljanu babu aljani mai tashen balaga da karfin gudu tamka ta,
A yau saura kwanaki sittin da huɗu cif jarumi Hibairu ya kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI.
Kun ga kenan ranar da zamu isa dajin ranar ne SARKIN SADAUKAI zai bayyana a sararin duniya,
Bani da tabbacin akwai wanda zai riga mu isa dajin Baitul-shamshan ɗin,
Koda jin wannan wajabi daga bakin aljani Marhutul-Azab sai Hizmal da sunaila suka cika da matukar farin maral misaltuwa,
Daga wannan furuci ne kowa yayi shiru aka cigaba da tafiya,
Wannan shi ne abinda ya faru da Jaruma Husnaila da saurayi Hizmal da yaro Humair makaho,
Bayan aljani Marhutul-Azab ya dauko su daga cikin gidan tsira,
*****
BAHREN
A Can ƙasar bahren kuwa, al'amarin sarki uslaim kuwa tun ranar da boka ƙarzum ya bayyana gare sa,
Domin ya yi masa bayani game da batar yar sa gimbiya zarifa,
Bai sake bayyana a gare sa ba sai wata rana da hantsi sarki uslaim na zaune a bisa karagar sa ta mulki a fadar sa,
A wannan lokaci fadar ta cika Maƙil da al'umma babu masaka tsinke kowa na zaune bisa kujera,
Kwatsam sai aka ga wani bakin duhu ya bayyana a tsakiyar fadar
Sannu a hankali sai duhun ya riƙiɗa izuwa wani dattijo fari kakkaura ma'abocin kwarjini,
Fuskar sa cike da ƙasumba da gemu farare sol
Sanye da jajayen tufafi, hannun sa riƙe da kwagirin tsafi dake canza launi izuwa siffa daban daban-daban,
Ba wani ba ne wannan dattijo ba face boka ƙarzum
Da bayyana sa sai ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa
Ga sarki ƙarzum,
Bayan sarki ya amshi gaisuwar sai boka ƙarzum ya miƙe tsaye tsam ya nufi wata ƙasaitacciyar kujera dake kusa daf da inda karagar mulki take yana mai dogare da kwagirin sa,
Ya na isa ya zauna abisa kujerar, sai ya juya ya fuskanci sarki uslaim fuskarsa babu yabo babu fallasa cikin wata irin kakkausar murya yace"ya shugaba na kayi sani cewa bisa binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na na gano cewa lokacin gudanar da tafiyar mu yayi domin saduwa da SARKIN SADAUKAI domin ka bayyana masa buƙatar ka na son ya ceto maka yarka gimbiya zarifa daga fadar Sarkin bokaye,
Ya shugaba na kayi sani cewa a halin yanzu ilimin tsafi ya tabbatar mini da cewa babu wani mahaluki dazai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI face wani yaro da ya kasance makaho ana kiransa da suna Humair,
A halin yanzu wani hadimin aljani da ake wa laƙabi da Marhutul-Azab ya dauki yaro Humair tare da waɗansu jarumai biyu domin su isa dajin Baitul-shamshan domin saduwa da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI
Domin su ma su bayyana ma sa nasa bukatun,
Saboda a halin yanzu ba mu da wani abin farauta da huce yaro Humair makaho,
Domin dole shine zai iya magana baki da baki da Sarkin sadauki,
Ya zama wajibi agare mu mubi sahun aljani Marhutul-Azab domin mu riski yaro Humair,
Sa'adda boka ƙarzum yazo dai dai nan a jawabin sa sai sarki uslaim ya cika da matukar farin ciki maral misaltuwa bai san sa'adda murmushi haɗe da yar karamar dariyar farin ciki suka suɓuce masa ba
Cikin hanzari sarki uslaim ya mike tsaye zumbur ya shiga izuwa gidan sarauta domin ya kimtsa,
Jim kadan sai gashi ya bayyana sanye cikin gagarumar shigar yaƙi tare da dakarun rakiya gudu dubu ashirin, haɗe abin guzuri da kuyangi masu hidima,
Batare da wani ɓata lokaci sarki uslaim ya miƙa rikon sarautar sa ga wazirinsa,
Sannan aka dunga aka fita izuwa wajen faɗa, bayan an fita ne sai boka ƙarzum ya kwalawa hadimin aljanin kira har sau huɗu,
Aljani ya bayyana gare sa ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa
Aljanin yakasance gabjejen kato mai tsawo da kwarjini sosai,
Komai jarumtakar Mutum idan yayi arba dashi sai ya ɗimauce saboda tsanin munin sa
Boka ƙarzum ya dubesa yace
"Yakai Darmanu ibn kauƙas kayi sani cewa bakomai ne yasanya na kirawo ka izuwa nan ba
Sai domin ina so ka ɗauke mu ni da wannan tawagar
Kabi sahun aljani Marhutul-Azab da halin yanzu ya durfafi dajin Baitul-shamshan,
Ina so ka cimmu su a Kowa ne, ya Darmanu ibn kauƙas kayi sani cewa matsawar ka gudanar da wannan aiki yadda na buƙata,
To zan yan taka da bauta da ka shafe tsawon shekaru kana yi agareni,
Koda jin wannan umarni daga bakin boka ƙarzum sai Aljani Darmanu ya sake risina agareshi yace
"An gama ya shugaba na yana Gama faɗin hakan sai ya shimfiɗe gadon bayan sa take sarki uslaim da boka ƙarzum suka hau bisa kan sa suka zauna,
Dakarun rakiya, guzuri gami da kuyangi suka koyi koyi dasu suka hau bisa gadon bayan Aljani Darmanu,
Cikin kuzari da karfin damtse Darmanu ya yunkura ya tashi izuwa sararin samaniya tare da kaɗa manyan fuka fukan sa,
Jama'a na ɗaga musu hannu tare yi musu fatan samun nasara har suka ɓace ɓat a cikin gajimare tamkar basu taɓa wanzuwa ba,
Wannan shi ne abinda ya faru da sarki Uslaim na Birnin bahren
wanda sarkin bokayen duniya ya sace masa yar sa gimbiya zarifa
Kuma a halin yanzu ya fito farautar yaro Humair makaho domin ya samu nasarar saduwa Hibairu SARKIN SADAUKAI.
Lokacin da aljani Haulatul-infal ya ɓace ɓat daga ɗakin sirri domin zartar da umarnin sarkin bokaye Dargas,
Kamar yadda boka Dargas ya umarce sa haka al'amarin ya kasance domin cikin abinda bai huce daƙiƙa hamsin ya bayyana a kofar gidan sarauta ɗauke da sarki shazwan da tawagar sa,
Bayan Haulatul-infal ya sauke su sarki shazwan sai ya yunkura ya sake tashi izuwa sararin samaniya ya ɓace ɓat
Sarki shazwan bai samu ganawa da Hushriba ba sai da gari ya waye bayan ya kammala kalaci sannan Hushriba da waziri Rufyan Sarkin bokaye da sauran tawagar matsafa suka iske sa a cikin turakar sa ta ganawa da baƙi,
A wannan lokaci sarki shazwan na zaune bisa wata ƙasaitacciyar kujera ya caɓa ado irin na hamshakan sarakai,
Kyawun surar sa ya bayyana a fili, jikin sa na fitar da wani irin kamshin turare mai daɗin gaske,
Lokacin da gimbiya Hushriba tayi arba da fuskar sarki shazwan sai taji zuciyar ta ta buga da karfi a karo na farko ta kasa gane shin mene ne abinda ya sanya zuciyar ta zata buga da karfin,
Shin ta faɗa farkon soyayya ne ko kuwa tsananin kwarjinin sarki shazwan ne
Amsar tambayoyin da Hushriba ta kasa bawa kanta kenan
Ta samu waje ta zauna bisa kujerar da aka tanadar mata dake fuskantar sarki shazwan,
Bayan kowa ya zauna ne bisa wajen zamansa
Sai sarki shazwan ya shiga kallon su ɗaya bayan ɗaya kamar mai nazarin wani abu,
Duk wanda sarki shazwan ya kurawa idanu sai kaga ya sunkiyar da kan sa ƙasa,
Amma bisa mamaki koda ya haɗa idanau da Hushriba sai ya ga ita ma ta ƙura masa idanun ko kiftawa bata yi,
Al'amarin da yayi matukar ba sa mamaki kenan yace a ransa shin wannan jarumi bata san Mene ne matsayi na ba ne ta ƙura mini idanu batare da ladabi ba
Wani ɓangare a zuciyar sa kuma na cewa shin baka lura da nau'in kallon da Hushriba ke yi maka ba ne,
Tabbas kallo mai ɗauke da alamun shauƙin so
To kai ma meyasa ka cigaba da ƙura mata idanun fiye da ƙima
Sa'adda sarki shazwan yazo Nan a tunanin sa sai yaji kunya ta kama sa,
Kawai sai ya dawo da duban sa ga Sarkin bokaye yayi gyaran murya sannan ya fara magana akaro na farko cikin nutsuwa
"Da farko ina yiwa dukkan waɗanda suka hallara a wannan waje Barka da zuwa tare da yiwa bakuwar jaruma maraba,
Bayan haka dalilin daya tara ku wannan waje shine domin na saurari dukkan bayani game da wannan musiba da ta afka mana ta GOBARAR DAJI da kuma karin bayani akan hanyar magance wannan al'amari,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki shazwan sai sarkin bokaye Dargas ya yi gyaran murya yace"Ya shugaba na dukkan wani bayani da Ya kamata nayi maka nayi maka shi game da bayyanar wannan jaruma wato Hushriba,
Abinda ya rage dai yanzu kawai shine mu saurari bayani daga bakin Hushriba akan hanyar da zamu kawar da wannan annoba,
Sa'adda sarkin bokaye Dargas ya zo nan azancen sai jaruma Hushriba tayi gyaran murya tace
"Yakai sarki shazwan kayi sani cewa babban muhimmin abinda ya kawo ni wannan ƙasa taka kuma har na ceci rayuwar al'ummar kasar ka daga ANNOBAR GOBARAR DAJI
Shine yaro Humair da kuke nema domin ku yanka da ku bayar da jinin sa ga abin Bautar ku domin kare kanku daga GOBARAR DAJI
A halin yanzu ni ma shi na fito farauta domin na cika burina na mallakar tsumin tsafi dake fadar Sarkin bokaye,
Hakan kuma ba zai tabbata ba face na sadu da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI na bayyana masa buƙata ta ta zuwa fadar Sarkin bokaye domin ya samo mini tsumin tsafi
Yaro Humair shine kaɗai yasan Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI
Kun ga kenan a halin yanzu ina matukar kaunar ganin Yaro Humair makaho a raye saɓanin ku da kuke yunkurin hallaka sa,
Hanyar da zaku kawar da wannan guguwar annoba kuwa shine,
A halin yanzu saura kwanaki ɗari uku da sittin da uku SARKIN SADAUKAI HUBAIRU ya kammala bawa tsuntsun tsafin sa horan yaƙi domin ya samu nasarar fito wa daga dajin Baitul-shamshan ya bayyana a wannan duniya tamu
Ya kai wannan sarki kayi sani cewa kasar ka ce ta farko da SARKIN SADAUKAI zai fara bajewa daga doran ƙasa,
Kuma yaro Humair ne kaɗai ne zai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI har ya fahimci hanyar da zai roƙar muku alfarma a wajen sa,
Kaga kenan a halin yanzu idan ma kun mallaki yaro Humair kun yanka sa kun bayar da jinin sa ga abin Bautar ku
Dai -dai da kun dabawa kanku wuƙa domin dazarar SARKIN SADAUKAI ya fito daga dajin Baitul-shamshan zai baje Birnin ka baki ɗaya babu wata halitta mai rai da zai bari ta cigaba da numfashi,
Sa'adda jaruma Hushriba tazo dai- dai nan a jawabin ta sai hankalin gaba ɗaya jama'ar dake cikin turakar ya dugunzuma ainun
Kuma ɗakin yayi shiru tamkar Mutuwa ta gifta,
Sai daga bisani Hushriba ta cigaba da cewa "A halin yanzu zama bai same mu ba,
Dole mu sake bazama farautar yaro Humair makaho domin ya zamo cewa mun mallake sa,
Domin hakan ne kawai zai sanya dukkan mu mu kai ga cika burikan mu, 08137237071
Wani abu da baku sani ba shine wannan mahayi da ceci rayuwar yaro Humair da saurayi Hizmal ba wani ba ne face yar uwa ta gimbiya Sunaila,
Nasan cewa ko wace yar uwa ta kuma nasan hanyar da zan rabata da yaro Humair
Lokacin da gimbiya Hushriba ta sake zuwa nan azancen ta sai kowa ya cika da matukar farin ciki gami da mamaki,
Hushriba tayi ajiyar zuciya ta ɗora da cewa "A daren yau nake so kayi umarni ga dukkan al'ummar wannan birni da su hallara a fada a lokacin da zamu tafi izuwa farautar yaro Humair domin masu iya magana na cewa da zafi-zafi akan daki ƙarfe,
Tabbas a lokacin da jama'a suka hallara zai basu wani sinadaran tsafi da zasu nasu kariya daga GOBARAR DAJI har zuwa lokacin da zamu dawo daga abin da muka fita farauta,
Koda jin wannan batu daga bakin Hushriba sai sarki shazwan ya cika da matukar farin ciki maral misaltuwa,
Nan take batare da wani ɓata lokaci ya umarci shamaki ya sanar da zagi cewa sarki yana son ganin kowa a fada kuma ba'a ɗauke wa kowa ba koda jariri ne sabuwar haihuwa,
Bayan sarki shazwan yayi wannan umarni nan take ya sallami su waziri Rufyan domin kowa yaje ya kammala shiri kuma yayi bankwana da iyalan sa,
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin jaruma Hushriba da su sarki shazwan.
*****
Lokacin da aljani Darmanu ya tsala da azababban gudu a sararin samaniya ɗauke da sarki Uslaim,boka ƙarzum,da dakarun rakiya domin rabi sahun aljani Marhutul-Azab dake ɗauke da yaro Humair,saurayi Hizmal da sunaila domin ya cimmu su,
Sai Darmanu ibn kauƙas ya wanzu yana tsala Azababban gudu babu sassauci yana keta gajimare,
Ana cikin wannan tafiya ne sai yazamana cewa rana ta kwalle tayi tsananin zafi,
Don haka sai boka ƙarzum ya umarci Aljani Darmanu da ya yada zango,
Koda jin wannan umarni sai Darmanu ya saki fuka- fukan ya sauka ƙasa luuuh!
Ya sauƙa a bisa turba, inda ya saukan ya kasance daji ne mai yalwar duwatsu, koramu haɗe kwazazzabai,
Har wasu daga cikin tawagar rakiya sun yunkura zasu sakko daga kan Aljani Darmanu sai boka ƙarzum ya daka musu tsawa yana mai nuna cewa su dakata,
Kawai sai ya dubi gabas,yamma,kudu da arewa,
Sannan ya juya ya dubi Sarki uslaim cikin ladabi yace
"Ya shugaba na wannan daji jikina bai kwanta da shi ba, da alamu akwai wani tarko mai cutar wa, ina ganin zai fi kyau mu sake cigaba da tafiya har sai mun samu waje mai cikekken tsaro sannan sai mu haɗa zangon,
Kafin boka ƙarzum ya gama rufe bakin sa sai kawai akaga waɗansu waɗansu ayarin gwaggwan birrai na fito wa daga kowace kusurwa a dajin waɗansu na dirowa daga saman bishiyoyin dajin waɗansu daga cikin ƙarƙashin ƙasa,
Kafin kace me yarin birran sun yi musu ƙawanya
Su dai birran suna da girma tamkar toran Giwa munin fuskokin su kuwa ya huce misali,gaba ɗaya jikin su cike yake da gashi buzu-buzu babu kyan gani gaba ɗayan su na shanye cikin sulken yaƙi nau'i daban -daban tamkar sun kasance bil'adama,
A hannayen su kuwa suna dauke da miyagun makamai masu barazana da dukkan wata halitta mai numfashi.
Lokacin da aka fara kallon- kallo tsakanin ayarin gwaggwan birrai da su sarki uslaim,
Sai aka shafe tsawon daƙiƙa goma a cikin wannan hali,
Sai daga bisani ne su sarki uslaim suka yi wuf suka zare makaman yaƙin su,
A lokacin da ayarin gwaggwan birran su kayi kukan kura suka yi ɗauki kansu,
Lokacin da aka haɗu da juna nan take waje ya kare da azababban yaƙi,
Bangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta
Ana fara wannan artabu ne fa su sarki uslaim suka