Showing 12001 words to 15000 words out of 21631 words

Chapter 5 - SARKIN SADAUKAI COMPLET PDF BY Sufi .txt

05 Aug 2025

526

tazo dai dai nan a labarin ta sai hawaye suka zubo daga idanuwan ta,
Al'amarin da ya sanya saurayi Hizmal yaji ya kamu da matukar tausayin ta kenan har kwalla ta zubo masa,
Shi kansa yaro Humair daya kasance makaho baya gani sai da yaji ya kamu da tausayin Husnaila,
Tsawon daƙiƙa hamsin Husnaila tana cikin wannan hali sai daga bisani ne ta sanya hannayen ta biyu ta share hawayen ta sannan ta cigaba dacewa
Kamar yadda mahaifina ya faɗa haka al'amarin yakasance ranar da kwana uku suka cika waziri yayi umarni akayi shela a cikin birni da kauye akan cewa sarki zai tura ya'yan sa izuwa nemo maganin lalurar sa duk wanda ya samu nasarar nemo maganin da ya warkar da shi da jinyar sa
Shine zai gaji karagar mulki, yayin da jama'a suka ji wannan shela sai sukayi cincirindo a fadar babu masaka tsinke kowa ya hallara,
Mu kaɗai ake jira, ana cikin wannan hali ne kwatsam sai yan uwa na su yarima ubaiyu suka shigo fadar shirye shirye cikin matsananciyar shigar yaƙi mai matukar kwarjini da ban tsoro,
Yayin da jama'a suka yi arba da su sai suka miƙe tsaye domin girmama wa a gare su,
Har sai da suka je suka zauna a wajen da aka tanadar mu su sannan fadar tayi tsit
Bayan shuɗewar Kamar daƙiƙa hamsin ne sai na shigo fadar tare da dakarun rakiya masu tsaron lafiya
Sa'adda jama'a suka yi arba dani nan take fadar ta rude da shewa da tafi inda wasu ke cewa ni ce zan gaji karagar mulki, wasu nace ni ce zan zamo shugabar su,. https://youtu.be/bq_-9I3FtnA
Al'amarin da ya harzuƙa zukatan yan uwana kenan suka kama tafarfasa tamkar zasu kone,
Duk wanda ya kalla ne daga cikin su sai naga ya kada mini uwar harara
Sai da kowa ya zauna abisa kujerar da aka tanadar ma sa Sannan waziri ya miƙe tsaye ya ɗaga hannun sa fadar tayi shiru tamkar Mutuwa ta gifta,
Sannan ya fuskanci jama'a yayi gyaran murya yace
"Da farko mu na yiwa jama'a Barka da zuwa wannan fada mai albarka barka da zuwa,
Bayan haka koda cewar mutane sun san abinda ya tara mu anan,
Amma akwai bukatar nayi ƙarin haske akai,
Sanin kanku ne cewa mai girma sarki ishwar ya kwanta jinyar rashin lafiya tsawon lokaci
Bisa wannan dalili ne yasan ya sarki yayi umarni da a tura su yarima ubaiyu su shiga izuwa duniya domin su nemo maganin da zai warkar da cutar mai martaba,
Dukkan wanda ya samu nasarar nemo maganin da ya warkar da cutar mai martaba to fa shine zai gaji karagar mulkin wannan birni mai albarka,
Saboda haka yanzu za muyi wa su yarima rakiya har izuwa kofar gari tun da dama tuni an tanadar musu dawakai da abin guzuri,
Koda waziri ya zo daidai nan azancen sa sai muka miƙe tsaye daga wajen zaman mu muka nufi kofar fita daga fada, waziri,yan majalissa da sauran jama'ar gari suka mara mana baya,
Yayin da aka fita sai muka kama dawakan mu muka sakar musu linzami,
Sai da aka yi mana rakiya har izuwa kofar gari sannan kowanne mu ya debi dakarun rakiyar sa guda Ɗari biyu da ɗoriya ya nausa cikin daji,
Ma'ana yarima ubaiyu ya nausa izuwa bangaren yamma, Hushriba gudu,yarima zafiyar arewa, ni kuma nayi gabas,
Kowa ya rabu da ɗan uwan sa, sai na shafe tsawon Sa'a uku i na gudu tare da dakaru na sannan na yada zango,
Bisa mamaki sai naga dakaru na na rakiya sun zare makaman yaƙi sun afka mini domin su hallaka ni dakyar da siɗin gishi na tsira da raina bayan na samu manyan raunuka.
Wannan shi ne taƙaitaccen labari na da kuma abinda ya sanya na fito farautar yaro Humair kuma na taimaka maka wajen ceton rayuwar sa domin ya taimaka mini na sadu da Humairu SARKIN SADAUKAI.
Sa'adda jaruma Husnaila tazo dai dai nan a labarin ta sai saurayi Hizmal ya kamu da matukar tausayin ta ya dube ta a nutse yace"yake Husnaila haƙiƙa labarin ki cike yake da ban tausayi,
Ina mai tabbatar miki dacewa matsawar ina numfashi zan taimaka miki wajen cika burin mahaifin ki,
Sa'adda Husnaila taji wannan batu daga bakin Hizmal sai ta cika da matukar farin ciki maral misaltuwa,
Daga wannan ne kuma sai fira ta ɓarke a tsakanin su,
Wannan shi ne abinda ya faru ga baƙon jarumi wato jaruma Husnaila,da saurayi Hizmal a cikin gidan tsira bayan sun samu nasarar tseratar da Yaro Humair makaho daga sharrin sarki shazwan wanda yake son ya hallakashi domin ya bayar da jinin sa ga abin Bautar su don tseratar da jama'ar birnin sa daga saharrin GOBARAR DAJI.
*****. *****. *****
Duk wanda ka gani a birnin tsakanin maza, mata, yara da manya kowa gudu yake domin ya tsira da rayuwar sa,
Kaico! Haƙiƙa tashin hankali ba'a sama sa rana kuma ita GUGUWAR ANNOBA idan ta taso babu mai ɗauke ta face Ubangiji,
Babu abinda zai karya zuciyar mutum kuma ya sanya shi zubar da hawaye
Face idan yaga yadda wata irin guguwar Wuta ke kama jikin yara ƙanana da mata suna ci da wuta suna ihu da kururuwar neman taimako amma babu mai ceto,
Wani abin takaici shine hatta kwalbati da hanyoyin ruwa wuta ke ciki babu wani waje da mutum zai sami fakewa,
Kafin shuɗewar rabin sa'a gaba ɗaya birnin ya cika da gawarwakin yara da tsofaffi,
Gidaje duk sun rushe sun ƙone kurmus,ihu da koke-koken ƙananan yara da mata ya cika dodon kunne, mutane suka dunga guje-guje gami da ifice-ifice,
Komai rashin imanin mutum idan yaga wannan ƙazamar musiba dole ne ya zubar da hawayen tausayi.
Ana cikin wannan musiba ne su Sarkin bokaye suka bayyana a dai dai kofar fada,
Sa'adda suka ga yadda wannan GOBARAR DAJI ke hallaka jama'ar birnin su sai suka cika da matukar tausayi da baƙin ciki,
Waziri Rufyan ya dubi Sarkin bokaye Dargas cikin tashin hankali yace
"Ya shugaban bokaye Yakamata kayi wani abu game da wannan musiba,
Domin fa idan musibar nan tayi tsamari karshe zamu iya rasa dukkan iyalan mu Bama jama'a birnin mu kaɗai,
Koda jin wannan batu daga bakin waziri Rufyan dai sarkin bokaye ya dake murtuke fuska ya dubi waziri Cikin alamun karayar zuci yace
Ya shugaba na shin ka manta ne cewa yau tsawon shekaru wannan musiba tana bayyana amma duk lokacin da zata taso ilimin tsafi baya taɓa tasiri akan ta,
Duk lokacin da nayi yunkurin aiwatar da wani al'amari akan hakan zan iya rasa dukkan sirrikan tsafi na, koda boka Dargas yazo dai dai a zancen sa sai idanun sa suka kaɗa kuma kwallar takaici ta zubo masa,
Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai a kaga wani mahayi ya bayyana bisa kan ingarman doki sanye cikin gagarumar shigar yaƙi ya tunkaro inda su Sarkin bokaye suke tsaye yana mai ratsawa ta cikin gagarumar wutar dake ci
Amma bisa mamaki shi dokin da yake kai wutar bata kama jikin su ba.
Al'amarin da yayi matukar ɗaurewa su Sarkin bokaye kai kenan kuma ya basu mamaki,
Kawai suka saki baki suka kura mahayin idanu,
Lokacin da yazamana tazarar dake tsakanin su bata huce taku hamsin ba,
A sannan ne su Sarkin bokaye suka fahimci cewa mahayin ya mace ce kyakkywa ta gaban kwatance,
Lokacin da yazamana tazarar dake tsakanin bata huce taku goma sai budurwar ta ja linzamin dokin ta ta tsaya cak,
Kawai sai buɗe bakin ta ta karanto waɗansu dalasimai
Tana mai nuna sararin samaniya da hannayen ta biyu
Tana gama rufe bakin ta sai wata walkiya da tsawa suka bayyana a sararin samaniya haɗe da ci da
Sannan ruwan sama ya kece tamakar da bakin kwarya,
Amma wani abun mamaki ruwan bai jiƙa budurwar ba,
Cikin Abinda bai gaza daƙiƙa hamsin ba gaba ɗaya GOBARAR DAJI dake birnin ta mutu ƙurmus,
A sannan ne jama'a suka fara dawowa cikin hayyacin sa kowa ya shiga duba irin muguwar asarar da yayi,
A lokaci guda ruwan saman ɗauke ɗif tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Cikin alamun tsananin farin ciki maral misaltuwa Sarkin bokaye, waziri Rufyan Sarkin yaƙi suka taka da kafafun su izuwa inda budurwar take tsaye,
Lokacin da suka isa daf da ita sai suka ƙara cika da mamaki ainun
Ita dai budurwar takasance kyakkyawa tagaban kwatance, tana da kyan diri da sura tamkar ita ce ta ƙera kanta yadda take buƙata, fatar jikin ta wankar tarwaɗa ce ma'ana ba baƙa ba ce ba fara ba,
A gadon bayan ta tana rataye da wata zabgegiyar takobi mai tsawo da kaifin tsiya, shekarun budurwar ba zasu haura ashirin ba
Lokacin da aka isa sai boka Dargas ya buɗi baki cikin tattausar murya fuskar sa cike da annuri ya dubi kyakkyawar budurwar yace
"Yake wannan jaruma ma'abociyar abubuwan ban al'ajabi mun zo ne gareki domin muyi miki godiya bisa wannan gagarumin taimako da kika yi mana na ceton miliyoyin jama'ar birnin mu daga musibar GOBARAR DAJI,
Sannan idan babu damuwa muna san ki sanar damu wace ce ke a cikin jerin bokayen duniya,?
Shin akwai wani abu da kike da bukata daga garemu har ya shigo dake cikin wannan ƙasa ta mu mai albarka?
Koda jin waɗannan tambayoyi daga bakin Sarkin bokaye Dargas sai kyakkyawar budurwar ta bushe da yar karamar dariya
Sannan daga bisani ta tsuke baki tayi gyaran murya cikin tattausar lafazi mai daɗin sauraro tace
"Yaƙi waɗannan SARAKAI kuyi sani cewa ceton rayuwar al'ummar ku a waje na tamkar taimakon kai na ne,
Nasan za kuyi mamakin jin na faɗi haka, amma zan sanar ɗaku abinda zai shafe mamakin a cikin amsoshin da zan baku anan gaba,
Da farko dai ni suna Hushriba bintu ishwar mahaifina ƙasurgumin matsafi ne da yayi shura
A halin yanzu na fito ne bisa umarnin mahaifina na ne mo masa maganin cutar da ke damunsa
Bisa binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na na gano cewa maganin dana fito nema tabbas yana da alaƙa da musibar da ta addabe ku ta ANNOBAR GOBARAR DAJI.
Don haka nake so mu haɗa karfi da karfe domin kowanne mu ya amfana
Ina nufin bani ƙishiri na baka manda, domin duka mu samu tsira,
Sa'adda Hushriba tazo dai dai nan azancen ta, sai sarkin bokaye Dargas ya dube ta cikin farin cikin matukar farin ciki maral misaltuwa yace
"Ya jaruma ma'abociyar abubuwan ban al'ajabi tabbas munyi matuƙar farin ciki da bayyanar ki a cikin wannan birni,
Akwai bukatar akai ki masauki ki samu hutu kiyi kalaci sannan daga bisani sai mu tattaunawa,
Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin bokaye sai Hushriba ta gyaɗa kai alamar gamsuwa,
Gama faɗin hakan keda wuya sai sarkin bokaye yayi wa wani badakare inkiya ta da hannu take badakare ya zaburi dokin sa ya shige gaba yana mai yiwa jaruma Hushriba nuni da ta biyo bayan sa,
Batare da wani jinkiri ba Hushriba ta sakarwa dokin ta linzami ta mara masa baya,
A sannanne Sarkin bokaye ya dawo da uban sa ga waziri ya dubesa cikin ladabi yace "ya shugaba na shin me ka fahimta game da wannan bakuwar jaruma Hushriba?
Koda jin wannan tambaya sai waziri ya nisa Sannan yayi ajiyar zuciya yace"Ya Sarkin bokaye kayi sani cewa duk da irin taimakon da Hushriba tayi mana baza mu saki jiki da ita ba
Lallai akwai bukatar ka gudanar da bincike bisa halarar tsafin ka domin ka tabbatar.
kuma wajibi ne mai martaba sarkin yasan da wannan al'amari
Dajin wannan batu sai sarkin bokaye yace "Maganar ka haƙƙun yakai waziri zan zartar da duk abinda ka umarta,
Daga wannan batu ne kowa ya kama gaban sa waziri ya huce izuwa cikin gidan sarauta,
Sarkin bokaye da sauran Yan uwan sa bokayen suka durfafi ɗakin sirri domin gudanar da bincike game da jaruma Hushriba.


****
BIRNIN TEHRAN
Acan birnin Tehran kuwa tun sa'adda sarauniya Abidatul-auliya ta gana da boka shubairu wanda ya bayyana gare ta acikin surar kyakkywan tsuntsu
Sai ta kasance a koda yaushe cikin zaƙuwa take domin ta ga cewa ranar tafiya izuwa dajin Baitul-shamshan tazo domin saduwa da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Bangare guda kuma zuciyar ta cike take da tsananin begen saurayi shubairu,
A kowa ne dare sai ta zauna a harabar turakar ta tana tana kallon inda saurayi Hibairu ya bayyana a gare ta tana mai karanta waƙoƙin so da bege,
Kaico ! Haƙiƙa so shine shammatar zuciya, tabbas Abidatul-auliya ta kamu da tsananin kaunar shubairu wacce baza ta misaltuwa ba,
Kuma wani abin mamaki shine raɗaɗin da ciwon ta ke yi mata sai yazamana ta samu sassauci,
Haƙiƙa SO yana tasiri matuka wajen ba wa jikin ɗan adam wata garkuwa ta musamman.
Wannan shi ne abinda ya faru ga sarauniya Abidatul-auliya dake birnin Tehran
Al'amarin su saurayi Hizmal kuwa sai da suka shafe tsawon kwanaki uku a cikin gidan tsira tare da yaro Humair makaho,
Tsawon wannan lokaci da suka shafe a cikin gidan duk wani abu da suke buƙata na sha'anin rayuwa da sun bukace shi sai suga ya bayyana gaban su,
Kuma a iya tsawon wannan lokaci shaƙuwar soyayya ta ƙara kullu wa ainun tsakanin jaruma Husnaila da saurayi Hizmal
A ranar kwana na ukun ne da la'asar sakaliya su Hizmal suka kammala shiri domin cigaba da gudun tsira, domin tseratar da rayuwar yaro Humair,
Bayan sun kammala shirin ne
Sai saurayi Hizmal ya giya yaro Humair a gadon bayan sa,
Sannan suka durfafi wata kofa ta musamman a cikin gidan domin su fita,
Lokacin da suka isa bakin kofar sai suka tarar da kofar a garƙame babu alamun wajen da za'a bude ta,
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin su kenan ainun suka shiga dogon nazari,
Suna cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai suka ga wani aljani ya bayyana gare su ya faɗi yayi sujjada,
Aljanin yakasance gabjejen kato mai tsawo da kwarjini, yana da fuka fukai guda huɗu, da jela guda ɗaya, yana da kwalakwalan idanu jajur tamkar garwashin wuta, hancin sa kuwa ashafe yake tamkar bada shi yake shaƙar numfashi ba, a haɓar sa yana maƙale da dogon gemu fari sol mai tsawon kamu huɗu
Hakika wannan aljani ya cika mai ban tsoro gami da muni
Su kansu su saurayi Hizmal a matsayin su na zaratan Jarumai sai da suka firgita da sukayi arba da aljanin,
Aljanin ya ɗago da kansa sama ya dubi Hizmal da sunaila ya buɗe tafkeken baƙin sa mai kama da kofar gari, sannan yace cikin kakkausar murya,
"Da farko dai suna na Marhutul-Azab kuma nine hadimin dake kula da wannan gidan tsira yau fice da shekaru dubu bakwai,
Ya ku waɗannan bil'adama ma'abota gudun tsira kuyi sani cewa na bayyana gareku ne domin na fitar daku daga cikin wannan gida na kai mu duk inda kuke bukata a fadin duniya,
Koda jin wannan batu daga bakin aljani Marhutul-Azab sai Hizmal da sunaila suka cika da mamaki ,
Sunaila tace "Yakai wannan aljani haƙiƙa munyi farin ciki maral misaltuwa bisa wannan taimako da zaka yi mana,
Amma fa wani hanzari ba gudu ba, ina so kayi sani cewa tafiya damu abu ne mai matukar wahalar gaske da zai iya jefa rayuwar ka a cikin tsaka tsaka mai wuya,
Ina ganin abinda zai fi kawai shine ka nuna mana hanyar da zamu fita kai kuma ka cigaba da gadin wannan gida kamar yadda ka saba ,
Koda jin wannan batu daga bakin sunaila sai Aljani Marhutul-Azab ya bushe da yar karamar dariya mai kama da haniniyar doki sannan yace
"Yaku waɗannan bil'adama kuyi sani cewa fiye da shekaru dubu biyu nasan da labarin bayyanar ku a cikin wannan gida dama abinda zai kawo ku nan ɗin
Da kuma abinda zaku tafi nema,
Bisa al'adar wannan gida kowa ne mai gadi zai shafe tsawon shekaru dubu huɗu ne cif,
Kuma a yau ne shekarun kammala aiki na suka cika na samu yanci zan iya shiga ko ina a duniya
Babban muradi na shine na sadu da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI wanda shine kuka fito ne ma
Tsawon shekaru na shafe ina jiran zuwan ranar da zan sadu daku domin na cika burina na ceto rayukan al'ummar kabilar mu,
Wanda a halin yanzu ruhikan su ke ajiye a can fadar Sarkin bokayen duniya DURUSUL-FANNAR
A bisa cikin wata akwatu ta baƙin ƙarfe,
Kowa ce rana Sarkin bokayen duniya sai na tsafe ruhikan kabilar mu da wani sinadaran sihiri,
Da zarar ya kammala sihirin waɗannan ruhikan zasu koma nasa,
Ma'ana kenan zai zamo cewa yana ɗauke da rayuka guda dubu arba'in, Kowa ne ruhi guda ɗaya zai shafe shekaru dubu huɗu kafin ya mutu,
Baban burin Sarkin bokayen duniya shine ya cigaba da rayuwa da waɗannan ruhikan bazai mutu ba har abada, zai cigaba da kasancewa SARKIN SARAKAI,
Bisa binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na na gano cewa babu wani mahaluki da zai iya zuwa fadar Sarkin bokaye ya ceto ruhikan kabilar mu face SARKIN SADAUKAI Hibairu,
Sannan babu wani abu dazai iya buɗe wannan akwatin baƙin ƙarfe face ZOBEN SHIRIn dake hannun jarumi Hibairu kuma zoben ne zai karya sihirin dake jikin ruhikan kabilar ta mu har ya dawo zuwa gangar jikin su su cigaba da rayuwa kamar kowa,
Sa'adda aljani Marhutul-Azab yazo nan azancen sa sai hawaye suka zubo daga idanuwan sa,
Al'amarin da yayi matukar bawa su saurayi Hizmal tausayin sa kenan,
Hizmal ya dube sa cikin matukar damuwa yace
"'yakai Marhutul-Azab kayi sani cewa haƙiƙa labarin ka akwai ban tausayi duk da ka bamu shi a takaice,
Ina mai tabbatar maka dacewa ni da abokiyar tafiya ta zamu taimaka ka har mu sadu da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI tun da dukkan bukatar mu kusan ɗaya ce
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lulluɓe zuciyar Marhutul-Azab ya buɗi baki karo na uku yace
Yaku abokanan tafiya ta kuyi sani cewa ina farin cikin sanar da ku cewa
Ina ɗauke da dukkan taswirar fadar Sarkin bokaye,
Wacce babu wani mahaluki dazai shiga wannan fada face yana tare da taswirar,
A halin yanzu nasan cewa kowa ya ɗora idanun sa akan taswirar,
Wacce ko shi kansa Sarkin bokaye basan cewa ina ɗauke da wannan taswira ba ,
Tsawon shekarun da na shafe ina gadin gidan tsira domin na mallaki wannan taswira ne,
Na ji ajikana cewa wannan tafiya tamu cike take da nasara,
Tun da gashi muna tare da taswirar fadar Sarkin bokaye da kuma yaro Humair makaho wanda shine kaɗai a faɗin duniya ya iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI,
Sa'adda aljani Marhutul-Azab yazo nan azancen sa sai kowa ya cika da matukar farin ciki maral misaltuwa,
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Marhutul-Azab ya shimfide gadon bayan sa Hizmal goye da yaro Humair da sunaila suka hau suka zauna,
Sannan Marhutul-Azab ya yunkura ya tashi izuwa sararin samaniya ya na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login