Showing 21001 words to 21631 words out of 21631 words

Chapter 8 - SARKIN SADAUKAI COMPLET PDF BY Sufi .txt

05 Aug 2025

522

ta firo wata jakar fata a gadon bayan ta ɗauko wani ƙyalle ta shiga goge mata jinin dake zuba a bakinta da hancin ta,
Bayan ta kammala ne ta ɗauki wani garin magani daga cikin jakar ta haɗa a cikin wani kofi na azurfa bayan ta zuba ruwa ta cakuɗa sai ta kafa budurwar a baki ta shanye,
Koda kammala shanye ruwan maganin nan take budurwar taji ƙarfi a jikin ta har ta iya muƙewa tsaye
Batare da wani ɓata lokaci ba sunaila da saurayi Hizmal suka yi wa budurwar jagora har bisa kan Aljani Marhutul-Azab suka ɗora bisa gadon bayan sa
Bayan kowa ya hau sai Marhutul-Azab ya sake yunkurawa ya tashi izuwa sararin samaniya ya shiga keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Bayan tafiyar su saurayi Hizmal tare da wannan budurwa da suka ceci rayuwar ta.
Sai sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka bayyana a wajen,
Sa'adda Nuwairat da Jadwar suka yi arba da gawarwakin halittun sai suka cika da matukar baƙin ciki maral misaltuwa su shiga kallon alamun takun sawayen inda aljani Marhutul-Azab ya sauka,
Cikin hanzari boka Jadwar ya buɗe bakin sa sannan ya runtse idanun sa ya karanto dalasiman tsafi yana Gama rufe bakin sa sai yayi nuna da hannun sa ga wata bishaya dake fuskantar inda suke tsaye sai ga hoton dukkanin abinda yafaru tsakanin budurwar da su saurayi Hizmal ya bayyana a jikin bishiyar tun daga farko har ƙarshe,
Cikin alamun tsananin takaici sarauniya Nuwairat ta dubi boka Jadwar tace "ya dodon bokaye shin yanzu Mene ne mafita
Haƙiƙa idanuwa basu taɓa rintsawa ba matsawar budurwa NIHLA tana numfashi a doran ƙasa
Kuma bazan taɓa koma izuwa ƙasa ta har sai yaga na hallaka ta na mallaki SARKIN SADAUKAI Hibairu amatsayin abokin rayuwa ta,
Koda jin wannan batu daga bakin Nuwairat sai boka Jadwar yayi shiru Sannan daga bisani ya buɗi baki yace"Ya shugaba ta tabbas nayi matuƙar baƙin ciki da bamu riski waɗannan jarumai ba da su ka samu nasarar ceton rayuwar budurwa Nihla ba,
Domin kuwa sune suke ɗauke da yaro Humair makaho wanda shine kaɗai ya iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI a kaf fadin duniya,
Sannan aljanin dake ɗauke da su kuwa shine ke dauke da taswirar fadar Sarkin bokaye,
Haƙiƙa bakamar asarar mukayi ba da mun riske su shi kenan burin mu ya cika na duniya baki ɗaya,
Yanzu abinda kawai za su muyi shine mu bazama farautar su domin mu cimma su,
Sai dai kuma ya shugabata wani hanzari ba gudu ba
Yanzu gashi zamu yi wannan tafiya kuma bakiyi sallama da jama'ar ki ba,
Koda jin wannan tambaya sai Nuwairat tace "nasan da hakan abinda nake buƙata kawai shine ka tashi Manzo na sihiri ya tafi izuwa Birni na domin ya sanar da jama'a ta labarin tafiya ta,
Koda jin wannan umarni sai boka Jadwar ya sake buɗurwar baki ya karanto waɗansu dalasiman tsafi sai ga wani saurayi ya bayyana a wajen,
Bayan Jadwar ya sanar da saurayin duk abinda ke wakana sai Saurayin na sihiri ya ɓace ɓat,
Sannan boka Jadwar ya karanta wadansu dalasiman a karo na uku take wata dardumar sihiri ta bayyana a wajen,
Ba tare da wani jinkiri ba sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka hau bisa kan Dardumar
Take Dardumar sihirin ta tashi sama a cikin iska ta shiga keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Hakika boka Jadwar yayi shura a fagen ilimin tsafi
Wannan shi ne abinda ya faru da budurwa Nihla da sarauniya Nuwairat ke son ta hallaka bayan ta kashe baki daya mutanen birnin su,
Da kuma abinda ya wakana tsakanin ta dasu saurayi Hizmal akan hanyar su ta sada yaro Humair makaho da SARKIN SADAUKAI Hibairu,
Mu haɗu a
GOGA SHA FAMA littafi na 1 Domin jin
cigaban wannan kayataccen labari,
Daga mai ɗebe miki kewa a kullum da ko yaushe

Mansur Usman Sufi
Sarkin marubutan yaƙi

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login