Showing 1 words to 3000 words out of 18444 words

Chapter 1 - RAINA KAMA KAGA GAYYA True Hausa Book Na Marubuciya billyn Abdul .pdf

RAINA KAMA..
{Kaga gayya}_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!
👉🏻1⃣





Matsananciyar hayaniyar dake tashi agidan ce taja hankalina, cikeda bak'in ciki natashi daga
barcin safen dana koma, fitinar gidanmu dabance data kowane family House dana Sani kona
ta6a jin labarinsa a rayuwata, haka gidan namu yake kullum tamkar kasuwar 'yan danbe, daga
matan gidan zuwa 'yan mata da yara tamkar muna ganin hanjin juna, saika rantse badaga
tsatso d'aya muka fitoba.
Kururuwar danaji maman Safara'u ta kurma yasani kuma jan dogon tsaki, sai kuma najiyo
muryar gwaggon haleema Na fad'in “kai amma wannan lamari baiyi dad'iba, kekuwa maman
biyu ya kamata ki canja wannan halin naki, dan tabbas inba wani abu kikayiba babu yanda
za'ayi yaronan Sadeequ yadage shi cikinsu *MUNAYA* yakeso, duka yaushe aka gama
maganar nan akan shafi'u amma shine zaki koma kan Sadeequ kuma yanzu?â€.
gaba nane ya fad'i, cikin zaro idanu waje nace, “ashema mu akanmu fitinar take yau?â€.
yink'urin sakko nake daga gadon Munubiya tashigo tana share kwalla, binta nayi da kallo harta
fad'a saman gadon ta kwanta rufda ciki tareda fashewa da kuka mai ban tausayi. Hakan
Yakuma tabbatar min lallai mud'inne dai ake hargowar akanmu. a fusace Na dirgo daga gadon
na nufi k'ofar fita, (ko kad'an banida hak'uri, musamman akan cin zarafin mahaifiyarmu da akeyi
agidan lokuta da dama idan irin hakan ta taso), taku biyu nayi naji an damk'oni, najiyo cikin
masifa dan nasan Munubiya ce.
“wlhy ki sakeni kafin nafara huce haushina akanki munu! yau saina gyarama kowacce 'yar
iskar mata zama agidannan dan kutu.....
Bankai ga k'arasawa ba Munubiya tai saurin rufe bakina da tafin hannunta.
Kici-kicin kwacewa nafarayi amma nakasa, dan bak'aramin ruk'o taminba, raina yak'ara 6aci
ainun danjin irin rashin kunyar da Safara'u ke zubama innarmu a tsakar gida, bansan na
wancakalar da Munubiya gefe ba nafice da gudu.
Babu Wanda yaga fitowata sai dai saukar sautin marin dana zubama Safara'u a farar fuskarta
sukaji.
Hakan yaja gidan yay tsit na wucin gadi, sai kuma hayaniya takuma 6allewa, Safara'u da
mamarsu sukayo kaina danufin duka....
Tsawar da baba k'arami ya bugace tasaka kowa dakatawa tsakanin ni dasu, hakama matan
gidan sai suka fara jan k'afafu danufin barin wajen.
A tsawace yace, “kar wadda tabar wajen!!â€.
Tsitt kakeji gidan yayi, tamkar bashi bane d'azun ya cakud'e da hayaniya tamkar ana biki ko
suna.
Jarabar gidanmu ba bak'on Abu bane a anguwarmu, danta rigada tazama tamkar ajininmu
take (yo ajininmu mana zance) tunda kullumne babu fashi sai anyi hayaniya, kodai matan gidan
kokuma mu 'ya'yan gidan. Babu mai d'agama wani k'afa koda na second d'ayane kuwa, yanzun

zakaji gidan shiru, anjima k'ad'an kaji an doka gangar shaid'an, musamman ma fad'an yara
dayafi komai saurin had'a fad'an matan gidan da a kulum, a rana sai ayi fad'a biyar akan yara
kawai, innarmu ce kawai da Maman Fauziyya keda k'ok'arin K'aucewa irin wannan fitintunun
dasuka zama tamkar shan ruwa acikin gidanmu. Baba k'arami yafara fad'a tamkar zai ari baki, inda yake shiga bata nan yake fitaba, kowa
yayi tsit yana saurarensa, (saboda kasancewar masifaffe shima) sai da yayi mai isarsa sannan
yajuya yafita yana fad'in nida Safara'u mu sameshi falonsa. harda iyayenmu mata.

Duk abinnan da akeyi innarmu na kicin tana had'a Karin kumallon safe, kuma kalma d'aya
bata tofaba a zancen nasu, datasan ma zan fito bazata barniba nima.

A falon baba jafaru yanemi jin ba'asin tushen fitinar, cikin d'aga muryar da hargowa maman
Safara'u tafara fad'in “Alhaji wlhy kashiga tsakanina da maman biyu a gidannan, idanfa tanama
sauran matan gidannan Yanda taske so, suna barinta nibazan bartaba, tasanni tasan waye
ubana ehe, kum....... Hannu yay saurin d'aga mata, “kinga Suwaiba nifa ba wannan ne yasani kiranku ba,
sonake naji minene ya kawo hayaniyar?â€.
Cikin jin haushin an tareta tace, “Alhaji akan yaronnan Sadeequ ne, kowa yasan wajen
Safara'u yake zuwa a unguwarnan, amma jiya da yamma sai ya aiko kiran Munaya, dayake
ALLAH yatashi tonon asirinsu sabida bayaune na farko ba sai d'an Aiken ya kwatsa maganar a
tsakar gida, babu dai Wanda yace komai, dan azatonmu ba Sadeeq d'in Safara'u baneba,
goshin magriba saiga Safara'u tashigo tana kuka. Na tsareta da tambaya da k'yar tacemin
cikinsu 'yan biyu tagani da Sadeeq a zauren gidan Malam halilu suna hira da dariya, kuma
hardama mata gwalo akayi. Saboda na gaskata zancenta na sake aiken Rahma taganomin da
idonta, harma taji Sadeeq d'in nafad'in ai koma miza'ayi bazai auri Safara'u ba, cikin wad'an nan
munafukan yaran daba ganesu akeba zai aura, saboda darene yasani d'inne maganar a raina
har safiyar yau d'inan, amma wlhy Alhaji da k'yar na iya barci nida Safara'u jiya.

“hummm†kawai nafad'a ina dafe kaina, saboda jin Yanda aka canja maganar.

Babak'arami ya kalleni yace, “Munubiya ce ko Munaya?†(dan basa ganemu saboda tsananin
kamata da hassana ta).
Zuciyata cikeda bak'in ciki nace, “Baba Munaya ceâ€.
“yauwa Munaya, ina 'yar uwarki?â€.
“Tana ciki babaâ€.
Baba ya kalli Safara'u daketa matse kwallan munafurci tun d'azun yace, “k! Safara'u tashi
kiramin Munubiya â€.
Batareda ta amsaba tatashi tafita, mintuna kad'an saigata sun dawo tareda Munubiya
datasha kuka idanu sukayi luhu-luhu. tsaki naja a raina ina hararta ta gefen ido, rashin jarumtar
ta na bani haushi, ta cika hak'uri da sanyin hali tamkar innarmu.......
Maganar baba ce tadawo dani daga tunanin dana tafi. nad'ago ina kallonsa saboda kiran
sunana dayayi, muryar a dake na amsa da “na'am babaâ€. kallonsa ya maida kan Safara'u yana
fad'in “wacece acikinsu kika gani tareda Saddik'un?â€.

Binmu da kallo Safara'u tayi, cikin matse kwalla tace, “baba niba ganesu nakeba, sai sun
banbanta min Kansu sannanâ€.
Baice komaiba dan shima yasan da hakan, (ta hallaya ne kawai kowa ke banbantamu
agidan, hatta da innarmu kuwa). Baba yabimu da kallo alamar son sanin wacece acikinmu.
Da sauri Munubiya tace, “baba niceâ€.
Nima na kar6e da fad'in “baba k'arya takeyi nice jiya Sadeeq ya aiko kira, kuma babu wata
alak'a dake tsakaninmu, hasalima ya kirani ne akan Safara'un, sune dai suka maida zancen
hakaâ€.
Daga Safara'u har mamanta harara suka ballamin, babu ragi nima na rama kuwa.
Baba ne yakatsemu da fad'in “miya faru to Munaya?â€.
Janye idona nayi daga Kansu na maida gareshi, kaina ak'asa Nace,
“baba ya kirani ne yana tambayata minene abinda Safara'u tafiso a rayuwarta, dan yanason
yabata gift na birthday d'inta, kuma soyake yayi mata bazata. shinefa nake lissafa masa muna
dariya saboda ina cewa ya had'o mata da gyad'a soyayya dan ita mayyarta ce, a dai-dai
lokacinne kuma na hangota zata shigo gida, nifa dama tsokana namata gwalon, Ashe ita ta
d'aukeshi wani Abu. Kuma wlhy Rahma k'arya takeyi, lokacin data fito tareda yaa Hameed ta
ganni yana bani kayansa nakai masa ciki shi zai shiga masallaci salla. Wannan shinefa abinda
yafaru, shine suke cewa nakwace mata Sadeeq, har ana cin zarafin innarmu da farar safiyar
nanâ€.

Ajiyar zuciya innarmu ta sauke a hankali, taji dad'i daba abinda suke zargin baneba.
Wata uwar harara baba jafaru ya watsama maman Safara'u, “kai Suwaiba kedai ALLAH ya
gyaraki, dan ALLAH kuringa bincike akan Abu idan yara sun fad'a muku, tokinji dai abinda
yafaru, kekuma Safara'u dayake bakida tarbiyya har bakinki yana iyama Ai'sha rashin kunya ko,
ki tabbatar saina saka Abdulhameed yacimin ubanku keda Rahama yau a gidannan. Ai'sha kiyi
hak'uri dan ALLAH â€.
Innarmu ta yink'ura zata mik'e tana fad'in babu komai babansu, ALLAH ya kauda fitinar
gabaâ€.
“Amin†muka fad'a muma muna mik'ewa mukabi innarmu a baya.

Koda muka fito, sai matan gidan suka zubo mana ido suna kallo tamkar yau suka fara
ganinmu, a raina nace munafukai, haka zaku k'are.

Ran innarmu ya6aci matuk'a a wannan karon, amma kasancewarta mutum mai hak'uri da
shanye damuwa sai bata nunaba.
Nida Munubiya kam kasa shanye 6acin ranmu mukayi, munsan koma wace irin wulak'antawa
za ai mana agidan *KAKARMU* ce taja mana, itace tabada kowacce iriyar k'ofar tozartamu,
idan kaga abubuwan da ake mana saika d'auka ba jinin gidan baneba, tunda muka taso a haka
muka tsinci kanmu, hakama mahaifiyarmu a wannan halin muka risketa tana fuskantar
k'ask'anci da wulak'anci daga Kakarmu da matan Abban mu, harma da matan k'annensa,
bamuda 'yanci irin na 'ya'ya, mahaifiyarmu batada kima irinta matar gida (Uwargida), hakan
yasamo asaline dalilin................âœí ¼í¿¼

👎🏻



Tofa masu karatu dalilin mi? Dani daku duk muna buk'atar jin wannan dalili a bakin MUNAYA!,
saiku kasance dani danjin Yanda wannan labari mai d'unbin harmutsi da tsalle-tsalle zai kaya,
miye manufarsa? ina kuma ya dosa?.

Amsa d'aya zan iya baku.👇🏻



*_LABARIN MAI TSAWONE_*

saikun kasance dani a hankali zancigaba da warware muku lauje cikin nad'i.
ALLAH yasa zaku bani had'in kai, tabbatarwata shine yanda zaku kar6i wannan labarin.


Dan haka kumuje zuwa🥺âœí ¼í¿¼âœí ¼í¿¼


One luv🥰




*_ALLAH ka gafartama mahaifanmuí ½í¸­í ½í±í ¼í¿»._*
[4/16, 9:53 AM] +234 811 277 0720: *_Typing📲_*



HASKE WRITERS ASSO...💡

*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_




*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

_Ban yarda wani yaymin amfani da labarin nanba tako wace irin hanya, idan hakan tafaru ban
yafeba gsky, ALLAH yabani ikon fad'ar abinda zai amfanar dani da Ku, ya tsare harshena daga
fad'ar abinda zai cutar damu baki d'aya._

*_ALLAH ka gafartama mahaifina da dukkan sauran musulmai dasuka kwanta dama, kabama
marasa lafiyarmu lafiyaí ½í±í ¼í¿»._*




👉🏻2⃣


...........Zan iya ce muku fitinar gidanmu ta farone daga tushe, dan kuwa ginannen abune tun
zamanin k'uruciyar iyayenmu...

Malam Faruku shine kakanmu, matarsa d'aya Marwa'natu (Innaro), 'ya'ya hud'u suka Haifa a
duniya, maza uku mace 1. Auwal, Hameesu, Saffiya, Jafaru.
ALLAH yayi Innaro mace mai mugun son abin duniya, arayuwarta tanason ace komai daga
gareta aka fara ganinsa, kokuma wajen 'ya'yanta, sun tsayama 'ya'yansu duk sunyi karatun
addini dana boko, sai dai Safiya iyakarta primary aka mata aure. Sukuma mazan duk sunkai
matakin babar makaranta (jami'a). wannan yasaka Innaro d'aukar burin duniya ta d'ora akan
'ya'yan, harma matan dazasu aura.
Auwal shine yafara kammala karatunsa, dan haka Malam faruku mahaifinsu yace ya fiddo
matar Aure.
Bai wani tsaya Jan rai ba ya gabatar da Ai'sha amatsayin wadda yakeso.
Kai tsaye innaro tace sam bata aminceba, d'anta bazai auri d'iyar buzayeba kuma 'Yar iska,
Auwal yayi lallashin yayi rok'on akan fahimtar da ita sonda sukema juna shi da Ai'sha, amma
Sam tak'i saurarensa balle ta fahimcesa.
Da farko Malam faruku yasaka musu ido, azatonsa innaro zata sakko cikin sauk'i, amma
ganin yanda ta kafe akan bakanta saiya sanya baki da tambayarta dalilin k'in amincewar.
Kai tsaye tace batason su Ai'shar ne, Dan ba'asan asalin suba, sannan kuma 'Yar iskace,
shima kuma yasani ai. cikin hikima Malam yaso fahimtar da ita halin k'addara kowa da irin tasa,
itama Aishar bayin kanta bane ba, amma tak'i saurarensa shima. ganin abin zai tasamma rashin
mutumci yace to aure tsakanin Auwalu da Ai'sha kamar anyi an gama. A wannan lokacin ba
k'aramin birkicewa innaro tayi musuba, amma Malam faruku yace tayi tagama, dan hujjarta
batada muhimmancin dazai haramta auren Auwal da Ai'sha. babu 6ata lokaci kuma aka fara
shirin bikin.

*Wacece Ai'sha?*
Ai'sha d'iyace gawasu buzaye 'yan k'asar Niger wad'anda k'addarar rayuwa ta jawosu zuwa
k'asar Nigeria, su biyu kacal iyayensu suka Haifa, Aisha itace babba, sai k'anwarta Rabi'atu,
wurjanjan suka shigo k'asar Nigeria, sun fara rayuwane awata tashar mota, inda anan tsautsayi
ya fad'ama Ai'sha wani mara imani yamata fyad'e anan cikin tasha da daddare, randa abin

yafaru Malam faruku yaje tashar zai bada sak'o akaima wani d'an uwansa dake garin Maiduguri,
ya taras anata cecekuce atashar, yayinda Ai'sha da iyayenta ke rungume da d'iyarsu sunata
kuka da kururuwa.
Malam faruku yatambayi abinda ke faruwa daga wajen mutanen dasuka zagayesu suna
kallo, babu 6ata lokaci matashin saurayi yafad'a masa komai.
Hankalin Malam faruku yayi matuk'ar tashi, danshi mutumne mai kishin al'umma, anan ya
d'auki Ai'sha da iyayenta suka nufi asibiti, saboda jinin daketa zuba daga jikinta (Dan bazata
wuce 15 ba sannan), duk wata kulawar da yakamata anbama Ai'sha a asibitin, har tsawon
kwanaki hud'u tasamu lafiya sarai, kamarma komai bai faruba, sai dai tabo Na zuciya da aka
bar mata itada iyayenta. tun suna zaman asibiti Malam faruku ya fiskanci iyayen Aisha basuda
wajen zama, dan haka yak'udiri niyyar taimakonsu.
Akwai wani d'aki k'arami ciki da falo dake gidansa, saiya zagaye musu shi da Katanga
yamasa gyara.
Tunda aka fara aikin innaro ta tada hankalinta, duk zatonta aure zai k'ara, ganin tana neman
tara masa k'asa ya zaunar da ita yamata bayani dallah-dallah, maimakon ta kwantar da
hankalinta tunda ba kishiyar bace saima takuma tadashi, tace bazata zauna da iyayen Aisha
ba. Malam faruku yace bata isaba, Dan gidansane babu mai hanashi ajiye Wanda yakeso
akuma lokacin dayaso.
Dole badan innaro tasoba su maman Aisha suka zauna agidan, sai dai ko kad'an basajin
dad'in zama da ita, kullum gori da cin mutunci take musu, su Aisha kam basuda sakat awajenta,
saita koma sakasu aiki tamkar boyi-boyinta. Malam faruku ne ya koyama mahaifin su Aisha
sana'a, har shima yasamu rufin asirin rik'e iyalensa dai-dai gwargwado, amma ko kama k'afar
Malam faruku baiyiba, lokuta da fama ma shine ke taimakonsa dawasu abubuwan Na rayuwa,
musamman d'inkin sitturar su Aisha da wasu matsaloli Na yau da kullum dasukan taso. tun
zuwansu gidan Auwal yafara k'aunar Aisha, duk da mahaifinsu ya Sanar musu da komai akan
k'addarar da ta fad'ama Aishan kuwa, shekararsu biyu suna soyayya, tun Aisha Na d'ari-d'ari
dashi saboda tsoron abinda aka aikata mata har tazo tasaki jikinta dashi, sai dai babu Wanda
yasan suna soyayyar sai Rabi'a k'anwarta.

Ana haka kuma Auwal yazo da zancen Aisha zai aura.

To haka dai akayi auren Auwal da Aisha badan innaro tasoba.
Wannan kuma yasakata d'aukar Karen tsana ta d'orama Aisha, kullum cikin zagi da cin
mutuncin Aisha take, sosai tazamar mata Uwar miji mai kishi da sarakuwa, ga gorin datake
mata akan ita 'Yar iskace, babu wani fyad'e da'aka mata, taje tayi iskancinta an fake da fyad'e
an dawo an lik'ema d'anta da asiri, tujara dai iri-iri dai ta innaro. Aisha tanada hak'uri, ko kad'an abinda innaro kemata bai hanata girmamata ba da bata
matsayi irinna uwa, amma innaro bata gani.
Watan aurensu 7 kacal innaro ta samoma Auwal wata yarinya mai suna Mero, mero d'iyace
ga wani matashin d'an kasuwa, tun alokacinma ana lissafashi a masu kud'in yankin balle yanzu
daya zama shahararre, Auwal bayason Mairo, amma dolensa ya aura saboda innaro tace zata
tsine masa. Shigowar Mairo Yakuma k'untata Aisha a gidan, dan tunkan ta shigo innaro tagama 6ata
sunan Aisha dana iyayenta awajensu mairo, shigowar mairo da wata 1 kacal kuma tasamu ciki,

wannan fa yakuma k'ara ta6ar6arewar al'amura, gashi sannan ALLAH ya yalwatama Auwal d'in
babu laifi, harma yasayi wasu filaye uku shida 'yan uwansa anan cikin anguwar kusada su
innaro, amma ba'a ginaba, dan babu kud'in ginin lokacin.
A wannan lokacinne kuma k'addara ta afkama iyayen Aisha, ranar wata alhamis da daddare
aka maka ruwa Na tashin hankali, Wanda yay sanadin fad'awar d'akin dasuke ciki suka rasu.
Aisha da Rabi'a sunshiga matuk'ar tashin hankali, hakama Malam faruku, innaro kam ko'a
jikinta.
Rasuwar iyayen Aisha yasaka rabi'a k'anwarta dawowa hannunta da zama, akuma
lokacinne Hameesu shima yace Rabi'a yakeso da aure. tashin farko innaro ta taka masa birki
da kukarin zata tsine masa kuwa. dole yabar maganar auren Rabi'ar yasamo wata Ruk'ayya ya
aura. A lokacinne Mairo ta haihu namiji, zokaga murna wajen innaro da mairo, Malam ma yayi
murna, hakama Aisha, dukda innaro tace Na munafurcine. ranar suna yaro yaci Abdulhameed,
koda wasa mairo bata ta6a yarda Aisha ta d'auki hameed ba, dan innaro tahana, Auwal yayi
fad'an shida Malam harsun gaji.
Rayuwa tacigaba da tafiya tsawon shekaru, zuwa sannan su Auwal sun had'a hannu sun
gina filinsu, kowa da 6angarensa, gidanmu yafara yawaita da 'ya'ya, dan matar Hameesu ma ta
haihu Namiji Shafi'u, hakama matan gidanmu sun k'aru, dan jafaru ma yayi aure, hakama
Hameesu yak'ara aure shima, ga iyayenmu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login