Showing 3001 words to 6000 words out of 24258 words
Chapter 2 - MATAN ASOKORO COMPLETE HAUSA NOVEL BY by M.Shakur.pdf
sabida direban ta nada yakoma garinsu kulada mahaifiyarshi da aka
cemai batada lpy, shi professional direba yakeda shi kullum direbanshi cikin suit yake da agogo
shikuma wanan local dan kauyen yakawo mata that cannot even read ABCD to Z, koyanaso tai
bala'i dashine dan tasan dagangan yamata haka ohonmai.
Jin ranta na tafarfasa yasa tajawo wayanta daga cikin jaka taciro tashiga dial calls dinta saiko
ga number Martala Driver tai dailing number shi, yana tsaye bakin titi suna hirada mai rake dake
yanka rake saiga wayanshi tashiga ringing dasauri yatura hannunshi cikin wandon yaciro wayan
techno yar rakani toilet, musamman yasa akamai Saving number Hajiya da S shikuma Alhaji da
A dan yagane idan takira yana ganin kiranta yadaura hannunshi aka amugun rude cikin
hausanshi nayan kauye yace "na shiga uku na lalace, Hajiya" dawani irin gudu yajuya ya kalli
asibitin hangota tsaye yasa damugun sauri yajuya yasake tura hannu cikin aljihu yaciro wata
500 yamikama mai raken yace "kai bani Hajiya ta tafito, yau nidai nasan na shiga uku" baima
jira cewanshi ba ya fizge ledan yawuce, Mai rake yace "ga chanjin ka kabari" titi yashiga da
gudunshi yace "nabaka" da gudu ya tsallaka titin ya shiga asibitin duk tana binshida mugun
kallo, yana karasowa gabanta ko wata wata baiyiba yawani irin zubewa agabanta yace "Hajiya
dan Allah kiyakuri, wlh nasan kinsha gayamin muka fita na tabbatar ina cikin mota idan kinfito,
tuba nake Hajiya, Allah yahuci zuciyanki, Allah ya sanyaya kafadunki, tubanake Hajiya" ayanda
takejin haushi zata iya shureshi da kafafunta tadai daure cikin fushi tace "my friend will u stand
up and open car for me" dasauri yace "eh Hajiya mekikace"? Wani irin runtse ido tayi cikeda
takaici tuna bamaya gane turenci, dan dagokai yayi ya kalleta ganin yanda tayi yasa yace "dan
girman Allah kiyakuri Hajiya wlh daman rake nasayo miki wlh" yamikamata raken dake leda,
bude idanunta tayi tadakamai tsawa. "Murtala katashi kabudemin mota nabar wajen nan!"
Abirkice dukya rude yatashi garin hakama yasaki ledan raken suka watse awajen tabishi da
mugun kallo dayasa yatashi da sauri yatura hannu a aljihu yaciro hadadden car key sanan
yadanna lock tabudu, kafin yabude kofar owner sit yasaukarda kanshi kasa yace "Allah yahuci
zuciyan Hajiya, tuba nake matan ranka shi dade, takawanki lpy uwargijiyata, shiga muje"
mtswww taja wani wahalallen tsaki tajuya tashiga cikin motar ahankali kanta na mugun sarawa
yamaida kofan yarufe, raken daya watse awajen ya kalla har ranshi soyake yatsugunna ya
kwashe kayanshi amman tsoron masifan hajiya yake, bude gaban motan yayi ya shiga ya rufe
yaja sit belt yasaka saikuma ahankali yaleko bayan sit din ya kalleta kanta na kasa tana kallon
wayanta datake latsawa kaman mara gaskiya ahankali yace "Allah huci zuciyan Hajiya"
dagokanta tayi tazubamai red eyes dinta dahar lokacin suke nuna alamun kuka, hakuri zai
batafa amman ganin yanayin idanunta yasa dasauri yace "Hajiya kuka kikayi? Innalillahi maiya
sameki anmiki wani abu a asibitin nanne? Waya batamiki rai eh inje inkoyamai hankali wlh saina
barar da mutum na shemar dashi, waye ne Hajiya"? Yanda taga yadamu sosai danya nuna
afuskanshi yasa har ranta saitaji dadi, dan yatsine fuska tayi cikedason yamata shiru dakuma
tarin gajiya tace "nagaji ne kaini gida kawai nahuta Murtala" da sauri yajuya yatada motar
yajada sauri yace "Hajiya sannu, kinga baki saba wanan aiki hakaba, keda kikeda likita dayake
zuwa har gida yadubaki maisa kikazo asibiti nan kikabi layi saisa kanki keciwo, sannu Hajiya,
Allah huci zuciyanki, yanda kikagajin nan bazanbi hanyar zuwa ASOKORO ba dan akwai go
slow, akwai wata short cut hanya dazanbi yanzun nan zakiga munkai ranki shi dade".
Chat me up directly by clicking on this link
https://wa.me/+2347012181461
_This is the only free page of this book, like I said, wanan novel din bakaman normal novel dina
bane, I interviewed so many couples, I want to show the world inda akafi samun matsaloli
arayuwan auren mu tayau and how to go about it. I trust my fans, u all knows yanayin rubuta, ku
gyara zama, wanan littafi shine ga darasi gakuma dadi, lemme say it again please , anybody
less than 18 shouldn't read this book, thank you._
Chat me up directly by clicking on this link https://wa.me/+2347012181461
_This book is 2k, idan kinaso pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank and send
evidence of payment to my watsapp number 07012181461 sainai adding naki a group din
danake posting_
_MATAN ASOKORO_
✍M SHAKUR
_RANAKUN POSTING *SUNDAYS*, *TUESDAYS,* *FRIDAYS*_
_DAN GIRMAN ALLAH KARKI KARANTA THIS BOOK IN BAKI BIYABA, KUJI TSORON
ALLAH_
EPISODE 2️⃣
Ko alamun taji magananshima batayiba saima cigaba da danne dannenta datayi awaya tana
chatting a group dinsu na ASOKORO WIVES, gajiya tayi saikawai ta ijiye wayan sabida yanda
kanta kewani irin sarawa datarasa maisa, sanan gently ta jinginar da kanta jikin kujera ta
lumshe ido. "Hajiya wai lapiyanki kalau"? Bude idanunta tayida sauri jin Murtala yasake mata
tambaya ta madubin mota suka hada ido dan gajeren wahalallen tsaki taja tamaida idanunta ta
lumshe su ahankali back, maida hankalinshi yayi kan tukin harsu ka shigo ASOKORO District,
Usman katsina street suka shiga yay horn agaban wani makeken mansion da tsayawa
bayaninshi aikine ganin ba'a bude gate dinba yasa yace "auuuu kullum saina manta abin nan"
yay maganan yanadan juyowa ya saci kallon Hajiya yaga tana kaman bacci danhar lokacin
idanunta a lumshe yasan inda idanunta biyu datamai bala'i kan kullum saiya mantada remote
din da ake bude gate dinsu dashi, remote din dake motar yadauka ya danna gate din yabude
sanan yasa kan motan suka shiga cikin gidan gate din yarufe kanshi, kafin ahankali yabude
kofa yafito sanan yazagayo ta bangarenta yabude kofa tareda bending kanshi cikeda respect
yakira sunanta ahankali danya tadata daga bacci. "Hajiya, Hajiya" dan bude idanunta tayi
ahankali tazubasu akanshi awulakance, baidamuba yace "mun iso gida ne daman saisa
natadake" yunkurowa tayi tanajin kaman kanta zai fice amman saita daure tafito hakan yasa
shima ya matsa yakoma baya, fitowa tayi daga motar ta tsaya da kyau da sauri tasake kulle
idanunta jin wani irin jiri take gani hakanan all of a sudden, hakan yasa Murtala daya koma baya
yace "Hajiya karkice nacika tambaya amman kaman bakida lpy wlh, duk jikinki ya nuna hakan"
bude idanunta tayi tazubamai wani matsiyacin kallo dayasa yaji cikinshi ya murda ahankali
yamaida kanshi kasa, daukekai tayi tace "kwasomin jakata da wayata" tai maganan sanan
tajuya tafara tafiya gashi daganan parking space zuwa flat dinta dadan tafiya, amman hakan
take tafiya ahankali dai dai gudun kartaje tazube dan bamatasan meke damuntaba jitake kaman
sauran kiris jikinta yakasa daukanta, akwai staircase haka dazai sadata da kofan shiga flat dinta
ahankali take hawa staircase din cikeda karfin hali irin nata da kyar ta iya daga kafanta tahau
na karshe batasan meya faruba tadaijita akasa sharaf, sanan kuma taji ihun Murtala sama
sama, kara lumshe ido tayi tabude sanan taga Murtalan agabanta ya tsugunna ya haukace
yakasa tabata sama sama takeji yana Hajiya, Hajiya, sake lumshe tayi tabude batasan meke
going on ba tadaiga waya akan kunnenshi saikuma kawai taji yadauketa, kadan kadan take
bude idanunta she could feel and see yanda heart dinshi ke beating, ke racing sosai na
fargaban kar wani abu yasameta saikuma dip ta dauke wuta.
Kwantarda ita yayi akan katafaren doguwan kujeran dake falon cikin jerin hadaddun kujerun
dake wajen, sanan yatashi da sauri hannunshi har rawa yake ya shiga dailing number Alhaji for
the second time yamugun damu dudda yasan Hajiya was never nice to him but still baisan wani
abu yasameta.......
Wajen 30 big men ne zaune awani babban conference room, sunci uban suit, wani hadadden
magidanci mutum dake zaune kan kujeran CEO ne ke magana yana bayani da turenci, ringing
dawayanshi yasakeyi for the forth time yasa yakalli wayan, daukan wayan yayi a hannu yatashi
tareda fadin "excuse me" sanan yafita daga conference hall din yakara wayan akunnenshi,
kafinma Murtala yay magana yashiga balbaleshi da masifa. "Ka kirani kace tasuma nace ka
dauketa ka shiga da ita ciki zan kira Dr, basaika jiraba, saidamuna kake da kira kasan wani irin
meeting nakeyi ne? Kaiwani irin wawan bakauyen yarone wai? In nagama I will call d Dr yazo
yadubata, kawai yanzu ka tsaya tareda ita, karka barta ita kadai, babu abinda zai sameta ai
Hassana is a strong woman she will be fine" ya katse wayan zai maida a aljihu saikuma yaciro
yama kashe wayan gabaki daya dan yasan Murtala baida hankali he will keep calling him this
meeting is very important anjima idan suka gama zai kira Dr su yasa yaje yadubata, da sauri
yawuce yakoma ciki wearing a smile akan face nashi yace "sorry gentlemen let's continue"......
Jikin Murtala har bari yake gabaki daya yama rasa maizaiyi gashi babu kowa gidan, dan ka'idan
su shine ma'aikatansu basu kwana, da maid, gardener da sauransu duk dasafe suke zuwa suyi
aiki sutafi, koma sunanan shibaisan mezaimataba, yana tsaye kanta chan yaga tai wani irin
nishi ta bankare ta tashi, saikuma tafara Jan numfashi kaman numfashinta naso yadauke tana
kakkama wuyanta, tsugunnawa yayi gaban kujeran cikeda damuwa yana tura hannunshi a
aljihu yana ciro wayanshi zai sake dailing number Alhaji yace "Hajiya meke damunki na shiga
uku, Hajiya badai mutuwa zakiyiba" ina Hajiya bamatasan wayeke akanta ba, yay dailing
number kashe, sau uku yana kira wai akashe daidai lokacin tafado dagakan kujera tana nishin
idanunta na kakkapewa shibaimasan meyakeba kawaidai yaganshi ya dauketa ko nauyinta
bayaji yafita da ita daga dakin yawuce yabude mota yasata yagyaramata kafafuwa yarufe sanan
yashiga gaba danna remote yayi gate yabude yasakai yafice aguje yana tuki yana juyowa yana
kallonta yanda yaga tana battling da numfashi yasa kawai yasaki kuka. "Hajiya kiwa Allah karki
mutu, kar yan biyu sudawo Marayu wayyo Allahna" kawai shima yahau kuka kaman yaro, wani
babban government asibiti dakenan a ASOKORO yakaita yay parking yana kuka sosai yay cikin
asibitin yana ganin wani Dr yafito shida nurse kawai fizgo hannun Dr yayi yana kuka sosai, Dr
ma tsorata yayi dan yadauka mahaukaci ne yace "Malam lafiya"? Cikin kuka Murtala yace
"Hajiyata batada lpy likita zoka taimaka mata dan Allah bata iya numfashi" jin maganan dayayi
yasa Dr yabishi Nurse din dasuke tarena binsu har motansu yakaishi yabude Dr naganin yanda
takeyi yama nurse alamu data kawo gado dasauri nurse tajuya shikuma Dr yashiga motan
trying to help her yabude mata baki yana tambayan Murtala dake kuka har lokacin yace "meya
sameta"? Cikin kuka sosai yace "kaman kanta keciwo saita sume saikuma tafara nishi haka"
daidai ankawo gadon da za'a daurata, kallon gadon yayi ya kalli yanda Dr da Nurse ke kokarin
cirota su sakata agado yace "ina zaku kaita"? Dr da hankalinshi baya kanshi yace "ward mu
mata treatment" dasauri yace "likita karufamin asiri kabata magani anan cikin mota kokamata
allura kawai mutafi yan gidansu basa kwanciyan asibiti sunada likitansu na gida, yanzu ma
babu kowa agidan ne" likitan baimabi takanshi ba dan daga gani kasan illiterate ne, idan yabar
matarnan within good 10min heart dinta zai daina aiki tamutu dan as it is ma yanzu heart dinta
is very weak, ciki sukaida ita Murtala nabinsu abaya yana gayamusu zasu sashi a matsala,
suna shigarda ita emergency room suka rufo kofa hakan yahanashi shiga, zama yayi akasan
wajen yana share hawaye na tausayi dakuma fargaban irin fadan dazaisha awajen Hajiya da
Alhaji yau yamusu asalin karambani wlh.
Yana zaune wajen wata nurse tabude kofa tafito yana ganinta yatashi da sauri yace "Ya jikin
Hajiya"? "Da sauki, yanzu munsamata oxygen and per hour is 15k, yanzu anaso kai deposit din
naira dubu hamsin" da sauri ya kalleta yace "eh dubu hamsin" gyadamai kai tayi tace "yes inba
hakaba bazamu cigaba da treatment dinta ba, yanzu dai ansamu munyi stabilizing situation din
idan kabiya kudine zamu cigaba" shiru yayi kaman wawa saikuma yace "kucigaba to bari naje
nadauko kudin agida" Nurse din tace "you have an hour daga yanzu zuwa Magrib" juyawa
yayida sauri yafita yaciro wayanshi yana dailing number Alhaji amman har lokacin akashe, rasa
yanda zaiyi yayi yawuce yakoma mota yaja motar yakoma chan gidan, bangarensu boysqutars
dakinsu yawuce direct, wata katuwar ganamasgo yayi yabude sanan ya shiga cirowa yana
ijiyewa kan katifa sanan yaciro watayar leda baka yakoma gefe ya zauna yabude ledan
albashinshine dayake cirewa yayi saving duka duka 80k ne yamaida ledan ya kulle sanan
yatashi yafito daga dakin dasauri lokacin ana shirin kiran salla komawa asibitin yayi yabiya
kudin komi yarike sauran 30 a aljihu sanan yatafi masallaci kafin yadawo yasake samun wuri
gaban dakin ya zauna yasake ciro wayanshi yay dailing har lokacin wayanshi akashe abin
yabatamai rai amman kuma meruwanshi shidan aikine tashi yayi yawuce masallaci jin ana kiran
isha'i yayi yafita waje yaje yasha shayi da indomie sanan yadawo yasake zama awajen shiru
babu wanda ya cemai wani abu har bacci yasake kwasheshi yay kwanciyanshi kan yar kujeran
yana sharara baccin shi gwanin ban tausayi kana ganinshi kasan yagaji.....
Kaman an tsikareta tabude idanunta ahankali tanabin inda takeda kallo tabbas tasan nanba
gidanta bane, ahankali tajuyarda kanta karin ruwa datagani dakuma oxygen da akai hanging
datagani yasa ta lumshe ido dan tagane she's sick but inane nan? Yunkurawa tayida kyar ta
tashi tazauna tanadanjin jiri kadan, sanan ta kakkalli gefenta but babu jakanta babu wayanta
balle takira wani, sakebin dakin asibitin tayida kallo taga emergency room ita kadaine aciki
nothing to talk about wanan wani irin local daki takene, jitayi warin asibiti da dakin keyi na
irritating nata yasa cikeda karfin hali irin nata ta yunkura tasauka daga kan gado tana zura
takalminta takama karfen da ruwan kejiki dasauri ta lunshe ido, ahankali taja tasaka hannu
tabude kofan tafita tana tafiya kaman zata fadi, tabi wajen dakallo babu kowa a wajen kaman
ance ta kalli side dinta Murtala tagani ya kudundune jikinshi kan kujeran wajen yana bacci yana
sosa hannu daga gani kasan sauro ke cizonshi, tsareshi tayida idanu ranta nabaci mesa
zaikawota irin wanan asibitin, wani irin sarawa kanta yayi sabida bacin ran dataji saikuma wani
irin mahaukacin jiri yazomata tai baya zata fadi tana kokarin rike karfwn da ruwanta ke sagale
shikuma yabugi bango yay lara hakan yasa firgigit Murtala yafarka tareda dagokanshi ganin
Hajiya idanunta na juyawa tana kokarin faduwa but tana kokarin hana kanta yasa yawaniyi
tsalle yace "Hajiya" tareda tarota tafada kan kirjinshi, ko kawo wani abu baiyiba kawai
yadauketa chak dukya rude sanan yaja karfen ruwan yabude dakin yace "mesa kika fito Hajiya
aidakin kirani" ahankali tabude idanunta tana kallon fuskanshi yanda damuwa yanuna ko'ina
akan fuskan, kirjinshi nabugawa fat fat fat tsoron karta fadi dayaji yasa taji something that is
very very strange azuciyanta, she just wish and wish inama Baban Khalid ne haka looking so
worried and so concern about her datafi kowace murna aduniyan nan. "Hajiya!" Firgigit tafarka
daga tunanin dataje ashema harya zaunar da ita kan gado, cikeda damuwa yace "menene
kikeso maiyasa kika fito tsakar daren nan? Jirifa ke mugun damunki? Meke miki ciwo yanzu?
Nakira Dr"? Tunda yakemata tambayoyin take kallonshi saida yagama sanan tahade rai tace
"ubanme nakeyi awanan kazamin asibitin? Wayakawoni nan?" Shiru yayi yasaukarda kanshi
kasa shidaman yasan yayi laifi. "Ina maka magana kamin shiru Murtala!" Tadakamai tsawa
dayasa tasake kama kanta dasauri jin kaman zaifita tace "wa....." ganin yadago kanshi ya
kalleta yasa tahadiye sauran wash din tai maza ta cire hannun tasake daure fuska zatai
magana yace "Hajiya dan Allah kiyihakuri kinji, bakida lafiya baki bukatan hayaniya da fada ko
fushi, kinajin sauki zan gayamiki komi kinji Hajiya" ahankali tajinginar da bayanta da bango
tanadan yatsine fuska tace "ka kira Alhaji? Meyasameni, mesa kakawoni nan"? Yanda tamai
maganan babu wasa yasa yace "kina sauka akan mota kika fita kin fara hawa stairs kawai
naganki akasa kina wani irin nishi........." nan yagayamata komi har zuwa yanzu, dan murmushi
tayi tace "ayya meeting din must be very serious, jeka kiramin Dr" tai maganan kaman bakomi
da sauri yafita daga dakin, daidainan hawayen data rikesu tunda yafara gayamata abinda
yafaru yazubo mata sharrrr yanzu inda ace Murtala bai kawota wanan kazamin asibitin ba
dahaka zata mutu abanza, Baban Khalid bai kira Dr ba saima kashe wayanshi dayayi irin ko
ajikinshi dinan, baimaso adameshi da batun rashin lafiyanta yana aikin office, Baban Khalid
Mijine wai ko Makiyi? Ta tambayi kanta! Jin alamun tafiya yasa da sauri ta share hawayenta
tass, daidai anbude kofa Dr yashigo Murtala biyedashi yana kallonta yace "Hajiya kuka kikayi"?
Wani irin mugun kallo tamai tace "fita daga dakin nan zanga Dr" babu gardama yajuya yafita
yarufomusu kofa, Dr yay murmushi yace "why are u treating someone that saved your life today
like this"? Murmushi yayi yakaraso gabanta yana gyara karin ruwan yace "I understand he's
your driver, but koma a direban ne i must applaud his effort, I am telling u dabadan guy dinan ba
we would've lost you by now, at the time daya shigo dake this hospital inda ace kin kara just
5min without seeing a Dr da heart dinki yadaina aiki, haka yashigo dake he was crying sosai"
dasauri ta kalli Dr tace "crying"? Murmushi Dr yayi yace "abin yabaki mamaki ko kema, aiko
kuka sosai kaman yaro wai dan Allah mutaimaki Hajiyan shi, ya tsareni wai a mota zan miki
treatment baki zuwa asibiti da kyar fa yabari muka shigodake that zakiyi fada" for the first time
tadansaki murmushi iya lebe, saikuma ta kalli Dr tace "what is wrong with me Dr, maisa nai
passout like that"? Kujera Dr yaja yazauna sanan yace "kinada wata damuwa ne, is there
anything wrong with you or bothering u"? Wani kallo tamai saikuma ta tabe baki tace "ni babu
abinda kedamuna, namaka kala damai damuwa ne kakemin wanan tambayan"