Showing 24001 words to 27000 words out of 28936 words
Chapter 9 - AMANI BOOK 3 HAUSA BOOK BY Takori Kabara .pdf
domin ta gaishe da Ummami, sai ta samu Uwar da Dan
suna magana, wato suna magana shi da Ummami amma maganar da ta dan
ja hankalin ta, don ji tayi Ummami na gaya masa Sarki ya karba masa
kyautar sadakoki wato kwarkwara guda biyu na yammata daga Sultanate
of Damagaram.
Amani ta yi sallama a shigifar Mowar Sarki, saidai kuma cikin rashin
saa ta riga ta ji magana ta karshe da Ummamin ta gama fadi wa Maina
yanzun, sai ta samu wuri gefen kafar Ummami ta zauna, kamar ta ji Ummami
tana fadin Sarki ya ce an baiwa Maina kyautar Sadaka, Ummami din tana
tambayar sa ko yana da bukatar amsar su? Yara ne masu matsakaitan
shekaru yanmata, lafiyayyu. Ummami ta kara bayani. Kamar da gayya don
Amani ta ji.
Amani wadda ta ji zancen alhalin tana shigowa, amma bata gane sosai
ba, don haka sai ta tambayi Ummami cikin rashin fahimta bayan ta samu
wuri ta zauna a gefen ta.
Ummami meye kuma Sa-daka?
Ta tambaya ne ganin kamar Mukhy bai so ta ji abinda suke tattaunawa
ba, ya zama kamar mara gaskiya daga shigowar ta, kuma fuskar sa ta ki
karantuwa duk ya bi ya daure fuska. Sannan bai ce komai a kan kyautar da
Ummamin ta ce an yi masa ba, sai faman hade giran sama dana kasa yake yi
yana Harare-harare. Ummami ta ce cikin kwantar da murya.
Sadaka yana nufin kwarkwara (concubines).
A dan rikice Amani ta ce kwarkwara kuma Ummami? Me yasa aka
bashi? Kwarkwara a wannan zamanin? Shi din ne ya ce a bashi ko shi ya ce
yana son su?
Amani ta jero tambayoyin cikin rudewa, rikicewa da da karkarwar
murya, ba tare da ta san lokacin da ta jero su din ba, tsakanin Mukhy da
Ummami, sai ka rasa wa ta jefawa tambayoyin, sai zare ido take a tsakanin su
su biyun, tana jiran dayan su ya bata amsa. Amma duk suka yi mata shiru.
Tsabar rudewa ta ma manta da wacece Ummami a gare ta. Haka ta kafawa
Mukhtar ido cikin tuhuma da tashin hankali. Mukhtar sai ya tashi zai fice
daga dakin, yana mamakin dalilin gigicewar ta da rikicewar ta haka don
kawai an ce an bashi kwarkwara, ba dai zai ce Amani kishi take ba, saboda ya
sha jin ana cewa sai da SO mata ke kishin mazajen su. Shi kuwa ai baida
wannan gatan da wannan alfarmar a wajen Amina-Amani.
Ta soma harzuka, tana kokarin komawa Amani Faskarin ta da kowa ya
sani wadda bata barin ko ta kwana, ganin ta rasa mai bata amsa a cikin su.
Gashi yana kokarin ficewa daga dakin ba tare da ya bata amsa ba.
Ya Mukhy! Magana nake yi. Yaya zaka fita baka bani amsa ba? Kai
kace a baka sadakan, me na yi maka? Am I not enough?
Mukhy har ya kai bakin kofa zai fita, sai ya juyo ya dube ta da warning
look a idanun sa, wato ta san a gaban wa take, da irin maganar da zata furta,
da alama ta manta Ummami na wajen, ya ce cikin fushi.
Are questioning or accusing me? Na yi kama da saan wasan ki da zaki
jefa min query? To ban sani ba din, sai kin matse baki na zaki ji amsar
tambayar taki.
Yayi tsaki ya fice ya bar musu dakin.
Rudewar da take ciki ya sa ta mancewa ko wacece Ummami gare ta, ta
ce don Allah Ummami shi ya roka? Ko shi ya ce muku yana son sadaka?
Ummami sai ta fito mata a mutum sak! Itama, ta dube ta ido cikin ido
ta ce, Amani! Kin ga na lura tun zuwan ku kallon juna kuke kamar ba aure
ne a tsakanin ku ba, alamu kuma sun nuna min tun a Nigeria ma haka kuke
zaune, Mukhtar in ya je fada Baban sa ya lura baya iya komai sai damuwa, in
an yi Magana sai yace naam wato sai an maimaita, shi kuma Mukhtar da
kike gani, Yarima ne maana (Maina ne) Sarki mai jiran gado, shine wanda
ake fatan ya gaji mahaifin sa a komai, bazai yiwu a kyale shi haka babu
kulawar mata ba, ko da sadakan ne don samun nutsuwar sa.
Shi yasa muka ga gara a bashi sadakan ko ba yawa kafin ku daidaita
kan ku, da sabanin da ke tsakanin ku, ki sani Mukhtar Sarki ne, halittar su
daban da ta sauran maza da kika sani a kan mata, kusan in ce miki, duk
yawancin sarakuna. A shekarun Mukhtar yayi hakurin da ya zarce kima
babu mace, gara kada a kure hakurin a bashi karin wasu matan na hutawa,
su kuma yi muku hidima ke da shi har zuwa ku daidaita.
Ko ita dakikiya ce zuwa yanzu ta fahimci me Ummami ke nufi yanzu,
tunda dai ta shiga aji, ba wai bata taba shiga aji ba.
Gata suke nufin zasu yi wa dan su, don sun gane bata bashi kulawar
data dace mace ta baiwa mijin ta na auratayya.
Kasa magana tayi, tayi kokarin rike hawayen ta bata bari sun zubo a
gaban Ummami ba, don kada a ga rashin juriyar ta da raunin ta, sannan ta
mike ta koma sassan su cikin sanyin jiki, sai Kuyangar ta mai kula da kitchen
wato Ramu ce ta biyo ta da wayar ta, don a can dakin Ummami ta manto ta
tsabar ta shiga rudu mai yawa, kuma Ummami bata sake bi ta kan ta ba,
bayan bayanin da ta yi mata. Ta san ta ahada mata bom yadda take so ya
tashi.
Duk da sanyin AC mai karfi da ke aiki a falon ta. Amma Amani zufa
take yi in ta tuno zancen nan. Idanun ta ba abunda suke hararo mata sai
kyawawan yammata abzinawan usli tare da Mukhtar, cikin irin yanayin su
da suka kasance jiya shi da ita, wannan alamari ba karamin daga hankalin
Tafisu ya yi ba.
Fisabilillah me yasa baa yi ma Mukhtar aure tun sanda ta tsane shi ba
sai yanzu da ta soma saka shi a ran ta, ta soma tsara musu rayuwa ta soyayya
mai tsafta a cikin zuciyar ta, kiris ya rage mata ta samu dama ta bayyana
masa son da take masa? Mafarkin ta na haifa ma Ummami da Mai Diffa
jikoki daga Mukhy ita kadai ran ta, ya tashi a banza Kenan muddin aka bashi
wasu matan suka riga ta shiga jikin sa?
A hankali ta soma sheshekar kuka, bata san cewa Mukhy yana cikin
dakin da ta jingina da kofar sa ba. Sautin kukan ta ya dame shi, yana ci masa
rai, don bilhaqqi take yin sa, hakan ya fiddo Mukhy daga dakin barcin nasa,
ya bude kofar saura kadan ta fadi, don a jikin kofar ta jigina duka jikin ta,
tunda ya baro su ita da Ummami gidan sa ya dawo, ya kwanta a daki ya rufe
kan sa yana tunanin karbar tayin mahaifin sa ne ko aah?
Ita bata ma san yana ciki ba, ya zo kan ta cikin fushi dama kuma ran
sa a bace yake da abinda ta yi masa gaban Ummami mai kama da raini, cikin
tsawa ya ce ke lafiya zaki zo ki daga min hankali da kuka haka ina kokarin
samun barci? Me aka yi miki? Wani aka ce ya mutu? Koko rashin hankalin ki
da kika saba?
Amani ta daga jikakkun idanun ta ta galla masa hararar nan tata da ta
dade bata yi masa irin ta ba. Sai yau da ji take gabadaya ta tsane shi bata ko
son ganin shi a idon ta. Sannan ta juya tana share hawayen ta don bata so ya
kama ta tana kukan nan ba, ko don tsira da sauran ajin ta, ta yi masa banza
ta cigaba da share hawayen ta da habar laffayar ta.
Ba gara mutuwa ba ta san kowanne mai rai mamaci ne. Wannan kuwa
tashin hankali ne na har abada ya same ta, in har ta bari ya faru, kishiya daga
zuwan ta gidan miji! Mijin ma Mukhy dan uwan ta da ta soma kallafawa a
ran ta bada jimawa ba, wanda bata kwatantashi da komai a yanzu, son sa
take bilhaqqi.
Mukhtar ya sassauta murya ganin cewa fada da daure fuska bazasuyi
tasiri a gare ta ba, har ya samu ta gaya masa kukan me take yi, ya ce pls
Amani! Na hadaki da Allah ki yi shiru, ki gaya min abinda ya yi sanadin
wannan kukan babu gaira babu dalili. Don sosai ta firgita shi, don kukan nata ba na wasa bane yau, ko na
sakarci irin wanda ta saba a yawancin lokuta, aah wannan kuka ne mai fita
daga kasan zuciyar matar da ke tsananin son mijin ta, kuma dare daya ya zo
ba zato ya ce zai mata kishiyoyi, kuka ne take yi bilhaqqi, baka da zuci, mai
nuna tsananin kishin ta akan abinda take so da zuciya daya.
A matukar fusace Amani ta dago, idanun ta sun yi jawur, hawaye ya
hade da majina ta ce ina rokon ka Allah Annabi ka bace min da gani Ya
Mukhy, sabida bana son ganin fuskar ka, ka tafi gun sadakan da ka je ka
roka a baka sabida na gaza, ka tambaye su kukan me nake yi, tunda kai baka
da hakuri, baka da bin komai a sannu. Son da na samu kaina da fara yi maka,
ina rokon Allah ya sa ya koma inda ya fito, kada Allah ya bar ni da koshin
wahala.
Mukhtar ya hadiye mamakin sa da dariyar data zo masa nan take, sai
yanzu ya gane musabbabin kukan, wanda bai taba ganin Amani na yin mai
zafi da cin ran sa ba, ya ce.
Tafisu yau ni kike kira mara hakuri? Shin a duniya akwai miji mai
hakuri ma iri na? Ni da aka kira bawan Alhaji, mara galihu, mara nasaba kai
har mai kama da shegu an ce min kuma na yi hakuri na Manzon Allah, ban
taba kallon ki da kalaman bakin ki ba, sai matsayin diyar ubangida na mai
daraja a idanu na. Ni tsintacce a bola, ke komai ma na batanci da rashin
galihu ni ne. To ki gayamin ya kike so in yi idan ban karbi wadanda zasu so ni
a yadda nake ba?
Ke da yake yar Qaruna ce kin ki yarda mu daidaita kan mu har yanzu,
sabida baki son yaron Alhaji, ni kuma iyaye na na na son ganin yaya na da
wuri, Maimartaba kuma na son gani na cikin nutsuwar data dace da kowanne
dan gata. Kullum in naje fada bani da nutsuwa in na ga babu yayan Mai ko daya
bayan ni, ina son samun yara wa iyaye na yara masu yawa, tun da su Allah
bai basu yaya masu yawa ba.
Ki fada min yanzu da lafiya ta da komai, an yi mana aure ya kusa rufa
watanni nawa amma har yanzu ban san irin nawa ba, Tafisu zina kike so in je
in yi in ban karbi kyautar sadakoki ba?
Ko kuma durkusa miki zan yi in roki alfaramr ki so ni, ki kuma bani
hakki na? Ai gara sa-dakan, ko ba su nake wa Son da nake yi miki ba, a kalla
zan dinga rage zafin da kike kunsa min dasu.
Amani ta zuba masa jikakkun idanun ta da ke zuba cikin tashin
hankali, bata ko kyaftawa, bata taba zaton Mukhtar zai iya wadannan
maganganun ba, Mukhy mai kawaici da kamewa. Mukhy ya kalle ta yana
murmushin tura haushi, ya kara guma mata da cewa. Kuma banda abun ki, banda shirme irin naki Sadaka ai ba matan
aure bane na hakika a wurin sarakuna, da zaki yi kishi da su, kada ki damu
ababen hutawa ne ga sarakuna kadai.
Amani na neman zaucewa yanzu ta ce au, bama daya bane har nawa
ne ka roko? Yace na roka ko aka bani kyauta? Su biyu ne kawai aka
kawomin daga Sultanate of Damagaram.
A wannan gabar Amani ta kusa dawowa tsohuwar Amanin ta yanzu,
domin jijiyoyin rashin kunya sun mimmike, tsigar jikin ta har tashi take,
manyan idanun ta suka firfito waje, ta ce.
Mukhtar! To kai din wane irin jarababbe ne da zaa kawo maka mata
biyu a lokaci daya? Plus me, three? Kwatakwata shekarun ka nawa?.
Mukhtar ya buda hannuwa irin na (ba matsalar ki bace) ya ce har
goma in ina so zan hada a lokaci guda, in kika bani dama ko yanzu sai ki ga
irin jarabar tawa.
Ya soma tunkaro ta, idanuwan sa na nuna yau ba mai raba shi da
Amani sai Allah yana balle botirin wuya da links din hannun farar shaddar
jikin shi, ta ce.
Allah ya suwake in hada miji da wasu, wallahi sai ka maida ni gidan
Uba na, kafin ka karbo su, ai ba kai kadai ne dan gata ba, nima nan da kake
gani na TAFISU ce har yanzu har gobe, bar ganin na yi sanyi, ina nan a
Tafisu na da ka sani in aka tabo ni.
In banda mugunta na taba cewa kada ka kusance ni? Ko kuwa ba kai
kake dakatawa don radin kan ka ba da son saka ni a damuwa Ya Mukhy? Za
dai ka karba ne don ka sanya ni a bacin rai, don ka ga na fara son ka
Mukhtar ba don komai ba! To idan so cuta ne to hakuri magani ne! na barwa sadakoki kai, ka
maida ni inda ka dauko ni gobe goben nan. Ta rushe da kuka, ta ce wallahi
Katsina zan koma wajen iyaye na, sai dai ka zaba ko ni ko sadakoki, ai da aka
bar ni a nan ba wai an ce gata na ya kare bane. Mukhy, yau ji yayi kamar yayi juyi a gaban ta don dadi, murmushin da
ke kan fuskar sa sai karuwa yake, for the first time ya fahimci Amani ta fara
son sa don radin kan ta, ba abinda yafi dadi ga da namiji irin ya fahimci
matar sa na tsananin kishin sa irin haka, yau ga Tafisu na kukan kishi a kan
sa kamar ta shide.
Niyyar sa da farko shine ya rungume ta, ya lallashe ta ya sumbace ta
son ran sa daga nan koma me zai faru ya faru yau, in yaso gobe yace a bar
sadakokin baya so, ya yi amfani da wannan damar ya gaya mata cewa son da
yake mata mai yawa ne da ya isa cike gurbin mata hudu! Ba wata mace da zai
iya yi wa irin son da yake mata.
Amma ko me Mukhtar ya tuna? Sai ya fasa rungumeta din da yayi
niyya ko ya lallashe ta, ya sa kai zai wuce ta gaban ta ba tare da ya tsinka
mata ba, amma a ran sa yana mamaki yana karawa, wato duk shakiyanci ne
abun nata, Amani ta san SO. Yau wace irin ranar saa ce a gare shi?
Amani ganin zai tafi ya bar ta a wurin, wato bashi da lokacin sauraron
ta, don bai dauke ta mai cikakken hankali ba, bata san sanda ta sha gaban sa
ba. Ba inda zaka je Mukhy, na rantse sai ka zaba ko ni ko sa-dakoki.
Kai tsaye Mukhtar ya wani irin dago, ya zuba mata fusatattun idanun
nan nasa masu kama da an diga musu zaiba, ya ce bani hanya in wuce kafin
in yi huce kan dami a kan ki, me zaki iya idan na ce na zabi sadakokin, tunda
zasu bani abinda Amani-Tafisu bata bani, zasu so ni su kaunace ni, son da
Amani-Tafisu bata yi min, zasu so ni duk rashin asali na da rashin kowa
nawa.
Amma Amani fa? Wadda kyawun Mukhy da ake fadi bai taba bugar da
ita ta So shi ba, saboda Mukhtar bai isa komai ba a idanun ta tunda ni
hadimin gidan su ne! Amani wadda da ta aure ni, ni da bani da asali, kuma ba
dan kowa bane gara ta auri tsohon mai kudi saan Baban ta Alhaji Sadisu
Talle?
Ni kuwa me zai hana ni karbar sadaka, idan har ba maza na rako
duniya ba kamar yadda Tafisu ta rako mata? Kamar wani wani wanda bai
san gatan iyaye ba irin wanda Amani ke tutiya da shi a koda yaushe?
Kullum ki saka a ran ki a wurin Alhaji ne kadai kike amsa sunan
TAFISU, amma baa wurin Mukhtar da sauran mutane ba, tun da ni ban
yarda Amani ta fi sauran mata komai ba sai iya sai rashin kunya da rashin
daa, duk halin banza shi ta fi su iyawa!. Maganganun sa sun ratsa ta, domin ta fahimci ya fidda tsatsar duka
maganganun ta ne dake kwance a ran sa, duk tsayin lokacin data yi masa su,
tana fatan tunda ya furta su yanzu, bayan ta jima da gasa masa su, daga yau
ya samu sanyin su daga ran sa, ko ta samu su bar zuciyar sa gabadaya.
Ta sunkuyar da kai. Guilty conscience na aikin sa ta koina yana
nunawa a fuskar ta. Jikin ta duk yayi dan sanyi musamman da ta ji a jikin ta
Mukhy ya kafe ta da kyawawan idanun sa, yana karantar reactions din nata,
amma Amani-Amani ce har gobe, sai in baka tabo ta ba, masu iya Magana
suka ce. A bar hali a ci me? to hakan yake ga Amani yau ma.
Domin kuwa share tasirin maganganun sa ta yi gefe ko ince ta hadiye
tasirin da suka yi mata ta ce.
Tunda ban fi su ba, shine na hakura na bar musu Mukhtar din, tunda
a duniyar ka mutum ba ya taba yin kuskure ya dawo ya tuba.
Ko mai yasa? Ita kan ta Amani bata sani ba. Amma ta san bata taba jin
faduwa da karaya sun same ta ba irin yau, duk da dai Mukhy yau cikin
subutar baki yayi gangancin gaya mata YANA SON TA, son da baya iya
kwatanta shi dana kowacce mace. Sai hawaye ya kara tsinkewa Amani, ji