Showing 27001 words to 28936 words out of 28936 words

Chapter 10 - AMANI BOOK 3 HAUSA BOOK BY Takori Kabara .pdf

take
gabadaya yau tata ta kare.
Ta samu kanta kawai da kifa kai a kirjin Mukhtar ta shiga sakin kuka
wiwi, tana rera shi cikin zaki muryar ta kamar sarewa”.
Ba kasafai kukan Amani ke bashi tausayi ba, saboda ya riga ya san ita
zuma ce sai da wuta, ta hakan ne kawai zai iya rama kadan daga abinda ta
dade tana yi masa, hakika Amani ta dade tana cutar da shi da kalaman fatar
bakin ta, yana shanyewa yana hadiyewa albarkar mahaifin ta. Amma ganin
irin karayar data same ta yau, ga ta kuma kwance akan kirjin sa sai ya ji
shima rauni ya shige shi, ya kuma san lallai dagaske Amani ta canza, ko a ce
ta fara canzawa, domin a irin zafin kan ta, babu karaya ko kadan a tare da ita
cikin tsarin ta. A ajandar halayen ta duka babu ‘given up’, ba zai ce saboda
sa-daka bane ta fara canzawa, ya dade yana karantar ta, ya san tun kafin
maganar sadaka ta samu canji a kan sa a zuciyar ta, haka ya san baka taba
kishin mijin da baka so har haka.

Zame ta yayi daga jikin sa cikin karfin hali, domin ta saka masa kasala
ba ‘yar kadan ba, ya juya zai fita, cikin mutuwar jiki, ba tare da ya kara cewa
komai ba.
Amani ta sake ruko shi da karfi, murya na karkarwa ta ce,
“Mukhy! Will you believe me, if I said I LOVE YOU?”
Sai ya juyo da dukkan idanun sa yana mata wani kallo, kamar na
warning din ta daina rike shi, amma kuma ya firgita da jin kalaman, domin
sun zo masa a bazata, a cikin idanun sa soyayya da kaunar ta ne tsantsa, haka
nata jikakkun idanun abinda ke kwance cikin su kenan, kallon da sukema
juna ya shiga tado wata irin sha’awar juna ta shiga tarnaki a zukatan su, ta
shiga ruruwa tun daga kwakwalen su har yatsar kafafun su, in bai yi kuskure
ba kamar yau ya taba jin sunan sa a bakin ta.
A yanayin da fuskar ta ta koma yanzu, kamar ta rasa duk wani gatan ta
sai shi kadai, a irin kallon data ke masa yanzu, kamar shi kadai ya rage mata
a fadin duniya, hawaye na zubar mata wasu na korar wasu ta zame daga jikin
sa ta durkusa masa, ta rike kafafun shi tanaci gaba da kukan sosai, tana
rokon sa da murya mai ban tausayi ya yi hakuri da duka halayen ta, daga yau
ta yi alkawari ta daina!
“Ya Mukhy, na yarda ka yi min komai don ka huce hali na na banza, na
yarda hali na da yawa mara kyau ne, na yarda zan canza daga Amanin da
baka so, zuwa Aminar da kake so, na yarda zan zama matar Maina Mukhtar
daga daren yau, abokiyar rayuwar sa ta har abada kuma abar hutawar sa
karkashin inuwar aure.
Amma ka yi min rai! Banda kishiya ko sadaka, saboda bana son su,
zuciyata baza ta iya dauka ba Ya Mukhy. Saboda bazan iya ‘sharing’ Mukhy
dina da wasu matan ba. Hakan zai iya manna min ciwon hauka da ciwon
damuwa. Ya Mukhy don Allah ka yi hakuri, ka yi min rai, kada ka karba!
Kaga ni tun fil azal ba Maina na aura ba Mukhtar na aura, ban san da
wadannan traditions din naku ba, na roke ka kada ka bari kokarin tabbatar
da ‘culture and tradition’ na gidan ku da basu zama dole ba a addidni su rusa
kyakkyawar dangantakar mu, da rayuwar dana yi mana tanadi daga yau”. Amani ta russuna ta sumbaci babban yatsan kafar sa cikin roko, duk
hawayen idon ta ya koma diga akan kafar sa.
Zuwa yanzun kam he’s touched, extremely touched! Kuma ya yarda
abinda take fada daga zuciyar ta yake fitowa, ba daga fatar bakin ta ba,
mamakin hakan da birbishin tausayin da so ke kimsa masa, suka taru suka
soma rinjayar dakiyar sa da pretending din sa, suka hana shi magana suka
hana shi motsin kirki, ita kuma ta kai sumba yatsan kafafun shi, Mukhtar
yayi mutuwar tsaye, amma dai yana gargadin kan sa a kan yayi taka-tsa-tsan

da nadamar Amani don akwai gaggawa a cikin ta, kuma sadaka da bata so ne
sila, yaushe har Amani ta fara son sa irin haka, da har ta shirya rayuwa da
shi haka?
Komai aka ce masa mace zata iya, in dai a kan kada a yi mata kishiya
ne yau kam zai iya yarda.
Mukhtar ya san tsakanin sa da Ubangiji yana matukar son Amani,
halayen ta da dabi’un ta ne dama baya so. Ganin ta tana neman shidewa a
gaban sa yau a kan kishin kada wasu matan su rabe shi ya yi matukar tasiri a
tare da shi ba kadan ba, ya kara masa son ta da jin tausayin ta, ya rage masa
kuzarin muzanta mata.
Duk da haka wani devilish bangare na zuciyar sa bai yarda da ingancin
nadamar tata da soyayyar tata ba, ya fi dangana yanayin ta na yau da KISHI.
Amma a irin kukan da take yi rike da kafafun sa harda sumbata, sai ta soma
saka masa rauni, wato ta soma samun ‘weakness’ din sa, sabida baya son
ganin kukan mace balle matar sa AMANI-AMANAR ALHAJI.
Domin ji yake sumbar da take ma yatsun sa na neman sumar da shi
daga tsaye, duk wasu tsofaffin ‘feelings’ din sa a kan Amani na sake dawowa
sabbi kar, suna sake sakin sabuwar yabanya ta korran ganyayyaki a fadin
zuciyar sa. Yau Ga TAFISU a kwance a kan kafar sa, tana neman gafara da jin kan
sa, daga soyayyar sa da kin kishiya, a irin yanayin da yau ko me ya nema zai
samu har mafiyin sa, ba tare da ya yi ‘hurting feeling’ din ta ba.
Amma duk da haka taurine rai irin nasa ya ki bari ya dago ta, yana
gayawa kan sa kada ya yarda ya bada kai yanzu, sai ya tabbatar da ingancin
wannan nadamar tata da canzawar tata, aka ce kowa ya tuba don wuya ba
lada, duk da cewa a cikin idanun ta ya ga nadama da soyayya tsantsa, sai dai
ya san wasu mata ko basa son miji suna kishin sa, tunda aure ne a tsakanin
su.
Sai kawai ya janye kafafun sa daga rikon ta a hankali, cikin karfin hali
ya taka ya fice ya bar ta a falon, zuciyar sa kamar ta fashe da son Tafisu, da
ke kara tumbatsa a kowanne sako na cikin ta. Yana gayawa kan sa Amani
Zuma ce sai da wuta, gara ya kara rike sha’awar sa a kan ta komai karfin ta,
zuwa lokacin da ya dace da ya amshi nadamar tata, amma ba yanzu da tsoron
sadaka ne yafi rinjaye a ran ta ba, ba soyayyar sa ba (a ganin sa).
**** **** ****

AMANI
A
wajen da Mukhy ya bar ta ta ci kukan ta ta koshi, tana gayawa kan ta
Mukhtar baya ta tata yanzu tunda ya zo cikin gatan sa, ko dama can yaya

lafiyar Kura? Dubi dai irin lallashi da roko da bada kan ta data yi amma
yayi funfurus! Itama kawai gara ta koyawa zuciyar ta hakuri da shi ta yi
zaman Ummami cikin gidan nan, tunda uwar ta ce ko ba Mukhtar a tsakani,
tunda in tace ta barwa sadakoki Mukhtar din, ita a maida ta Katsina ba
sauraron ta za’ayi ba, ba kuma maida ta za’a yin ba, ta san ta shigo gidannan
kenan har abada ba saki ba yaji, sunan auren nan mutuka raba in ji
Ummami, zata koyawa kan ta juriya ta rabu da shi ya auro ko goma ne ta
koma gefe ta yi kallon su.
Tunda shi baya amsar tuban dan adam, ba’a kuskure a nemi gyarawa
ya yarda ya bada ‘second chance’, Allah da kan sa mai afuwa ne, kuma yana
son bayin sa masu afuwa, yana amsar tuban bayin sa idan sun yi repenting,
sun tsarkake zukatan su daga sake aikata wannan kuskure, then why not
him?
Wanda shima ba sama yake da aikata kuskure ba, tunda ba ma’asumi
bane ba kuma Annabi b.
​ Ai bari kawai ta nuna masa har gobe tana nan a Tafisun ta, ajin ta bai
tsinke ba, halin ta na banza na girman kai da raina mutane da wulakanta su
kawai ta bari.
Tana wannan sake-saken tana hadiyar zuciya sabida kukan data ci,
daga bisani ta wuce uwar dakin ta ta kwanta bisa gado, da tunanin Mukhy
barcin wahala ya sure ta a wajen.

Cikin barcin ta, tsabar yadda ta saka Mukhy a ran ta, da son ya
lallashe ta koda da kalaman fatar baki ne, amma ya saka kafa ya fice ya yi
banza da kukan ta, ba tare da ya ce ya fasa amsar sadakokin da aka yi masa
tayi ba wadanda tunanin su kadai neman haukatata yake. Ta tsinci kan ta a duniyar mafarkin ta tare da MOUKHTAR
ISSOUFFOU MASSAOUDOU cikin wani nau’I na soyayyar auratayya mai
shiga jiki da zuciya, tare da dan Issouffou jikan Massaoudou Balaraben Diffa
mai abun mamaki, ta gan su cikin mafarkin Mukhtar yana sumbatar ta iya
sumbata, yana juya ta duk ta yadda yake so, daga hakan sai kawai ta ji ya
dauke ta suna tafiya zuwa turakar sa, yana rada mata cikin kunnuwan ta
cewa.
“Tafisu kin fi sauran mata a zuciya ta!”.

Irin mafarkin da in dan adam yana yi baya so ko sauro ya cije shi ya
farka.
Sai kawai Amani taji muryar Baba Sahura a cikin kwanyar ta.

“Uwa Uwa, Uwa, ke wai lafiya kike barci haka a kasa, ko fadowa kika yi
daga gadon, da baki na faman motsi kamar kina cin tsutsa, ga hawaye kina
faman yi, kuma a bakin kofar daki kamar wata wadda uwa ta yi wa baki?”
Sai lokacin ta ankara wai ashe duk wannan a mafarki ne, kenan ita tata
soyayyar bata zo da wasa ba, Mukhtar har a cikin mafarki neman zautata
yake don ya ga ta gama mika wuya ga soyayyar sa.
Ta mike zaune, bata san yaushe ta fado daga gadon har ta mirgina
kofar daki ba, ita dai ta gan su suna mirginawa a cikin korran ciyayi ita da
Mukkhy, sannan ta dubi Baba Sahura, ta tabbatar mafarki take hakan bai
faru ba, Mukhtar tunda yasa kafa ya fice bai dawo gidan bama, ta kama
Babar ta Sahura ta rungume jikin ta na kyarma, sai ta fashe da kuka, ta ce
“Baba Sahura wai kin ji sadaka za’a bashi?” Sahura ta ce,
“Au! Shine kike neman haukata kan ki Uwa? Yo in dai a kan zancen
sadaka ne Uban ki ma ya auri mata yana saki sun fi goma, shi a kan me zaki
hana shi cika al’ada? Gaki ke ban ga alamar kina masa wani amfani ba sai
shegen kaudi da rashin kunya da kika fi kowacce mace iyawa”. **** **** ****

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login