Showing 3001 words to 6000 words out of 28936 words
Chapter 2 - AMANI BOOK 3 HAUSA BOOK BY Takori Kabara .pdf
karatun ta nutsu, nan dai kin gani gidan sarauta ne babu ta
yadda zaayi su dauki halayen ki na banza da wofi, idan ma bamu koma tare
ba kenan, tunda ke din ba yar sarauta bace, na san kuma yayan sarakuna
yayan sarakuna ya uwan su kawai suke aure.
Mamma Jalan ta ce da ta fi gane shayi ruwa ne. Don in ba Mukhtar
din ba sarkin hakuri da girmama iyayen ta wa zai iya kwasar ta? Ai Amani
an rako mata!
Yau dai gaki gidan sarautar Diffa, ko ki iya takun ki, ko ki ji ki a kofar
masarauta, ko kuma ki kare karkashin azaba da mulkin kishiyoyi.
Idanun Amani suka wani irin raina fata, zuciyar ta ta tsinke, wai bata
san tana da kishi ba sai yau da Mamma ta yi mata fatan kishiya, to ta Allah
ba tasu ba su duka, ta san Mukhtar yana son ta ko bai fada ba, ta ga hakan
muraran ranar su ta karshe da shi a Saliyo gidan Mamma, ta san ko saboda
Alhaji ba zai wulakantata ba balle yayi mata kishiya. Ta san ta yi kuskure ba
kadan ba amma a bata dama zata gyara. Ba wai a bita da mugun fata ba. Sai
ta saka kuka tana cewa.
Mamma ke uwa ta ce, duk abinda kika fada zai iya kama ni, ki fadi
alkhairi a kaina da Mukhy ko kiyi shuru. Ta yaya zaki yi min fatan kora ko
kuma na kishiya? Baba Sahura ta fashe da dariya tana fadin yau kuma?
Lallai Amale ya ga Zaki. Yarinya wa ya gaya miki Bornu gabas take, miji irin
wannan ake cewa baa so banda wauta da hauka?
Daddy ne kawai ya ji tausayin ta, yadda suka taru suka yi mata caaa!
Ganin yadda duk ta bi ta muzanta. Yanzu kam ta gama saddaqarwa Mukhy
ya fi karfin ta, idan bata yi saa bama tare da iyayenta zata koma Katsina a
matsayin sakakkiyar bazawara. Sunan ta ya koma bazawara. Irin iskancin da
ta tata masa da kaskanci da rainin hankali da kyar zai iya yafe mata tunda ya
dawo cikin gatan sa.
Na tuba Ya Ubangiji na tuba! Amani ta fada a fili tana hawaye. Alhaji
daga zaune ya mika mata hannu ya ce zo nan Uwata, rabu da su kin ji!
Bakin su ya sari danyen kashi. In dai Mukhtar dina ne dana sani wallahi zai
yafe miki, kuma shi mutum ne kaifi daya bana jin rashin hankalin ki na
damun sa, tunda yace ya amshe ki to da gaske ya amshe ki, bana jin dawowar
sa gida zata sa ya canza magana. Ke dai ki yi kokari daga rana irin ta yau ki
canza halayen ki, ta hanyar komawa AMINA ba AMANI ba.
Aminatu Mamar Manzo maaobociyar ilmi da hankali da iya zama da
mutane, kin ji?
Ya shiga bubbuga bayan ta yana lallashin ta domin kukan nadama take
yi tukuru. Tana mai adduar kada Allah ya kama ta da laifukan ta a kan mijin
ta Mukhtar.
Daddy kai kadai ne ka yi min fatan alkhairi, na gode Daddy har abada
na san inada kai, na san ba zaka bari a wulakantani ba, wai don nayi laifi na
kuma gane na yi laifi na tuba.
Mamma don Allah ki hyi hakuri ki sa min albarka.
Mamma ta kora ruwan tataccen inibi a tambulan na tangaran mai garai
garai ta dube ta yanzu da rahma a idanun ta, ta ce idan da gaske kike kin
tuba, Shi Ubangiji mai afuwa ne kuma yana son masu yawan tuba daga laifin
da suka san sun aikata. Ni kuma zan taya ki da adddua a kan Allah ya huwwace miki zuciyar
sa, ya baki dukkan soyayyar da ke zuciyar sa, ya kade fitina a zaman ku, ya
baku zuria mai albarka.
Amani ta ruga da gudu ta rungume Maman ta tana na gode Mamma,
na gode sosai.
Sun kwana suna tattauna alamarin nan cikin tuajjibi da mamaki
iri-iri, Mukhtar dan baiwa ne hakika, wanda bai taba alaqanta kan sa da
wata daukaka irin haka ba a inda ya tabbatar baa san ko shi waye ba, amma
hakika wasu attributes nasa da yawancin personality din sa masu tsinkaye a
cikin su irin Mamma, sun ce sun sha alaqanta shi da babbar sarauta ko
babbar nasaba.
Suka kwana hira da tsarkake tsarkin mulkin Ubangiji.
**** **** *****
Haka suma Uba da dan da mahaifiyar sa, sun kwana tare a turakar
Sarkin Diffa, kamar su maida dan nasu Mukhtar cikin su. Wani abu ne da
Mukhtar bai taba samu tare da su ba tun haihuwar sa, wato closeness sai yau.
Don haka (he cant control his tears). Maina ina ka je? Maina ina ka shiga? Maina ka bar mu, shekara goma
sha biyar ba kwana goma ba Maina in ji Ummami, tana share hawaye da
gefen laffayar ta.
Ummami I thought kun fi son hakan, kun fi son in yi nisa da ku din, ba
kwa so in rabe ku, kamar ba ku kuka haife ni ba.
Na yi kokari na jure hakan tun haihuwa ta amma dana fara girma sai
abun yake neman zame min ciwo a zuciya ta, dole na zabi in tafi in yi rayuwa
a inda bazaku ko samu labari na ba, tunda zamana tare da ku bai da wani
amfani a gare ku. Daga baya kuma kullum na yi kokarin juyowa gida bana iyawa
sakamakon dabaibayin dake zuciya ta.
Rana daya Allah ya yaye min wannan dabaibayi, naji hankali na ya yo
gida, Im so sorry Ummami, har aure na yi babu jimawa bada sani da yardar
ku ba, but I have no choice, saboda mahaifin ta has been my savior, my
shelter for a very long time. Nan ya gaya musu cewa bayan ya karbi kwalin kammala karatun
sakandire tare da yayan bayin gidan a makarantar gwamnatin Diffa da yayi
ya kasa cigaba da zaman kasar Nijar, ya yanke shawarar shiga duniya ya
nemi ilmin da zai taimaka masa ya dogara da kan sa. Tunda sun nuna basa
bukatar shi a rayuwar su sun bar shi a bangaren bayi yana rayuwa tare da
yayan bayi, karkashin kulawar Jakadiya da mijin ta Sarkin fada, wato
Bafade Katchalla wanda shi ya fara gane shi yanzu ma da ya dawo.
Ya ce tunda na taso na ganni a hannun jakadiyar Ummami, ita ta raine
ni, saidai lokaci lokaci ta kaini gun Ummami ta kuma dawo dani bangaren da
take wato bangaren bayi.
Dana fara girma, ma sai ta rage kai ni gun Ummami, itama ba koyaushe
take wuni da ni ba tafi wuni a cikin gida, sai dai in yi ta wasa da yaranta maza
guda biyu saanni na, sai na dauka ma su suka haife ni wato ni dan jakadiya
da Baba Katchalla ne, musamman da suka saka ni a makaranta tare da
Shettima da Ari, wato yayan su, muke zuwa tare kullum muna dawowa.
A hakan sai na fara mantawa da Ummami, wadda nake gani lokaci
lokaci, kai kuwa Maimartaba dama ba a zancen ka, don tsakani na da kai sai
dai in hango ka a turakar ka ko a fada, ko a kan Rakumi idan ana wani
festivities din kamar misali bikin sallah ko na aure ko na nadin sarauta. A baya Baba Katchalla na zuwa da ni fada mu zauna a gefe nida shi,
bazan manta ranar da kayi masa tsawa ba, ka ce kada ya kara kawo ni fada,
mai bakin baya ne ni, tunda ga kai na ko batan wata baa kara yi a gidan ka
ba. A ranar ne ma wasu a fada suka san ni dan Sarki ne. Nan ne aka yi ta
kuskus a gari wai ashe Sarki yana da Da namiji amma baya son yaron. Ya
barwa bayi shi.
Wannan zance har a makaranta an yi min gorin sa, lokacin ina karatun
sakandire. A wani dare na tsuye jakadiya ina tambayar ta da gaske ni dan
sarki ne? Kuma Mowar Sarki wato Ummami da muke zuwa wajen ta lokaci
lokaci har wani lokaci ta bani apple ita ce mahaifiya ta? Jakadiya ta tabbatar
min haka ne, amma bata san dalilin ku na ajiye ni tare da su ba, kodayake
tace Sarki da Mowar gida basu da trusted servants a cikin bayin su kamar ita
da Katchalla.
Tace Sarkin Diffa ba mai yawan haihuwa bane, shiyasa yake ta aure
daga kasa-kasa don ya samu haihuwa, a irin haka ne ya auro mahaifiya ta
daga wata kasa cikin kasashen Afrika, yayan sa biyu kacal kuma duk mata
ne tare da matar sa ta lalle wato uwargidan sa da mai bi mata wato mata ta
biyu. Daga kan su bai kara samun haihuwa ba sai da ya auri Ummami, kuma
tun haihuwa ta suka bata ni, shayarwa ma a boye Ummami ta shayar da ni
don sai ta bita cikin sirri ta roke ta.
Bayan ta yaye ni ma kuwa bata bukatar a kai mata ni inda take. Ni ne
dai dana yi hankali na ji ba wanda nake so a duniya irin ki Ummami, sai nake
satar jiki ina zuwa inda kuke, wani lokacin inna leka inda kuke zama da
laasar zan same ku kuna sallah tare ke da Sarki, ko kina zuba masa abinci ko
kina masa yankar farce, har rannan wani bafade ya kama ni ina leken ku ya
taska min mari, shine fa ban kara leken ku ba daga ranar.
Watarana Baba Katchalla yace muje ana bikin Yaya ta a cikin gida, nan
na bishi muka je har fada naga irin auren gata da aka yi wa yar uwata, akan
taguwa aka kai ta Tahoa inda ta auri dan sarkin Tahoa, ni kuwa inna shiga
cikin gidan na hau rabe-rabe kenan kamar mara gaskiya, hatta sittiru na tare
ake din ka mana da Ari da Shettima, babu wani banbanci tsakanina da su. A
makaranta ma ajin mu daya da su.
Dana fara hankali sai nake tambayar kaina to meye dalilin hakan da
sarki da Ummami suka zabarwa rayuwa ta? Na sa a raina bakin bayan da ya
taba ambata min ne dalili, wato daga kaina ko batan wata wata matar sa bata
kara yi ba har ita Ummamin. Amma ai wannan bai isa dalilin da zasu sarayar
da rayuwa ta a hannun bayin su ba, sai ma dai yayi dalilin da zasu daukaka
daraja ta fiye data kowa a masarautar.
Bani da wata shakuwa ko kusanci da ku da zai sa na iya yi muku
wannan tambayar. Ban ma isa in je inda kuke kai tsaye ba.
Na yarda iyaye na kun haife ni ne da gaske, amma kuma baku kauna
ta!
In na tuna hakan sai wani irin bakin ciki ya murde ni, har ya zame min
habit, daga baya bayan na kammala sakandire na ji bazan iya cigaba da zama
a Diffa ba, gara in tafi inda bazaku kara jin labari na ba, tunda kun haife ni
bisa kuskure amma bakwa kaunata ko miskala zarratin. Wannan abu ya cigaba da bakanta min dare da rana, har na koma
tamkar depressed, na daina walwala, na daina shiga cikin saanni na, na yarda
bakin baya na zai iya shafar kowanne yaro iyayen sa su tsane shi.
Duk da babu abinda Baba Katchalla da Jakadiya suka raga min, suna
ma kula da ni ne har fiye da yadda suke kula da yayan su Ari da Shettima.
Rana daya na yanke shawarar barin Diffa, to amma ina zani bani da ko sisi?
A hakan ne aka ce sakamakon mu na sakandire ya fito, kuma na ci
jarrabawa ta da sakamako mai kyau wanda yafi na kowa, don haka
gwannatin kasar Nijar ta dauki nauyin karatun mu ni da wasu dalibai
zakakurai iri na zuwa kasar goyon mu wato Faransa. Aka damka min
admission dina da tikitin jirgi, na so in gayawa Baba Katchalla amma zuciya
ta ta kwabe ni, kan cewa zai iya hana ni tafiya, ku kuwa dama na san ba
damuwar ku bace rayuwa ta ce, baku da matsala da wannan, hasalima na yi
amanna farin ciki zaku yi in yau aka ce na bar Diffa.
Hatta malaman makarantar mu basu san cewa ni Maina ne ba, sun
dauka ni dan bawa Katchalla ne wanda kusan kullum shi yake kawo mu
makaranta ya kuma zo ya dauke mu.
Don haka da aka fara jigilar daliban da suka samu scholarship na sulale
na tafi Agadez tare da sauran dalibai yan uwa na, inda daga can jirgin mu ya
daga zuwa France. Acan ne aka rarraba mu zuwa jamioI daban daban a
cikin Faransa, ni aka bar ni a Jamiar Paris Saclay University. ***** **** ****
RAYUWA TA A FARANSA
R
ayuwa ta a matsayin dalibi a birnin Paris, rayuwa ce irin ta kowanne dalibi
mara gata sai na gwamnati, mai fafutuka da neman ilmi da gumin sa,
gwamnatin kasar mu na bamu alawus wanda da shi muke rike kan mu. Na yi
wani dogon rashin lafiya bayan tahowa ta kamar bazan rayu ba, don sai da na
kwashe watanni biyu a asibiti bansan inda kaina yake ba, bayan na farfado da
kyar, na ji a cikin kaina bani da buri irin na kara nesanta kaina da gida,
kuma har Paris din ji nake ta min kusa da Nijar amma hakika ina son samun
kwalin degree dinnan, shiyasa na tsaya. Da kyar na samu na hada karatun
domin banida cikakkiyar lafiya kuma likitocin kasar duk kwarewar su sun
kasa gano takamaimai me ke damu na.
Akwai wani abokin karatuna Musulmi, Faiq, da ya zo daga kasar
Masar, shi ya bani laqanin kullum in karanta ayatul kursiiyu kafa bakwai in
tofa a ruwa da safe in sha kafin in ci komai. Da wannan lakanin na fara
samun lafiya har na kammala karatu na da kyakkyawan sakamako. Daga wannan lokacin ne tallafin da kasar mu ke bamu ya yanke mana,
wato dama scholarship din mu iya degree ne, sai na shiga tunanin hanyar da
zan bi in yi sponsoring karatu na na gaba wato masters, duk dai don in samu
damar cigaba da zama a Paris kada in koma gida. Ayyuka na neman rufin asirin dalibi iri-iri babu wadanda ban yi ba, tun
daga wanke-wanke da share-share a hotel, direban bus, jiran shago, zaman
library da kuma receptionist, da haka na kukkulla na kukkula na dinga biyan
kudin karatun masters dina in instalments (a rarrabe) har Allah ya taimake
ni na samu shaidar kammala degree na biyu, daga nan na dukufa neman aiki
kwakkwara amma ban samu ba, ko in ce ban dace ba, ina tunanin fallewa
zuwa Hong-Kong again, don neman aikin yi, Allah ya hada ni da Ubangida na
na yanzu, wato Alhaji Usman Faskari.
Nan ya labarta musu komai na irin haduwar da suka yi da Alhaji, ya
biyo shi Najeriya ya bashi gida da aiki ya kuma ja shi jikin sa da amana irin
yadda ko yan uwan sa bai yi wa ba, duk tarin alkhairin Alhaji gare shi sai da
ya fada musu har zuwa lalurar data same shi wadda tayi sanadin bashi auren
AMANI da Alhaji Usman yayi. Yadda a rana daya yaji duk wani dabaibayi da
ke zuciyar sa a kan Diffa ya yaye, da kuma karfin zuciyar da ya samu na
dawowa gida karkashin umarnin Alhaji duk ya fada musu.
Tun kafin Mukhtar yayi nisa da labarin nan daga Maimartaba Sultan
Issoffou Massaoudou har maidakin sa Ummami kuka suke yi sosai.
Sarki Issoufoou ya janyo Mukhtar jikin sa ya rungume shi yana kuka
sosai da hawayen sa, yana rokon sa ya yafe masa, ya ce da Mukhy (cikin
vernacular language din su).
Moukhtar, duk abinda muka yi dinnnan muna sane, we did it to
protect you from envy, hatred, evil eyes, bad luck, and to save you, as the only
male child that I have, to make sure you get the throne of Diffa Emirate at an
appropriate time. Ni da kaina na hana mahaifiyar ka jan ka a jikin ta, nida kaina na ce ta
fidda kai daga ran ta, Allah zai raya mana kai. Ba zaka taba zama sarki ba
idan ka samu gatan da yayan sarakuna ke samu, kasancewar kai din daban
ne, zagaye nake da makiya haka mahaifiyar ka zagayeta ke da kaidin mata
yan uwan ta iri iri musamman da ta haife ka, kasancewar ni mutum ne mai
yawan aure-aure, amma tunda muka watsar da kai sai duk hankalin su ya bar
kan ka, ya koma kan yadda zasu yi su samu nasu yayan suma, don na nuna
bana kaunar ka ban damu da rayuwar ka ba.
Mukhar dauriya iya dauriya irin wadda ba duka iyaye zasu iya ba a
kan dan da suka haifa kwalli daya muka yi a kan ka, domin mu tseratar da
rayuwar ka, amma duk halin da kake ciki a gidan Katchalla wallahi mun
sani. Kuma muna kulawa da komai naka. Hatta tafiyar ka Farisa mun san da ita, nine kuma na sa aka baka
scholarship daga ofishin Baare Mainasara (shugaban kasar Nijar na wancan
karnin).
Haka daga sanda ka bar Farisa ne muka daina samun labarin ka
sannan bamu san ina ka koma ba.
Malamai na daban-daban na cikin gida kullum gayamin suke in
kwantar da hankali na domin kana raye, kuma a kyakkyawan hannu mai
tsafta, amma na kasa kwantar da hankalin nawa.
Kullum (blaming) kaina nake yi kan ko dai hukuncin dana yi wa
rayuwar ka ba dabara bace karbabbiya? Ko dai kuskure na yi maimakon
(saving life) din ka?
Wannan tunanin da wannan nadamar su suka taru suka kwantar da ni
na lokaci mai tsaho.