Showing 1 words to 3000 words out of 28936 words
Chapter 1 - AMANI BOOK 3 HAUSA BOOK BY Takori Kabara .pdf
AMANI
3
Littafin
SUMAYYAH ABDULKADIR
(TAKORI)
takorikabara@gmail.com
07030137870
TAFIYA ZUWA DIFFA
M
asu iya magana suka ce tafiya mabudin ilmi, wasu kuma suka ce tafiya yankin
azaba. To duka dai Alhaji da iyalin sa da yan uwan sa babu wanda basu
fuskanta ba a hanyar su ta zuwa jihar Diffa ta kasar Nijar. Ga Karin ilmi
suna ta samu a kan garuruwa da Baba Idi ke musu bayani kasancewar ya
taba zuwa fatauci Nguigmi daga Maiduguri tun yana saurayi, ga kuma
yanayi na wahalar zafin ranar sahara wadda tasa hatta A/c din motar daina
bada sanyi ta ke yi lokaci-lokaci saboda zafin rana da zafin rairayi irin na
sahara. A hakan ma don sun yi zagaye ne ta Maine-Soroa da Nguigmi basu bi
ta cikin Bama din Maiduguri ba.
Kasancewar sun fito tun asubah, tafiya non-stop, kuma mota lafiyayya,
zuwa yamma sai gasu a cikin Maine-Soroa, makwabtan Diffa, anan ne suka
tsaya suka yi sallah azahar da laasar da ta riske su a hanya, suka sayi
gasashshen naman rakumi da madarar rakumi mai dumi sabuwar tatsa da
sabon cukui a nan cikin garin Maine-Saroa suka ci, suka sha, Mukhy har
Shayin su na Tubawa ya saya ya sha, dama kuma dai sun yo guzurin su yadda
ya dace na abinci da abin sha, wanda tun dare Rakiya ta shirya musu suka
taho da su, wadanda ba masu lalacewa ba, snacks ne da soyayyun kaji
(pepper chicken), don haka basa tare da yunwa har suka shiga jihar Diffa.
Shigar su garin ke da wuya komai ya soma kwancewa Mukhtar, (his
in-born character) ya soma aiki a kan sa, ta yadda hatta gashin jikin sa dana
kan sa sai da ya mimmike da duk wani gashi da ke jikin sa. Amani da ke
gefen sa yana tuki, ta lura da yadda Mukhtar ke canzawa a yanayin sa da
halittar sa, wata irin kamala da nutsuwa suka bayyana a tare da shi, suka
lullube ainahin Mukhy saurayi nan dan gaye suka maida shi cikakken
MOUKHTAR din sa, tsigar jikin sa har wani tashi take yi kamar mai jin
sanyi. Jinin Issouffou Massaoudou ya soma circulating yana kurdawa a cikin
jikin sa, yana sauya shi daga normal Mukhtar din sa da kowa ya sani zuwa
Mainan Diffa na asali. Amani bata san me Mukhy yake kwancewa daga leda
ba ta ga dai Mukhtar ya saka hannu ya janyo wani farin kyakkyawan tsohon
amawali (rawani) daga cikin leda, ya kashe motar su a gefen titi.
Rawanin nan ya hau nannadawa cikin iyawa da kwarewa, saida ya nade
kyakkyawar fuskar sa tsaf, sai tsinin karan hancin sa da manyan idon sa ne
kadai ya bayyana, kwatankwacin yadda taga nadi a fuskar mafi yawancin
jamaar garin maza, wato nadin rawani irin na buzayen asali ko kuwa
Tubawa, ko kuwa a kira su da yadda aka san su da shi wato Larabawan Diffa.
Sai bata yi mamaki ba, don kuwa ta san cewa baa canzawa tuwo suna,
Mukhtar duk dadewar sa tare dasu, idan aka taho gida, shi buzu ne na
hakika.
Ya ja motar suka cigaba da tafiya. Baba Idi na tsokanar sa wato kowa
ya bar gida-gida ya bar shi, kyawun kowanne tsuntsu yayi kukan gidan su.
Mukhtar yayi dan murmushin miskilanci ta cikin amawalin sa, bai ce komai
ba. Amma ya yarda da maganar Baba Idrisu cewa kukan gidan su har da
kururuwar gidan su yake yi yanzu.
Zuwa lokacin sun shiga tsakiyar gari, Amani ta bude hanci da ido tana
shan kallon alummar wannan jiha dake cikin janhuriyyar Nijar, ta fahimci
cewa sittiru, kamanni na halitta da dukkan aladar su ta barranta da ta inda
ta fito, suna ta gudanar da harkokin su na yau da kullum cikin sukuni da
godiyar Ubangiji, domin kuwa alummar wannan yanki na Diffa mafi yawa
talakawa ne likis, masu abin yi daga kiwon dabbobi (livestock production),
kasuwancin waje (export trade), jimar fatar rakumi da sauran su. Sun kuma
kasance maabota biyayya ga shuwagabannin su, wato sarakunan yankin
Diffa.
Shiga nan fita can Muktar bai manta hanya ba, bai manta koina ba,
kamar wanda ake bankado komai daga cikin kwakwalwar sa ana nuna masa,
kamar jiyan nan ya tafi daga Diffa. Haka yake ji yanzu da ya dawo cikin ta
kamar ba shekara goma sha biyar ba, haka rayuwar sa ta baya ke rewinding
kamar kaset din video a cikin kan sa, tana tuna masa duk abinda ya faru a
baya.
Sai suka hau wani mikakken titi dodar mai nisa, wanda daga shi Amani
ta soma hango wani dogon kasaitaccen gini, wanda tsahon sa da fadin sa ya
kai daidai da kilomeita (2,988), wani katafaren gini suke dosa wanda daga can
sama aka rubuta da harshen larabci Al-iimaarat-al Diffa wato Diffa
Emirate da harshen turanci. Suka cigaba da tafiya Amani na cewa a ran ta
wato in ka zo garin, sai ka fara kaiwa sarki gaisuwa dole, kafin a bar ka ka
tafi cikin gari inda ka zo.
Can kuma ta ce Watakila kuma Baban sa bawan sarki ne, shi yasa ya
tura shi birni neman kudi maimakon ya makale abin sa su yi bauta tare.
Ai kuwa ta kasa shiru, ta kasa barin tunanin ta a ran ta, lokacin da ta
ga sun hau titi fetal wanda ya mika har cikin fadar Diffa. Masu tsaron babbar
kofar masarauta ta farko suka tare su a kofar shiga, amma da Mukhtar ya
sauke tagar sa, suka ga wannan nadin dake kansa da wannan amawalin da
kuma tambarin da ke jikin rawanin, sai kawai suka daga musu kofa suka
wuce ciki. Gasunan gasu nan har gate na biyu, shima kamar na farko daga ya
sauke glass sun ga irin nadin sa da amawalin sa sai suka daga masa kofar
masarauta suka nausa ciki.
Daga nan sai gate na karshe, wanda shine na uku kuma daga shi sai
fada.
Anan ne aka dan takura da binciken bayan motar su kafin Mukhtar ya
sauke glass, Amani na cewa Daddy ashe dan naka bawan sarki ne? Ko ko
dan bayi ne ka ga duk sun san shi. Mamma Jalan ta kusa zagin ta, don ita
jikin ta ya fara bata abubuwa masu yawa, amma Amani tana haukan ta irin
wanda bata san ranar shiryuwar ta ba. Baba Idi ne ya ce mata shi dan bayi
ba mutum bane? Jaira marar mutunci. Sai tayi dif!
Wani tsohon bafade tukuf, ya dogaro cikin kayan dogarai na jikin sarki
sosai ya zo bakin tagar da Muktar yake, yace Samari, na gan ka da
Amawalin gidan nan, Amawalin dana baiwa Mainan Diffa, amma ban shaida
ka ba, ko zaka bude amawalin in gan ka sosai, kafin mu yi muku iznin yin
parking a kofar fada?
Sai kawai Mukhtar ya sa hannu yana warware rawanin kan sa, yanayi
wa tsohon nan murmushi idanun sa fal hawaye. A hankali ya ce Baba na
Katchalla! Tsoho Bafaden nan sai ya fadi kasa, yana fadin Allah ya taimaki
Mainan Diffa, barka da dawowa hasken Diffa! Wannan batu da wannan tsohon bafade ke yi shi ya janyo hankalin
sauran fadawa duk suka taho da gudun gaske, wajen hannu goma ne ya
budewa Mukhtar kofa a gigice, suna faduwa suna tashi suna fadin Hasken
Diffa ya dawo, barka da dawowa hasken Diffa, barka da dawowa tauraron
Diffa, Maina ka sauka lafiya ka taka a hankali.
Allah ya kare tauraron Diffa, haske maganin duhu, hadari malafar
duniya.
Daga nan aka bude musu kofa a ka bazawa Mukhtar babbar riga aka
kareshi ya sauko daga motar.
Tuni har wani ya sheka labari cikin gida wai ana tsammanin Mainan
Diffa ya dawo, zancen nan nan da nan ya isa kunnen Sarki Issouffou
Massaoudou, wanda ke kwance a turakar sa a lokacin bayan ya sha magani,
ya soma shirin dan mikewa ya kwanta kafin lokacin da zai fita fada. Sai ga
wayar sarkin fada wanda ya manta shekaru nawa rabon da ya kira shi a
waya, don a kaida fadawa basa kiran sa a waya.
Kamar bazai dauka ba amma sai yayi tunanin banza bata kai zomo
kasuwa haka kawai Katchalla ba zai kira shi ba, sai ya daga. Yana dagawa
kuwa sarkin fada ya fashe da kuka yana fadin nayi rantsuwa da Allah ga
Maina ya dawo, ka san dai cikin kowanne hali bazan kasa gane shi ba ko da
bai zo da rawanin sa ba.
Sarki Issouffou Massaoudou a kwance yake, amma sai ganin sa yayi a
bakin kofa ya manta cewa jar hula ce da ake kira Dara da rigar shan iska
mara hannu kadai a jikin sa, ya kama hanyar kofar da zata sada shi da
hanyar fada. Fadawan da ke tsaron kofa sun kidima da ganin fitowar Sarki a haka
yana ta surfa uban sauri, aka kuma rasa wanda zai tare shi ya tuna masa
babu amawali da alkyabbar sa a tare da shi. Farin dattijo amma ba tukuf ba,
kyakkyawan Balaraben Diffa na gaske wanda yawan shekarun sa bai boye
kyawun surar sa na lokacin kuruciya da tsananin kamannin sa da Mukhtar
ba.
A lokacin har an shigar dasu Mukhtar fada, baka jin komai sai tashin
kirarin da fadawa ke zubewa a kasa suna yi masa.
Hadari malafar duniya, hadari sa gaban ka inda kake so, gaba salamun,
baya salamun, haske maganin duhu Zaki dan Zaki, Majina gishirin yaro, tsawa
mai ratsa gidan arna. Kunun bagaruwa cika ciki har makogaro. Dan Sarki jikan
Sarki kuma sarki mai jiran gado.
(Wannan kirari ba da hausa suke yin sa ba, suna yin sa ne da
vernacular language din su wato Chadian Arabic daya daga cikin yaren
Diffa Arab). Wani babban bafaden kuma yace Zakin duniya makiyanka
fadawan ka, ana kin ka ana rusuna maka, ba yin kan ka bane yardar Allah ne
da adduar iyaye ya dawo mana da kai. Allah Ubangaji ga Mukhtar dan
Issouffou Massaoudou ya dawo gida. Hasken Diffa ya dawo, duhu ya yaye!.
Amani da iyayen ta da ke kallon abinda ke faruwa kamar a majigi, sun
kasa ko motsin kirki. Amani ta lura hatta tafiyar Mukhtar ta canza kan ta da
kan ta, ba irin wadda yake yi a baya bace. Me ke faruwa ne haka a gaban
idon ta? Wanene wannan Mukhtar din? Wane alamari ne tattare da shi
haka?
Jalan, wadda ke tura Alhaji cikin wheelchair zamu iya cewa mamakin
ta ragagge ne, ko dama a tunanin ta tun ganin ta da shi na farko, bai yi mata
kama da komai ba sai dan sarauta maabocin kyakkyawar nasaba, duk wasu
attributes na sarauta sun bayyana kan su a tare da shi da halayen sa. Baba Idi da Baba Sahura sai zare ido suke don kuwa Sahura har fitsari
ta yi a wando data ga wani katon Zaki mai rai a zaune, amma bai ci kowa ba,
sai daga baya ta gane zane ne da aka yi da ceramic (architect) amma kamar
real image na zaki mai rai, tambarin Issouffou Massaoudou Kenan, wato
Zaki dan Zaki, zakin Diffa.
Alhaji Usman dai hawaye yake sharewa a fakaice, ba tare da ya bari an
gane kuka yake ba, Mukhtar ya shammace shi yadda baya zato, ashe dan
sarkin Diffa ne mai jiran gado yake masa bauta iya bauta shekaru kusan
goma! Dadin abun ya kyautata masa ya kaunace shi, irin yadda ko yan wan sa
na jini bai yiwa hakan ba. Allah ne ya hada shi da Mukhy amma bai taba
kawowa ran sa wai dan sarki bane mai jiran gado. Yafi dangantawa ma da
cewa bashi da kowa a duniya shiyasa baya ko so a yi masa zancen ya je ganin
gida.
Karyar ku makiya da mahassada, karyar ku ta kare mahainta, yau Allah
ya maido Mainan Diffa gida (Maina na nufin Yarima mai jiran gado a Diffa,
kamar yadda Biyamaradi yake a Maradi).
Ire-iren kirarin da ake ta yi wa Mukhtar kenan har aka bashi kujera
kusa data Sarkin Diffa, amma sai ya ki zama ya zube a kasa yana kukan farin
ciki da godiya ga Allah.
A haka Sarki ya fado fadar, sarkin fada ya biyo shi da Alkyabbar sa da
amawalin sa suka rufe kofar fadar aka hana kowa shiga bayan shigewar
Sarki.
Yana zuwa da Mukhtar ya fara tozali, ya ce Mon pils (Da na) Mukhtar
da gaske nake gani? Koko ire-iren mafarkai na ne? Sai yayi baya luuu! Zai
fadi, kasancewar dama yana fama da hawan jini tun tafiyar Mukhtar wanda
ake treating din sa tun lokacin, cikin zafin nama Mukhtar ya tare mahaifin sa
ya rungumo shi a kirjin sa, (for the first time) a rayuwar sa da jikin sa ya
shafi na mahaifin sa, suka zube a kasa tare.
Nan fadawa suka kare scene din da hannayen manyan rigunan su aka
umarci kowa ya fita sai manyan fada kadai. Mukhtar sai firfita yake ma sarki
da rawanin sa yana fadin ka yafe ni Ya Abiy, na dawo kenan babu inda zan
kara zuwa, koda zan cigaba da rayuwa yadda kake so. Da kyar aka samu Sarki Issoufou ya zauna a kujerar sa, sannan ya yi
umarni da ayi wa wadanda suka kawo Mukhtar sauka ta alfarma a babban
masaukin bakin sa.
Ummami na can cikin gida amma tuni labari ya kai mata ta bakin
Jakadiyar Sarki marikiya ga Mukhtar, wadda ta shiga turakar ta kai tsaye ba
tareda ta jira an mata iso ba, ta same ta tana haki, tana cewa yanzu wani
bafade ya gaya mata wai Maina yana cikin fada bata san ko da gaske bane
don yace an kulle fada, an hana kowa shiga.
Mowar Sarki, sai ta mike ba tareda rakiyar kowa ba aka ga ta kama
hanyar fita, akwai wata boyayyar kofa ta cikin turakar Sarki wadda yakan
shiga fada ta cikin ta wani lokacin, ta can Mowar Sarki ta bi ta isa fada,
Mukhtar sai ganin Ummami yayi a gaban sa, ta dubi Mukhtar shima ya dube
ta ta taba shi ta tabbatar dan ta ne kwalli daya a duniya Mukhtar dan
Issouffou Massaoudou, wanda ya bar su yau shekaru goma sha biyar! Kafin
Mukhtar ya ambaci sunanta wanda ya kakare a makogaron sa ya kasa fita,
Ummami ta fado jikin sa luuu! A sume.
Mukhtar yana fadin Ummami kada ki yi min haka
.. kada ki mutu
bamu gana ba, bamu fayyacewa juna zuciyar mu ba. Na yi nadamar tafiya ba
tareda na fayyace muku abinda ke rai na ba, kuma kun bani uzurin ku!
Yanzu da girma ya same ni na san kuna da uzuri fiye da nawa. Aka
yayyafawa Ummami ruwa ta farfado sai ta rike Mukhtar ta fashe da kuka.
A lokacin an fita dasu Amani da Mamma da Daddy da su Baba Idi
zuwa masaukin da Sarki yayi umarnin a kai su. Wani hamshakin gini ne na
sarauta da yaji kujeru royal chairs na alfarma, da dakunan barci da aka
kawata da gadaje na kasaita, babu abinda babu a wannan guest house din ga
dakunan barci rututu. Aka shiga sauke musu kabakin abinci har da naman
Dawisu, aka ce su kintsa kafin washegari Sarki ya gama ganawa da Maina zai
neme su.
In ka ga fuskar Amani a cikin guest room dinnan ta koma kamar
jikakken tsumma, sabida yadda tayi cooling, tana ambaton Ya Salaamu
sallim, a cikin ran ta, harda su istighfari, tana neman wanda zasu hada ido ko
karin bayani ne ta samu, amma ina! Mamma Jalan ko kallon ta taki yi, sai
hidima take da mara lafiyan mijin ta. Wata irin nadama da dana sani suka zo
suka lullube Amani, mutumin data raina ta ke wulakantawa, ta cewa shege, ta
cewa bawan gidan su, kai babu irin sunan kaskancin da bata kira Mukhtar da
shi ba shekara da shekaru ashe ya fi ta kyawun nasaba, dan Sarki ne jikan
sarki mai jiran gado, wanda in nasaba zaa bi ba ikon Allah ba, da bata isa
zama matar sa ba.
Ta daga ido tana kallon wannan kasaitattar hamshakiyar masarauta
wadda ko masarautar Katsina bakidaya data sani bata kama kafar ta a
kasaita da shaharar mulki ba.
Kada dai Allah ne yake yi mata talala da laifukan ta, kalaman ta
marasa Tauhidi da girman kan ta? Yanzu wace izza zata kara yiwa Mukhtar
da gorin nasaba? Dama Jalan ta ce mata ta guji ranar dana sani.
Ya Ilahal alaameena na tuba! Na tuba Ya Ubangiji na tuba, daga yau
baki na ya daina fadar abinda ba alkhairi bane a kan kowanne dan adam, na
daina raina kowa, na daina tunain nafi kowa gata!
Ita kadai take furta wadannan kalaman kamar zautatta sabon kamu,
cikin kidima, Mamma da Daddy duk suna jin ta, Sahura na yagar cinyar
Dawisu ta ce ah to ai duniya makaranta ce, ta ishi kowa riga da wando har
da hula. Allah da kan sa yayi hani da girman kai, ya bada misali da Shaidan
da Annabi Adamu Alaihissalamu,
Ubangiji da ya halicci dan adam ya karrama shi akan dukkan halittun
sa, kai dan adam waye da zaka kaskanta dan adam dan uwan ka, don kawai
kana tunanin ka fi shi arziki? Ai ko hausawa sun ce rabon bawa da arziki
mutuwa ce. Baba Idrisu ya ce kwarai da gaske, baka debewa bawa tsammani da
arziki sai ya mutu! Uwa ki ji tsoron Allah ki gyara halayen ki na raina
mutane, kiyi